Showing 153001 words to 155892 words out of 155892 words
fitowa daga wannan wata 11/ 2019 zuwa 1/1 2020 zai iya bayyana
β€ *ABincin Zuciyata* β€
8β£0β£
"Man wai meke faruwane kadameni da k'ira haka, Habib ya tambayi Kabir da yake zaune acikin Mota, bai bashi amsaba sai bud'e motan da Yayi yamasa ishara da ya shigo ba musu ya shige,
Sai da Kabir ya nausa kan titi kafin yace, " Bikon mata ta zaka rakani Gidan Mami, nayi shirun nayi kawaicin naga basu gane hakanba, gwanda infito fili in nimi alfarma, nagaji wlh, Kazan Halin Mami,
Habib yace "ikon Allah to kabari tayi arba'in d'inmana, kai baka da hak'uri wlh,
Kabir yaja dogon tsakin da yasa Habib saurin sake kallonsa,
" Wani shegen arba'in d'in da yak'i zuwa yak'i wucewa, yau kwanansu arba'in da uku, Anma wlh ji nakeyi kaman sunyi shekara, wannan Al'ada baiyiba wlh Sam,
Da matarka kanaji kana gani a maidaka gouro da k'arfi, dubi yanda nazamo maraya fisabilillah,
Habib ya kwashe da Dariya,
"kaidai kawai kafai rakine, anma meye ajikin kwana araba'in? Da sauri Kabir ya dubeshi da mamaki, har kan motan yana niman yak'wace a hanunsa,
" Gaskiya kai Azzalumine, Kabir ya fad'a yana mai da Kansa ga kallon titi, Habib ya sake kwashewa da Dariya, daidai lokacin Yayi Horn a k'ofan gidan Mami, Mai gadi ya bud'emusu suka Shiga, Mami tana tsaye ajikin mota da alama fita zatayi, ganin motan KB ya shigone yasa ta fasa bud'e nata motan tana dakonsa,
KB na baya Habib nagaba suka k'araso wajenta, suka gaisheta cikin giramamawa, ta amsa tana k'are musu kallo, sanin hali yafi Sanin kama, ta gano da magana sukazo,
"Daga ina kuke haka da yammannan? Ta tambaya gami da basarwa,
Habib ya Sosa k'eya ya cakalo Kabir da yake ta muzurai abaya, KB ma ya cakaleshi a lamun wai shi yafara Magana,
Mami tayi murmushi, " Wato kubaku Girma sam, Halinku tun na k'uruciya na nantare daku, kuyi magana ko intafi abuna, sauri nake kunaji,
"Mnm Mami dama.....
" Dama me? Wani shirmen kuma yau kukazomin dashi?
Ta katse Habib da Yayi magana,
"No ba shirme bane Mami dama munzone muji yaushe Khadijah zata koma gidanta?
Mami tayi dariya sosai tana lek'a fuskan KB dayake ta sinnewa abayan Habib,
Tace " Kabir d'ago ka kalleni, ba da bakinka kayi alk'awari ma Khadijah cewa tana arba'in zata je Ganin iyayentaba?
KB ya dubeta asanyaye zaiyi magana, tace "Karkace komi agabana akayi haka, ni nacikamaka alk'awarin jiya na turata ta tafi,
Dum Dum KB yaji maganan kaman anduma masa wani abu, ji Yayi kaman hakan yana nufin ya rabu da Dijahnsa kenan, to wannan karonkuma me Maminsan ta shiryamasa? Kodai har yanzu bata gamsu da Son da yakeyima Khadijah bane,
Ya had'iye wani wahallallen yawu,Ya daure yace " Hakane Mami Allah ya dawo dasu lfy,
Amin tace gami da bud'e motanta ta shihga, har ta fice KB na tsaye a wajen kaman andasashi,
"KB, Habib ya k'ira sunansa,
KB ya sauk'e ajiyan zuciya ya kalleshi,
" jeka Barin shiga ingai da Iya, daganan zan kwanta gobe zamu had'u daga haka ya shige cikin,
Su Dijah suna da sati d'aya Kabir ya sallami su Mami yabi bayansu,
Da yamma lis ya shiga Rugan juma, Yayi pakin a k'ofan makeken gidan da yasa aka Gina ma Baffah, Yayi tabin gidan da kallo, sosai gidan ya masa kyau, Dan rabonsa da gidan tun ana ginin,
Da sallamansa ya shiga, inna tana zaune a falonta tana zargan zogale, Baby Zarah tana kwance a cikin Net d'inta k'asa da ita,
Cikin fara'a ta amsa Sallaman gami da bada izinin shigowa,
A k'asa ya zauna kusa da Zarah, Fuskansa d'auke da murmushi yana kallonta,
"A haba Likita ya kazauna ak'asa,
" Ba komi lnna nanma Yayi, ya fad'a yana bud'e Net d'in Zarah, ya d'aukota ya Rungumeta a k'irjinsa yana dariya, "Mamana ya kike,
Daidai lokacin lnna ta dawo daga k'iro Dijah, ta nufi frich ta kawo masa Ruwa, ta ajiye a gabanshi sannan ta zauna,
Ya gyara zama gami da tan k'washe gwiwa, ya gaidata ta amsa gami da tambayan su Mami,
"Lfy suke sunce agai daku,
" tom muna amsawa,
"Baffah ya fitane?
" Eh yaje jeji,
Kabir yad'an yatsina fuska, "lnna har yanzu Baffah baidaina zuwa jejinnanba?
" To kasan abundan mutum yasaba, sai ahankali,
Ya d'anyi shiru yana kalle2 ta Ina zaiga tauraruwan nashi, shiru bai gantaba, kasa hak'uri Yayi, yace "lnna Khadijah fa?
" Dijah tana chan sashinku, na je dubota najita abayi tana wanka, ka k'arasamana wata k'ila ma yanzu ta fito,
Yasauk'e sanyayan ajiyan zuciya, ya ajiye Zarah ya mik'e, ahankali yake taku yana jinsa kaman agajimare,
D'an Jim Yayi a k'ofan yana sauraron ko zaijiyo motsi, jin shirune yasashi yin kasadan murd'a Handle d'in ya tura kansa,
Zaune take agaban Mirrow tana shafa mai, ta lula Duniyan tunanin da yazamemata jiki, sam bataji shigowansaba,
A hankali yake takowa wajenta, ta d'auko Humra ta zuba a hanunta tana shafe jikinta dashi kenan ta dubi Mirrow, a razane tasake kwalban Humran a k'asa ta mik'e, da zafin nama ya rik'eta,
"Sory my sweet, na tsorataki ko, ya fad'a yana mannata da k'irjinsa, ta k'wace jikinta cikin mamaki ta bishi da kallo, duk da wani irin farin Cikin ganinsa da ya mamayeta, tasani tayi kewan mijinta ba kad'anba,
Ya d'an langab'ar da Kansa, alaman i'am sory!
Juyawa tayi da sauri zata fita, Yayi saurin shan gabanta, yana juya kai idonsa Yayi jazur,
" Haba babyna! Gurinkifa nazo, baki yi farin ciki da ganinabane?
"Ni baruwana da kai me kazoyi garinmu?
Tafad'a kaman zatayi kuma,
Murmushi Yayi sosai da yabayyana hak'oransa a waje, ya k'ara matseta a k'irjinsa,
"Ni kam ina da Ruwa da ke har da tsaki, Barin gaji da gayamiki sirrin zuciyataba khadijah wlh ina sonki son da bansan yanda zan lissafamikiba, pls kibani dama na k'arshe nasan laifina agurinki, ina niman afuwa, ya k'arashe kaman zai durk'usa mata,
Cikin takaici Dijah tafad'a k'irjinsa tana bubbuga k'irjin, " Likita meyasa kakeson kadinga yaudaranane?
Kana wasa da zuciyata da yawa, tasake rushewa da kuka,
A hankali ya cireta a jikinsa ya kalli fuskanta gami da sharemata hawayen da yake tabin fuskanta,
"Bayaudaranki nakeba Khadijah gaskiyan da ke zuciyata nagayamiki wlh ina sonki Khadijah, ya k'arashe yana murza yatsun hanunta,
Ta k'wace Hanunta tana k'ara share hawayenta, ido cikin ido take kallonsa,
"Kamanta likita? Agabana kacema Aunty Nafisa itace Zab'inka, itakad'ai kakeso,
ni bakasona Mami ce ta auramaka ni, shine yanzu Dan ka yaudaren zakace ni kad'ai kakeso?
Wai meyasa maza kukeyin hakane? Live me a long,
Sosai KB yadara, daman yasan laifinsa kenan agunta, tun aranan yasan yadasa abunda zai girba da hanunsa,
Yakama hanunta ya zaunar da ita abakin gado ya zauna a gefe, suna fuskanta juna,
A hankali yace " Khadijah pls ki ajiye wannan magana Nafisa tariga da ta wuce wucewa na har abada,
Tun randa aka harbi Nafisa likitanta ya tabbatar min da Bazata Rayuwaba saboda a zuciya aka harbeta harsashi ya ragargaza zuciyanta,
Dole na tattara duk kulawana na Tara gareta Dan in cikamata burinta kar ta mutu da rad'ad'i mai yawa game dani a zuciyanta,
yarinyan ta jima tana dakon soyayyana Khadijah pls karkiyi kishi da wacce bata Raye, yanzu filin ya rage nidake ne kawai dai dai namu yazo,
"Eh naji anma ai da gaske kana sonta,
KB Yayi dariya yasa yatsunsa yaja lips d'inta da ta turo, yace " Khadijah sark'a mai rikicin gangan,
" Karfa kimanta Nafisa 'yar'uwa tace da muka tashi tare, bansan dad'in d'an'uwa ba sai akanta, ki ajiye wannan batun Dijahna, Soyayyarki ta dabanne, pls kiyarda dani,
Ya fad'a yana rungumanta gami da manna mata kis, tayi saurin k'wacewa ta mik'e tana buga k'afa, "ni dai ban yarda da wannan tsarinba, ya tashi Yayi kanta ta juya da gudu, nan suka shiga kewaya d'aki suna dariya,
π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄
Sati d'aya da zuwan KB rugan ya d'auke matarsa da yarsa suka musu sallama, suka wuce Umrah, anan suka sake sabon cin amarci, basu suka dawoba har sai da sukayi aikin hajji,
Anan Baffah da lnnah suka tarar dasu, ana gama aikin hajji suka wuce London yin wani cus, yayinda lnnah BAFFAH suka koma Nigeria,
basu suka dawoba, sai da Dijah tasake Haihuwan Yaro mai Suna Abubakara Sadiq,
Randa suka dawo Anyi Bidiri ba kad'anba, Walimah Mami ta tanadar musu na komawa sabon Gida, tsohon Gidansu suka bar ma Jebu aminiyar Dijah da Mijanta jauro, Dan tun suna can Kabir yamasa waya kan ya dawo nan da zama,
Yayinda Bintalo ma suka koma sabon Gidansu kusa da Mami,
Haka Rayuwa ta cigaba da lulawa, a ahankali rana yakan zamo dare, dare ya zamo yini, a kullum bawa na kusantan k'abarinsa,
Bayan shekara Goma sha shida,
Jebu da ake k'ira Hajiya Zainab a wannan k'arnin ta had'a gagarumin waliman samun Nasaran da Fatima Kabir da Abubakar Kabir da yaranta Hafasa da Khadijah da yaran Bintalo sukayi na Haddace Alk'ur'ani mai Girma, alokacin suna Ss 2,
Anci ansha sosai a wannan Walimah Da ya d'auki jama'a masu yawa daga gurare daban2, Ciki Har da Rugan Juma,
Yayin da tsoffi lnna da Baffah suka zo wannan Walima, suka sauk'a a gidan da Dijah da Bintalo suka Gina musu,
Washi gari kuwa Mami na gano cikin Shiga ta Alfarma zaune a tsakanin jikokinta, guda bakwai da Dijahn Kabir ta haifamata, zuciyanta cike taf da farin ciki, abunda ta jima tana Burin gani kenan, taga Kabir d'anta tilo, ya haifarmata zuri'a mai yawa,
Hanal ce 'yar gidan Bintalo ta shigo da gudu tana fad'in Mami tsohuwa! Mami tsohuwa!! Kina ina? Cikin Dariya Mami tace yar bad'o gani anan me zaki bani?
"Kwana zan miki yau Abbana yace sai gobe yazo d'aukana,
" Oh ni Fatima Gaba d'aya sai Ku dinga barin gidan iyayenku kuna zuwa kuna cinyemin tuwo,
Zarah ta k'yalk'yale da Dariya,
"Naga dai Mami tuwonma mu mukeyi, ba keba, inbamuzo ba ki matsa da waya kina cewa mun gujeki, in anzo kice ana cinyemiki tuwo,
Gaba d'aya yaran suka kwashe da Dariya, dai 2 lokacin Kabir Yayi Sallama, Gaba d'ayansu sukayi kanshi da Oyoyo, har yaga ji da d'aukan wannan ya jiye ya d'auki wannan ya ajiye,
Ya zube kusa da Mami, " Wash! Mami na kinga yarannan zasu k'ararmin da k'arfi,
"A kaga zaka iyane Kabir, ni inyimana,
Zarah ta matso kusa ta shagwab'e fuskanta, "Dady nifa baka d'agani ba,
Ya zaro ido " haba Mamata in d'agakifa kikace k'atuwa dake?
Gaba d'aya yaran sukasa dariya, ta tashi tayi Kansu duk suka fita da gudu, ta rufamusu baya da d'an sassarfa,
Mami ta kalli KB da guntun dariya a fuskanta, shima dariyan yakeyi, ta muskuta tana kallonsa, "Kabir wai yaya Maganan Baffanka Alhaji Ya'u ne?
" Mami tun Ranan nagayamiki, Abokaina da suke Maiduguri sun cemin suna ganinsa yana tsince2 Abola,
"Eh ai nasani tun bayan da nasa kayi belinshi a gidan yarinnan akacemin Yayi hauka tuburan,
Yazamo maka dole Kasa akamashi a killaceshi a waje d'aya Kabir, bai kamata kabarshi hakaba, hanunka baya rub'ewa ka yanke ka yar, ko yayane dai d'an uwan mahaifinkane, ta d'an nisa,
Illan bin bokaye kenan, kagama kewaye kewayenka, kayi asara da yawa kai ba kaga biyan buk'ataba kai ka nisanta kanka da mahallicinka, daga k'arshe kuma kaga sakamako mai muni a duniya tun kafin kaje k'iyaman, Allah dai yasa mufi k'arfin zuk'atanmu,
Wannan isharane Babba garemu, muyi Hattara mu barma Allah lamarin mu baki d'aya,
" Amin KB yafad'a gami da sauk'e ajiyan zuciya, "insha Allah zansa a kamashi,
" to kadaiyi k'ok'ari jiya munyi Maganan da yayana da Abban Habib, tafad'a tana tashi, shima mik'ewa Yayi,
"Mami barin wuce,
" To kar dai ka yarda kace zaka tafi da yarannan dukansu, ka tafi da Babanka kawai sarkin tsokana, Dan nasan baza ka iya barinsu dukaba,
Dariya kawai Yayi,
yace "to Mami Baban nawane Sarkin tsokana,
" iyi inkaji anakawo k'ara a k'arshe zakaji ance Mahmud da kansa kaman k'wallo,
Kabir ya fice yana Dariya,
A kitchin ya samu Dijah, ta rangad'a kwalliya Cikin Riga da sket na atamfa, ta tsara d'aurin d'an kwaki kai ka rantse a akanta aka Hallicceshi, wani irin asircaccen k'amshine ke fitowa ajikinta,
Ta baya yadinga k'aremata kallo yana sauk'e ajiyan zuciya, batayi auneba taji an rungumeta ta baya ana kissing nata, Ta juyo tana kallonsa Da k'ayataccen Mumushi kwance a fuskanta,
"Ur Welcome Honey na farin cikina, abun alfaharina,
"Nak'i wayon zo mu haye sama a can zan anmsa nawa gaisuwan, ta d'an shagwab'e fuska,
" Mhn mhn fa Honey bangama girkinba kuma kaga yarannanfa zasu shigo kasani,
Ya rik'e hanunta har jikin gas d'in sannan ya kashe ya rik'ota suka fito yana kallonta yana murmushi, girkinma angama, yara kuwa Na mik'asu Gidan Zainab, Yau Ba sauk'i yarinya, yafad'a yana kashemata ido, aikuwa basu suka sauk'oba sai kusan Magriba, yaje ya d'ebo yara, a gidan jebu,
Washi Gari Dijah tana zaune a falo Cikin shigan dakakken shadda Ruwan k'asa Zarah ta shigo da Uniform a jikinta, ta zauna kusa da Dijah, "Wash Ummi wlh nagaji,
" Mhm to Sannu ina k'annankin?
"Sun bi Abban mu ya tafi dasu da yazo d'aukan Mufida,
Dijah ta rik'e Baki " Oh yau kuma wa Aunty Sauda aka kai Maganan, zata tab'a taji,
Ke meyasa baki bisuba?
"Naga za'abarki ke kad'aice Shiyasa nace masa ni Gida zan dawo,
" to kin kyauta jeki cire Uniform kizo kici Abinci anjim Zan fita,
"To Ummi kinyi kyau sosai,
Murmushi kawai Dijah tayi ta mik'e batare da tace komiba, Dan in da sabo ta saba da wannan a gun d'iyan nata,
Sama ta haye kai tsaye wajen DR KB, yana zaune da system a gabansa, ta shigo da Sallamanta,
Ya Amsa gami da d'ago kai, da sauri ya ture System d'in gefe ya bud'e Hanunsa da Murmushi yana mata ishara da ta fad'o,
Ba musu tayi yanda yacen ya Rungumeta suna dariya,
" Ummin Zarah kullum k'ara kyau kikeyi, kullum wutan sonki k'ara ruruwa yakeyi azuciyata, wai meye Sirrinne Baby na anya bakya tsayiwan dare akaina? yafad'a yana Jan Hancinta,
Dijah ta k'ara lafewa ajikinsa, tana shafa kwancaccen sajenshi, tace "To Mijina inbanyi tsayiwan dare akan kakaba akanme zanyi? Kaine farin ciki na na Duniya da Lahira, kullum duk'ufa nakeyi wajen Addu'an Allah ya mallakamin zuciyanka kaman yanda ya mallakamaka nawa Allah yabani ikon yin Biyyaya gareka kaman yanda Allah ya Umurceni inmaka,
Allah yagani bana bin boka ko d'an tsubbu akanka, anma kullum ina rok'on Allah akanka,
Likita ina sonka ba kad'anba sai yanzu nagane abunda ya jefa Aunty Nafisa bin matsubbata akanka, Gaskiya so mungun dafine hak'ik'a mu Mata Allah ya jarrabemu akanku, Soyyayar mace akan mijinta Likita shi yake sa mace inbatayi tawakalliba tafad'a halakan Bin bokayi Dan ganin ta mallaki mijinta ita kad'anta ba tare da wata ta gifta atsakaninsuba,
Dan Allah Likita kaima ka tayani Addu'a kuma kar infad'a Cikin irin wannan mummunan jarabawan nabin wani ba Allah ba, sannan kaima kamin Adalci mijina kar kaga wata wacce tamaka ka juyamin baya, ka tuna nima ka mori k'uruciyata kaji, ta k'arashe maganan Cikin sharan k'ollah,
Gaba d'aya jikin Kabir Yayi sanyi, ya dad'a rungumota jikinsa, Cikin sanyi, yace "Ki kwantar da hankalinki mata ta koda k'ddara zata gifta wata tashiga tsakaninmu insha Allah bazan juyamiki bayaba, Khadijah, kisa aranki ni Kabir nakine na har abada, bana ma jin ajikina zan kuma sauraran wata mace, duk da basan Abunda Allah ya kaddara a rayuwataba,
Ki kwantar da Hankalinki nida ke masoyan junanne na har Abada Khadijah kin zamo sashin Rayuwana banajin zan yi Rayuwa mai inganci Inna juyamiki Baya,
Ya k'arashe yana kallonta da d'an murmushi yana shafa fuskanta Itama Murmushin takeyi tace " Nagode Mijina Allah ya cikamana Burinmu na Alkhairi, Allah yajik'an Aunty Nafisa yasadamu da ita a Aljannah,
"Amin babyn Likita, ya fad'a yana k'ok'arin zaremata Riga Dijah tayi saurin rik'e hanunsa tana juya kai Cikin shagwab'a,
" Pls likita kasanfa Sunan Jamila k'awata zanje wannan karon ta haifi mace, kuma yarinya kyakkyawa ta bugawa a mujalla yau kawai bidiri, Su Aunty Binta da Aunty Sauda da Jebuna sunacan suna jirana a gidan Mami, Dan Allah pls bajimawa zanyiba, zan dawo,
"Kinyi Alk'awari inkindawo zaki kawo kanki basai na nimekiba? Yau d'innan insha Allah zan ajiyemiki Mai Sunan Aunty Nafisankinnan da kike ma yawan Addu'ah, a cikinki, kuma dama kinyi alk'awarin yimata ta kwara,
D'an war tayi da ido tace " eh zanzo insha Allah, nayi alk'awari,
"OK Allah yadawomin dake lafiya, ki d'auki 30 thousands a Cikin drowern da nake ajiyan kud'innan ki kaimata, ta mik'e tana gyara riganta,
" Tom Honey na nagode Allah ya k'ara bud'i mai albarka,
Ta d'auki kud'in tana murmushin son tuno musu k'uruciyansu, da ido yarakata fuskanta d'auke da murmushi, saida takai bakin k'ofa ta rik'e kunkumi ta juyo ta kalleshi ta murmugud'a baki,
"Ank'i adawon Har da wani titsiyeni wait sai nayi alk'awarin kawo kaina, to anfasa alk'awarin,
Kafin ta kai k'arshe Kabir ya zaburo zai kamata ta kwasa aguje ta fita tana k'yatan dariya a falo, π€£
Shima Kabir a kan Sofa ya zube yana shan dariyansa, Sosai ya tuno Draman da suka dinga tafakawa Abaya,
Dijah Dijahn BAFFAH *Ba ki mantuwa ba ki Hak'uri komi akamiki sai kin rama Dijah Qayah ba kisan na gidaba,*
Alhamdulillah anan wannan labari na *Dijah Qqyah* yakawo k'arshe, π€πΏπ€πΏ
Allah nagodemaka da baiwanka a gareni, Allah kasa duk Wanda ya karanta littafinnan ya bud'i bakinsa mai ALBARKA ya nimamin Gafaran kuren Dana tafaka a Cikin wannan labari,
*Ummu Fatima jirgin Dan k'aro ce* ππ€ͺπ’ ππ π¦π΄