Showing 18001 words to 21000 words out of 155892 words

Chapter 7 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

465

guard d'innasa ba'asamu lbrnsuba?
Uncle Musa yad'ago ya kalli Abban Habib, ya sauk'e ajiyan zuciya, dai2 lokacin wayan Mami ya hau ruri,
Nafisa sunan da yabayyana akan wayan kenan, d'auka tayi tasa ahans free cikin matsanancin kuka Nafisa tafara magana "Mami ashe ankashe yaya KB tun ran Asabar amma ba wanda yagayamin? Cikin tashin Hankali Mami tace "waya gayamiki wannan magana Nafisa?
"Dady ne yak'irani yanzu yake gayamin wai ahanyarsa ta zuwa Abuja aka kashwshi, kuma wai bai yarda inzoba wlh sai nadawo ko zai kasheni nabar England har Abada, Mami kam kusan suman tsaye tayi awajen, idonta taf k'wala, ahaka wayan yasulale yafad'i ta zube akan kujera tanayima yayanta kallon tuhuma,
"Yaya meyasa kuka b'oyemin Mutuwan Kabir? Bani na halliceshiba don me za ab'oyemin mahaliccinsa ya karb'eshi? Uncle Musa ya katseta da fad'in Fatima ki kwantar da Hankalinki wlh bamu samu lbrn mutuwan Kabirba amma bari muk'ira wanda akaji abakinsa, yalalub'o no. Alokacin Alhaji ya'u suna zaune da su Kila awani tafkeken Hotel suna pertyn samun nasara ganin mai k'iranshinne yasa shi tashi awurin dayake ya canza waje, bayan sungaisa Uncle Musa yace "Ashe kasamu lbrn mutuwar d'anka KB? Shine bakasanar damuba? Cikin firgici Alhaji ya'u yace "ni ni kuma? Ta ta ina kennan?
"mhmm yanzu "yarka Nafisa tayi waya take sanardamu kuma tace kai kagayamata,
Arud'e yace "no no bata fahimceniba bahaka nagaya mataba,
Kallon Kallo Uncle Musa da Abban Habib sukayi sannan yakashe wayan yana kallon Mami data zuba masa ido, dai dai lokacin Habib ya shigo bako sallama yazauna yana kallonsu "mmn Dady nasmu lbrn KB na yanzu akak'ira asibitinmu akasanardamu KB yana Yana national Hospital Abuja ai gaba d'ayansu mik'ewa sukayi suna k'ara tambayansa Mami kam sauk'ar da kanta k'asa tayi tana kirari ma mahaliccinta tana hawaye, bata majin mesuke fad'a ita dai taji yayanta yana waya murya k'asa2

"Fatima kitashi kishiga ciki yanzu zamu Je Asibitin garinnan muduba Sani daga nan kuma zamu wuce Abujan ajirgi sannan kuma ki iya ma bakinki, karkisanar da kowa cewa ansamu lbrn Kabir harsai mun gano masu hanu akan son salwantar dashi,
Asanyaye tace "wasune ko? Suka mishi wani abun?

"Ranan lahadi da azahar masu tsaronsa suka zo gidana suka shaidamin wasu sun tsaresu ahanya sun kashe mutum biyu acikinsu sauran sun kub'uta da k'yar da raunuka wasu kuma ba raunuka, amma basuga uban gidan nasuba shiyasa bazasu iya zuwa gidannan ba shine sukazo su sanarmin, nikuma nasanar masu Ibrahim, yanzu haka wanda suka samu raunin suna asibiti muna kula dasu sukuma ma matan munje ga iyayensu munsanardasu munmusu ta'aziya harda d'an ihsani,

Cikin tashin hankali Mami tace muje tare inga Sanin,

Tumdaga nesa da Mami ta hango Sani ta rud'e, kallonta yakeyi har ta matsoshi, sai mirmushi yake mata ta dafa jikin hadonsa tana kallonsa harsu uncle Musa suka gaidashi da jajan tawa, sam Sani baiji dad'in ganin hawaye afuskan Mami asanyaye ya k'irata tad'an sunkuyo tana kallonsa "laifin Kabir yashafeka ko Sani sunyi niyan kashe Kabir kaima sun nakasaka duk wannan gurbin harsashine haka ajikinka? Ta k'arasa maganan cikin kuka, Sani ya ya marairaita fuska yana kallonta yace "Haba Mami don ALLAH kidaina kukannan dagaske oga KB yana raye? Yafad'a da muryan kuka, Habib yadafa kansa yace "ka kwantar da hankalinka Sani nacemaka yana raye bak'arya namakaba yana Abuja yanzu haka wajensa zamuje, "Don Allah inkaje kak'ira wani da kasani a asibitinnan yabani wayan kahad'amu inji muryansa, "insha Allah zanyi yanda ka fad"an Allah yabaku lfy "Ameen mami ta amsa Abban Habib yace mata tazo amaidata gida tunda akwai masu kula da Sani, tak'i tace anan zata zauna, ahaka suka tafi suka barta har dare tana wajen sai wuraren 1:00 ta koma gida,

Awannan dare kam sam Mami bata rintsaba juyi kawai takeyi akan gado data rufe idonta Hoton Kabir take gani, gashi tun da rana a Asibiti tayi ta k'iran su uncle Musa Amma wayansu baya shiga sosai ta k'ara razana, washi gari kuwa tun safe tagama shirinta taje taduba jikin Sani daga nan tawuce air pot, tana shiga Abuja kai tsaye Hospital ta wuce,

Gadajen word d'in take bi da kallo can tahango sojoji da police ajikin wani gado k'ura musu ido tayi, abayanta taji ance Fatima tana juyowa ta ido biyu da yayanta yana dariya yace "kin kasa hak'uri ne? Duk da k'in nimanki danayi awaya, to zo muk'arasa ga gadonsa can jami'an tsarone ke gadinsa, suna k'arasawa da uncle Musa yagabatar da ita amatsayin mahaifiyarsa gaba d'aya suka watse suka basu guri, ahankali Mami take d'aga k'afa kaman wanda k'wai yafashe ma aciki, Kabir kuwa sai k'ok'arin k'ak'alo murmushin k'arfin Hali, yana kallonta duk yanda Mami taso ta daure abun ya gagara hawayen da taso b'oyewane suka hau sintiri afuskanta ta dafa goshinsa da d'ayan hanunta tana share k'olla da d'ayan tace "Sannu Kabir irin jarabawan da mukuma aka jarrabe mu dashi kenan, juya kanshi yakeyi ahankali ya d'ora Hanunsa asaman hanunta kaman zaiyi kuka yana kallo idonta, yace "Pls Mami ko mutuwa nayi bai kamata kimin kukaba, Addu'anki nake buk'ata Mami wlh wannan hawayankin yafi min raunukan jikina Mami,

Cikin sheshshek'an kuka Mami tace "wayene Kabir? Waye yake son ganin bayanka? Meka musu Kabir?
Kabir ya tura hanunsa ya jawo kujera yasaka mata ta zauna tana shafa gashin kanashi,

"araunane yace Mami wlh bawanda ya isa ya kasheni sai kwana na ya k'are,

Da son ransune da yanzu bana nan, amma kinga da Allah bai soba gani araye pls kikwantar da hankalinki Mamina yafad'a yana sharemata hawaye,

Mami ya lbrn Sani?
" yana Asibiti jikinsa da sauk'i har yafi naka,
"su Bala fa?
"Duk jikinsu da sauk'i, sai Alokacin Mami ta kalli su Habib da Abbansa suka gaisa,




Sannu sannu Su KB suke samun sauk'i da ikon Allah,

Acikin watanni Biyu duk wani raunuka ya warke Sani kam tuni har Ansallameshi Uncle Musa ya d'auleshi yakaishi Gombe campanin KB yace masa yazauna anan don haryanzu mutane basu san Ansamesuba,


Alokacinne kuma aka kunce karayan KB amma wani abun tashin hankali shine sam karayan bai d'oruba ba k'aramin tashin hanlali suka shigaba,

Ahaka aka sake wata d'aya aka kunce Amma baiyuwuba, ganin haka yasa Uncle Musa yace Asallamesu kawai zasu kaishi amasa na gida haka Kuwa aka sallamesu aranda zasu tafi police d'in da case d'in yake hanunsa yazo, cike da girmamawa yagaida Mami, ya tambayeta jikinsa,

Mami ta jinjina kai "jiki da sauk'i saidai karayanne bai gyaruba shiyasa zamu koma gida agwada na gidan agani ko Allah zaisa Adace, shiru yayi nad'an lokaci yace "kunada wanda ya iyagyarane?
"a'a gaskiya saidai zamu bincika
"acan k'auyen da nake aikinnan kuwa akwai wani datijjo wanda yazo yasanar mana lokacin da yagansu acikin mummunan halinnan ya iya gyaran karaya sosai don naji ance har daganan akan kaimasa masu karaya, ko zaku gwada kukagani?
"Abban Habib yakarb'e da cewa "Eh sai kawai mukaishi can awani garine? Wani Rugan fulanine can k'arshen Adamawa sunan Rugan Juma sunan mutumin kuma *Malam Bukar maid'ori* nan yagaya musu tanda akayi kafin akawo KB nan Mami tajinjina kai to Allah yasa Adace,

Uncle Musa yace "Ameen, tunda hakane kawai sai mufasa zuwa gidan ke Fatima Gobe in Allah yakaimu sai ki koma gida mukuma jibi sai mushirya mukaishi,


*Tirk'ashi masu kartu ga Dr KB fa yana shirin zuwa gidansu Dijah k'aya abokiyar Hamayyansa cab ga Shi wai ita Dijah bata mantuwa wai wani wainan za'a totane?*








*Ummu Fatimace* 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬

*ALLAH yabar k'auna*🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣2⃣


Ranan juma'a shine Ranan da za'akai KB Rugan Juma,

Basu samu flight ba sai wajen k'arfe uku,
a airpot suna sauk'a dama sunyi bucking Amubulance kasancewan k'afan bayi ko lank'wasuwa,

Basu suka isa cikin Rugamba sai da aka idar da sallahn isha'i,
suna shiga cikin Garin suka tambayi Gidan *Malam Bukar Maid'ori* ba wani b'ata lokaci aka kaisu,
ak'ofan Gida suka sameshi sunacin Abinci shi da mak'ocinsa Baban Jebu,
Uncle Musa ne ya musu sallama Hanu biyu suka karb'eshi hami da bashi wajen zama,

Bayn sun gaisa Uncle Musa yace "Munzo wajen Malam Bukar ne,
"Ayyah nine Malam Bukar, nan yasanar dashi abun da ke tafe da su, Mik'ewa yayi da sauri yashiga Gida "Dijah! Dijah!!
"Na'am ta Amsa da sauri ta fito,
"Maza d'ibi taburmai kije can d'akin Bak'i ki shimdid'a ankawo mara lfy yana fad'an haka ya juya yafita

a jikin mota yasamu Uncle Musa yana tsaye, "Bismillah kushigar dashi Habib da Driver da Abban Habibne suka d'aukeshi,
Uncle Musa da Malam Bukar suka rufa musu Baya dama Gidan k'ofa biyu yake dashi d'ayan K'ofan shine zai sadaka da cikin Gidan inda su inna suke,
sannan akwai k'ofan da zai sadaka da d'ayan side d'in ananne Baffa yake kwantar da marasa lfy,
kasancewan akwai wanda suke zuwa daga nesa,

D'akine ciki da falo wanda akayi da bluck d'in k'asa aka maasa Rufi da ciyawa irin dai d'akunan k'auye sai dai wanna yasha flasta sosai da flu na siminti uwar d'akinkuma har da Gadon k'asa a falo aka shimfid'a taburman
Suna ajiyeshi Habib yayi sauri yaje yad'auko blancket ya shimfid'amasa yasa pillow suka taimaka masa ya kwanta nan suka zauna aka sake sabon gaisawa Baffa yace sai in Allah ya kai rai da safe zamu fara aiki,

Shiga cikin yayi yasa aka kawo musu Abinci,
Habib ya matso kusa da Habib yana kallonsa "KB me kk son kaci?
"Nothing,
"to barin Had'ama tea
" bazan shaba kabarshi kawai
"naga kaman bakaso zuwannan ba kayi hak'uri insha Allah daka samu lfy shikenan,
"Gaskiya ni bana iya zama a duhu wannan shine kawai matsalata, wlh yanzu jina nake kaman a kurku,
"a'a baza abarka aduhuba ka kwantar da hankalinka,

Yauwa KB pls kayi magana da yarinyannan mana tadamu taji voice d'inka wlh tadameni seriously,
tsaki KB yayi ya kalli inda su Uncle Musa suke suna Hiransu,
"ko zamuyi magana badai yauba sai ka bari da safe, daga haka ya mai da kanshi ya kwanta,

Washi Gari tunda safe Baffa yafara had'a magungunan da zai masa d'auri,
Bintalo da Dijah ne suka musu abun karya, Doya Baffa ya sayo akasoyamusu aka dafa musu Ruwan shayi da yasha kayan k'amshi, Inna ta jere ma Dijah a k'aton tray takaimusu, a falon ta samesu dukansu KB da Habib suna kwance Uncle Musa da Abban Habib suna zaune suna Hira, cikin kunya irin nata ta gaidasu dondai duk tsiwan Dijah takan ji kunya maza sosai, Uncle Musa yace meye Sunan ki "yanmata? Dijah tafad'a tana mik'ewa, "a'a asai dai uwatace guda awajen, sannu ko uwata ita dai murmushi kawai tayi tafita,

Abban ya d'aga su KB ya gabatar musu da abun kari, sunaci suna Hira KB kan Shayin kawai yasha, sosai yaji dad'in Ruwan shayin don Haka yasha sosai,

Baffa yana gama karyawansa, yafito, yashiga wajensu tunda ga nesa KB yake kallon Baffa har yashigo yasamu guri yazauna, KB yana mamakin yanda hakan yakasance, ikon Allah, Baffa ya Gaisa dasu Uncle Musa sannan yajuyo wajesu KB, Baffa kam sake baki yayi cike da mamaki yana kallon sa "Likita! Ikon Allah Dama kaine Mara lfyn?
Allah Sarki D'annan meyasamekane haka? Ya fad'a yana kallon k'afan da ya kumbra suntum, Uncle Musa yace "Ayyah acnce mana kuma kai kasamesu abakin kogi ka k'ira Hukuma "innalillahi wainna ilaihirraji'un kanason kacemin Likitane na tarar dasu abakin kogi jinajina? "Eh haka dai police d'in yagayamana, ikon Allah asai kasanshi,
Baffa yayi ajiyan zuciya cike da tausayi "wannan yaro ai bazan tab'a mancewa dashiba,
Ya kwashe duk abunda KB ya musu lokacin da yakai Dijah Asibiti,
"Rayuwa kenan da kakai masa mara lfy, yau gashi shima ankawo maka shi amatsayin mara lfy,
Shiyasa arayuwa akeso kazama nakowa saboda bakasan yanda wataran zaka kasanceba, cewan Abban Habib,
Baffa yajuyo da kallonsa ga Kabir da shimad'in shiyake kallo yana murmushi, KB yace "Ashe anan kake? ai inayawan zuwa tanan, "Allah sarki shiyasa kasan mutuncinmu kasan mutanenmu sam basa mutunta fulani,
Dukansu suka sa Dariya "ai dole yasan darajan fulani don Uwarsama bafulatanace, inji Uncle Musa Baffa ya matso Kabir yana cewa a kace bazamu samu matsala wajen aikin k'afanba tunda ya had'a zuriya da fulani, kasanmu akwai dauriya, Habib ya kwashe da dariya "ah Baffa kar ka zugashi don naciro wayata zan masa vidio, kabir ya harareshi " yaro ancemaka ni kaine? Allura mafa inza'amaka sai katara mana mutane,

Baffa yana dariya yakamo k'afan Kabir yafaramasa aiki, sosai Baffa yatausaya masa don har da tsagewan k'ashi ak'afan gashi yayi tsami,
Kabir kuwa tunda Baffa yakama k'afanshi yakamo lip d'insa na k'asa yana tsotso ya rufe idonsa gam sai zufa yakeyi, duka d'akin bawanda bai tausaya masaba,
Har aka gama duka biyun bai ko bud'e idoba, yanajin Angama ya kwanta tuni bacci yayi gaba dashi,

Godiya suka mishi sosai, Uncle Musa yanisa "to Malam nawane kud'in aikin?

Baffa yad'anyi murmushi yace "ai koda bani namishi aikinba nizan biya amishi Balle kuma ninayi, wlh tun zuwana Asibiti abunda yaronnan yamin nake jinsa kaman d'an dana haifa,

Inzakuyar da kubarni da Kabir zan masa duk abunda yakamata fatana dai Allah yabashi lfy,

Godiya suka masa sosai sannan Abba yace "mu yau zamu koma zamu barshi da d'an'uwansa,
Saidai kayi Hakuri zamu saka Generator agidannan don munga ba kuwani samun wuta sosai,
"A'a wannan bawani abun damuwa bane, yafad'a yana mik'ewa, "nizan d'an fita sadai inaga zan dawo kafin kufita,
"to Allah ya kare muma zamuje cikin gari midawo, tare suka fita, suka koma cikin gari donyin sayayya,

Inna tana zaune agindin murhu tana Raba Abinci Bintalo tayi sallama, ta Amsa mata tana kallon bayanta, ina Dijah? "mhmm Dijah suntsaya can ita da Jebu wai zasu daki wata yarinya, inna rafka salati tana rik'e baki yanzu duk fad'an danayima yarinyannan Shekaranjiya batajiba, kenan nayi asaran yawun bakin? "Mhmm inna waifa akan lado ne, wai ancemata anganta da Lado adandali shine tunda akatashi a makaranta suka sha d'amara ita da Jebu ba irin maganan da ba mumusuba nida Ma'u basu kulamuba, cikin takaici Inna tace maza kije kice mata tazo injini intak'i kuma ranta zai b'aci,

Bintalo kan tsayawa tayi cike da mamki tun isanta gun,

Dijah ta haye kan wani itace ta hard'e k'afa tanagani k'awayenta Jebu da Har, da sude suna ta dambe da larito da k'awatanta,

Cikin zafin nama ta cafko jebu tana mata fad'a "yanzu fisabilillahi Jebu ku wasu irin marasa hankaline, Dujah ta maidaku sakarkaru, tanimo fad'a tabarku da dambe ita masifa ga tsoron tsiya, kukuma ga k'arfiko?
Dijah ta jawo hanun Jebu daga cikin na Bintalo, ta hankad'ata cikin fad'a,
" Jebu har yanzu bakin Larito baiyi jiniba kifasa mata baki sai mutafi, tafad'a tana zabga ma Bintalo harara
"wlh BIntalo nasha gayamiki kifita ahanyana bafa tsaoronki nakejiba,
Cike da talaici Bintalo tace "sai ki wuce mutafi Inna tana k'iranki,
zaro ido Dijah tayi tana kallonta, "sharri kikaje kikamin?
Bintalo batace mata komiba,
Ta rik'o hanun Jebu "zo mutafi ta kalli Larito wlh karki aza kin tsirane zan kamaki,
Suna tafiya tana ta surutu ma Bintalo ko kulata Bintalo batayiba har suka shiga cikin gida, arumfa suka samu inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login