Showing 51001 words to 54000 words out of 155892 words
da danne2 wayansa, Wani dogon tsaki Nafisa taja tana Hararanta tace "Dan k'auye be iya wayewaba, d'an matsiyaci bai iya samun wajeba, Tir da mai Halin Tinkiya.
Dariya kawai Dijah takuma yi ta ja Hanun Jamila suka fita, a bakin gate tasamu mai d'aukanta nan sukayi sallama tashige mota da tarin tambayoyi abakinta,
Lokacin da Dijah tadawo daf da gate d'in tasamu Nafisa tana tsaye tacika fam yau kam tasha Alwashin sai taci Uban wannan 'yar k'auyen ta fad'a aranta, cikin kakkausan Murya tace "Ke Banza 'yar k'auye y'ar matsiyata dabba Tinkiya, ma wa kk dariyan Rashin kunya.
Wani irin Dariya Dijah takuma fashewa dashi, ta tako ta k'araso gabanta "basai kin sake Maimaitawaba inasane zan baki Amsanki yake 'yar masu arzik'i ai babu matsiyaci aduniya, watak'ila 'ya'yan masu arzik'i basu shiga ajin lslamiyyane shiyasa bakisan hakanba
Babu wanda yasan Matsiyaci sai Allah watak'ila wanda yake tink'aho da arzik'i aduniya shine matsaiyaci alahira, d'an talakanma kuma zai iya zamowa matsiyacin wannandai Gaibune da Allah shi kad'ai yabar ma kansa sani, Sannan kuma da karya ai gara tinkiya Hidiman gabanta kawaitakeyi bata Abin tir da Allah wadai, sab'anin karya da take lank'aye da wani duk inda suka gifta ana Tir da ita,
daga Haka tajuya zata tafi cikin zafin Nama Nafisa ta fincikota takai mata Mari da sauri ta sunkuya ta Mari lska,
"Dan Ubanki wacece Karyan? Ta tambayeta tana shirin kai mata wani marin "Hey Stop it Nafisa Kabir yafad'a cikin tsawa, yana k'are ma Dijah kallo,
"Kb kabarni inci Uban yarinyannan ni take cewa karya?
"Kece Karya kona fad'a ko ban fad'aba inba karyaba wacece Kullumtana jikin Namiji ba dare ba Rana abun Haushi ba Miijinkiba, ba Muharraminkiba mtsss taja dogon tsaki ta wuce zata bi bayanta Kabir yace Nafisa nace miki kirabu da ita Wannan indai wajen fad'a da dambene bazaki iya da itaba shugabace wajen Rashin kunya kirabu da ita pls, Cikin zafi tace wai Kabir ita wannan d'in yar gidan Uban waye? Waye ya kwasota yakawota gidannan?
Had'e Fuska Kabir yayi "ai ba agidana kika gantaba dazakimin wannan Tambayan kije ki tambayi me gidan Itake da Amsan Tambayanki.
Daga haka yashige part d'insa, afusace tashige ciki tana surutu wlh yau sai na yima yarinyannan mugun duka tabar gidannan.
A falo ta sami Mami kai tsaye d'akin Dijah ta shiga bata ganta ad'akinba tafito tana Huci,
"Lfy kuwa Nafisa meke faruwane? Mami ta tambayeta.
"Wannan yarinyan nake nima Mami wlh yau sai na b'allata,
"Wata yarinyafa? Mami ta Tambaya tana Rik'e Hab'a.
Dai2 Tabata Amsa Dijah tafito daga kitchen Rik'e da goran Ruwa zata kawo ma Mami.
Dasauri Nafisa tayi kanta zata tad'auketa da Mari Mami tayi hanzarin tashi ta rik'eta lfy Nafisa laifi tamiki Mami kibarni in ci uwar ta wlh yau sai tagane ni Karyace, Zaunar da ita Mami tayi akan kujera.
"Metamiki? Gayamin ni nasan mezanyi akai, ban baki Hukunci a hanun kiba Nafisa.
"wai ni yarinyannan takece ma karya shikuma Kabir wai har zai cemin wai indai Dambe da fad'ane ban isa da wanna yarinyanba wlh k'aryane, yau sai namata kafirin duka agidannan,
Mami ta jinjina kai "inna fahimceki kaman Kabir ne yahad'a wannan fad'an, takalli Dijah da tayi tsilli2 da ldo Khadijah jeki ki k'irakimin shi, dasauri Nafisa tace "a'a Mami bashi yahad'aba,
"lnce dai yana wurin? K'irashi Khadijah ayi komi agabansa sai yazamo shaida tunda abun yakasance haka,
Karo na farko da Dijah ta tink'ari part d'in Kabir tundaga k'ofan falo taji wani sassanyan k'amshi natashi gami da wak'an india na Falgoni, hanunta na b'ari ta k'wank'wasa k'ofan, sai da yarage sautin Kid'an sannan yace "yes come in, Murd'a Handle d'in tayi ta shiga azaune yake akan kujera ya tallafi Hab'ansa da Hanunsa maganganun Khadijah da tagaya ma Nafisa nata yawo akansa, Metake nufi da wannan maganan? shine tambayan da yake tayi ma kansa,
Khadijah kam sake baki tayi tana k'are ma falon Kallo duk Had'uwan falon Mami da har yau bata gajiya da kallonsa yayi baikai wannan ba komi na d'akin Fatine k'al gashi komi bisa tsari yake, daidai da Tv.
ga wasu flawowi da aka kewaye gaba d'aya dungun Falon dasu.
Kansa asunkuye har yanzu bai d'agoba atunaninsa Nafisa ce tashigo jin batayi maganaba kuma bata zaunabane yasa shi fad'in Baby zo Kizauna kusa dani kiji, sai alokacin Ta kalleshi har ya watsa Ruwa ya sauya kaya Tree Quater ne ajikinsa mai tsantsi da Rigansa amless, wani uban tsaki taja sannan tayi baya "ance maka ni 'yar iskace Mami na ne take k'iranka, da sauri ya d'ago ido yakalleta wani lrin kallon ashe abunda kukeyi kenan? Take masa cikin zafin nama ya tashi yayi kanta aguje ta juya sai dai kafin takai ga k'ofan ya damk'ota, (kunsa Dijah da k'ara)
wani irin k'ara tasake Har saida Mami tajiyota, sai b'ari takeyi tana k'ok'arin k'wacewa k'ara fizgota yayi ta fad'a jikinsa da sauri kuma ya cireta yana kallonta "inke ba 'yar iska bace to waye d'an iskan? Zata sake sakin ihu ya buge mata baki da bayan Hanunsa.
Ganin yana nima yadawomata zaki ne ta sassautar da Murya "Mami ce fa take k'iranka wlh ba k'arya bane, jin ya d'anyi sako sako da rik'ontane ta fauce ta fita aguje, yabiyo bayanta.
duk saurin datayi kusan ajere suka shiga falon, daf da Mami Khadijah ta zauna tana haki shikuma gogan sai sinne2 kai yakeyi yak'i su had'a ldo,
Mami ta kalli Khadijah "kekuma ihun me kikeyi?
"Shine ai yatab'amin Jiki Mami nagaya miki wlh lskanci sukeyi yanzuma....
"Ke Khadijah wai meyasa kike da yawan Surutu ne? Iya ta katseta tana fitowa daga d'aki agefen Kabir dayagama jik'ewa da zufan jin abunda Dijah tafad'a ta zauna "Fatima wai meye yake faruwa?
Mami ta nuna Nafisa "Fad'i abun da ya had'aku,
Nafisa ta tab'e baki Yarinyannan tajima tanamin Kallon banza Nida gidanmu, shine yau wai har dacemin Karuwa mai bin Maza.
Iya ta Rafka salati tana tafa Hanu "Anyah Kuadijah mai yakaiki? Kinkosan Hukuncin Magananki? Irin wannan katob'ara da kikayi, Da Hankalinki? Ai dai koba komi Nafisa tayi k'anwa dake ak'alla sau biyu,
Saida Iya tagama fad'anta sannan Mami ta dubi Khadijah da taketa Zub da k'walla, tace "Meya had'aku Khadijah? Da har kikamata irin wannan Furucin.
cikin kuka tace "Mami niba Karuwa nace mataba Karya nace mata Saboda Allah ku baku gani kullumfa indai Likita yana gida tana tare dashi kuma wlh sau dayawa ina ganin suna... "Shout up Mami ta tadakamata tsawa, "Abunda yahad'aku kenan? "ita tafara cemin Tinkiya nan ta fad'i yadda sukayi.
Cikin kuka tace kullum sai tamin gorin gida, kuma ai nima muna da gidan.
Mami ta kalli Kabir da ya Dafe goshinsa yana kallon k'asa cikin zafi tace "Kabir wace ce mai Gaskiya acikinsu?
Ahankali ya d'ago yana Kallon su, yasan cewa indai a Gaskiyane to Khadijah ita tafad'i gaskiyan yanda akayi yayi mamakin Nafisa da tafetta k'arya haka, saidai amma tsananin Haushin Khadijah dayake Ransa, daya iya k'arya tabbas da ya k'aryatata, to inyayi haka kuma shima yayi k'arya abunda bai iyaba.
"Ana tambayanka kayi Shiru me kake Nufi? Inji Mami,
Sunkuyar da kansa kawai yayi yace "Kiyi Hak'uri Mami,
"Eh zakace inyi Hak'uri mana kana Namiji yara suyi fad'a agabanka, amma kakasa Yin komi akai,
"Mami bakisan Halin wannan Yarinyanba, Wlh bata da Kunya koda na Rabasu bazata saurarenba.
Iya tarik'e Hab'a saboda Allah Kabir tambayanda akamaka kenan? Kaba da shaida akan Halin Khadijah ko kuma kayi shaida akan fadansu kaifa Namijine Anyah zaka iya Adalci a tsakani Matanka?
Nafisa tazaro ldo mata? Lallai ma lya Allah yasawak'e yatara Mata ancemiki shi irin wancan tshohon Mijin kinnan ne dayataraku ku biyu wlh nikam nid'ayace bawatta banzan da zata shigomin Gida,
Iya tayi Murmushi "To Allah ya taimaka matan mai mace d'aya, ammadai inaga da ba'a k'arin dake ko shi Mijinkinda kikewa Soyayyan ba d'aya acikinku daga haka ta mik'e ta tafi.
Mami takalli Khadijah datake ta resa Kuka cike da tausayi don ko ba a gayamataba tasan Kukan tuna lyayenta takeyi.
Khadijah yi Hak'uri kitashi kije kiishirya ga Malamin Islamiyyanki yazo kije kiyi Kartunki, kar insake jin kincema watama ba Nafisaba Karya, Kinji? Kai ta gyad'a sannan ta tashi ta tafi
Mami tajuyo ta kalli Nafisa da take ta jijjiga tace "Nafisa kema kar kisake cemata tinkiya sannan na rok'eki kimin Kara kidaina Mata Gorin Gida,
Yarinyannan 'yar gatace agurin iyayenta bak'aramin artabu nayiba akanta, da k'yar sukayarda sukabani, lta don haka kitaimaka kidaina Mata gori inbadai kinason kinunamin cewa ban isa in kawo wata Gidankubane.
Inkuma kinci Gaba to dani kikeyi bada itaba.
Tashi Nafisa tayi ta shiga ciki jimawa kad'an tafito da makullin Mota "Mami Na fita, "to adawo lfy kawai tace atak'aice.
Kabir yatashi Zai fita Mami tace "Kabir zo dama ina da Magana dakai,
Gyara Zama tayi tana Fuskantansa Sosai Tafara Magana "Kabir inason ka bud'e kunnenka Sosai kaji Abunda zangaya maka, lnafatan zaka fahimceni fahimta mai kyau,
sake gyara xama tayi tana fuskantansa, Amatsayina na Mahaifiyar ka Kabir Namaka Aure!!! Ko ince nasa and'aura maka Aure! Bada saninkaba.
Dukda abaya kai kabani wannan daman saidai yanzu naga kaman ka sauya ra'ayi.
*Tirk'ashi wai yaya Kabir d'an gidan Mami zai d'auki maganan da Mahaifiyarsa Maminsa maiso da k'aunarsa tazo masa dashi shin yaya zaiyi da Nafisa gashi dama ra'ayinsa bana mata biyuba* *gashi an auramasa matar da baisaniba*
shin wai meyasa khadijah tamatsa dacewa Kabir da Nafisa 'yan iskane??
Karkumanta Comments d'inku shine yake bani k'arfin gwiwaππ»
08065091824
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 3β£1β£
Shiru ne na Lokaci ya biyo baya, Wani lrin sanyi mai gauraye da zufane yake ratsa jikin Kabir,
Yarasa wani yanayi yake jin Kansa, azahiri dai shi bai kawo Aure ma kansa nan kusaba don har yau shi baiga matar data dace dashiba, duk dai dama yasa ma ransa zaiyi Aure ne don d'abbak'a Suna, da son cika ma Mamin sa Burinta, Don yasan inyace don so zaiyi to bazaiyiba Har Abada don shi bai yarda da Akwai wani Abu mai suna Soyayya ba bayan na d'a da Uwa, sannan awani b'angaren kuma yana son Zab'in Mamin sa, yana son ganin Farin cikinta, saidai bai yi tunanin Dagaske Mamin zata masa Auren Doleba kamar yadda tasha gayamasa asigan Wasa.
"Kabir! Mami ta k'ira Sunasa cikin sanyi da damuwa, aduniya Abu mafi d'aga ma Mamin Hankali shine ta ga Kabir d'in cikin Damuwa.
"Na maka laifi ko Kabir?
Ban kyauta maka bako?
Sai kuma tayi shiru tasake d'agowa ta kalleshi shid'inma itan yake Kallo cikin damuwa, "kayi Hak'ur.... "Mami!! Yak'ira Sunanta cikin sanyi Murya cike da damuwa ya k'araso yarik'e k'afanta "Don Allah Mamina kar kiban Hak'uri Nine fa Kabir d'inkinnan Mami da kikaci kashi da fitsarinsa, kika jure d'auwainiyansa Na miki Kuka.
damuwata tahana ki Bacci, Mami kinyi dai2 Abunda kikayi Baki b'ataminba wlh ban isa ince kinmin laifiba, Nagode Mami Allah yasa hakan shiyafi min Alkhairi Duniya da lahira.
Kallonsa kawai Mamin takeyi dukda ta karanci tsantsan firgici a ldonsa Kalamansa sun kwantar mata da Hankali, Tabbas Tasan Allah yamata Baiwa da samun nagarceccen d'a mai son ganin farincikinta akullum.
"Allah yamaka Albarka Kabir lnsha Allah wannan aure zai zamo Alkhairi garemu baki d'aya kaci gaba da Addu'a Kabir lnsha Allah zakayi farin ciki madawwami da matarka, da yardan Allah kaima zaka samu 'ya'ya Na gari masu biyyaya agareka tashi kaje.
Cikin Sanyin jiki ya fita tsaban wani abu da yake damunsa wanda bai ganeba shin farin cikine ko damuwa, Waje ya fita ba tare da yaganeba, yajima yanatsaye abakin gate yana tunani gami da Tambayoyi ma kansa, Why Mami ta masa wannan auren? Meye matsayin Auren Nafisa awajensa yanzu? bayan Har yabada sadaki ansa Rana?
"No Mami bazan lya auren Mata Biyu ba pls ya fad'a yana ya mutsa gashin Kansa.
Kimanin mintuna 40 yana zaga wajen daga bisani yashiga part d'insa Toilet yashige don Rage Ma kansa damuwa.
Kwance take kan Gadonta tanata juyi gami da sharan k'olla, yau abun da yafaru tsakaninta da Nafisa ya tunamata da Baffanta shauk'in su yacika zuciyanta, Baffanta Mai Bin bayan ta kotana Dagaskiya kobata dashi, Burinsa kawai kar yaganta cikin Damuwa, Bai tab'a yarda ya d'ora wani akantaba sai dai ta Rarrasheta, wayanta ta d'auko ta dinga bin Contacts d'in d'aya bayan d'aya, aranta tana tunanin Meyasa Fir Mami tahanata Numbern Baffanta saidai tak'irashi da wayanta suyi magana agabanta, ko meyasa hakan? Tabbas da tanada Numbernsa data k'irashi awannan Lokacin.
Ji tayi Karatunma yafita aranta Inna da Baffanta kawai take son Gani, tashi tayi tashige Toilet tana wanka ta jiyo Muryan Mami gyaran Murya tayi, tacigaba da wankanta, koda ta fito bata Sametaba, Rigan Bacci tasa mai santsi dayakawo har gwiwanta, ta tufke Gashinta ta D'aure da K'aton Band tafito, a Falo tasami Mamin ita kad'ai tun kafin ta zauna Mami tace "Haba Khadijah na ko kowa zai gujeni bai kamata kema ki Gujeniba, Nafisa ta gudu agidan gaba d'aya saboda na nunamata kurenta amatsayina na Uwarta, Kabir ma tunda yafita bai dawoba.
kekuma meyasa kika b'uya ad'aki kika k'i fitowa? Kema namiki laifiko? tafad'a tana k'are mata kallo.
Akasalance tace "Bakomi Mami wlh banyi fushi dakeba bakimin komiba.
Ba abin da zakimin Mami inyi Fushi dake.
Cike da Tausayi Mamin tace To shikenan Khadijah je kici Abinci kije ki kwanta Gobe ln Allah yakaimu da safe ki shirya zamuje gidan Fatima, Zanje in kwanta nasha Magani, kitabbatar kinci Abinci kafin ki kwanta, daga Haka ta Haye samanta,
Dijah tajima azaune agun kafin ta tashi ta Haye daining ta duba Abincin gaba d'aya ba wanda yamata, dan haka ta tashi daniyan barin wajen ta shiga d'akinta, Kabir tagani atsaye Hanunsa acikin Aljihun Wandonsa, Fuskansa amirtuk'e sai Binta da Kallo yakeyi, Ahankali yafara takowa yana Nufota, tana ja da baya yana binta Har sai da suka kai dungun d'akin Sanin Halinta ne yasa yayi saurin sa Hanu ya toshe bakinta sannan ya d'agota suna Shak'an numfahin juna, Jawota yayi sai da ya danganata da wani corridor kusa da k'ofan Fallon yasaketa yana Kallonta gaba d'aya ldonta sunfito waje, amma sabida Hali lrin na Dijah Qaya takalleshi cike da tsiwa tafara Magana "Meye Haka? Malam ina zaka kaini? Kaga baniso ka matsamin ln wuce.
Yatsunsa Biyu ya had'a ya d'ani Lips d'inta, sanna ya kamasu da k'arfi yana kallonta Fuskansa A murtuk'e
"Ma waye kike cewa d'an lska? Gayamin lnji.
Hannayenta ta d'ago ta d'ora akan nashi tana juya kanta, zame Hanunsan yayi yana yarfewa yana kallonta tasa Hanu tana shafa lnda yarik'en cike da jin zafi.
Zaki gayamin ko sai na cire wannan bakinki mai Faccakala maganan ya fad'a yana shirin sake kamo Bakin,
"Nifa ba d'an iska nace makaba, cewa nayi naga kuna lskanci kai da wancan Banzan kuma wlh nasha ganinku.
Cike da tsoron Furucinta yake binta da kallo ya lura da iya Gaskiyanta tayi maganan.
"Khadijah menene Iskanci?
"ohon maka kai kasani wlh Har maganan lskanci kunayi ai lnajinku kullum abayan Windowna kuke zama.
Kafin ta Rufe bakinta ya kaima Bakin bugu da bayan Hanunsa zatayi lhu yayi saurin Rufe bakin kika sake kikamin wannan k'arankin sai na B'urma miki baki, yarinya k'arama dake kin iya sa ldo da yin sharri.
Bawani lskancin da kika tab'a gani banza 'yar k'auye kuma ma lnkin ganin lna Ruwanki kiyi damuwan gabanki mana sai kin zauna kina terere na agari, manufarki Dabam Manufar wanda zaiji wannan Furucin abakinki dabam, kuma lnna sake ji kin Zagamin Mata sai na B'allaki ahasale tace "wlh ba matanka bace tunda ba ad'aura muku aureba, kuma wayace kudinga cewa wani l luve u a l missed u kuma kullum sai ta shiga d'akinka ai wlh da agarinmu kuke sai an muku wak'a, sake baki yayi yana kallonta har sai da ta kai Aya gani yayi inba da gaske ya mataba baza ta daina shiga Rayuwansaba.
Ya fara k'ok'arin ciro Belt d'insa ganin Haka yasa ta fara shiga Hankalinta don tasan zai lya jibganta awannan lungu kukanta abanza.
"To ai Mami ma tace kar insake fad'a kuma nace bazan sakeba kaban hanya lnje in kwanta bazan sakeba.
"kidai cigaba da min tsiwan dakika saba kawai.
"Allah Likita bazan sakeba, kayi Hak'uri nikamma na daina lek'aku.
Mai da Belt d'in yayi ya gyara tsayuwa yana kallonta "karma kidaina lek'amu ki cigaba da lek'enki amma dai kidaina min sharri inma zakiyi gulman to kinimi sani akai kafin ki fad'a lnkink'i sai na farfasa wannan bakin kin.
Kafin ya Rufe baki ta shige ta osinsa ya juyo suka had'a ldo ta tab'e baki "wlh nikam innaga anyi abu fad'a zanyi lnkuma ba'ason lnfad'a sai dai abari, ai ko auren ma kukayi nasan abunda zakuje kunayi kenan k'afansa ya d'aga da sauri ta juya ta shige d'akin lya da gudu, alokacin lya tana kallon labarai tana gyangyad'i taji anruntumo d'akin firgit ta mik'e tana nima wurin b'uya "Lfy Khadijah meye ya biyoki? Ko kinyi mafarkine? Sai da ta zauna akan gado kafin tace Likita ne lya ki Rufe k'ofan.
Iya ta zaro ldo Likitan ya dawo abun tsokananki ne?
Anya Khadijah ki mai da Hankalifa ni matsamin ln kwanta Bacci nake ji gara ke, lnkin gama ki rufe min k'ofan.
tana tsaye awajan Har lya ta fara Bacci, ta gefen labule ta lek'a