Showing 123001 words to 126000 words out of 155892 words
nasara.
Nan Mutanen Gidan suka fara cika d'akin daga masu zuwa Gaisuwa sai masu kawo masa Abin sawa abaki,
Har aka k'ira lsha'i Yana fama da jama'ah ad'akin lya Har yanzu kuwa dube2 yakeyi baiga wacca yake nimanba, Cikin sanyi Jiki ya tashi suka shiga Masallaci,
Tun fitowansa yake cigaba da Amsan Gaisuwa Daga Bisani yashiga,
Bai samu lya palour ba, Dan haka yabita Bed room cikin zumud'i dan yasan anan zaiga Dijah, inma tak'i fitowane d'azun,
Saidai abunda ya k'ara rikitashi, shine Ganin lya ita kad'ai kwance kan Gado tana waya,
Ya tsata yana k'arema d'akin Kallo sam baiga wani abunda yadanganci Dijah ad'akinba, nan zuciyansa ya d'anyance da Tunani iri2.
Yanashirin fita ta ajiye Wayan tana fad'in "Dawo kaci Abinci tun d'azu na aika ayi k'iranka dan nasan mutanen naka baxasu barka kashigo da wuriba, musammanma sun kwan biyu basu gankaba, ta fad'a tana jere masa kayan Abinci kan shinfid'an da tamasa,
Zama yayi kan shinfid'an gami da tank'washe k'afa ya bud'e Abincin yana dubawa,
"Kai lya Wlh najima Rabona da Tuwon Biski, lnaso anma Mami bata cikayiba,
Iya tayi Murmushi Tana kallonsa Batace komiba, Saima mik'ewa da tayi dan kawo masa Ruwa,
Duk yanda yaso ya share yaci Abincin kafin yayi Maganan Dijah kasawa yayi, ji yai baxai iya koda loma ba sai yaji labarin Dijah,
Ya d'ago ldo araunane ya kalli lya, "lya wai lna Mata tace? Yayi tambayan batare da yashirya yiba,
"Matarka kuma agidannan?
"Eh lya Dan Allah karkicemin batanan kinji, ancemin tare kuka xo da ita,
"Tabbas tare Mukazo anma inaga kana cikin Yola ta shiga, Ma'ana inaga kana fitowa ita kuma tana shiga,
Zuru kawai ya mata da ido yana kallonta ko k'ifta idon yakasa, Zuciyansa na masa zafi Sam shi baiga laifin da yayiba da ake ta masa Horo haka Akan Khadijah, Dafe k'irjinsa yayi ya kalli lya da idonsa da suka canza daga farare zuwa jajaye, cikin shak'ek'k'iyar Murya yace "Inama Mutum yana iya cire wani abu a zuciyansa da Dahanuna zan yakice Son Khadijah inhuta tunda ku bakwa sona da ita, Wlh nayi2 in hak'ura da ita Nakasa pls lya kisa baki ki taimaka kiyi wani abu akai, kada kimin haka nasan kinsan inda Khadijah take kitamka kibani ita, ya karashe kaman zaiyi kuka,
Cikin jin tausayinsa lya tace "Kayi hak'uri Muhamdu Kabir, Da bamu Sonka da Khadijah ai baza'a aura maka itaba, Ka koma Gidanka zaka sameta lnsha Allah,
Ciza lips d'insa kawai yayi cikin takaici dan aganinsa itama bakinsu d'aya da Mami Ashe haka So yake?
Ya tambayi Zuciyansa ahankali kuma ya tashi ya fita bai kula da k'iran da lya take masaba, ya nufi Makwancinsa, Ba yadda bai Soba ya cire tunani aransa Anma ya kasa, Wayansa ya d'auko ya bud'e Missed call d'in Nafisa nan take yak'irata, yasanarda ita tafiya ta kamashi sai Gobe zai dawo, Mimirna tayi dan tasamu daman zuwa Gidan Meena Gobe da sassafe,
**********
Da Misalin k'arfe Goma Na safe 'yan jere suka Dira a gidan Kabir,
Basuyi mamakin Rashin ganin Matan Gidan agidaba, Kasancewan sun san Halin yawonta,
pert d'in kusa Da KB akayi Jeren Da Mami ta kashe Mak'udan kud'i Wajen sayansu,
Kafin la'asar sun gama tsara komi kama daga kitchen palour, da Bed Rooms,
Su kansu masu jeren Sun yaba da yanda side d'in ya tsaru,
Acan Gidan Mami kuma Khadijah ce Zaune tare da Bintalo, Sauda, Jamila, da wasu k'awayenta Guda biyu, ta kifa Kanta Sai Kuka takeyi ba irin Rarrashin da basu mataba tak'i tayi Shiru, Ahaka Mami ta Ratsa ta kamo Hanunta ba ta tsayar da ita ko inaba sai bakin Bed ta zauna kan kujeran da yake kallon Bed d'in suna Fuskantan Juna,
Nasiha Mami ta mata mai Ratsa jiki, Sosai ta gwada mata Muhimmancin Addu'a da Rik'o da ibada, Tana gamawa ta rik'e Hanunta ta fito da ita palour ta Damk'ata a hanun Maman Sauda,
Tana juyawa Dijah tasa Kuka mai tsuma Zuciya tana mik'o Hanu,
"Mami na Dan Allah kar kibari a tafi dani,
Da sauri Mami ta k'arasa shiga d'aki tana sharan k'ollahn da ya wanke mata fuska,
Gaba d'ayan mutanen Gidan sai da Dijah tasasu Kuka,
Haka suka kai *Nana Khadijah* Gidan *Muhammad Kabir* ana k'iran Sallahn lsha'i, Basu wani b'ata lokaciba suka watse Suka bar Gidan ya Rage sauran ita da Jamila Magiya tayi tayima Jamila gami da Kuka akan ta kwana,
Jamila ta k'wace Hanunta, tana zaro ido, "Cab inkwanafa kikace So kike Dr KB yazo ya turani store? Badaniba gad'a a kotu bakiga yanda ya haukace yana nimankibane ldo arufe badaniba tafiyata zanyi,
Sosai Dijah taji zafin furucin Jamila dangani take kaman gatse tamata dan ita atunaninta yanzu bata gaban KB,
Tanaji tana kallo Jamila ta tafi ta tashi ta rufe side d'in ta koma ta kwanta akan gado gami da rushewa da Sabon kuka.
Misalin k'arfe Tara Kb yayi Horn a gidansa Cikin gaggawa mai gadi ya bud'e masa ya shiga, Yanayin perking ya fito nan suka fara Gaidashi yana Amsawa har ya shige ciki,
Wurgi yayi da key d'in Hanunsa, gami da xubewa asaman Bed d'insa ba tare da yako cire takalminsaba,
Ya rintse idonsa Yana d'an mirgina kansa a kan pillow, cike da Gajiya, Kusan 3o minuts yana ahaka kafin ya tashi ya shiga toilet dan Ragema kansa Gajiya,
Ruwa mai xafi ya tara ya shiga ciki, yajima aciki kafin yayi wanka ya fito d'aure da towell a k'ugunsa yaji anbud'e Get ya yaye labulen Windown danyaga meke faruwa, d'aya daga cikin Mototinsa yaga ya shigo, Kallon Motan yake har Nafisa ta fito ta shiga sashinta, ba tare da fargaba ya maida labulen yasake yana jijjiga kai, ya dubi agogo 10 saura Minti goma
Sannan yasa Rigansa na bacci ya fita ya shiga wajenta zaune yasameta a bakin gado tana ware d'aurin d'an kwalinta, sai taunan Cingum take tana hurawa tana fasawa.
Rai ab'ace yanunata da yatsa, "Ke Nafisa da izinin wa kika fita?
Sannan sai yanzu kike shigowa, Mekika maida Aurena dake kankine?
Cikin fargaba ta kalleshi muryanta na d'an b'ari, "mhh Asibiti naje Kb cikinane kemin ciwo shine naje....
"Shout off, yadaka tsawanda yasa Dijah had'iye kukanta daga kan Gadonta da take kwance, tsoto yakara kamata don inba b'ata ji tayiba kaman muryan Maigidan tajiyo, Ko da ita yakeyi oho? Ta taya a ranta,
"Rufemin Baki banson Maganan Banza karki maidani bansan me nakeyiba,
Ya sassaitar da murya gami da takowa daf da ita ya nunata da yatsa, "Daga yau kika kuskura ki kasake fita ba da izininaba zakiga abinda zai biyo baya, Naga kinason maidani bansan me nakeyiba ina sane da irin ya wace yawacen da kikeyi, bazan daiki iskanciba, stupid kawai wacce batasan darajan kantaba,
Daga haka ya fice ya bar Nafisa da takaicin furucinsa,
Birgima suke tayi asaman Bed dukansu Uku kowa da abinda zuciyarsa take sak'awa,
Da haka bacci ya kwashesu su biyun yayinda Dijah kam tayi kusan kwana zaune, dan zuciyanta tagama tsinkewa da lamarin Drn nata, aranta tana tunanin ai yagama da ita tunda ya karb'i Budurcinta dama ance haka Mazan suke, watakila shiyasa Mamin take kaffa2 da ita gashi ya kaita ya barota,
Washe gari da Sassafe KB yayi shirinsa na zuwa aiki, tun time dinsa bai gama cikawaba, hakanan yaji gidan ya gundureshe,
Ya fito Main palour yana k'arema palourn kallon yanda datti yake shirin kasheshi k'arfi da yaji, yaja dogon tsaki cike da takaici arayuwansa inda abunda ya tsana k'azantane,
Yana fita kai tsaye Campaninsa yaje, don yau yake son ya kammala komi na sabon tsarin da yayi ma campanin,
Sai da ya d'auki kimanin 3Hours sannan ya k'ira Sani kancewa yazo nan ya sameshi, Ba b'ata lokaci Sanin ya iso,
Kujera ya jawo kusa da Kb ya zauna yana mik'a masa Hanu, "Ango har ka fito da wuri haka?? Ban tsammani yau za'aga idonka a wajeba, Sani ya fad'a masa cikin tsokana,
Hararansa Kb yayi gami da mik'amasa takardu, adak'ile yace "Sani ga Amana na damk'amaka, Kafi kowa sanin abunda yake tafe a campanin nan, Dan haka inason ka jajirce duk rintsi kar Alhaji Ya'u yayi Nasaran burinsa akan Campanin dan nasan kan zaka fuskanci kalu bale daga gareshi,
Sani ya jinjina kai yana duba Takardun cikin so da kaunan wannan Aboki da yaxamarmasa Uwa da Uba, yace "Insha Allah KB zanyi kokari inga na sauk'e wannan k'aton nauyi da ka d'auramin, Kabir bani da Bakinki Godiya gareka sai tarin Addu'a... Da sauri Kb ya dakatar dashi ta
Hanyan kamo Hanunsa, yana fad'in "Zo muje inhad'aka da Musa ya maka karin bayani ina saurine, zan fita,
Yana gamawa ya Shiga Motarsa bai tsaya ko inaba sai Gidan Alhaji Ya'u Zaune ya sameshi a farfajiyan Gidan inda yasaba xaman shan iska ya rafaka tagumi yana saka da warwaran da yajina yanayi anba nasara,
Kujeran dake daf dashi Kabir yajawo yazauna kasancewan yayi ta rafka masa sallama baijiba,
Motsin kujeranne ya dawo dashi Daga Duniyan da ya lula,
Yad'ago sukayi ido hud'u da KB da yake kallonsa cike da gadara da izza,
Murmushi Kabir yayi ya shafi sajensa, "Ina wuni Dadyn mu, wani irin kallon tsana da takaicin Alhaji ya'u yamasa, Baida niyan Amsawa dan haka KB ya mik'a masa wata takarda yana cigaba da masa Murmushin rainin Hankali,
*Kuyi hakuri kunji* ππΌββ
*Ummu Fatima ce* π
[9/20, 9:08 PM] Ummu Fatyma: πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π¦π¦
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
6β£4β£
Kaman ba zai karb'a ba ya mik'a Hanu ya karb'a, Ya ware takardan Ya duba nad'an lokaci, ya dubi Kabir da son jin k'arin Bayani,
kB ya d'an Numfasa, "Takardan Super Market d'ina ne nacan hanyan Jos, Na bakashi yazama Mallakinka Dady Duniya da Lahira,
D'an Jimm Alhaji Ya'u yayi aransa kaman yayi farin ciki da hakan dan yasan Ba k'aramin Dukiyabane a wannan Store d'in,
Saidai Bak'ar Zuciyansa ta hanashi hakan,
Kabir ya mik'e har yanzu fuskansa da guntun Murmushi, ya kuma Mik'o masa wata takardan Wannan karon da Sauri Alhaji Ya'u ya karb'a yana dubawa,
"Na Damk'a ma Sani Campanin munnan Dady yanzu shine Manaja komi na hanunsa, Saboda ka Girma yanxu Hutu kake buk'ata,
Wani irin zabura Alhaji Ya'u yayi Gami da jifa da takardun duka biyu ya mik'e tsaye yana masa mugun kallo, cikin Huci ya nunashi da yatsa, "Kayi k'arya Kabiru wlh baka isa kazomin da Rainin Hankali hakaba,
Tun Ubanka na Raye Campaninnan yake Hanuna, Banga Mahaluk'in da ya isa ya nisantani da Dukiyan d'an'uwanaba, Wlh baku isaba daga kai har Uwartaka data kitsamaka wannan Magana,
Maganganunasa Sunba KB dariya anma sai ya daure Asanyaye, yace "No Dady baka fahimci Manufatabane ba ina nufin rabaka da Campaninbane, Anyanxu kana Buk'atan Hutu Dady yakamata ka huta kagafa d'awainiyan Campanin yana da yawa, inyaso saika d'an dinga lek'awa Time 2 time kana ganin abunda akeyi acan, shima Store d'innan zanso ka d'aura wani akai yadinga kulamaka dashi,
Shiru Alhaji Ya'u yayi yana nazarin Maganan, Anya baka sake samun wani damaba kuwa Nacin karanka Ba Babbaka kayi yanda kakeso da Kud'in Campanin ba mai samaka ido, ga kuma wani Garab'asan,
Wani shu'umin Murmushi yayi ya d'ago ya kalli KB da ya tsareshi da Ido yana Nazartansa,
"Kabir wani zaka Rainama Hankali? Ya masa Tambayan cikin son ya shafantashi,
KB yayi taku biyu gami da sa Hanu a Aljihun wandonsa, Baice dashi komiba, Sai d'an Kalle2 cikin Gidan da yakeyi,
Alhaji Ya'u ya tashi yana Hucin K'arya, "Xanje insamu Uwartaka inji daga gareta, Sannan ya duk'a ya d'auki Takardan Stote d'in, ya shiga Ciki,
d'an Murmushi KB yayi ya d'aga kafad'ansa, ya shiga Mota,
A Falo ya tarar da Mami Ya zube cikin kujera yana fad'ib "Wasshh!! Mami Nagaji da yawa,
"Tashi ka d'auko Abinci kaxo, Mami ta Umurceshi,
Ya d'auko ya dawo kusa da ita ya zauna, Ba b'ata Lokaci ya fara ci dan yunwa yakeji Ba kad'anba,
Zuba masa ido Mami tayi sosai tana Kallonsa,
Aranta tana Mamakin sauyawansa da yawa Haka,
"Mami Goben zaki tafi Maidugurinko?
Mami ta Girgixa Kai "Nafasa Saboda wani Dalili, In Allah yasa aKayi auren Naje inga d'akinta,
Yayi Shiru yana kallonta,
"Lfy kuwa Kabir? Ko akwai wani Matsalanne?
Kabir ya sauk'e ajiyan Zuciya,
"Mami Khadijah Dan Allah Mami kitausayamin ki dawomin da Khadijah Badon Halinaba, Ki dubi Halin da nake ciki kinji Mamina,
Ya k'arashe cikin Marairaicewa kaman mai shirin yin Kuka,
*Ummu Fatima ce* π
[9/22, 8:40 PM] βͺ+234 816 155 6998β¬: πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*UMMU FATIMA CE*π¦π¦
π *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......π
_Lamarin social Media abun Mamaki, Wasu kan suna tsammanin duk abunda suka shuka a wannan kafa bazai tsiroba,_ π€
_Wlh 'yar'uwa inkin shuka khairan a wannan kafa zaki Girbi kayanki inma sharranne zaki Girbi abunki, Wlh Allah baya bacci_
ππ» *Kukan Kurciya*ππ»
_Ubangiji ka karemu da Rubuta wani abu da zaizamomana fitina da danasani agabanka Ξ± ranan da d'a ke gudun Uwarsa Miji ke gudun Matarsa kowa nak'iran Nafsy! Nafsy!! Nafsy!!!_ πππ
6β£5β£
Mami ta zuba masa Ido na lokaci aranta tana Mamaki, wani irin Rayuwa yakeyi a cikin gidansa da har za akai masa Mata Gidan ta kwana bai Saniba, π€
"Anyah Kabir kana Sauk'e Nauyin da yake kan kuwa?
Kana kula da Gidanka yanda yadace kuwa?
Nhmm ka daiji tsoron Allah idan baka Ganinsa shi yana Ganinka, Dolene ka kula da hak'k'in Wa inda Allah ya d'oramaka Hak'k'insu Akanka,
Zai kuma yin Magana, ta dakatar dashi " Nadai gayamaka kaji tsoron Allah Duk Mutumin da ya rikito zama da Mata biyu yasan zaiyi Adalcine inkai ba Adalibane karma ka fara,
Nasiha ta dinga masa Sosai Mai shiga Jiki, Daga Bisani tace masa tashi katafi Gidanka, Allah ya tsare,
Mik'ewa yayi jiki ba k'arfi aransa yana Mamakin Fad'an da ta masa akan zama da mata biyu, Bayan Mace d'ayace agidansa, ta rik'e d'ayan ta hanashi.
Yana shiga Motarsa ya mata Key ya fice agidan, yana tafiya a Hanya yana magana shi kad'ai kaman zautacce,
"Why Mami?? Ya zanyi? Allah ka ciremin Abunda nakeji gameda yarinyannan araina, in huta zuciyatama ta huta,
Ya d'an had'iyi yawu "Daga yau baxan sake miki Maganantaba Mami Xan Hak'ura da Khadijah kwata2 xanyi ta Addu'a Allah ya ciremin ita araina, ya dafe k'irjinsa da Hanu d'aya yana yuk'i da d'ayan, Ahankali yana sauk'e ajiyan Zuciya, har ya isa Gida zuciyansa na masa Suya,
Tsaye take ajikin Window cikin Rantsatstsen Kwalliya tana k'arema Gidan kallo,
bata damu da Jin bud'e Gate da akayiba, har sai da yafito yafara Tafiya, ta maida dubanta gareshi Har yanzu Hanunsa, Dafe da k'irjinsa Yake yana tafiya, Kallo d'aya zaka masa kabashi Marar lfy Mai tsanani,
Kallonsa takeyi ko k'iftawa batayi Ko wani takunsa dai2 yake da Bugun Zuciyanta, sosai tayi Mamakin Ramansa,
Ganin kaman xai gantane yasa tad'an yi Nisa da jikin Windown tana cigaba da kallonsa, Har ya shige ciki takoma ta xauna akan Sofa tana maida Numfashi, aranta tana girmama yaudara irin na d'a Namiji ta tuna irin Maganganun da KB yadinga mata kafin wannan Lokaci,
anma gashi anwayi gari tana zaune acikin Gidansa yau kwana na biyu kenan baiko lek'o inda takeba,
"ko dayake awancan Lokacin Akwai abunda yake buk'ata awajenane yasa tafad'a a fili,
Tasa hanu ta share Hawayenta, aranta tace "dama tun kafin nan ya furta cewa Nafisa itace Masoyiyarsa inyasameta Magana ya k'are,
Haka ta mik'e ta kwanta aranta tana tunanin Maganin matsalanta k'waya d'ayane shine Tasamu ta tafi Wajen iyayenta, Tayi Rayuwanta cikin Aminci a inda tafi wayo
Yana shiga d"akinsa wanka yayi yafito cikin Kananan kaya Brawn jeans da shirt Milk colour, mai guntun Hanu, ya xauna a falo ya d'auki romot yana canxa tasha Nafisa ta iso, ta zauna daf dashi kaman zata shige jikinsa, ta Marairaice kaman zatayi Kuka ta rik'e Hannayensa Tana murzawa
"Haba my Sweet har yanzu baka daina Fushi daniba? Kayi hakuri dan Allah bazan sakeba namaka Alk'awari Allah my sweet
Bazan sakeba, Ta karashe cikin kuka, da yaso ya shareta anma yanda ta dage take bin jikinsa tana Magiya yasashi kallonta,
Ya rausayar da kai, "To daina kukan haka,
Da sauri tasa Hanu ta share hawayenta ya jawota jikinsa yana shafa bayanta
"Banson yawace2 Nafisa Ba mutuncinmu bane ni dake ace duk lokacin da kika dama zaki fita ba zaki dawoba sai dare, ai baiyiba,
"Allah na daina sweet baxan sakeba