Showing 147001 words to 150000 words out of 155892 words
Gaskiya yaya Kabir na dawo daga rakiyan bokaye da 'yan tsubbu, wlh ba komi tare dasu sai b'ata da tab'ewa, koda kasamu biyan buk'ata na lokaci kad'anne, watarana zai waste, gashi ka rabu da Allah da manzonsa, Yaya Kabir Dan Allah kayafemin, ba laifinaba ne mahaifiyata ce tasani awannan hanyan, nasan duk kun sani, Dan Allah kunimamana gafaran mahaliccinmu, ni da Mahaifana, Sannan banjin zafin harbinnan sosai, yau rana ta farko danaga tausayi da kulawata a fuskanka masoyina, ta kai hanu ta shafi fuskansa, ta ci gaba, Bani na gayyatosu suzoba, Nima k'irana Abbana Yayi awaya yace nasan duk yanda zanyi in shigo dasu kar securities sugansu, ya basu wani sak'one su kawomin, Ko dana tambayeshi Me zasu kawomin, sai yace "wai maganin da zan mallake Kabir, ya daina kallon duk wata mace amatsayin Mace in a niba, sosai naji dad'in hakan, Dan bani da burin da ya wuce in mallaki Masoyina Kabir,
Nayi duk abunda zanyi na kawar da security a wajen, na zauna ina jiran isowansu, koda suka zo NA tambayesu ina sak'o sai sukacemin wai babu wancan sai dai sun zomin da Wanda yafi wancand'in shine kashe Dijah, saga farko nak'i NA tubure musu, kancewa ban yarda da wannan tsarinba, nan suka zaremin ido, har da rantsuwan wlh bazasu bar gidannanba sai sunyi abunda ya kawosu, inna matsama KB zasu kashe, jin hakane yasa NA yarda da k'udirinsu, Abba da Mama sun cuci Rayuwata, ta k'arashe maganan cikin matsanancin kuka taja dogon numfashi alamun zuciyarta ta cunkushe
Daga haka Nafisa bata kuma cewa komiba, A tsorace Dijah ta jijjigata tana k'iran Sunanta,
" Suma tayi Kabir ya fad'a araunane dai2 lokacin Habib ya shigo da 'yansanda guda biyu,
Ba b'ata lokaci aka garzaya Asibiti da ita.
Wani irin ihu Alhaji ya'u Yayi lokacin da labarin Harbin da akayi ma 'yarsa ya iskeshi, wurgi Yayi da wayan ya fita aguje kaman mahaukaci, bai tsaya ko inaba sai Asibiti a lokacin likitoti sun Rufu a kanta ancire harsasai ajikinta, Dan haka bai samu daman ganintaba, kaiwa da ka wowa Yayi tayi a bakin ward ne, daga bisani ya nufi d'akin maman Nafisan, dai2 lokacin ta fito daga bayi tana dogara sandanta, Rassss taji gabanta yayenke lokacin da sukayi ido hud'u da Mijintan, na irin tashin hankalin da ta gani afuskanta,
"to ko takardana ya kawomin? Ta fad'a aranta.
" Nagaji da wannan masifa daga wannan sai wannan, ya akayi kikabar Nafisa ta kamu da Son matsiyacin yaronnan haka? Da har zata iya taran mutuwa Dan ya rayu? Na tura Kila su kasheshi, ta tari Harbin, 'yata k'waya d'aya da nake gani inji Sanyi, wlh inta mutu sai nakashe duk zuri'anku, Ke kikasata son Kabir, duk Abunda ya samamin 'ya wlh sai na kasheki, kai wlh har Fatima uwar Kabir sai na kasheta
"Wayyo Allahna nashiga Ukuna, Nafisan nawa Alhaji 'yata k'waya d'ayan ita kake k'ira ma Mutuwa? Wlh Nafisa bazata mutu yanzuba, sai dai Kaine zaka mutu, ta kuma rushewa da kuka,
Sallama Mami ta kuma musu, Ganin har yanzu basu Sanda ita bane yasa ta shigowa, rai ab'ace take binsu da kallo, su d'inma irin kallon suke mata,
D'an taku tayi ta k'araso gaban Alhaji ya'u tanabinsa da k'azancacen kallo, " Waya gayamaka cewa komi zai tafi maka bisa yanda ka tsarishi Ya'u?
Allah ba azzalumin sarkibane, Yakaga sakamako ya kai Azzalumi ya'u? Butulu mai butulci ma ubangijinsa, ka butulce ma ni'iman da Rabbi ya maka, Azzalumi mai mummunan zuciya, Butulu, Kaje kashe d'an wani ka kashe taka 'yar,
Sannan kazo kana kumfan baki, Zaka kasheni, To sai me Ya'u Dan ka kasheni, yau ina Mahaifiyarka? Ina mahaifinka? Ina d'a'uwanka dakayi ta farautan Rayuwansa? Kadinga turamasa 'yan fashi kala2 duk basunan kai ka shesu ko su suka kashe Kansu?
Mutumin da ya maka gata yamaka abun alkhairi shi kayiwa Mummunan sakamako, Anma har yau bakasamu yanda ka soba a haka zaka k'are kai da ganin haske a rayuwarka har abada, Fatima tana nan Kabir yana nan Dukiyarsa kuwa sai dad'a bunk'asa takeyi fiye da yanda kake zato, in har ka isa ka dakatar dashi, inka isa ka yi ma kanka makamancinsa, Jahilai wa inda basu San Allah ba,
Wato Ku kunsan zafin 'Yar da kuka Haifa, shi kuma wannan ba a San zafinsaba, Tunda Baku ku ka haifeshiba, damuwanku kawai ya mutu kuci dukiyarsa Ku da 'yarku,
To wlh yanzu ba dabane Ya'u namaka kawaici Anma na lura kai ba irin Wanda ake ma hakanbane,
To daga yau ba kai ba d'ana, Na cire Hanunka gaba d'aya akan Kabir da dukiyansa, zan d'auki mataki sosai akanka duk randa kasake ka kuskura ka shigamin sabgan d'ah, zan nunamaka dama kawai kawaici nakemaka ba wai bana sonsa bane, Ina sane da duk tuggun da kake tuggawa tun mahaifinsa yana da rai, kasani daga yau ko kare mai haushi ne ya shiga gidan Kabir, to kai ka turashi kuma zan d'auki mataki.
Daga Haka ta juya security suka taka mata baya tana taku d'ad'aya, (kai Ran mata yab'aci π)
Kuyi hak'uri da wannan
Banyu editing ba kuyi hak'uri
Ummu Fatima ceππΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π¦π¦
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*k'awa Momyn Sadiq*
*Hajiya Zuwaira*
Wannan nakune kubama wanda kuka dama inkunga dama Ku bama su *Mmn Beauty* *su kemxe* da sauran yan group πππ
7β£7β£
Tsaye ta samu Kabir abakin ward d'in da Nafisan take, ya dafe hanunsa a jikin bango ya d'ora goshinsa akan Hanun, kallo d'aya zakamasa ka gano tsantsan damuwa da tashin hankali da yake ciki, duk ya koma kalan tausayi,
Sosai Hankalin Maminma ya tashi ganin tilon d'annata awannan yanayi, "Kabir! Ta k'ira sunansa a sanyaye, Anma ina ya lula cikin Duniyan tunani baimasan tanayiba,
Ta k'ara taku d'aya ta dafa kafad'ansa, ta sake k'iran Sunansa, ya d'ago a hankali ya kalleta da idonsa da sukayi jazur,
" Kabir kazamo mai tawakkali, kayi hak'uri insha Allah zatayi lfy, ka daina d'agama kanka hankali haka, duk abunda ya sami bawa da sanin Ubangijinsa, kaji Son!
A hankali ya sauk'e ajiyan Zuciya, Mami Rayuwannan ya k'ara bani tsoro, kiga yanda Nafisa ta koma a d'an k'ank'anin lokaci, Numfashinta da k'yar take fita, Duniya a in tsoro,
Mami ta d'an yi yak'e gami da furza iska mai zafi, tace " is OK ka kwantar da hankalinka, shiyasa kullum nake maka nasihan kan Rayuwa kabita a sannu, Canzawa take lokaci bayan lokaci, in yau kai wane ne gobe kana iya zama ba waneba, abun hawa da sauk'ane, yakamata akullum ka dinga tuna wannan jarabawa takan iya zuwanma ka ta kowani irin hali, shiyasa ake son ka shuka khairan, ka girbi khairan, Allah yasa mudace, ta k'arasa araunane, muje muganta, sunce sun fito da ita, Suna juyawa Yayi ido hud'u da Dijah, ta jingina bayanta da bango hanunta hard'e a k'irjinta tana kallonsu, idonta taf k'ollah, maganganun Mami sun shigeta, ya d'an diririce, Mami ta wuce gaba, da sauri Dijah ta rufamata baya,
Ikon Allah Rayuwa kenan Nafisa 'Yar gayu mai ji da isa, wacce Rayuwan Duniya kad'ai tasa agaba bata ko tuna mutuwa, bare kwanciyan k'abari, bare Tsayuwan k'iyama, haye sirad'i, da Hisabi, yau itace kwance, kamar gawa, idonta arufe kirif yake, sai alaman da zaka gani bakinta na d'an motsi, istigfari kawai ta dawo yi, da tasbihi,
Tagama tsorata ta sakankance tafiyace tazomata, Doguwar tafiya, taa zauna ta lissafa taga bata da guzurin wannan tafiya, bata aje komiba a wannan b'angare, tayi wasa sosai da damanta, to dai dai da Sallah Nafisa bata cikayinsa akan lokaciba, Bare ta d'an d'ora walha koda raka'a biyune, gashi abune mai wahala tayi magana bata d'an surka d'an k'arya acikiba koda kad'anne, Wanda koda hakan akan barta tasani bazata kwashe ta dad'i agaban mai dukaba, bare uwa uba bin bokaye da matsubbatan da suke zama a zaure suna k'iran Kansu da malamai, lallai tasan cewa Rayuwa da mutuwan duka sau d'aya akeyi, idan har ka kuskura ka mutu baka gyara tsakaninka da mai dukaba, kagama yawo, Dan baza'adawo dakai dan ka gyaraba, haka zalika tasani Allah baya maka uzurin jahilci, matik'ar baka da ilimi ka tashi kanima kawai shine mafita a gareka,
Sannan tasani cewa mutuwa bata da Alama ko lokaci, ma'ana idan ta kusantokama bazaka luraba, har sai ta damk'eka, wad'anannan sune dalilan da sukasa Nafisa cikin tashin hankali Da yasa takoma ga Ubangijinta, Dan tasan shid'in mahak'urcine, mai Rahma, mai gafara ga dukkan bawan da yanimi gafara gareshi, tasan cewa tana da sauran lokacin da idan Allah ya taimaketa zatayi tuban da ake k'ira taubatun nasuhah, Dan sai yanzune take tuna irin kura kuran da ta tafka,
Mami ta jawo kujera ta mik'ama Dijah ta zauna, sannan itama ta zauna "Nafisa ya jikin? Mamin ta Tambaya cikin matsanancin tausayinta, Ahankali ta bud'e ido ta Amsa da " Alhadulillah, sai kuma ta fasje da kuka " Mami Dan Allah kiyafemin duk abunda na miki, ki rok'amin yaya Kabir da Matarsa gafara, ba Dan halinaba, kinji Mami ta k'arashe cikin kuka mai cin rai,
Mami tasa hanu ta share hawayen da ya gangaromata, sannan ta sharema Nafisanma nata,
"Baki min komiba Nafisa, inma kin min Na yafemiki, fatana Allah yabaki, lfy,
" Allah yasa in cika da imani zakice Mami, Allah kuwa mutuwa zanyi,
"Bazaki mutuba Aunty Nafisa, zaki samu lfy insha Allah, Dijah ta fad'a tana sharan k'olla, Nafisa ta kalketa tayi Murmushin k'arfin Hali, daidai lokacin Mmn Nafisa ta shigo,
Cikin tashin Hankali tazo kusan gadon tana Kuka " Nafisa haka ki ka dawo?
Sai da akasan yanda akayi aka kwantarmin dake ko? To wlh sai na d'auki mataki, yau d'innan basai gone ba zan d'auki fansa, Na tafi Niger,
Ta juya tana dogara Sandanta, cikin dishashshiyar murya, Nafisa ta fara magiya, "Mama Dan Allah kidawo, kar kije, kizo nimi gafaran abunda kikayi abaya ba sai mun k'ara waniba,
" Kar kidamu Nafisa na rantse inzanyi yawo tsirara sai na karb'amiki 'yanci, Nafisa tasa Hanunta aka ta rushe da kuka, mai zafi,
*Ummu Fatima CE* ππΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π¦π¦
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*Ummu Fauzan*
*Nisher jay* ba India π
Yaba kyauta tukwici na Baku wannan page kyauta, Sai yanda kukayi dashi,
7β£8β£
Shiru d'akin Yayi ba mai cewa komi, inbanda sautin kukan Nafisa da yake tashi, kimanin minti sha biyar suna a haka,
Kabir ya tako a hankali har zuwa gabanta, yasa yatsunsa biyu akan lips d'in ta, "shiittt ya isa haka, yakamata ki cire ire iren wa innan damuwan aranki, kiji da abunda yake gabanki pls, ya fad'a yana jijjiga kansa, idonsa na kanta, itanma shi take kallo,
Da yatsun ya d'auke K'ollahn da yake kan fuskanta, yace " kinsha maganinki? Ta d'an girgiza kai, yace "kingani, anma kinzo kina sa wani Abu aranki, tashi ki sha,
Da kansa ya d'agata ya zaunar da ita akan gadon ya jinginata da pillow yana kallon k'irjinta da aka nannd'e da Bandeji, ya d'auko maganin ya b'are yabata tasha, kallonsa takeyi bako k'iftawa, ya d'an huremata ido yasakar mata murmushi,
Yana juyowa suka had'a ido da Dijah tayi saurin Sadda kanta k'asa, ta mik'e zata fita Kabir yace " ina zakije? Inaji Mami tace kijirata tana zuwa,
"Zan jirata a waje ta fad'a muryanta na sark'ewa ta fice da Sauri, gaba d'aya Sai yaji jikinsa Yayi sanyi, Sam baiyi tunanin hakan zai faruba ganin Halin da Nafisan take ci,
Nafisan ce ta dawo dashi duniyan daya Lula ta hanyan kama hanunsa, " Ya Kabir kaje gareta ka bata hak'uri kacemata yanzu Nafisa kaman bak'uwa take atsakaninku, nan bada jimawaba zata Baku guri,
Dan Allah ka rarrasheta, kaga ba ita kad'ai bace, ta k'arasa tana k'ok'arin Danne kukan da yake Son k'wacemata,
"Nafisa wai bana hanaki irin wannan maganganunba? Ko kinason indaina zuwa inda kikene?
Ta girgiza kanta tana to she bakinta da Hanunta,
" To kidaina inkinnason mu shirya, yau ake Harbin mutum ya Rayu? Wani akan masa Harbi yafi goma inbaizo da ajaliba sai kiga ya Rayu,
"Haka ne Miji na nagode, Dan Allah kaje wajenta, mik'ewa kawai Yayi ya fita, a Mota ya hango Dijah ta had'a kai Da gwiwa tana zaune tana jiran Mami da suke tattaunawa da Likitan Nafisa, Dan ita so take a fitar da ita waje,
Yajima yana kallon Dijah aranshi yana tunanin abunda ke damunta, ciwon Nafisanne? Ko wani abunne?
Ya bud'e Motan ya shiga ya zauna, dai dai lokacin ta d'ago suka had'a ido, tayi mugun d'aure fuska, ko mi ta tuna? sai kuma ta d'an sassautar da Fuskan, Murmushi ya sakarmata, ta d'an kau da fuskanta gefe, Dan son gaskata zarginsa sai yakamo hanunta, " Honey na ya naganki a motan Mami bara kibari mu koma tareba?
"Ai tare mukazo a motan kaga kuwa dole tare zamu koma,
" Kijirani yanzu zanje inga wani Likitane minti 2 kacal zan dawo mutafi gidanmu kinji?
"Mhm katafi kuma? Kai da kake jinya, ta fad'a tana k'wace Hanunta a cikin nashi, ya k'uramata ido a ranshi yana mamki Wato su mata dama haka suke kishinsu? Duk damuwan da tashiga na halin da Nafisan take ciki bai hanata kishinba, haka itama Nafisan ya lura Dannewa kawai takeyi,
Ahakane maza suke mata hud'u to ya sukeyi dasu? Yayi tambayan a fili ba tare da yasan ya fitoba,
Dijah tayi saurin d'agowa, sai kuma taji d'an kunya ya kamata, dai dai lokacin Mami ta k'araso, kallo d'aya ta musu ta Glass ta bud'e ta zauna, ta d'an juyo ta kalli Kabir, yadai son?
Ya d'an Sosa k'eya " Mami kud'an jirani zanga Dr ilya ne minti biyu zan dawo mutafi, sake kallonsa tayi sannan ta kalli Dijah, ta maida kanta tana kallon sitiyari, Gaskiya nikam bazan iya jiranka har kaga wani likita kadawoba, sauri nake, saidai in matarka zata jiraka,
Khadija fita kijirashi inyagama Ku koma gidanku, dama gidanmu ba d'ayaba,
Dijah ta turo Baki kaman zatayi kuka, "Mami nima barin jirashiba wlh mutafi kawai,
Kabir ya gyara zama gami da gyara rufe murfin motan yace, " OK mutafi,
Dijah ta kalli Mami, "To inmuka tafi dashi tawagansafa? Mototi shidafa sukazo dashi, ta fad'a tana nuna jerin mototin da suke Jere awajen,
Mami ta juyo ta kalleshi, da idonta ta maimaita Tambayan da Dijahn tayi,
ya d'an Harari Dijah sannan ya kalli Mamin, " Su Sani zasu dawo dasu Mami,
"A'a ban yarda da wannan tsarinba, fita ka koma da ayarinka, ta fad'a tana mai da kanta,
Kabir ya muskuto kusa da Dijah ya tura Hanunsa cikin Riganta da fuska ya mata Alama da wai ta bashi Babynsa kafin ta tafi,
ta dage da k'arfinta, ta cire Hanunsa ta ture,
dukansu suka kalli Inda Mami take,
hankalinta na waje, da hanu ya yafatota yamata alama da I need u, l miss u,
da ido da hanunta tamishi alama da zance kenan, ya kuma jawota jikinsa ta k'wace tamasa kallon kafa fita hanyana, da idonsa yamata kallon zankamaki,
itama tamasa martanin ka kamad'in, yanuna k'irjinsa yana jinjina kai alaman Dani kike? Ta jinjia kai gami da murgud'amasa baki, Yayi caraf ya damk'o lips d'inta da yatsunsa,
Ta rik'e Hanunsa gami da sakin k'aran da yasa Mami saurin juyowa garesu,
Da sauri ya k'wace Hanunsa yana muzurai,
Mami tace " lfy kuwa Kabir?
Mhmm wato dai tun sanin Dana muku halinku baya canzawa ko, to fita kabani wuri,
Ya bud'e murfin motan yafita yana Murmushi, Ya rufe ya juyo, dai dai lokacin Dijah ta zuge Glass d'in tana kallonsa tana dariya k'asa k'asa, yamata kallon zamu had'e anjima ki kuka da kanki, ta rik'e kunnenta tana masa gwalo,
Har Mami ta tada Motan ya d'an bubbuga alaman ta tsaya, ta tsaya gami da zuge Glass ta lek'o, "ya akayi kuma? ya kwab'e fuska, " Mami wlh gwalo takemin, Dijah tayi saurin gimtse Dariyanta,
"A'ah Mami sharri yamin, Murmushi kawai Mami tayi gami da girgiza kai tayi key ta tafara Tafiya,
Yana tsaye a wajen yana kallon iyashegen da Dijah take masa da Hanu da fusaka,
Murmushi kawai yake yana jinjina kai har sukafice a Asibitin, ya hard'e Hanunsa a k'irji ya juya yana cigaba da Murmushi, Sosai yake jinta acikin Zuciyarsa,
Itama murmushin take tayi tanajin shauk'in mijinnata, Ganin Mami ta d'auki