Showing 111001 words to 114000 words out of 155892 words

Chapter 38 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

440

a tsanake,


Yad'an harareta "wato ita tana kwance hankalinta akwance shi kuma yana can yakasa Bacci, hayewa gadon yayi ahankali ya zare pillows d'in ya maye gurbinsu ya jawota jikinsa sosai na shirin ko karta kwana dan yasan tana iya masa ihu a darennan,

Wani irin ajiyan zuciya ya sauke yana k'ara mannata da jikinsa,

Acikin Baccin itama tasaki ajiyan zuciya gami da k'ara shigewa jikinsa tana rungumansa, Romacing nata yashiga yi sosai,


Lokacin da zance yafar canzawane ta farka jin tana tureshi yasashi saurin kunna wuta yana kallonta tana murk'ushe ido tana kallonsa ta tashi ta zauna ta turo baki,

"to meyakawoka d'akina? Nifa bana so,


Murya akasalance yace "Sory Khadijah wai me namikine kikayi fushi dani haka mai tsawo? Rabon danaganki fa namanta,

"Nidai kafitamin ko nak'ira Mami, yad'an murmsa yace "kiyi hak'uri dan Allah kar ki k'irata ki taimakeni yafad'a amarairaice kaman zaiyi kuka yana k'ara ahiga jikinta, duk yanda Dijah ta k'udura a ranta zata masa duk randa ya shigomata kasawa tayi sakamakon hakama sai taji tausayinsa yakama yanda taga duk jikinsa yana b'ari ta langab'ar da kai "to meyasa kake zagina agaban matarka?

"Banzagekiba Khadijah kinsan koni da ke bana zaginki bare agaban wani, "Kaxagenimana kace min stupid mara hankali kuma ka shanyani kaje kuna hira,


Yad'ago idonsa da suka rine dan tsaban buk'ata a sanyaye yace "Bazan sakeba Khadijah ki yarda dani, ya fad'a yana jawota jikinsa,

(mhhmmm Na mijiii!!) πŸ€”πŸ€ͺ


Yau take juma'a Ranan farin ciki gasu Khadijah dan a yaune suka kammala jarabawansu suna ta d'aukan photo cike da Alhinin Rabuwa da juna,

Jamila ta dafa kafad'an Khadijah tana nuna mata motan Kb da yajima atsaye awajen tace "Khadijah kije ku tafi tuntuni fa yake jiranki wlh yanzu kam ya gaji,

Murmushi Dijah tayi suka cigaba da d'aukan pic d'insu sai da suakyi mai isansu sukayi sallama da juna ta iso gareshi ta bud'e Motan ta shiga tana rufewa yayi caraf yakamota ya kwantar kan cinyansa, ya mannabakinsa akan nata yafara tsotsa kaman mayuwanci abunda yabashi mamaki shine yanda yaji tana tayashi,


Har sai da suka fara fita hayyacinsu ya saketa gami da d'agata tayi surin kifa kanta acinyanta ta rufe idonta, tsaban kunyan da yakamata, murmushi yayi yana shafa bayanta ya rank'wafo dai2 kunnenta "Kai Khadijah baki da dama wlh yaushe kikazama haka, nifa punishing naki nakeyi na shanyani da kikayi anan na kusan 2hours, to ke kumafa kodai kinfara iskan..... Ya rufe bakinsa yana dariya yaja motan suka tafi duk yanda yayi yajata da hira ta sake tak'i sai b'oye Fuskanta takeyi ahaka har suka kai gida, yana perking tafita da sauri ta shige ciki yabita da dariya yana girgiza kai yace "Khadijah problem,


Da daddare Tana zaune abakin gado saiga Kabir ya shigo hanunsa rik'e da ledoji ya ajiye ya zauna kusa da ita yana kallonta,

"Madam ba ko sannune? Tad'anyi murmushi tace sannu, yauwa d'auko plate da 2 Cups a kitchen kizo tashi tayi tasa hijab ta fita tazo dasu ta ajiye ya ciro kaza gassashe ya d'ora akan plate d'in ya ciro fresh milk mai sanyi ya tsiayaya aduka cups d'in yace

"Bismillah nasan murnan graduation bai barki kinci komiba, babu musu tafara ci dan yunwan takeji gashi yau tana cikin farin ciki, tace "Likita yaushe zamu tafi?

"Ina?
"Ruganmu mana,

Murmushi yayi ya kurb'i Fresh milk ya ajiye "Wato baki mantabako? To ai baki cika sharad'in nakiba kinmanta jiyama kinyi taurin kai, ya fad'a yana d'aga Gira,

Kaman zatayi kuka tace "Banyibafa dai2 lokacin sukaji anyi nocking k'ofan d'akin anmurd'a handle d'in cikinzafin nama Kb ya tashi ya shiga toilet dai2 lokacin aka bud'e k'ofan aka shigo Mami tasaki baki tana kallon ikon Allah ga k'amshin turaren Kabir da yake yawo a hancinta,

ta kalli plate d'in ta kalli cups d'in dake wajan sannan ta kalli wayoyinsa Biyu da Hulansa da yacire ya ajiye awajan,


Sannan ta maida kallonta ga Khadijah da tayi suman zaune, kaman k'asa ya bud'e ta shige, Mami ta tab'e Baki tace "Ina Kabir d'in ya shiga?


Murya na b'ari Dijah tace "Mnnm babu,

"Dana d'aukoki daga d'akinsa shine kika kawoshi d'akinki ko Khadijah? Har kin iya b'oyeshi, yaushe kika iya irin haka? Tad'an sassauta murya k'asa gami da d'an ran k'wafowa yanda tasan bazaijiba,


Tace "wato ke dad'i miji ko? To kimayar da Hankalinki ba'ayiwa Namiji haka, Khadijah so nake nakarb'armiki 'yanci, baki ganeba,

daga haka ta juya sai da takai bakin k'ofa ta d'aga Murya yanda zai ji tace kuma kisanar dashi zamu had'une daga haka ta rufo musu k'ofa tana d'an murmushi Aranta tace Kabir d'an Duniya wato sai da yasan yanda yayi ya yaudareki har kika amincemasa zaman d'akinki batare da nasanaiba saidai dama na dade ina zargin hakan, nasan yanda zan b'ullomuku dukanku zanyi maganinku yara zaku gane baku da wayau,



Washi gari Kabir da k'yar ya iya zuwa gaida Mami saidai bata nunamasa komiba ta amsa da fara'anta har yafita batace dashi.komiba,


Ganin hakane
Yasa washi gari yazo takanas yasameta, akan kujera ya zauna itakuma tana bakin gado,


Bayan sund'anyi 'yar hirane ya gyara zama yana kallonta yace "Mami jibinefa zan tafi Lagos

Mami tace "Eh inasane Allah yasa kaje lfy kadawo lfy Kabir Allah ya katemin kai,

" Amen yace gami da kallonta yace "dama inason in ajiye Khadijah a rugansune sai inwuce inna dawo sai in d'aukota indawo miki da ita,


Cike da Mamaki Mami ta kalleshi aranta tace tofa gawani tsari ta inda ka bullo kenan? Har zakacemin wai kadawo min da ita, kama cire kanka, Ayyah yaro ka makaro nagano logonka yanzu zamaka mai gaba d'aya ayita ta ka're Kabir.



πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ

*Wai shin da gaske Kabir Rugan zaikai Dijah ko dai akwai abunda ya shiryane?*


*to inma can zai kaita anyah Mamin zata yarda musamman yanda talura yaran nata namata wasa da hankali*

*To Ya Dijah zataji in Mami ta hanata wannan tafiyan dabatasan ingancinsaba ma'an Rugan xai kaita ko wani wajan?*

Ya Kabir zaiyi tunda yanzu baya iya barci hakanan?

Nidai nace in anhanashi Dijah yaje ya d'auki Nafisa mai nimansa ido arufe πŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ

Anmafa Shawaratace wannan ke meye shawaranki? Sai naji daga gareku


*Ummu Fatima ce* 😘
[8/30, 9:51 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š

_kai Gaskiya inashan k'orafinku kala2_ πŸ€¦πŸΌβ€β™€

_Sam kunk'i karb'an uzurina fans da gaske jikinrin littafin ba sonabane_ 😰

_Nasadauk'armuku da wannan page gaba d'ayanku masu k'irana fa masu min massage ta inbox da watsao grouo da prvt duka akan Rashin ganin sabon page_

Karfa kuce cin hancine πŸ™ˆπŸ™ˆ


Wanda ban amsamusu maganaba a prvt kuyi hakuri wayance tayi Rsetoring😰


5⃣8⃣


Wani kallon baka da wayo Mami ta bishi dashi tayi murmushin inka san wata baka san wataba, ta d'an muskuta suna facing d'in juna sosai,

Tace "ka k'osa ko Kabir? Ka k'osa tayi ta barmuku gida,

ka k'ara Hak'uri ina sane da Ak'awarin da na maka, duk yaushenema tagama makarantan?

Cikin wani irin yanayi Kabir yake kallon Mahaifiyar tashi, jin tamasa wani fasarra na daban,

ya girgiza kai "No Mami ba haka nake nufiba.. Da hanu ta da katar dashi, ta d'an had'e Rai "ya isa Kabir kai da zaka Lagos a jirgi mai xai kaika wannan Rugan?

Kayi tafiyanka kawai ni na d'auko Khadijah daga wajen iyayenta da Hanuna, kuma ni xan mayar da ita garesu da Hanuna, kayi tafiyanka kawai kabarmin abata.

Ahankali ya d'ago ya kalleta sam ba alaman wasa a fuskanta,

"Ayyah Mami baki fahimceniba, ba manufata kenanba, ya fad'a azuciyansa,

Yaso ya fahimtar da ita, anma Ganin bai samu fuskaba yasa ya mik'e jiki ba k'wari ya fita,


A k'ofan pertd'insa ya zauna ya rafka tagumi yana tunani da jin Haushin kansa na yanda ya bari yake shiga cikin lamarin yarinyan da yawa haka,


Can yayi tsaki gami da mik'ewa aranshi yana tunanin gara yayi tafiyansa ma shi kad'ai yasan kafin ya dawo ya manta ta kwata2

Da wannan shawara Kabir yayi shirinsa a tsanake, cikin kwana Biyun ko nimanta baiyiba, duk da yanda yake jin zuciyansa da gangan jikinsa nayi, na Rashin ta akwana biyun, anma ya dake gani yake da yatafi shikenan ya manta da ita

******************

Tun shida ya fara shirin tafiyansa ayau, dan da wuri yake son barin gidan sabida abinda yakeji na fizgansa game da Khadijahn,


Fararen tas d'in Suit yasa dw wandonsa, yayinda na cikin ya kasance coffe brawn, takalminsa ma Sau ciki cofee brawn yafito a asalin Likita Gogagge kuma wayayye sai da yagama had'a duk takardun da yake da buk'ata sannan ya manne idonsa da Glass mai fararen kwalba wanda kake iya ganin komi na idonsa tas tacikin kwalban yayin da Hanun galss d'in ya kasance coffe brown ya d'aura agogon fata ahanunsa shima brown ya d'auki brief case d'insa brown ya fito, sauri yakeyi sukayi kicib'us da Sani A falo, dukansu fuskansu da guntun Murmushi suka mik'a ma juna hanu,

Sani yad'an gyara tsayuwa yana kallonsa, "Haba Kb meyasa yanzu inzaka fita sam bakasanr dani kuma kasan aikina ne fita dakai,

Kabir yayi murmushi yaja Hanunsa suka fita yace "Abokina ta yaya zan dinga d'aukanka muna tafiye2 kullum bayan yanzu kazama nai lyali?

Tuni na canzamaka aiki abubuwanne basu gama kankama ba shiyasa bansanar dakaiba, Na mai dakai Campaninnan yanzu kaine Manerger,

zaro ldo sani yayi ya tsaya cak da tafiyan da yakeyi "Kana nufin Zaka karb'a ahanun Alahji ya'u kabani? Kb yayi murmushi gami da d'an dukan kafad'ansa "shirin da nakeyi kenan Abokina, kasan nidashi d'in kowa shiri yake akan d'an uwansa, ninawa shirin kenan akansa inyagama farautanan,

Daga haka ya wuce cikin pert d'in Mami, yabar Sani da tarin Mamaki yarasa hali irin na Kb sam bayada k'yashi ko Hassada, Burinsa wani yasamu ak'ark'ashinsa, yasan duk irin Abunda Alhaji ya'u yake shukawa akansa anma yayi burus ya zuba ido yana jiran sai yagama.


D'akin Mami ya nufa jin Motsi akitchen yasashi dawowa a tuanainsa Manince aciki,


Khadijah ya gani tana share Hanunta da Towel dan wanke2 datagama, Dam!! Sukaji zuciyoyinsu ya buga a tare,

Da sauri ya juya ba tare da yace komi itama da saurin ta yarda towel d'in da yake hanunta ta nufoshi gami da k'iran Sunansa, "Doctor!! Cak yatsaya ya juyo yana kallonta, ta matsoshi asanyaye daf dashi ta tsaya ido da ido suke kallon Juna,

Numfashinsu na turereniya, ta d'an girgiza kanta tana ci gaba da kallon k'wayan idonsa da shima ya bud'esu sosai yana kallonta dasu, yanajin wani abu na ratsa illahirin jikinsa, Cikin wani irin Murya mai d'auke da damuwa tace "Likita kafasa kaini Gidanmunne?

D'an ajiyan zuciya ya sauk'e yayi kaman zai juya tayi caraf ta cafko Hanunsa tana murza cikin tafin Hanunsa da yatsunta kaman yanda yake mata aduk lokacin da yake son shawo kanta akn wani abu ta d'an langab'ar da kai, Murya Asanyaye


Idonta taf da Hawaye tace "Baka tab'amin Alk'awari kacikaba Likita, meyasa kazamo mai magana biyu? Meyasa kake yawan yaudarana?


Cikin mutuwan jiki da kalamnsa da kuma abun da take masa ya jawota jikinsa yamanneta ak'irjinsa, yanajin zogi aransa harga Allah yaso tafiya da ita suje Rugansu suyi kwana biyu sai su wuce Lagos kafin su dawo, dan ayanzu ji yake kaman bazai iya Rayuwa ba itaba, duk da yasan ba sonta yakeyiba anma zuwa yanzu yasan tana da matik'ar Muhimmaci a Rayuwansa,

Anma ina Mami ta hana faruwan hakan.

Kuka tasake gami da K'ok'arin k'wace jikinta dan yanzu ta gama ganewa jikinta yakeso shiyasa yake yawan yaudaranta sai ya samu yanda yake so sai ya shareta,

shiyasa yanzu ya yaudareta dacewa inbata bashi kanta bazai kaita gun Baffantaba inkuwa tana Amincewa da shi zai kaita tayi sati ya dawo da ita,

bayan wata yasake maidata, Ashe duk yaudaranta yakeyi,


"Khadijah ba laifina bane ya fad'a Araunane, da sauri ta k'arasa k'wace jikinta ta kalleshi "Likita na dawo daga Rakiyanka bazan sake yarda duk wani furuci da zai fito daga bakinkaba,

Cak magananta ya tsaya sakamakon Had'e Bakinsu waje d'aya da yayi kissing nata yakeyi cikin k'warewa jin suna niman su fad'ine ya manneta da jikin Gini ya tura Hannayensa Cikin Riganta, Shiru tayi ta kasa Koda motsi ne sai k'ara lafewa takeyi ajikinsa tana fitar da Numfashi, tanajin kaman tana Son abinda yake matan,

Jin takun k'afa Alamun ana dosowa kitchen d'inne yasashi zare Hanunsa da Bakinsa ajikinta, ya d'anyi baya kad'an dai2 lokacin Mami ta shigo tana fad'in "Khadijah har yanzu baki gamabane?

Nan idonta ya sauk'a akansu kallo d'aya ta musu ta gano halin da suka fad'a da sauri ta janye idonta tana k'ara tusuwa cikin kitchen d'in cikin dakewa tace "Af Kabir kar dai har kagama shiri, ai nayi zaton kana Bacci ne inata k'iran wayanka baka d'agaba,


Gefensa Khadijah tabi ta fice cikin azama ji yake kaman yabita ya kamota ya maidata jikinsa,


Ya gyara tsayuwa kansa ak'asa yana facing Mami da tak'i yarda su had'a ido tana ta had'a abinci a Basket sai da yayi gyaran murya kusan sau uku kafin ya iya fara Magana duk da Maganan baya fitowa sosai, yace "Ni zan wuce Mami amana Addu'a sai lokacin ta d'ago ta kalleshi,

"zaka wuce bakayi Break ba Kabir?
"Nayi a pert d'ina Mami sauri nakeyi kar asamu matsala kai ta jinjina, tafara Jero masa Addu'o'i yana Amsawa da Ameen har ya fito a a falo yasamu lya,


Yamata sallama tace "Ayyah nima bazaka dawo kasameniba Kabiru Gobe insaha Allah zan wuce Maiduguri,

Yace Haba lya wai me kikeyi a Maidugirinnane haka da kika k'i hak'ura da shi?

Dariya tayi tace "abunda kakeyi a yola haba Kabir ni da mahaifata ga zuri'ata duk acan kace me nakeyi,

"to ki k'ara hutu anan sai ki koma
"a'ah gaskiya ina kewan gidanmu,
"Ok kibari to inna dawo nanda sati sai inmayar dake da kaina, tace "Anyah zan iya? Sati zakayi acan?
"Eh Ran ata yau zan dawo insha Allah,
"to barin gani dai,
Nan sukayi sallama ta masa fatan sauk'a lfy ya fice zuciyansa na ga Khadijah ya rasa wani irin Hukunci Maminsan takeson yankemasa,


Dijah kuwa tun shiganta d'akinta ta shige wanka dan tasaha Alwashin zatayi ma Mami Rikici ta barta taje wajen 'yar'uwanta ta wuni ko zata huce takaicin da Kabir ya d'ura mata tafito kenan taji hayaniya ta window, ta yaye labule tana kallonsa yanda sceuiritynsa suka kewayeshi yana tabasu hanu,


Zuciyantane taji na mata d'aci tana kallonsa har ya shige Motan ta saki labulen gami da fad'awa kan gado ta saki Kuka mai cin rai da irin yaudaran da yamata, sannan awani fannin tanaji ajikinta ya koyamata jarabansa, dan kwana biyunnan da yayi ba tajita ajikinsaba da k'yar take iya Bacci,


Tafi Awa biyu tana risgan kuka kafin ta tashi da k'yar ta shirya,

tana d'aurin d'an kwali Mami ta shigo, kallo d'aya tamata ta gano kukan da taci aranta tana mamakin yanada akayi nan danan ta hango tsananin zazzafan so da shak'uwa a tsakaninsu wato ita dai tana Gidan Sun maidata Hotiho tana musu kallon suna fad'a gami da sukan juna ashe akwai wani sirri tsakaninsu,

Dan ba k'aramin mamakin yanayin da ta gansu d'azu tajiba, dan dukansu fuskansu ya nuna tsananin buk'atuwa da k'aunan junansu,


D'an tab'e baki tayi aranta tace bazan janye k'udurinaba Khadijah inna janye wlh kece aciki muddin bangara Kabir akankiba Nafisa da Uwarta zasuyi saurin cin Nasara akanki,

anma inya garu yasan zafinki to ko zasuyi nasara ba dukaba zai nayi yana tuna cewa ked'in mai tsadace inkin kub'uce masa zai sha wuya, Ta sauk'e ajiyan zuciya awani gefen kuma tana tausayinsu, tace "Khadijah kizo ki karya Sai kije kiyi ma Fatima sallam Gobe in Allah ya kaimu zaku tafi maiduguri da lya kije kid'anyi Hutu akwai autar lya dazata miki gyaran jiki inkun gama sai kidawo kuje can wajensu Baffah,


Wani irin kallo Dijah tayima Mami sannan ta kau da kai aranta tana tunani "to kodai haka duk mutanen garin suke da yaudara?


"Kiyi hak'uri Khadijah nasan hankalinki ya tafi wajen son ganin mahaifanki zaki je lnsha Allah, ta fad'a cikin rarrashi kaman tasan abunda Dijahn take tunani,

Mik'ewa Dijah tayi tana kauda damuwanta ta fita.


Dama tuni Mami tagama tsara lya akan tafiyan takuma gama shirya yanda komi zai tafi dan haka washi Gari da safe suka wuce Maiduguri,

BaK'aramin Mamaki Dijah tayiba yanda aka dinga nan danan da ita agarin duk wanda ya shigo lya tace masa ga matan Kabir sai taga ank'ara karramata haka sukayi ta tururuwan zuwa ganinta, sosai tasake acikinsu,


Washi gari lya ta damk'ata ahanun Ya Fannah, kamar yanda Mami ta gayamata,

wayyo Nan ya Fannah ta fara aiki akan Dijah na musamman dan tuni tariga da tasan komi game da Dijah da Nafisa dama ba k'aramin haushin iyayen Nafisa takejiba akwai k'ulli tsakaninsu Shiyasa bayanda basuyiba kan ta gyara Nafisan fir tak'i,

abubuwa take koyamata tunda ga kan yanda zata zauna da Mijinta da kishiyanta, girki, tsafta kula da shimfid'an miji, da yanda k'amshi zai kama jikinta koda yaushe, kafin sati Dijah ta canza kala gaba d'aya dan wannan sana'an Yafannah ce na shekara da shekaru ba k'aramin k'warewa akai tayiba dan gari da gari ana zuwan mata,

*****************

*Kabir* tun fitansa agidan cikin damuwa yake ahaka har ya isa cikin garin Lagos ya sauk'a a hotel d'in da aka tanadar masa bayan yayi wankan gajiya ya haye kan gadonsa ba abunda yakeso da k'aunan gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login