Showing 126001 words to 129000 words out of 155892 words

Chapter 43 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

450


"To shikenan ya wuce, yafad'a yana d'an Shan Murr, k'ara lafewa tayi a jikinsa tana Shashafashi, Sunkai kusan sha d'aya awajen kafin tace "Sweet muje mu kwanta Gobe da safe Mama tace zamu tafi, Kuma kud'innan bazai isheniba Sweet kataimaka ka k'aramin, tashi yayi ya kashe kayan kallon, ya kalleta nawane za'ak'aramiki?

"To da zansamu k'arin Dubu d'arima yayi, kansa ya gyad'a Alamun ya gamsu, Sannan ya rik'e Hanunta suka nufi Bed room d'insa,

"Naga ke baki ko damu zaki tafi kibarni ni kad'ai agidaba, Damuwanki kawai kije biki, Dai2 Lokacin Dijah tayaye labulen Windownta tana kallonsu,

Nafisa ta kwanta ajikinsa "Haba sweet kaji yanda nake ji kuwa? Dan murmushi yayi, yaja hancinta k'arya kikeyi bakijin komi gashi har kara jaddadamin tafiyan kike,

Sake labulenta Dijah tayi gami da jan dogon tsaki,

sai Akunnen Nafisa cikin tsoro ta dakata da tafiya Gami da Cire jikinta a na KB ta kalleshi, ta kalli d'akin,

"Sweet Naji kaman motsin Mutum anan d'akin ya kalli d'akin yayi murmushi "Mutum kuma?
Kedai kin tsoratane wani mutum ne zai shigo har ya Shige d'aki?,

ya murd'a handle d'in k'ofan "arufema pert din yake,

Gaskiya to ni kaje ka d'auko Key ka bud'e mugani Allah da safema naji kaman mganan mutum,

Yasa hanu a Aljihunsa ya ciro key ya zira a kofan yana kiciniyara budewa, bai Bud'eba dan haka ya zare Key din ya mayar a Aljihunsa, "Muje in dauko key din a d'aki, suka wuce tana biye dashi yana shiga ya zare Rigansa ya ajiye,

Da Sauri Nafisa ta fad'a ak'irjinsa tana shafashi, tun yana tureata yana ce suje ya bude dakin suga meye a ciki har ya xube akan Gadon ya fara maidamata Martani,


***********
Washi gari kuwa da sassafe Nafisa tafita kaman yanda ta gayamasa, taje tasamu Mamanta suka d'au Hanyan Borno,

********
Kusan Satin Dijah agidan anma bata tab'a fitowaba, haka Kabir bai san da Zamanta agidanba,


Yau Lahadi tana tsaye a jikin Window kaman yanda ta saba Lek'enta, hakan yazamemata jiki, tana tunani tun shekaran jiya rabonda taga daya daga cikin mutanen Gidan ya gilma, Wata kila basa nanne tafada aranta gami da tabe bakinta,


Ta dawo jikin Mirow tana kallon kanta wandone tree quater na jins a jikinta blue mai kwalliyan pink ajiki sai Rigansa pink mai hanun ves da yasha kwalliya Da stons jajaye da blue, ta k'ara tace gashin kanta ta d'aureshi da katon Ribon Pink ta gyara kanta ba k'aramin kayau tayiba, ta bud'e k'ofa, rana ta farko da taji aranta tana son su had'a ido da Rana agidan,

jan kofan tayi ta nufi gardeen ta k'ofan pert d'inta, hanunta rik'e da wayanta, kalle2n wajan ta shigayi cikin annashawa,

iskane mai sanyi ke tashi a wajen gami da k'amshin Furanni, Ta ware hannayenta tana juyi a wajan tana murmushi,

Aranta tana tunani meyasa bata taba zuwa nan tashaki ni'imar ubangijiba?
Lallai da tasan haka wajan yake da dadi da bata b'ata lokacinta wajen zaman tunani da koke2 ba,


Cikin shauk'in Rugansu ta zauna akan lilo tana d'an xillo aciki tana cigaba da Murmusawa, taji Wayanta ya hau Ruri wanda shi ya jawo hankalin Kabir da fitowansa kenan daga wanka yana tsane jikinsa da towel, ya tako ya yaye labulen Windown, Dam! Dam!! Yaji k'irjinsa yana bugawa, yanzu abun har yakai haka? Tunanin yarinyan da yake yawan yi har yakai ya fara ganin Gixonta?


Cikin Murmushi Dijah ta d'aga wayan Mami ta kara a kunnenta, "Helo Mami na, naga missed Call d'inki d'axu da na fito daga wanka,

"Mhnn shine baki kiraniba ko,
"Banda kud'i awayan nefa Mami, tafad'a da d'an shawagwab'a, irin na Y'a da Uwa,
"To kintashi lfy?
"lfy Mami,
"Dama na k'ira inji lfynkine Ina Kabir?
Dijah ta zaro ido yau kuma bata san mexatace mataba, tafara kame2 can kuma tace Ya shiga wanka Mami ko inmik'amasa wayanne?


Mami ta d'anyi Murmushi cikin jin dad'in b'oye sirrinsu da Dijah takeyi, dan tasan cewa har yanzu mutanen Gidan basu san da zamanta agidanba,


Tace "a'a Barshi kawai Khadijah na, inyafito kigaidamin shi,

"to zaiji Mami,
"Yauwa bari yanxu zan turomiki kud'i da Numbern Wayan Baffanki ki k'irashi kugaisa, cikin wani lrin Zumud'i Dijah ta diro daga cikin Lilon tana tsalle, "Yehhh! Mami na nagode sosai, Mami ta kashe wayana tana dariya, "Khadijah Manya!.

Dijah tacigaba da tsalle da dariyanta awajan ta fara wak'an da Baffanta yake mata idan ta tada tsininta da Fulatanci, sosai take jin Kewan Mahaifan nata, badai yanda ta iyane kawai,

Tsaban yana son ya dad'a tabbatarda abunda idonsa ke ganimasane yasa ya zuge glass d'in Windown wanda hakan ya jawo hankalin Dijah ta kalli Windown cikin tsoro duk da bata ganin na cikin tasan ita ake kallo dan haka ta tsayar da tsallen da takeyi ta tab'e baki a fili tace ashe "yan iskan suna nan, ta nufi hanyan sashinta,


Hakanne ya bashi tabbacin Wacca idonsa ya nuna masanne, ba Gixobane,

Cikin wani irin hali da k'yar yasa Ves da wando tree quater ya fito da sauri2 ya nufi inda yaga ta shiga, cikin sa'a yana tura k'ofan ya bud'e, wani sassanyan k'amshi mai dad'in shak'a da yajima bai shak'i irinsabane ya doki Hancinsa,


Ya sauk'e ajiyan zuciya gami da Lumshe idonsa, yana k'ara jawo k'amshin cikin hancinsa Yanabin k'aton palourn da Kallo, cikin wani irin kwanciyan hankali da Nitsuwa da yajima bai samu kansa a cikiba, komi tsab yake a palourn kaman yanda yake son gani tsarin palourn ba k'aramin Burgeshi yayiba, yaushe aka masa wannan gatan baisaniba?,

"wayyo Mami na kingamamin komi ya fad'a aransa, cikin Murmushin da yakasa tsaidashi a fuskansa,



Ya kutsa kansa cikin d'aya daga cikin Bed room d'in bai gantaba ya k'arasa ya bude toilet nanma bai gantaba, ya fito ya bud'e d'ayan nanma wayam,

Ya sake fitowa ya tura na tsakiyan, gam yaji a rufe da key, hakanne yabashi tabbacin anan take,

Yad'anyi Murmushi yace "Khadijah case!!

Ahankali ya shiga k'onk'osawa, hararan k'ofan tayi, cikin zafi tace "Waye?


Ya jingina da jikin k'ofan yana Murmushi yace "Mai gidanne abud'e masa, taja tsaki gami da sake hararan k'ofan ta koma ta kwanta cikin takaici,

Ahankali yasake cewa "ko baza'a bud'eba,

"Eh baza'a bud'eba kayi abunda za kayi,

Dakewa yayi ya kausasa Muryansa, "Ke Malama kixo ki bud'emin k'ofa dan kinsan ba gidankibane inkuma kink'i insa matata ta kawomin key inbud'e mata ta shiga ta dakaminke,


Cikin wani irin huci ta diro akan gadon ta k'araso bakin k'ofa tana bugawa da Hanunta har tana b'ari tsaban Masifa,
"Ba Wata banzan matarka kawai xaka gayyatoba ka had'o da wainnan k'awayenta 'yanbarikin wlh ni Dijah na isheku riga da wando, mtsss ta jaa tsaki,

Kb ya danne dariyan da yakeson kub'uce masa yace
"Keeee Matar tawa kikece ma Banxa? Ki shiga hankali inkink'i zan b'b'b'alaki agidannan bana wasa dake ko kad'an,

"Angayamata banza kuyi abunda zakuyi wlh ta wuce Banzama awajena, har wofima itace, ta fad'a cikin Kuka,

"To in kin isa ke mara kunyace Khadijah ki bud'e k'ofan, kifito agabana ki zagarmin mata kiga yanda zanyi k'asa2 dake,

"Bazan bud'eba kai dai indai da gaske kana da matar da zata k'watamaka 'yanci kaje ka k'irata,

Kwanciya yayi a jikin kofan yana jin yanda take kuka har da sheshek'a, yayi murmshi yana mamakin Halinta ita zata tsokani fada tayi fadan kuma tayi kuka,



Asanyaye yace "Khadijah! Ki bud'e k'ofan pls!! Tun Raina bai gama b'aciba,

Komawa tayi ta kwanta akan gado tana cigaba da Kukanta,


Ya fita ya tafi sahinsa, cikin wani irin hali ya shirya, shi kad'ansa sai Murmushi yakeyi ya tafi wajen mitting din campaninsa,



Da yamma ya dawo kai tsaye pert d'in Dijah ya shiga, sam ta manta ba ta rufe kofanba,


Zaune take a palourn Cikin Gaown jaah mai jikin Roba iyakarasa gwiwan kafanta, daga saman rigan a tsuke yake yayinda k'asan ya bud'e kaman k'asan rafa sket, ta d'aure kanta da Igiyan da yazo da Rigan, a matsayin Ribon, kwalliya tayi sosai a fuskanta sai kace sabuwar amarya,


Sam bata lura da anbud'e k'ofan har anshigoba, tanata aikin canja tasha, sai da ya kawo tsakiyan palourn ta d'ago ta kalleshi, ya susuce da kallonta baki a bud'e,


Da sauri ta mik'e, yana daf da ita ta zaga ta shiga bayan Kujera ta nunashi da yatsa, "Kai Malam dakata kar ka matsoni kafita a Hanyana nagayamaka me yakawoka inda nake?


Tsayawa yayi cak kansa a langab'e yake kallonta, tayi mugun canzamasa kaman wanda akasata cikin wani na'ura mai sauya mutum,


Cike da isa yace "Gidanane nan ina da ikon shiga inda na gadama ba wanada ya isa yamin shamaki da wani Wuri,

"To sai kabari sai randa nabar gidan sai kadinga shigowa nan, Masu gida masu gorin gidaje, ta k'arasa maganan cikin kuka,


Hararanta yafara yi cikin wani hali yafara taka k'afa da sauri ta kuma ja da Baya, "Nagayamaka kar ka matsoni, indai dan kana gadaran ina gidankane to ka gaggauta cewa inbarmaka gida kagani ko zan k'ara seconds a gidan,


"Ok haka kikeso ince? To maza zokibarmin gida, ban gayyatokiba wannan gidan naginashine dagani sai matata abar sona,


Wani irin tuk'uk'in b'acin raine ya xiyaraci zuciyarta, Ta ware idonta ta watsa masa harara, "Allah yasa nima muna gida, kuma naji dad'in wannan furucin naka,


"Inba tsoroba kice kina gidamana kaman yanda na fad'a, ai inkaji namu da maishi, ko taku baki dashi, kibar masu shi su fad'a,

Common Malama zokificemin daga Gida tun bansa Matata ta b'ab'b'alakiba,


Aguje Dijah tabi ta bayan Kujeran ta nufi d'aki tana kuka tana maganan dabaya fitowa,


Sake jakansa da ke rataye a kafad'ansa yayi yabita cikin zafin nama, tana shiga d'akin yana biye da ita yakaimata cafka Tayi saurin Shigewa Toilet ta mayar ta rufe, ta jingina bayanta da k'ofan.

*Wannan Daru haka? πŸ€” Su Malam KB haka ake Tarban bak'uwa?* πŸ€”πŸ˜

*Ummu Fatima ce* 😍
[9/24, 5:49 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


6⃣6⃣


Shima jingina cikinsa yayi kan k'ofan yana son ya bud'e ta k'arfi sai dai yana tsoron kar yajimata ciwo,


"To waima meyasa kike guduna? Ko jarumtankin na k'aryane?

Jin bata Amsaba yasashi ya bar wajan gami da bud'e k'ofa jin yafitane yasa ta fito tana share hawaye, da sauri ta maida k'ofan ta Rufe harda murd'a key,


Tadawo ta sauk'o da Akwatinta a saman sif, ta fara jibge kayanta aciki, tana gamawa ta nufi mirow tafara tattare kayan kwalliyanta,

Tana cikin tattarewa ta hangi Mutun kwance asaman Bed d'inta Hannayensa nad'e akan k'irjinsa ya tsura ma Hips d'inta ido ba k'ak'k'autawa, ta cikin Mirrow,

Axabure ta juyo suka had'a ido ya kannemata ido d'aya yana Murmushin Baki da wayo, sauri2 tayi ta rufe jakanta batare da ta tuna Hijab ba ta fara jan jakan takai bakin k'ofa ta taso da Ximman bud'e k'ofa taga baki key ajikin k'ofan ta juyo sukayi ido hud'u da Kb yayi mutmushi gami da kad'a makullan a hanunsa, yana d'agemata Gira.


Wani irin kuka mai tsanani Dijah ta sake gami da kifa kanta a jikin k'ofan tana Bugawa da Hannayenta tana goga goshinta a jikin k'ofan, Tana jin kaman Zuciyanta xai fito waje,


A tsorace Kabir ya diro daga gadon ya nufota, a fusace ta juyo ta d'auki Kwalban turare ta kwad'ashi da k'asa ya tarwatse a wajan, ta nunashi da yatsa,

"Kar kasake ka matsoni wlh zan illataka ka bud'emin k'ofa infita daga wannan banxan Gidannaka,


Sosai jikin Kabir yayi sanyi, yasan ya tsokaneta dan Nishad'ine duk da yasan itad'in ba kanwan lasabace, saidai sam baiyi tsammanin hakanba,


Ya langab'ar da kansa a sanyaye yace "Yi hak'uri Khadijah, xan bud'emiki ki tafi anma kidaina wannan kukan,

"Ba Ruwanka da kukana ka bud'emin k'ofa kawai ta fad'a cikin k'araji,


Ya juya ya nufi k'ofan ya bud'e, ya juyo yamata kallon inkinsan wata baki san wataba,


Ta jawo jakan ta fita har takai tsakiyan palourn ya sha gabanta,
"Haka zaki fita ba mayafi Khadijah?

Sai alokacin ta tuna da mayafi, anma tayi kaman batajishiba, ya sake maimaita mata, d'an jim tayi ta kalli kanta, tasan bai dace ta fita a hakanba,


Dan haka ta sake jakan kayantan awajen, ta juya ta nufi Bed room d'in da sauri ya d'auke jakan ya fita dashi,

Ta dinga jijjiga k'ofan anma yak'i bud'ewa,

"Kash! na manta naja k'ofan ya rufe gashi key d'in na ciki, ta jiyo muryan Kb abayanta,

Ta juyo ta kalleshi da Rinnanun idonta,


Ta fita palour ba tare da tace mishi komiba,

Turus tayi tana kallon wajan da ta ajiye jakanta, babu,

Kabir ya rab'a gefenta ya wuce zai fita, Da sauri ta sha gabansa, cikin dashashiyar murya tace "Malam kaban jakana, xan d'au mayafina,

"Oh nasamiki jakanki acikin Mota, Muje inbaki, ta galla masa Harara, zatayi magana,

Ya d'an had'e Fuska, Yana kallon agogon Hanunsa, So nake na ajiyeki agidanku in wuce sauri nakeyi, Muje ko.

Wani irin kallon Rainin hankali ta masa, farin Sani ta masa wajan iya wasa da Hankalin mutum,

"Bance ka kaini ko inaba, ba kai ka kawoniba, kabani kayana, ta karashe cikin tsawa,

"Ok ba damuwa Muje ki karb'a ya wuce gaba ta bishi, wani Coridor Yabi sai gasu a wani tafkeken palour, suna shiga ya mayar da k'ofan ya rufe,


Ya kalleta, Yace "Ina xuwa,


Tsayuwa tayi a wajen tana kalle2 Duk da ba fahimtan komi datake kallon takeyi ba, tsaban b'acin ran dake jikinta, Har wani jiri takeji Sosai ta juye ta fito a asalin bafulatananta,


Kusan Minti biyar ta b'ata tsaye a wajen, bai fitoba, a fusace tabi hanyan da taga yabi, tayi tafiya kad'an taga d'aki ba b'ata lokaci ta hankad'a k'ofan tashiga,

System tagani da takardu barbaje a tsakiyan palourn alamun yanzu Mutum ya tashi a wajen, ta dinga bin d'akin da kallo daki2, ba motsin komi sai na na'urorin da suke aiki a d'akin,

Ta jah dogon tsaki ta juya, danbatasan d'akinma na wayeba,


Sai dai tana kaiwa bakin k'ofan tayi2 ta bud'e abu ya gagara,
Wani irin kuka ta kuma sakewa mai tsima zuciya ta sulalle a jikin k'ofan ta jingina kanta ta cigaba da rera kukanta, a haka bacci yayi gaba da ita,

wani irin nannauyan ajiyan zuciya Kabir ya sauk'e daga inda yake b'oye a bayan Sif yana kallonta, a hankali ya tako gabanta ya tsuguna, zuciyansa tana harbawa, sau biyu yana mik'a hanu zai tab'ata yana janyewa, saboda tsoron kar tatashi,

Ya tsura mata ido yana kallonta cikin Mutuwar jiki, a haankali ya shafi Gefen fuskanta,

"Khadijah Case yaushe zaki daina bani matsala haka?

A hankali ya d'auketa yana taku da ita kaman wanda ya d'auki k'wai ya kaita kan gado ya kwantar da ita, ya gyarata yaja tattausan Bargo ya rufeta dashi,

Sai ajiyan xuciya takeyi irin na wanda yaci kuka ya gaji shikuma ya xuba mata ido kaman zai cinyeta,


Yasa hanunsa yana shafan gashin kanta a hankali yana Murmushi, Xuciyarsa cike da farin cikin yau gashi ga Khadijahn sa dayake yawan Mafarkinta,

Yayinda wani sashin kuma yake cike da fargaban ya zasu kwashe intafarka? Yasan yariga da ya tsokanota yau Allah kad'ai yasan yanda zasu kaya.


K'iran Azaharne ya sashi ya tashi ya shige Bayi ya d'auro Alola yazo ya wuce Masallaci,

Har yadawo bata farkaba, ya zare Jallabiyan Jikinsa ya ajiye, ya juyokenan yaga tana motsi alamun zata farka,

Damm! Yaji k'irjinsa ya buga a hankali yafara Addu'a "Ya Allah ka kub'utar dani daga Rikicin Wannan baiwa taka,

A hankali ya tako ya k'araso bakin Gadon yatsaya yana Murmushi, dai2 lokacin ta bud'e idonta tana k'are ma d'akin kallo har idonta ya sauk'a a kansa Zunbur tayi ta tashi tana kallonsa,


Cikin wani irin Murya tace "Likita Wlh bazan tab'a yafemakaba duk Abunda kake min kabani kayana intafi Ruganmu, zata sa kuka ya zauna a bakin gadon ya janyota jikinsa ya rungumeta,

Nan tafara kiciniyar k'wacewa anma takasa, tasaki Ajiyan Zuciya mai k'arfi ta manne ajikinsa tana sheshek'a,


Kabir kan gaba d'aya Jikinsa ya d'au b'ari shi kansa baisan daliliba, yana jin yanda ta lafe ajikinsa tana ajiyan xuciya, yanason ya d'an fad'amata kalma koda gudane dazai k'ara sanyayamata anma yakasa,


Tsawon lokaci suna a haka yaji d'umin hawayenta, sai alokacin yasamu ya fitar da wani Numfashi mai k'arfi ya d'agota suka had'a ido, a raunane tace "Likita ka barni intafi dan Allah!

"Ba inda zan barki kije Khadijah, Wannan tafiyan da kikayi kibarni tsawon wannan lokacin bai ishekiba?

Ta tureshi tana masa kallon sama da k'asa, "Ko kazaci da Nafisan kake tare da zakace haka?

"Nasani da Khadijana nake tare Nan gindamunne Khadijah Ba inda xakije kibarni,

"Gidanku dai kai da Nafisa,

"Mu Ukune har da ke Khadijah kecefa Uwargidana, ko kinmanta? Kinzama Jinin jikina inbaki bazan iya rayiwa mai kyauba, dan Allah karkisake tafiya kibarni,


Kuka kawai Dijah ta sake don ta lura abunda yasaba zai mata wato yaudara,

Ya sake manneta da jikinsa tanason ta k'wace anma ta kasa,


Saida yagama jagulata san ransa yamatso saitin kunneta, yace "Zakiyi sallah? Kai ta d'agamasa alaman eh, yayi murmushi ya tashi da ita ajikinsa yamata rakiya har bayi,

wanka tayi sannan tayo Alola tana fitowa ta samu kayanta akan gado har da na kwalliya da hijabi, d'an Simple make up tayi dan yanzu bata iya zama batayi kwalliyaba, tunda ta zauna da Yafannah,
tana sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login