Showing 42001 words to 45000 words out of 155892 words
kaita da alamu kayan ciki basufi sati dasawaba komi sabone dal ad'akin abakin k'ayataccen gadon dayasha gyara ta zaunar da ita,
Ta jawo stool d'in Mirrow ta zauna tana fuskantan ta.
"Haba Khadijah uwata!! Kinzo konimana bakiba kinacan cikin 'yan'uwanki kin shareni nikuma inannan ina d'okin ganinki,
Murmushi Dijah tayi tana bin d'akin da kallo zuciyanta sai Harbawa yakeyi da sauri2 Haka kawai yau kuma taji wani iri game da Mamin Anyah kuwa Maganan mutanen garinsu bazai tabbataba irin wannan Gida? Ashe haka suke rayuwa shine har suke iya zuwa Rugansu suna zama.
Gaskiya itama yaukam tana ganin sayar dasu za'ayi dukansu,
Mami ta kamo hanunta kaman tasan abun da take tunani tace "ki kwantar da Hankalinki Khadijah Bazamu tab'a cutar dakuba insha Allah.
kusa aranku kowa da yanda Allah ya tsaramasa Rayuwansa wannan shine banbancinmu daku ba wani abuba, kinji ko?
Dijah ta gyad'a kanta tana cigaba da kallon d'akin a tsorace Mami tace ina zuwa ta fita Dijah ta tashi tana k'are ma d'akin kallo ahankali tana taku, har ta iso gaban Mirrow ta lek'a azatonta taga fuskanta sai kawai taga wata matashiya atsaye ta hard'e Hanunta tana kallonta gefenta kuma watace atsaye amma bata ganin fuskanta, arazane tasa tafin hannayenta ta Rufe Fuskanta ta tsala ihu mai tsanani da sauri Mami da sauda sukayo kanta Mami ta rik'ota "Khadijah menene?
"wayyo Allah na don Allah amaidani wajen Baffana wlh bazan sakeba Don Allah ku maidani,
"wai meye kimin bayanimana khadija??
Aljanu nagani acikin Madubi don Allah kukaini Baffa yamin Ruk'iya.
Mami ta dad'a rik'e Hanunta "ba Aljanu kika ganiba Khadija mune,
"wlh banyardaba waima kud'in ta ina kuka shigo waiyo na shiga ukuna.
Duk maganan da takeyi idonta arufe takeyinsa cikin kuka,
Sauda ko me zatayi inba dariyaba,
Dak'yar Mami ta shawo kan Dijah har ta yarda ta bud'e idonta, "Munshigo munsamu kina kallon d'kinki Khadijah shiyasa muka tsaya muna kallonki, Mu kika gani a madubin ba Aljanuba kinga wannan tanumata Sauda ita kikagani a mdubin ko ba itaba?
"itace to amma ta ina kuka shigo?
"ta k'ofa muka shigo Khadijah ki kwantar da hanakalinki,
Nan d'akinkine ke kad'anki na kawomiki k'anwanki ta gwada miki yanda zakiyi wasu abubuwane, kallon sama da k'asa tayima Sauda sannan ta kalli Mami "Wannan gundu memiyance k'anwata?
"Af Addanki ce na manta, Sauda ki nunamata yanda zatayi amfani da bayan gidan tayi wanka ga kayanta akan gado intafito tasa sai kuzo muci Abinci, daga Haka ta juya ta fita.
Sauda tana Murmushi tace "zomuje Beutiful girl kina da kyau Amma don Allah karkisake yin irin wannan k'aran daga gani kinsaba da shine ko? Kanta ta girgiza har yanzu atsorace take cikin 'yan mintuna kad'an, sai ga Dijah ta koma Khadijah tare suka fito suka tarar da Mami akan Dinining suna waya da Kabir,
*Kuyi hak'uri Fans bayawa wlh inacikin damuwa pls pray for me* ππΌπ
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
*Masoya masu k'irana sumin Addu'a da masu min massage na gode sosai kuma Allah ya biya muku Buk'atunku na Alkhairi nagode sosai Ummu Fatima taku ce* π€π»π€π»
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 2β£5β£
Sauda ta jawo mata kujera ta zauna tafara saving nasu, sai da tagama zuba na kowa ta zauna dai2 lokacin Mami ta gama wayan ta kalli Dijah ta ke takure acikin kujera "Kici Abinci Khadijah, nanfa gidankine kidaina d'ari2,
Haka suka ci Abinci Mami tana musu Hira jifa2 takansako Dijah aciki dak'yar tad'an saki jikinta,
Rana ta farko arayuwan Dijah data kwanta dasunan Barcin dare ad'aki ita d'aya gaba d'aya jitayi d'akin yamata mugun girma Allah sarki Bintalona ta fad'a tana share guntun Hawayen da yagangaromata, juyi ta dinga yi ahaka har bacci yayi gaba da ita.
Washi gari akaci gaba da shagalin buki yayinda Mami tad'auko masu Gyaran Amarya nagaske duk abunda akyi wa Amarya Mami tasa anyima Dijah,
Kafin yamma inkinga Amarya da k'anwanta bazaki ganesuba gaba d'aya kamanninsu ya canza, aharaban Gidan aka gudanar da tsararren Walima daya d'ibi maza da Mata,
Angoda da Amarya sai Haska waje suke kaman wasu taurari, sai daf Magriba aka tashi,
Duk abunda akeyi Dijah tana takure akan kujera dama ita ba gwanan shiga taroba, gawani Kwalliya da akamata gaba d'aya tana jin fuskanta yamata nauyi, tun daga nisa tajiyo Muryan sani yana k'wala mata k'ira ta tashi ta isoshi sai Kallonta yakeyi yana murmushi "Khadijah kece haka gaba d'aya banganekiba? Murmushi kawai tayi tace " ya Sani kaima ka ganka kuwa da muryanka kawai naganeka,
Kai da Bintalo sai kace ansakemu ku wani k'ira. Sani yad'an had'e rai "ke Daga yau nasoke wannan Sunan Aunty Fatima zaki dinga cewa ba Auntynki bace ba,
Dijah ta k'yalk'yale da Dariya "ok dariya ma nabaki? Insake jin sunan abakinki,
Zo muje kigaisa da su Hajiyata, yana tafe tana binshi abaya suka shiga pert d'i n da 'yan'uwansa suke, sosai Hajiya taja Dijah ajiki, tajima awurin suna Hira,
Harsaida Mami tanimeta.
Bayan Walima ba abunda aka kumayi awajen don Mami tace Albarka ake nima baza'ayi abunda yasab'a ma shari'a ba,
Sai washi gari aka kai Amarya gidanta tare da Rakiyan 'yan'uwata, Bakaramin kokari Mami tayiba
Wajen tsara gidan Amarya komi yaji saidai fatan Allah yaba da zaman lfy,
Washi garin kai Amarya ne 'yan'uwanta da 'yan'uwa Ango sukayi shirin komawa Garinsu, lokacin dasukazo tafiya and'an fafata da Dijah don tace sam Baffanta bai Amince ta zaunaba,
Harsai da Mami ta k'irashi awaya aka bata yace mata ta kwantar da Hankalinta zai zo ganin d'akin Amarya daganan sai su dawo tare (kamar yanda yake a Al'adan garunsu bayan Amarya tacika Sati BabππΌπ
anta yakanje ganin d'aki,)
Da kad'an kad'an Dijah tasaki jikinta da Mami sosai yanzu take jin dad'inzaman gidan haka tafannin abubuwa Sauda tana koyamata Sosai, tare suke shiga kicin da Mami suyi Abinci kasancewan dama Dijah bata da son jiki shiyasa ta dage kafin tacika wata uku ahanun Mami tuni ta goge ta iya abubuwa da dama, time to time takanbi Sauda suje gidansu nanma bak'aramin Experians take samuba, Mahaifiyar sauda tana bata kulawa sosai don haka tazamo bata da matsala
Dijah tana da wata Hud'u cif Mami tasamamata gurbiny karatu a Polytechnic,
Ita da kanta tad'auketa a mota takaita har cikin makaranta wajen Aminiyanta da take koyarwa a wajen takaita Malama Sadiya, a Office tasameta ta tareta da fara'a suka gaisa,
''yau wata Rana Hajiya Fati kece a Office d'ina?
Gaskiya baki da kirki gaba d'aya kingujeni,
Mami tayi dariya tace "yanzumma bahaka kawai nazoba nakawo miki Amanar 'yatace, gatanan tana nan Depertmen d'in Mass communication,
Malama Sadiya ta kalli inda Dijah take "Masha Allah Hajiya Fati 'yar waye?
"yatace pls don Allah inaso asamata Ido kinga Bak'uwace batasan kowaba kar abarta da k'awayen Banza,
"Ok bakomi akwai 'yata Nana zanhad'asu surik'a zama tare,
To nagode Mami ta fad'a tana mik'ewa dukansu tare suka fito suka tsaya ajikin Motan Mami,
Malama Sadiya tak'ira wayan 'yarta, ba'a jimaba sai gata tazo wajen, kallo d'aya tayi ma Dijah tahau yatsina fuska saidai tagai da Mami cikin girmamawa,
Nan mahaifiyarta tagabatar mata da Dijah amatsayin Sabuwar k'awa sannan ta gargad'eta da kar tabarta tayi k'awance da wasu shashashun k'awaye,
Mami tadafa kan Dijah tace "Khadijah kikula kinji? Kiyi abunda yakawoki, inkuntashi Driver zaizo ya d'aukeki akwai no. sa awayanki sai kik'irashi, cikin girmamawa tace mata "to"
Nana tana gaba Dijah tana baya ahaka suka isa ajin,
Nana tak'arasa wajen K'awayenta tad'an sukuya ta musu magana akunne gaba d'aya suka kwashe da dariya suna kallon Dijah suna nunata da yatsa,
Wani irin malolon bak'in cikine ya ziyarci Dijah.
*pls Karku manta dani cikin Addu'o'inku inkayi ma d'an'uwanka musulmi Addu'a mala'iku zasu maka kutaimaka 'yan'uwana*
*Nagode Nagode Nagode*ππΌ
Mmn temah π
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π³π¬
*Gaisuwa Gareki* *Maik'rago* π
*Maryam Tijjani*
*My Bysty Mmn Hydar*
*Mmn*βπ»
*Balkisu* mai gadon Zinareπ€
*Kemxee* πππ
*Allah yabar k'auna*
*Hajara sarkin complain ai ban isa inyi tuya inmanta Albasba kema kina nand'ina* β€
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
*page* 2β£6β£
Ab'angaren Nafisa kuwa, bayan Dijah ta shiga d'aki Mami ma ta haura Sama,
Afusace Nafisa ta tashi batare da taci Abuncinba, ko jakanta bata d'aukaba, haka tafice batako bi takan Motan da yanzu ta matsa ma Dadynta yasayamataba, don batason Mamin ta fahimci tayi Fushi asiyasa take sonbinta, okada ta hau ya sauk'eta har cikin Gidansu, ko kud'insa awajen mai Gadi yakarb'a dam batako bi takansaba tayi wucewanta,
Afalo ta tarar da iyayen nata kowannesu yayi tagumi, kowa danashi damuwan jikin Mamanta tafad'a tasaki kuka mai tsanani.
Tunkafin su tambayeta cikin Kuka tafara magana.
"Mama banagaya mikiba wlh Mamin Kb ce tahana shi ya Aureni, Duk son da datake nunamin na k'aryane yanzu abu kad'an sai tanimi tab'atamin Rai nidai wlh inban Auri Kb ba Mutuwa zanyi zankashe kaina.
Afirgice dadynta ya taso yazo kusa da ita "a'a Nafisa kidaina wannan furuncin ke d'aya yanzu nake gani inji sanyi araina Anyi ma d'an'uwanki Asiri inaji ina gani yanzu yamin Nisa,
Kidaina furta zaki kashe kanki, Waye Kabir? Da Har zaki kashe kanki akansa, Muddin yadawo k'asannan bashi da mata sai ke ninagayamiki wannan.
"gayamin me Maminsan tamiki yanzu? Mamanta ta tambayeta, cikin b'acin Rai.
K'arya da Gaskiya Nafisa tafad'amusu afusace Maman ta tashi tana surfa Bala'i "Barinje insameta, lallai Fatima tasamu waje, Duk zuri'ansu bawanda zata kawo ya fiki gadara da wannan gidan keda Gidan Ubanki, shine har zata d'ora wata kucakan k'auye akanki dan samun wuri.
Yau za'ayita ta k'are Kabir kuwa kinma aureshi angama ko tak'i ko taso.
Tana yafa gyalenta zata fita Alhaji ya'u ya kamota, "Karkiyi haka Rabi kefa kika shirya komi ko kinmantane?
Kiyi Hak'uri har plan d'inmu yagama shiryuwa, k'iris yaragefa.
Wani Dogon tsaki taja tace "Wlh daka barni naje naci mutuncinta tukun, naga batasan kawaiciba.
Kunnenta ya matso yagaya mata magana, komawa tayi tazauna tana Murmushi tajawo Hanun Nafisa da ta baza ido da Kunne tana sauraransu.
"kiyi Hak'uri Nafisata kwana kad'an yarage Mafarkinki yazama Gaskiya zaki Mallaki Kabir yanda kikeso Kinji?
Ta gyd'a Kanta Alaman Eh sannan takalli Maman, "Wlh Mama sai Naci Uban wannan yarinya "yar k'auyen tun Randa nafara ganinta naga tanamin Kallon Raini, Natsaneta Kuma wlh sai na gyaramata zama.
"Eh karkiyarda wata 'yark'auye takawomiki Raini, keda Gidanki, ayanzu kinmafi ita Fatiman Gadara da Gidan da kin Auri Kabir Magana ta k'are Gida yazamo Naki.
Wani Murmushin Farin ciki tayi don Aduniya ba abunda kesata cikin farin ciki irin ace da ita Matar Kabir.
Dahaka ta tashi takoma dan dama da shirinyin kwanaki taje Gidan.
Sannu Ahankali Rayuwa take nisa ma Dijah.
Rayuwa takeyi cikin Aminci a gidan Mami dan ba k'aramin kulawa take samuba ta kowani ab'angaren Mami tazamomata katanga sosai Dijah ta Kile tawaye, ta ko'ina, ab'angaren karatuma sambata da matsala tanasamun kulawa tanan fanni awurin Jamila da Auwal dayagama macewa a Son Dijah tun yana iya b'oyewa har yafito dashi fili itama tun tana sharewa Har tabada kai bori ya hau, ma'ana yanzu acikin school bawanda bai san da soyayyan dake tsakaninsuba.
Yau Juma'a shine Ranan da suka kammala jarabawansu na karshen 1semester.
Ajere suka Jeru da Jamila suka fito bakin gate suna tafiya suna tad'awa d'an Gefe suka samu suka zauna, sai Ga Auwal, tunda Dijah tad'ago ta kalleshi yana mata Murmushi ta sunkuyar da Kanta, yad'an matso, yace "Aunty Jamila Don Allah kitaimaka min Khadijah tak'i ban Adress d'inta Har yanzu, gashi anyi Hutu yakamata ace na isa cikin Gida Ansan dani aiko?
Jamila tayi Dariya "Kar kadamu Auwal a duk lokacin daka shirya kazo zand'auke ka inkaika har Gidansu,
"Kai Jamila Amma wlh nagode sosai banda kamarki, Barinje ana jirana sai munyi waya daga Haka ya wuce,
Dai2 Lokacin driver yazo d'aukan Dijah,
Jamila tace "to Khadijah sai munzo Dijah tana dariya tace "Wlh Jami ni kunya nakeji to inyazo sai ince ma Mami Me?
"Anzo Hira wajenkiman ko kinfison sai ya turo yafara Zuwa?
"Zandai yi shawara pls karki wani kawoshi, zanyi magana da Sauda tukun.
"to sarkin kunya Inajiranki Dariya kawai tayi tashige Mota.
Tun shigowansu Dijah take bin Gidan da kallo bak'aramin Gyara akayi ma Gidanba ad'an fitanta daga safiya zuwa yanzu har Anfente gidan tsaf ga gyaran Da 'akayiwa furanni abundai ba acewa komi.
Ak'ofar dazata shiga ciki tayi kicib'us da Nafisa, kallo d'aya zakamata ka fahimci tsantsan Farin cikin datakeciki, ta gefe Dijah tarab'a zata wuce, cikin zafi Ta fincikota tayi baya da ita, tana zabga mata Harara,
"ke wai me kika takane? Gidan na Ubanki ne? Dahar zakizo ki bugeni ki wuce?
Indan nace bazaki shigaba kin isa kishigane?
Taja dogon tsaki ta d'ora da Banza 'yar k'auye kawai, tajuya fuuu ta shige tabar Dijah awajen tayi sakare tana kallon Hanyan databi.
Kusan Minti biyu sannan tashige ciki, kai tsaye d'akinta ta shige da Abu biyu aranta na farko abunda Nafisa tamata na biyu tana mamakin yanda Gidan yakoma hatta Falon ancanza masa komi.
Tashige d'akinta komi na d'akin ancanza zu yasha gyara komi fes2 sai k'amshine ke tashi ga Mamakinta har suturanta ancanza mata sabi tun daga English wears, Harsu Atamfofi.
Kan mirownta cike da kayan kwalliya iri2
Ta fito daga wanka kenan taji ana Nocking ba k'ak'k'autawa, da sauri ta tashi tanufi k'ofan, ta bud'e.
Tsohuwace fara fat doguwa da ita kallo d'aya zaka mata kasan data zuba kyau da gayu alokacin K'uruciyanta, wayayyiyace sosai da sosai Sannan Hutune ya ainihin b'oye shekarunta, don Azahiri ta manyanta da yawa.
Irin Kallon da Dijah take binta dashi ne yasa tsohuwa d'an had'e Fuska, Tace "kebaki iya tarban bak'oba ko?
Ko dayake lefin Uwankince data Aiko batazo da kanta tace kije ki gaida Uwar gidankiba.
Barinje inturo miki ita.
Daga haka ta juya, Murmushi Dijah tayi sosai ta tuno mata da Goggoji.
Tana shirin Rufe k'ofan kenan Mami ta iso.
"Khadijah tund'azu naturo Nafisa tak'iraki Kizo ki gaida Iya bakizoba har tagaji ta biyo sawunki.
Kame2 Dijah tashigayi don ita ko idon Nafisa bata ganiba balle tace tazo.
"Maza shirya kizo Kugaisa, inajiranki anan to tace,
Sannan tajuyo tana dariya gami da d'an yarfe Hanu Mami Sabbin Kayan wadrop d'innan duk nawane?
"Eh Nakine Khadijah duka, wasuma suna Gun d'inki, cike da Murna tace Nagode Mami Allah yasaka da khairan.
Ameen Shiga kisako kayan kisameni ad'akin dake gefen nawannan, kar iya tayi Fushi Mahaifiyar Dadyn Kabir ne yau da safe tazo taryansa.
Af na manta bangayamikiba, Gobe insha Allah Kabir zai dawo zasu taso da Asuba.
Daga Haka Mami ta wuce tabarta tsaye awajen Kimanin Mintuna 2 Dijah tana tsaye a wajen tarasa mema zata Tuna dan ita azahirin Gaskiya ta Manta da Kabir.
Cikin mutuwan Jiki ta zira douwar Riga na Material fari mai Jajayen flawowi tayi Rollin da jan gyale, tafito Shar da ita Fuskanta ba Kwalliya ta nufi d'akin da Mami tagayamata.
Tun shiganta iya take tamata tsiya kin wani saka jan mayafi sai tashin Tirare kikeyi ancemiki zaki tsoratanine?
Itadai Dijah Murmushi kawai takeyi suka gaisa nanfa Hira ya kaure dandai Iya badai Tad'iba kam, Gata da saurin sabo, da Mai da d'an wani nata, tana da dattako da kara, sosai Dijah taji dad'in Hiran nasu tasake da ita sosai tare sukaci Abinci.
Da dare yayima anan Dijah tace Mami tabarta su kwana.
Labarai kam Dijah tashasu duk yawancin Labarin na zaman takewanta da Mijintane, Dijah kam daga baya lbrn kunya yake bata dan haka tayi bacci ba shiri.
Dukda dogon Hiran dasukayi bai Hana Iya tashin yin Nafilanta datasaba Na dareba, har aka fara kiran sallah Asuba sannan tad'aga Dijah, tare sukayi Salatul fajri Wanda Manzon Allah (S A W) yace yafi Duniya da Abunda ke cikinta.
Bayan Sun ldar sukayi karatun k'ur'ani tare.
Sosai Dijah tayi mamakin yanda tsohuwan take Fitar da Kartun k'ur'ani mai Girma.
Shida dai2 Dijah tafito gaida Mami bak'aramin Mamakin ganin Mamin a kitchen tayiba awannan lokacin.
Bayan tagaisheta tace "Mami Da Asubannan kika shiga kitchen? Yaufa Asabat ne pls Mami kije ki huta.
Da Dariya Mami ta kalleta tana tuno complain d'in Kabir duk lokacin da yaganta da safe haka.
"yau Kabir zai dawo Khadijah shiyasa nashigo dakaina inshiryamasa Abinci yanzu haka yana jirgi.
Jinjina Kai Dijah tayi tana Mamakin irin wannan Soyyaya na d'a da uwa.
Tare sukayi komi suka gama, Dijah da Indo mai aiki suka shirya komi akan Daining, bata jira komiba ta wuce d'akinta tahaye gado dan tsaban bacci take ji taso tayi wanka amma ina Bacci yaci k'arfinta.
Wajajen Goma dai2 ta dinga jin hayaniya acikin bacci tashi tayi tazauna tana mutsikke ldo, Sai