Showing 9001 words to 12000 words out of 155892 words

Chapter 4 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

475

kuka kasa kashe shi.


kila yakece da dariya haba dai oga ba kasa kasheshi mukayiba,
bom d'inne yayi saurin tashi da motar tunkafin yashiga,
amma wannnan karonkan namaka Alk'awarin baza'a samu matsalaba,


















*tofah wai shi taya d'an Adam zaiyi mawani bawa abunda mahallicinsa bai masaba kodayake komi yana da sanadi wai ina lbrn Dijah k'ayah ne*

*Kubiyoni UMMU FATIMAπŸ‡³πŸ‡¬πŸ˜˜*
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MAY* *ALLAH HELP OUR COUNTRY NIGERIA*πŸ‡³πŸ‡³πŸ‡¬




*inamik'a ta'aziyana gareki FA'IZA (ANFA) Marubuciyan sweet novel d'innan D'AN FASHI Narasuwan Mahaifnki da ",yar'uwarsa ALLAH Ya gafrtamusu yasa Aljannace makomarsu ALLAH ya tallafi iyalansu dasu kabari ALLAH Yak'aramuku hak'uri da juriyan rashi*πŸ™πŸΌπŸ˜­πŸ˜­



*🌈KANUWA WRITTERS ASSACIATION* ...........πŸ–Š



*page* 6⃣


Cikin k'ank'anin lokaci kila ya iso kai tsaye fallon Alhaji ya'u yawuce.


Zaune yasameshi ya had'a hannayensa biyu ya tallafi hab'ansa da su.


Yana ganinshi yatashi cikin taku d'ad'd'aya yana goye da hannayensa a bayansa ya matsoshi, cikin dakkakiyar murya yafara magana,


"Shekaru masu yawa ina mafrkin na mallake Dukiyar ya Mahmud, tun bayan mutuwansa nake fad'i tashin ganin markina ya tabbata.


Ya furzar da iska, sanan yacigaba, "nabi hanyoyi da dama ciki kuwa harda son Auren fatima don insamu abun da nake buri cikin sauk'i batare da nasalwantar mata da D'anta ba amma fir tak'i Amincewa, Ba hanyar da banbi ta Aura masa "yata Nafisa don mu had'a kai da ita amma sunk'i

"shekaru biyar kenan da baka contract d'in kashe Kabir nanma ya gagareku, inbazaka iyaba kawai kasanar dani innimi wanda zai iya.



Kila yayi wani mahaukacin dariya ya karkace kai yana kallon Alhaji Ya'u da yake masa kallon kashiga taitayinka,

Yace Ranka ya dad'e kashe Kabir ba abu mai sauk'i bane saboda irin tsaron da Mahaifiyarsa tasa masa da sojoji yake fita masu muggan makamai, duk wani motsinsa sunatare, kaga kuwa kasheshi sai anshirya sosai.


Amma ina da shawara aganina kashe Kabir shikad'ai bashi bane mufara da wannan seceurytin sannan Sani, daganan sai akau da Uwar tasa shikenan in anyi haka angama dashi,

Ahankali yake taku har sai da yazauna akan sofa yakalli Kila "wannan ai long prosses ne nikuma da gaggawa nakeson ayita tak'are Don haka jeka kawai zan san abunyi, Matsoshi kila yayi yace "No my Boss kabani nan da one weak zakaje ma fatima ta'aziyan mutuwan Kabir, Dasuri Alhji Ya'u yad'ago kai yakalli kilman dan jin kalman da yafiso yafuto Abkinsa, baiga Alamun wasa afuskan Kila,


Wani nannauyan ajiyan Zuciya ya sauk'e don yasan Kila idan ya aminci zaiyi abu zaiyi Sannan kisa awajen Kila bakomibane ya shek'e wa inda suka fi Kabir ma tsaro.


Hanu Kila ya mik'omasa Alamun inji dumus Dariya yayi sannan yashige d'aki ya fitomasa da kud'i Aleda "kafara da wannan namaka Alk'awarin indai Kabir yabar Duniya zaka mallaki abunda yafi wannan,

"Ranka ya dad'e ahad'a har da uwar tashi kawai "no kabarta kawai ita wannan ba kowa bace kan dukiyan batasan komiba, sannan ina gudun kar asamu matsala hara mutane sugane.


Sosai yaji dad'i aransa har yafara lissafa yanada zai dawo millonian nanda sati d'aya yayi wani dariya ya mik'e yana fad'in barima inje ind'auko Nafisa ta koma makarantanta.



🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
Tun acikin bacci yake jin gumzan kukanta arazane ya tashi yana mutstsuke idonsa Durk'ushe ya ganta a gefen Gadonsa ta kifakai a bakin gadon cikin kad'uwa yace "ke Nafisa lfy? Meyafaru? Waye ya mutu kuma? D'ago kanta tayi ta kalleshi da rinannun idonta sukyai jazur asanyaye yazamo da k'afafunsa k'asa "pls Nafisa gayamin meyafaru? Matsoshi tayi tad'ora kanta akan k'afanshi tana shshshek'a "Dady ne yazo wai lallai sai na koma school agobe wani irin ajiyan azuciya ya sauk'e yasa hanu ya d'ago kanta suka zuba wa juna ido hankacif ya d'ago akan bed side ya mik'amata share hawayen ba musu ta karb'a tashare tas sannan ya nunamata stool tazauna suna fuskanta juna,

"Haba Nafisa yanzu akan wannanne yasaki iri wannan kuka kinsan yanda kika d'agan Hankali kuwa? Karatunne bakiso?

Langab'ar da kanta tayi "har yau bansan matsayina agunkaba duk tsawon zamana da nayi sa agidannan KB sabo da kai nayishi saboda niman soyyayarka, duk da Mami tace min kana sona amman zuciyata tana waswasi KB wlh inasonka inna rasaka bansan yanda zanyiba ta k'arasa da muryan kuka, KB kan k'uramata ido yayi yanzu kam ta daina bashi haushi mamkinta yake ji gami da tausayi wai abunda take fad'a har ranta take fad'a? Shidai yanaji anace so amma bai san yaya ake jinsaba, amma dai ko ma yayane yanaganin amatsayinta na "ya mace bai kamata ta nuna har hakaba, bai yi auneba sai jinta yayi ajikinsa tana wani sabon kuka " pls KB kar kabari sonka ya illatani ahanzarce yacireta ajikinsa "stop it Nafisa is ok kije zan fito zamuyi maganan pls yafad'a gami da mik'ewa sake rik'oshi tayi ganin tana niman tajefashi awani hali yasashi daka mata tsawa "leave me mana Nafisa k'ara rushewa da kuka tayi ta kuma shegewa jikinsa,

Gaba d'aya yarasa yanda zai da ita dai dai lokacin Mami tashigo dama tun da dadyn Nafisa yace mata lallai gobe zata koma tasa kuka tayo part d'in Kabir Hankalin Mami yayo wajen duk datana kyautata zato ma d'annata hankalinta bai kwantaba don tasan sharrin keb'antuwan namiji damace, ganin shirune yasa ta biyo baya, sosai ta girgiza da yanda taga Nafisa manne ajikin Kabir wani irin kallon tuhuma tabishi dashi dukda ya cire Nafisan ajikinsa bata daina masa wannan kallonba Hanun Nafisan kawai takama tafita da ita batare da tace komiba, jikin Kabir bak'aramin sanyi yayiba me Mami zata d'aukeni? Meyasa takemin wannan kallo?

Ganin baida Amsane yasa yashige bayi yayi wanka yayi Allolan zuhur yashige masjid bashi yashigoba sai da akayi la'asar nanma Mamice tamishi waya lallai yazo yaci Abinci,


Bayan sallahn isha ne Mami ta tarasu batare da taji daga garesuba tace Nafisa tashirya gobe ta koma in Allah yasa Kabir mijinta ne tana dawo wa wani hutu za'amusu baiko daga haka ta umurci kowa yawuce makoncinsa
🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴 "Dijah! Dijah!!
"Na'am ta amsa sannan ta nufi inda ake k'iranta, agefe ta tsuguna inda "yar'uwanta take tsugune

"gani Inna, inna ta harareta "wai meyasa kika raina Bintalo ne,

shin ba yar ki bace? Ta turo baki tace "inna fa nariga tad'aukan tulun,

" kinrigata d'auka bayan kowa da nasa, meyasa bazaki d'auki naki ta d'auki nataba?

"inna fa nawan ya tsufane wlh ni banasonsa, wannan nakeso,

cikin sanyi Bintalo tace "inna nabar mata nawan zan dinga d'aukan natan, da tun farko ma tace tafison nawan dana bata

"bazaki bataba inma kin bata kwanannan zatace kisake bata wannand'in, tashi kitafi abunki, in Ruwanne bazata d'ibo tabarshi kawai,
Bintalo ta tashi kenan Baffa yashigo,

ai Dijah tana ganin Baffa tasa ihu da sauri ya k'araso inda take yana kallon inna

" mene ne kuma? Me kukamta saboda Allah ku kunfison kullum yarinyannan tayi ta kuka kumafa kunsan illan kukantannan fa Lamindo na gayamiki,

inna ta tab'e baki sannan tayima Baffa bayanin yanda akayi Baffa yace
" assha indai akan tulu ne karkidamu mamata maza jeki wajen Barde kizab'i wanda kikeso inna fito zanbashi kud'in ai bai rufe bakinsa ba tadaka tsalle ta tashi ta je dai dai fuskan Bintalo ta zaro harcenta da k'arfi tanamata woooo woooo wululu ta fice daga inna har Baffa sai da sukayi Dariya, Baffa yadafa kafad'an Bintalo yace "nasan kina hak'uri da Dijah kiK'ara kinji ummata? Murmushi Bintalo tayi ta gyad'a kai ta da'uki tulun ta tafita


Su hud'u suka jero Bintalo da ma'u sai Dijah da Aminiyanta jebu k'anwar ma'u, kowacce d'auke da tulun Ruwanta, haka suke ko dayaushe inzasuje rafi d'ibo Ruwa tare suke zuwa sai dai randa Dijah ta k'wayance, shine zasu tafi daban daban.

Dijah ta lakato jebu sukayi baya alamun zasuyi magana "ke bakiga nayi sabon tulu bane? Nan tabata lbrn yanda akayi Baffa yasayamata suka k'yalk'yake da dariya har su Bintalo suka juyo suka kallesu jebu tace "ai kafin in iso rafi lado ya tareni ya fad'amin da sauri Dijah ta juyo ta zaro ido takalleta lado? Yaushe yaganni? "Yace min yaganki lokacin da kikaje wajen Barde saya,

Jebu batayi auneba sai ganin Dijah tayi ta sauk'e tulun tazauna akai tasa hanunta tarufe bakinta, tana son tuno mema tayi lokacin da taje wajen Barde, jebu ta kwashe da dariya ke dalla kitashi mutafi, kunya Dijah taji kamar k'asa yatsage tashiga shikenan tabari saurayinta yaganta tana gudu tsaki taja tad'auki Ruwanta taja bakin gyalanta da tasha d'amara dashi tarufe fuskanta, jebu kuwa sai dariya takeyi Dijah tace "yasin yau bazan je Dandaliba, "kai Dijah matsalata dake kenan abu kad'an ki k'i zuwa dandali Alk'ur'an innaje dandali bakinan sam bani jin dad'i "ai sai kiyi tundanace bazanjeba kema kin san bazanjeba, "to shikenan muje gidan jummala Amarya,
"cab wlh bazanjeba jummala ita da Mijinta "yan iskane, ba abunda sukeyi agidan inba iskanciba wlh da k'yar imba asasu awutaba, ni wlh natsani d'an iska arayuwa, jebu tace "ke ancefa haka akeyi in anyi auren, wani dogon tsaki Dijah taja "wlh k'arya ne, da haka suka iso kowa tashige gidansu Lokacin da Dijah ta shigo gida tasamu Bintalo tayi wanka har tana kwalliya, "Bintalo harkinyi wankane?
"Iyi bakun tsaya Hira ahanyaba? Harnazo nayi wankana, zakije dandaline? "Bansaninba tafad'a tana murgud'a baki ko kyauma bakiyiba Aljana akwaba, murmushi kawai Bintalo tayi ta tashi tasa kaya ba irin tsokanan ta da Dijah batayiba amma tak'i kulata, dan Bintalo akwaita da Hak'uri duk abun da Dijah zata mata bata tankawa sai dai intak'urota nan kuma intarik'eta jibganta takeyi son ranta, da Baffa kuma yaji zai hauta da fad'a duk dayasan niman tsokana irin na Dijah da hak'urin da Bintalo takeyi da ita,

Haka ta k'araci murgud'e murgud'en bakinta tafita batare da Bintalo ta kulataba, ak'ofan d'aki taci karo da inna da tafito daga wanka, "inna kinga kirabani da Bintalo kallonta kawai inna takeyi batare da tacemata komiba ta wuce tana d'an k'unk'uni wlh wataran sai nafasa ma yarinya Baki inna ta girgiza kai tana d'an murmushin gefen baki ahankali tace Allah ya shiryar dake Dijah am,


Muje zuwa
~ummu fatima~ πŸ‡³πŸ‡¬
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡³πŸ‡¬

*ISLAM MY RELIGION* πŸ˜˜πŸ•‹

*jinjina gareku group d'in DAMATA (3) BATUL'S NOVEL* πŸ€πŸ»πŸ‘πŸ» inajin dad'in zama da ku sosai Allah yabar k'auna😍😘



*sis Sameena Aliyu* 😍😘
*sis Batul Adam jattako* πŸ˜πŸ™‡πŸΌβ€β™€

_Inayinku sosai don haka nabaku kyautan wannan page baki dayansa_
*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 7⃣



Tunda ta fito daga wanka tayi sallahn azarhar, tazauna da madubi ahanunta tanata d'ige 2 duk ta fente fuskanta da janbaki da kwalli, sai kallon fuskanta takeyi a madubi ta zaro ido ta murgud'a baki anjima kuma ta kece da dariya abin da takeyi kenan har akayi k'iran la'asar tana zaune agun tana wannan shiririta,

Ahaka jebu tashigo ta sameta turus tayi tana kallon Aminiyar tata, don kuwa tsawon zamanta da Dijah bata tab'a ganin makamancin hakan afuskantaba idanma taga masuyi ta dinga tsokanansu kenan tana dariya, agefenta ta zauna tana kallonta "Dijah yau lfy kuwa?


Cigaba tayi da zanen fuskanta abunta ko kallon inda jebun take batayiba "irin wannan kwalliyan Dijah ko zamuje Dandalinne?

wlh kar kiga yanda ya cika da jama'a lado ma yanacan yasha kwalliya sai nimanki yakeyi, kusan sati ukufa kenan baki lek'a dandaliba, Don Allah kizo mutafi karkato da madubin Dijah tayi dai 2 yanda suke kallon fuskan juna, Harara Dijah ta galla mata sannan ta jinjina kai alamun ki kiyayeni, sannan tacigaba da kwalliyanta,


jebu ta riga datasan halin Dijah tunda batayi niyan maganaba tasan bazatayinba,

haka tasan Dijah bata cika zuwa dandaliba dan acewanta duk randa taje sai kanta yayi mata ciwo,


Saidai yanda lado ya matsamata akan maganan Dijah ne yasa tace bari tagwada sa'anta tagani,

gashi tazo tasamu Dijah akan tsini tunda ko arzik'in magana bata samuba,

Sada ta gama don kanta ta shiga niman kayan da zata sa wani riga da zani tad'uko pink mai hoton taurari blue ajikinsu dariya tayi lokacin da take ware kayan don ranta yanason pink colour,

Har tagama shirinta tayi sallah jebu tana zaune tana jiranta, tare suka fito sukashiga d'akin inna, sosai inna takebinta da kallo, sannan tayi magana Dijare am yau kece da wannan kwalliyan haka? Ina zuwa? Dariya tayi tace "inna zanje gaida goggoji ne "to kice ina gaisheta,

Suna fita Dijah tarik'o hanun jebu "ke kan tudu zanje can waje larito don jiya amakaranta ancemin tayi gulmana, cike da tsoro jebu takalleta don tasan fad'an Dijah ba abu mai sauk'i bane, intafar batajin zata daina, wani hikimane yazo ma jebu, "wai me tace miki? Wai cewa tayi ni masifaffiyace,

"kinsan Allah k'arya akamata don kawai anga kuna shirine shiyasa za'ahad'aku fad'a cewa tayi tanasonki da k'awa inbaki yardaba kuma zo muje dandali ki tambayeta tanacan,

Dijah ta tab'e baki nifa nacemiki bazan je Dandaliba zo kawai muje mu gaida goggoji,



Acan dandali kuwa Lado yayi jiran tauraruwan tasa har yagaji, yana tsaye yana kallon Abokansa kowa da budurwarsa, ga "yan mata dayawa wa inda suka fi Dijah girma suna sonsa amma shi Dijah kawai yakeso, dik da har yanzu bai gane inda ta dosaba, shin tana sonsa koba tasonsa, bata yarda suyi hira ko yaje k'ofar gidansu gudunsa takeyi,

Duk dahaka ya kasa rabuwa da ita don Dijah one in townce kykkyawace na bugawa amujalla duk rugan juma ba "yar data takaita kyau, tana da fasali mai kyau sosai, samaruka da yawa sunyi yunk'urin niman Dija saidai basu samun fuska ladone kawai daya nuna yana sonta bata balbaleshi da masifa,


Lado d'an gidan Hard'on garine Hard'o afualatanci yana nufin sarki, lado yayi zaman Birni dan haka kaf Rugansu ba saurayin da yakishi gayu dawayewa, shiyasama Dijah takesonsa don tanason d'angaye arayuwanta, saidai shiriritanta, yahana lado ya gane tana sonsa, Dondai Dijah ba dai shiriritaba,


Washi gari da dafe Dijah tunda ta idar da sallah take takiciniyar ayyukan Gidansu kamar yadda tasabatayi sharanta fes ta ttara wanke wanke tayi tana kife kwanuka Baffa yashigo da keke da jarkan ruwa akai da gudu tanufoshi tarik'e masa keken tana ta jero masa sannu sai k'ok'arin sauk'e jarkan takeyi Baffa yace "a'a mamata barshi bazaki iyaba, "Allah Baffa zan iya "to barin kama miki, tare suka kama suka juye aranda, ya juya yana kallonta da wutsiyan ido, yana d'aure jarkan ajikin keken tazo tarik'e kamar zatayi kuka

Baffa dan Allah karka koma zamu je mud'ibo ni da Bintalo,

murmushi yayi daman yasan za'ayi haka, sam indai Dijah tana gida bata barin Baffa yayi komi ko itace saitace zasuje suyi shikuma tausaya musu yakeyi amtsayinsu na "ya"ya mata baya son suke wannan wahala,

shiyasa tunkafin tatashi daga barci sai yaje yadebi ruwa yayo iatace, inta tashi tayi tamitan batason yake wahala sunanan.

Cikin sigan Rarrashi ya dafa kafad'anta karkidamu mamata sawu d'aya zank'aro kinga fa zaku tafi makaranta, inkince sai kun d'ebone zakuyi latti amuku bulala, a'a Baffa kabarshi wlh bazu d'ebo ganin tan shirin yin kukane yasashi ajiye jarkan, dai dai lokacin Bintalo tafito donyi musu abun kari, ita kuma Dijah ta d'auki tulu ta tafi d'ibo Ruwan,

Tafe suke cikin Unifoam Riga da wando da hijabi Blue du hud'u kamar yanda suka saba ko ina zasuje Bintalo da ma'u dune agaba Dijah da jebu suna baya hiransu sukeyi harsu ka iso gida su jebune da yarta ma'u sukafara shiga gida sai su Dijah tunda tacire unifom take kwance, inna ta shigo tasameta "Dijah kifita kuci Abinci tund'azu Bintalo take k'iranki kinyi burus, ta yatsina fuska "inna mekika dafa? "Shiinkafa da miya, "nidai nak'oshi tafad'a tana turo baki "mhmm dama nasan za'arina inna tafad'a tana fita,


Sai da tagama kwanciyanta tafito anan tasamu Bintalo tana zaune gefenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login