Showing 138001 words to 141000 words out of 155892 words

Chapter 47 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

447

inma wacce yake nimanta kawai badan zai auretaba, anma zakiga yana sauraranta fiye dake da kyawawan kalamain da bakisanma ya iyaba,


Ikon Allah kuma sai kuma kiga matansu basu ragesu da komiba, sannan suna hak'uri da duk yanayinsu, tunda sun san ibada sukeyi,

Bare naki da da bahaka yakeba, kiyi hak'uri kiyi ta Addu'a sannan kar kigajiya da hidima dashi Allah baya barci yana kallon abunda kikeyi kuma komi nada k'arshensa wata rana zaki bada labari kai inma ke baki bayarba wasu zasu bayar kuma hakan ba k'aramin riba bane gareki kinji Khadijana!!

Inkad'aici ya dameki d'auki Qur'ani kiyi ta hira dashi ko wani Harafinsa lada Gomane, inkin juri hakan bazaki tab'a tab'ewa ba, ta k'arashe tana dafa tsakiyar kan Dijahn,


Dijah tasa hanu ta share Hawayen da yagama wanke mata Fuska cikin jin Sanyi lafuzan na Mamin tace "Nagode Mami Kinkasance Uwa ta gari ga 'ya'yanki ba abunda zance dake sai dai Allah yamiki sakayyah da gidan Aljannah Allah yabarmana ke, lallai da haka ko wace uwa take dagewa wajen d'ora 'ya'yan kan Hanyan kad'aita Allah da biyayya gareshi da dayawan al'umma basu tab'eba,


Mami Tace "Ameen "anma kisani Allah baya barin wani dan wani Khadijah ni zan wuce, ta ciro rafan kud'i ta ajiyemata,

Zata tashi sai taga kaman bakin @yar nata da magana, ta koma ta zauna, tace "me kike son fad'ane Khadijah baki da kamana duk garinnan ki d'aukeni abokiyar shawara kuma abokiyar Sirrinki,


"Dama Wata yar Jamila k'awatan nane jiya dasuka zo,


Ta kwashe duk yanda sukayi ta gayamata, cikin mamaki Mami take bin Dijahn da kallo, Ta girgiza kai da ta tuna Dijah yarinyace k'arama, ta gyara zama sosai tana kallonta,


"Khadijah ko bayan bani da Rai inamiki wassiya da kar kiyarda da niman wani abu awajen wanin Allah wannan shine mafi girman kure da zaki tafka a rayuwarki,


Kar kiyarda da irin wa innan mutanen da suna ganinki zasu gayamiki magana makamancin wanda wannan tagayamiki, kisani duk wani mutum mai aiki da Aljanu wlh boka ne Ko yace shi ba boka bane k'aryane, bawanda yasan gaibu sai Allah, kai ko niman magani kike irin nagargajiyannan kikaje gun mai magani yana ganinki bai bari kin fad'i matsalarkiba yacemiki yasan abunda ya kawoki to wlh Boka ne,


Kai inma ba Dagaske suke aikinba to 'yan damfarane so suke du yaudareki suci kud'inki, kinga sunyi riba biyu dake sun rabaki da kud'inki, sun rabaki da imaninki, inafata zaki kiyaye, kar kuma kishiga wata jarabawan da zai sa ki kauce hanya,

Dan mafi munin jarabawa kenan Ajarrabeki ki kauce hanya, Allah ya karemu ya kare Imaninmu,

Asanyaye Dijah tace "Ameen Mami, dama nak'iyarda nace sai na sanar dake,


Atare suka fito cikin hikima Mami take cigaba damata Nasiha,


Mami tana shirin shiga Mota, motar Sani ya danno gidan,

Mami ta gyara tsayuwanta tanason sugaisa kafin ta wuce,


Yana perking ya fito, Ya isosu cikin Girmamawa, Ya gaida Mamin, Khadijah ta gaisheshi,

Mami tace ya Binta da Maigidan nawa suna nan lfy ko?

"Eh suna lfy Mami,

"To Alhamdulillah daga ina kake haka?
ya gyara tsayuwansa, "Wlh tun d'azu KB yamin waya akan wai zai tafi Abujah, ban samu na fitoba, ina kwance bani jin dad'i,


Anma yanzu afujajan Nafito, ina kwance naga Binta ta d'auki wani abu a hanunta zata fita dashi na tambayeta meye? Sai kawai ta nunamin wasu layu wai a d'akin Khadijah suka samu ak'asan katifanta tun Ranan da taxo sai yau tace bari ta k'onasu,

Abun yaban tsoro nadinga tunani har na tuno wani Rana da mukazo gidannan naga Nafisa da Mamanta Acan bakin gate Cikin yanayin rashin gaskiya bayan na fito sai naga alamun kaman antone wajen, anma wlh bankawo komi arainaba, duk da ban yarda dasuba, sai dai yanzu da naga layunnan nafara wasu tunane2 musamman dana tuna yanda lamuran Dr KB suka rikice gaba d'aya,


Mami ta sauk'e ajiyan zuciya tana kallon Mototin cikin gidan,

Yanzu haka Kabir yatafi Abujah bansaniba?

"Kiyi hak'uri Mami kinsan da bahaka yakeba, d'azu yatafi ko minti 20 baiyiba inaga inma kinjima agidannan to kina nan ya tafi, Mami tayi Murmushi mai ciwo, "ba komi Sani ai na godema Allah ma, yanxu har yana zuwa wajena kuma yakan gayamin abunda yakeji har yace inyita masa Addu'a ai Allah yakawo k'arshen Abun insha Allah dama wai ance cutane ke shiga farat d'aya sauk'i sai ahankali,


"Hakane Mami ni yanzu zan duba ko Allah zai sa indace da inda aka saka abun,


Mami tace "Muje Allah ya datar damu,

Sosai Sani da Sceurityn gidan Suka duk'ufa da tono anma basu samu komiba, tun Mami da Khadijah suna tsayuwan jiran sugani har Mami ta gaji,


Cikin karaya tacema Dijah ta shiga ciki itama zata tafi, in Allah yasa ansamu Sani yagayamata Awaya, dahaka sukayi sallama da juna,



*Ummu Fatima ce* 😘
[10/20, 5:18 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


_Godiya mai tarin yawa gareku masoya Ummu Fatima Alhamdulillah Yarona yasamu lfy masu k'ira masu Text Mus'ab ya gaida Mummy's da Aunty's jiki yayi sauk'i_

*Group d'in Ummu Fatima ku nadabanne* ❀

*Zainab Jibrin & Meera* πŸ‘πŸ»



7⃣3⃣


Dijah tana Zaune Akan Sallahya tun bayan da ta idar da Sallah Ta Rafka tagumi tana sauraron Maganganun su Sani a Farfajiyan Gidan, da alama basu samu abunda suke nimanba, Tanajin Fitan Motan Sani Ta sauk'e nannauyan ajiyan Zuciya Hawaye na tsiyaya a idonta, ta Rumtse Idonta da K'arfi, tasa bayan Hanunta ta share Hawayen gami da Jingina kanta da Gado a hankali take karanto Addu'o'i, tana a haka har a kayi Isha'i, ta tashi tayi Ishan, ta d'ora shafa'i da wutri, Ta shiga Bayi ta sallo wanka ta fito Humra kawai ta shafa ta zira Rigan Baccinta, tana zaune a bakin Gado tana karanto Addu'o'in Bacci k'iran Mami ya shigo wayanta,

Sai da tashafa sannan ta d'auka gami da karawa a kunnenta, tayi Sallama,


"Hallo Mami ina wuni?"
"Lfy Khadijah, kinci Abinci kuwa?"
"Eh Naci Mami"
"Good to kiyi Addu'a ki kwanta ki kwantar da Hankalinki Khadijah ba Abunda zai sameki da yardan Allah, kinji ko? Duk abunda yasamu bawa da sanin Ubangijinsa kinji?

Dijah ta gyad'a kai Gami da cewa "tou Mami,


Tayi ta bata baki da Magana mai kwantar da Hankali, Da haka sukayi Sallama, Dijah taja Bargo ta rufa gami da Lumshe ldonta, Lallai tasani ta fad'a cikin jarabawa, anma ba wanda yafi tsayamata irin Rashin Jin Mijinta kusanta kullum da kewanshi take kwana take tashi, Takan Rasa Abunda ke mata dad'i,

ta lumshe Idonta ta bud'e "Ya Allah gani gareka tafad'a afili tana gyara kwanciyanta,


****
Washi gari Dijah tana zaune a cikin lambu ta Rafka tagumi tana kallon tsuntsayen da suke ta d'an kaiwa da kawowa a wajen, su sauk'a su tashi,


Daga d'an can nesa taji anafad'in "Wlh yau za'ayita ta k'are Duka zanmata har sai shegen cikintannan ya fita kowama ya huta, Inga ta iskancin wancan Guzumar, dan nasan shi wanda aka lik'a masa cikin ko ajikinsa, wai antsakari kakkausa,


Dijah ta k'ura ido ma Hanyan da ta jiyo Muryan Nafisan, tana mai niman tsarin sahrrinta a zuciyanta,

Rik'e take da K'atuwar Dorina, gefenta meena ce sai dad'a zugata takeyi, kallonsu kawai Dijah takeyi Har wani tsima jikinta yakeyi, Wai ita Nafisa zata buga da wannan Dorina? Tayi wani D'an Murmishi tana jinjina kai,


"Ke k'aramar mara kunya wani d'an iskan kikasa ya tonemin gida haka ba tare da niman izininaba? Shegiya 'yar masu tsubbace2 to koma meye kikasa aka dasamin a gida, Wlh yau sai kin tonosu da Hanunki, kuma ingayamiki ni nafi k'arfinki duk wani Asirinki nan zaki ganni daram ki barni,


Dijah da ta hard'e Hanunta a k'irjinta tana d'an jefa k'afa tayi Murmushi Mai Sauti, Gami dacewa "A'uzubillahi Minnashshaid'anirrajim, Allah ina niman tsari da kariya a wajenka dan kaine mai iyawa,


Meena ta waro ido tana Kallon Nafisa,

"Gaskiya Nafze kinyi sake da yawa har wannan kucankan k'araman yarinyan tasamu daman gayamiki magana irin haka?
Gaskiya kinyi Bacci da yawa, wlh danine da tuni na sallmaeta Aduniyanma baki d'aya, Haba Kinyi sake wlh,


A Hasale Nafisa tayo kan Dijah "Dan Allah meena daina fad'an Haka, karki tunzurani inkashe banza, yanzu da wannan shegen cikin tukun nakeyi banzo kansuba tukun ita da wancan da ta d'aure mata Gindi, Ke tashi kije ki tono abu da kikasa nace ko baki jine?

Wani Murmushin Dijah takumayi ba tare da tace Komiba,

Nafisa ta d'aga Dorina tsakaninta da Allah zata zabgamata, cikin zafin Nama Dijah ta rik'e Dorinnan ta tashi tsaye Rai ab'ace take kallonta

"Yake Mushirika mai kai ma wanin Allah k'aran Allah, ki shiga hankalinki, ko yawon zuwa wajen Bokayen yafara tab'amiki Hankaline?
Ko dake najima da cireku a sahun Masu Hankali keda Baaba mai kaiki wajen Bokaye, kisani ni Da Mahaliccin Bokan na Dogara, Ban had'ashi da kowaba wajen niman buk'atana, Nasani bazan tab'a tab'ewaba, ko borin kunya kikazo mindashi dan kinga asirinku ya tonu angano Binne2 da kukeyi,

Yakamata ki Daddara haka kigane Wannan Hanyan bazata kaiki ko inaba sai Halaka, Kiyi tunani meyasa har yau baki samu yanda kikesoba? Meyasa ke kullum cikin Bak'in ciki da rashin samun biyan buk'atanki, Wanda kikeyi danshid'in Baida wacca ya tsana sama dake, anma kinkasa ganewa,

KI koma ga Mahaliccinki dan shine maiyi na gaskiya kuma baya gushewa,

Nafisa tasaki wani k'ara najin takaicin Maganganun Dijah ta finciki bulalan zata tsulamata,

A hasale Dijah ta fauce ta shiga tsulamata ido arufe, da tayi kaman zata kamata, zata hankad'eta tacigaba da zabgamata Ta ko ina, ba tare da tsoro ko tunanin wani abunba,


(Lallai Ba Barbariya tashiga Hanun Ba fulatana)πŸ€” πŸ€ͺ


Meena da take gefe ba k'aramin tsorata tayiba dan ganin yanda k'awar nata take kwasan kashinta A hanun yarinyan da suka raina, taso ta shigarmata sai dai tana tsoron kar itama amata taya2 da jiki irin na Nafisan, A dabarance tazo ta baya ta rik'e Dijah da iya k'arfinta ta kalli Nafisa da take ta mutsu2 a k'asa tana sosa wajen Bulalun

"tashi kiyi ta Dukan cikin shegiya har sai ya fashe abin cikin yayo waje,


Dak'yar da tangad'i Nafisa ta tashi ta dunk'ule Hanunta ta kaima Cikin duka ta sake d'aga k'afa ta tokari cikin, wani irin k'ara Dijah ta sake najin azaba,

Nafisa ta d'auki wani k'aton Dutse a wajen ta d'aga zata kwad'a ma cikin tana fad'in Wlh yau wannan shegen da bashi da Asalin sai ya fita shegiya Matsiyaciya,


Tasssssss!!!!!! Nafisa taji and'auketa da Marin da ya watso mata gilmawan wasu jajayen taurari Dutsin Hanunta ya fad'i akan k'afan Meena cikin azaba ta duk'a zata tab'a Gurin da jini ya faso a k'afantan, taji ansauk'emata nata marin itama, Ball dasu aka shigayi ba ji ba gani, tun suna iya ihu har suka kasa,



A guje yabi bayan Dijah da tafara takawa a hankali tana dafa Bishiya zata fita,


Ido Biyu sukayi dashi gaba d'aya yafita ahayyacinsa idonsa ya kad'a yayi jazur, Rana na Farko da Dijah taji wani irin Haushin Mijin nata har cikin ranta,


Ya rik'e hanunta ya kasa furta komi, ta k'wace Hanunta a guje ta nufi sashinta kaman batajin ciwon jikinta, ya Rufa mata baya, anma kafin ya kaimata tuni tayi ma k'ofan key,


Ya shiga buga k'ofan cikin tashin Hankali yana fad'in "plss Khadijah ki bud'e k'ofannan muje Asibiti a dubamin lfyn d'ana Dan Allah badon niba, ba yanda baiyiba tak'i ta bud'e ya dunk'ula Hanunsa ya bugi k'ofan ya juya ya nufo gurin su Nafisa,


Meena da ta hangoshi tayi ta maza ta mik'e tana d'ingisawa da k'yar ta nufi hanyan Fita, bai bi takantaba ya k'arasa gun Nafisa da take ja da baya tana girgiza kai "Kayi Hak'uri KB katsaya kaji abunda yarinyannan ta aikata,


A fusace yace "banson jin komi daga gareki Nafisa sakayyan da zakimin kenan? K'arfi da yaji zaki halakamin d'an da baizo na ganshi ya ganniba?

Me namiki da zakimin wannan sakayya?


Harkike Furtama cikin da akasameshi ta hanyan aure shege? Menamiki?


"Kayarda dani KB yarinyannan Amananka take ci inbakanan, kabani dama in kawmaka shaidu dan ka yarda, a matsayina na 'yar'uwanka bazan iya ganin ana ha'intanka invariba,


Kaduba jikina kaga irin yanda kwartonta yamin kadai san tana da Ciki bazata iyamin hakaba, bare kace sharri na mata,
Kasani bantab'amata k'arayaba,


Cikin wani irin bugun zuciya Kabir yabi Jikinta da kallon can kuma kaman an tsakaleshi yajuya da sauri ya fice,



Dijah tana kwance akan Kujera tana sharan k'ollah a idonta tana dafe da cikinta da yake ta juyi kaman zai fito ta cibinta ga a zabbaben ciwo da maranta ke mata,


Taji ana buga k'ofa, Tajiyo Muryan Mami tana fad'in "Bud'e k'ofan Khadijah nice yi Hak'uri ki bud'e kinji Dear,

ko d'aya baxata iya bijire ma Maminba dan haka ta tashi a hanakali tana bin gini taje ta bud'e arud'e Mamin ta danno kai cikin tashin hankali ta rungumota jikinta,


Tayi saurin zaunar da ita, dai2 Lokacin Dr Husna da KB suka shigo,

Dijah ta runtse ido dan sam taji batason ganinsa,

"Fita kabamu guri Mami ta fad'a,

Ba musu ya juya, Dr ta shigar da ita d'akin magani ta fara bincikenta,


Nafisa tana kwance a d'aki jiki da zuciyanta sai zogi yake mata tana rik'e da waya tana niman Layin Mamanta bata samu, ta nima yafi abunda yafi tasha Alwashin zata bar Nigeria dan ta nimo Bokan da zai mata yanda takeso dan taji lbrn wani Boka mai cika aiki Achadi, tagaji da aikin bokayen Nigeria ba wani ci gaba dan hat yau sun kasa samarmata da farin cikin da take buri,


Jin wayan a kashe yasa tayi jifa dashi tana ci gaba da kuka, Tana bin jikinta da ya farfashe da Kallo,


Can ta jiyo Ringing d'in wayantan ta d'aga sabon layine dan haka ta kara akunne batare da tace Komiba,


Taji ance "Nafisace?
"Eh itace ta Amsa murya a dishe,
"Maza kizo asibiti Antsinci wata mace da tayi hatsari A hanyan jos a daren jiya nidai inaga kaman Mamankice duk da tayi damage da yawa anma ki hanzarta zuwa dan likitoci sunce baza su tab'ataba har sai ansamu danginta yanzu haka tana kwance..... Ai Batakai gajin k'arshen magananba tayi Wurgi da wayan gami dasaka ihu ta fita a guje, sam masu gadi basuyi yunk'urin Hanataba, dan sunjima suna Addu'an ganin Ranan da Mai gidan zai rakota aguje haka, dan ta ishesu haushinta sukeji kaman su karta, a idonsu ake duk wani iyashege, Suna sane da komi da suke Haddasawa agidan ita da uwarta

*Manage pls har yarona yana manne dani sam baya barina ya tafi wasansa bare in d'an typer muku da yawa kunsan sha'anin yaro inyayi ciwo ko baya kiwuya zai tsiri yi*

Nagode da Addu'o'inku Masoyan Gaskiya Allah yasadamu a Aljannah inganku ku ganni πŸ‘πŸ‘πŸ˜πŸ˜


*Ummmu Fatimace* 😘
[10/29, 8:24 PM] Hauwa Jameel: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


7⃣4⃣


A bakin Hanya ta tsari mashin ta hau, kai tsaye a Asibiti ya direta bata ko tsaya bashi kud'iba kaman Mahaukaciya ta shiga ciki abunda ta ganine ya dad'a tayarmata da Hankali, Mahaifiyarta a kwance a barandan Asibiti kamar matacciya, duk wanda yazo wucewa sai yayi ta kallonta cike da k'yama ba tausayawa,

(ko me yajawo haka?πŸ€”)

Cikin matsanancin tashin Hankali ta fad'a kanta tana jijjigata tana kuka, Da k'yar taga ta motsa, daidai lokacin wani Likita yazo zai wuce, har ya d'an wuce ya dawo yana kallonta,

"Ke 'yar'uwartace?
A hargitse Nafisa ta tashi ta nufoshi,
"Eh... Eh ... mahaifiyatace pls Likita kataimakeni ashiga da ita a dubata,


Likita ya Girgiza kai Gaskiya bazamu iya dubataba, Dan akwai Harbi ajikinta damuka kasa gane na meye kinga tab'ata hatsarine awajenmu, Sannan munsameta da wasu abubuwa dasuka d'auremana kai,


Ido waje Nafisa take Kallonsa,
"Likita harbifa kace! Waya Harbeta? Wani Azzaluminne Mara tsoron Allah? Metayi? Kuma Wasu abubuwanne kukasamu ajikinta da zai Hana ku dubata? Pls Dr karkubarmin Uwa ta mutu anan, ta k'arashe cikin matsanancin Kuka,

"Zo Muje Office ki gani Ma Idonki, Dr yafad'a yana tafiya, kallo tabishi dashi, Har sai da ya shige Office d'in Sannan tabi bayansa da sauri,


Taja kujeran da ke fuskantansa ta zauna tana kallonsa, yajawo Wani drower ya fito da wani k'aton Leda ya juye akan Table, Yana kallonta,


Cikin mutuwan jiki da wani irin Kunya, take kallon abubuwan daga gani Ba tambaya wanda Boka yabatane, layune Manya2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login