Showing 141001 words to 144000 words out of 155892 words

Chapter 48 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

471

da K'anana, masu tarin yawa da k'ullin Magunguna a hargitse, da wani tsoka da aka caccakkamasa Allura duk jikinsa, da kan zabuwa antusa acikin Bakin kwad'o,

Yace "Kinga abunda aka kawomana Mahaifiyarki dashi, wani Driver ne ya kawota, yace shima a bakin Hanya ya sameta kwance cikin Jini,

Wan Mahaifinane, badin hakabama bazamu karb'etaba, mun karb'etane akan zamuyi cikiyan 'yan'uwanta ba wai dan jinyaba,


Dai2 Lokacin aka turo k'ofa akashigo, Bata damu da ganin wanda ya shigonba, Tazamo k'asa kan gwiwanta tana kuka cur2 "Dan Allah Likita kataimakeni, ka dubamin Mahaifiyata duk garinnan banda kamanta kaji tausayina pls Dr, Dan Allah kayi taimakon Addinin Musulunci,


Dai2 lokacin ta d'ago ta kalli wanda ya shigon nan sukayi ido hud'u da Habib, da Sauri ta juya gareshi,

"yauwa ga d'an'uwana, Yaya Habib ka masa Magana, a shiga da Mama ku dubata Dan Allah, zata Mutu,

Cike da Mamaki Habib ya kalli tarkacen dake gaban Dr Na'im yakalli Nafisa, "Kina nufin kicemun Mahaifiyarkice Matan da ta kwana a wajennan Nafisa?

Cike da tashin Hankali tace "itace, Wlh itace Yaya Habib,


Gyad'a kai Habib yayi ya furzar da iska, zai fita ta tashi tasha gabansa,

Yace "kiyi Hak'uri Nafisa bani da Daman insa a mata wani abu sai jami'an tsaro sunsa Hanu, k'iransu cikin case d'in kuma zai iya tada wani abun,

Ta durk'usa a gabansa,

".Ya Habib ko bana auren KB ni k'anwarkace tunda ni k'anwarsace, ka taimakamin, kar in rasa Mahaifiyata.


Da k'yar da sid'in Goshi, Habib yayi ciku2 akashiga da ita aka sata a gado suka fara dubata,


*****

Cikin tashin Hankali Alhaji Ya'u ya fito daga cikin gida, ya nufi Motansa, yana kiciniyar bud'ewa yaji Sallama a bayansa,

Binsu yake da kallo cikin damuwa, d'aya daga cikinsu ya mik'a masa Hanu Bai damu da yanayin da yaganshiba, yafara masa bayanin dalilin zuwansu,


"Munzone daga office d'in SS, Wanda suke Bincike
Game da Guban da Dr KB yaci, d'an Gida Alhaji Mahmud Maitama, Mun d'au lokaci muna gudanar da Bincike sai yanzu mukasamu Cikakken Sakamakon Bincikenmu tare da Gamsassun Bayanai daga Bakin Mutune uku,


Na farko K'awar 'yarka Mai Suna Meenat, da ita maiyin cake d'in, da wacca suke xaune Gida d'aya, kancewa Mahaifiyar Nafisa Matarka kenan, ita tabada Guban da Hanunta ta bayarma mai tayata aikin Cake d'in Guba tasa a Cake d'in tabata kud'i Naira Dubu Goma,


Shine mukazo zamu tafi da ita, idan ta amsa daga nan sai Mu mik'ata Kotu,

Ayankemata Hukunci,


Alhaji Ya'u ya share zufan da ya ketomasa,

Yace " ita Baiwar Allahn da kuke Magana akantan yanzu haka tana Gadon Asibiti, yanzu akamin waya aka sanar da ni, ya fad'a cikin tashin Hankali da bugawan zuciya,


"d'aya daga cikin ss d'in yace to ba damuwa muje Office d'in namu da kai, akwai tambayoyin da kaima zamumaka,


Haka suka tusa k'eyansa suka tafi dashi,


*******
Yau Kwanan Maman Nafisa Uku a gadon Asibiti cikin mawuyacin Halin da har yanzu ba asan matsayintaba,

Nafisan tana zaune akan kujeran da yake Fuskantanta, Rik'e da Hanun da aka mata k'arin Ruwa,

Wayanta yayi Ruri cikin Sauri ta d'auka ta kara akunnenta, lokaci d'aya ta saki kuka tana fad'in "Hello Umma Hauwa dan Allah kitaimakeni inacikin wani Hali na tashin Hankali, ki k'ira Bokannan ya miki bayanin yanda za'ayi amfani da Magungunan da yaba Mama, naga tazo da magungunan da bata tab'a zuwa dashiba, da alama wannan na musamman ne Za'ayi Nasara,


Shiru tay na d'an lokaci sannan ta k'ara sautin kukanta, cikin Magiya tace, "Yauwa Umma ta ki taimakeni wlh duk wanda mukayi ya karye, Rayuwata tana cikin Hatsari in Boka bai taimakeniba, da wanne zanji ga Maman kwance kaman zata mutu, ga Dadyna wai yana hanun Ss, Sannan ga KB tunda yazo sau biyu bai k'ara lek'oniba, Narasa inda zansa Rayuwana, ta rushe da Kuka,


Ahnkali Mami ta turo k'ofa ta shigo, da Sallamanta, Nafisa ta juyo ta kalleta tana share Hawaye, tayi saurin katse k'iran tana mata sannu da zuwa,


Mami ta amsa gami da jawo kujera ta zauna, tana kallonta cikin matsanancin tausayin Halin da mahaifiyarta tajefata,


Na yanda ta mik'a lamuranta gaba d'aya ma wanin Allah, sai yanzu da taji wayan da Nafisan tayi ta k'ara yarda da tagama Nisa Sosai, tayi imani da lamarin Bokaye fiye da tunanin Mutum, ta yarda cewa ba zata samu wani abuba sai ta hanyansu, taja dogon Numfashi cikin takaici da tuna cewa watak'ila tana iya haihuwa da d'anta, itama ta tarbiyartar mata da jika da irin Tarbiyan da akamata,


"Ina wuni, muryan Nafisan ya dawo da ita duniyar tunanin data lula,

Ta kalleta Gami da fad'in "lfy, ya Mai jikin?
"Da sauk'i tace kanta a sunkuye dan ta tsargu da irin Kallon da Mamin take mata,

Dai2 Lokacin DR KB ya turo k'ofa ya shigo k'ananan kayane ajikinsa, sai Lab coart da ya d'ora akai, wanda aka Rubuta, Cunsult KB ajiki, Idonsa sanye da farin glass, yana rataye da abinnan nasu na Doctors akafad'ansa, wata Nurse tana biye dashi, Fuskansa a murtuk'e ba fara'a, ko kallon inda Nafisan take baiyiba, ya zarce wajen magungunansu yazari Hand glove, ya zira a hanunsa, ya k'arasa jikin Maman ya mannan abu a k'irjinta, yasa akunnensa, na d'an lokaci Sannan ya cire ya d'an ja k'afantan da yake nannad'e da bandage ya jujjuyashi, Sannan ya zare Glove d'in yasa a Dosbing, ya juya zai fita, Mami tace "Dr bakamana bayanin awani Conditoin fetiant d'inmu takeba, da sauri ya maida kallonsa ga inda yaji Muryan Maminsa, dan sam yaga alaman da mutum a d'akin anma bai d'aga kai ya kalla wajenba, dan gudun kar yaga wacca ya tsana acikin Mutanen Nafisa, wato Meena.


Murmushi ya fitar da ya bayyana Hak'oransa a fili yana shafa kansa, "My Mum dama kece anan?

Mami tad'an had'e Rai, "No likita inason jin halin da Majinyaciyanmu take cikine ba wani abuba,

Yad'an gyara tsayuwansa, ya gyad'a kai "Ba wani sabon abubane bayan wanda a kagayamuku, sakamakon harbin dake kafad'anta da k'afanta ya jawo za'a yanke K'afan dan harbin ya illata k'ashin wajen ta yanda ba zai gyaruba sai dai a cire, sai kuma Sanadin wani dalili da mu ba musanshiba, yasa Zuciyanta ya buga ta yanda dai Rayuwanta sai ahankali,


Wani irin ihun da Nafisa tayine ya dakatar dashi, tare da firgitasu gaba d'ayansu d'akin, hatta Mamantan da take halin Bacci ko suma ne oho, sai da ta zabura, ahankali take bud'e idonta har ta bud'esu gaba d'aya, Ta gefe KB yabi ya fice daga d'akin yabar Nafisa tana kuka gami da Maganganu marasa dad'i,

Tunanin Halin da baro Dijah take yakeyi, dukda Dr Husna tace yaron cikinta yana cikin k'oshin lfy.

"Aminu Aminu kaine haka? Haka kadawo? Fashi!!..... Ni .....zaka harba.....nifa nahaifeka...... Kazo mukoma munasonka.... Dan Allah Aminu...

Cikin Sauri Nafisa da Mami sukayi kanta, Nafisa Tasa Hanu ta rufemata baki, cikin kuka tace "Mama kinsa Aminunki da yawa a ranki, zaki ganshi da yardan Allah zai dawo garemu bata wannan mummunan hanya da kike fad'iba ta ya d'anki na cikinki zai harbeki? Koda akayima yaya Aminu Asiri ya shiga Duniya bazai tab'ayin fashiba, Ta k'arashe cikin kuka tana janye Hanunta a bakinta,


Cikin dishashshiyar Murya Maman tace "Shine Nafisa Aminune acikin 'yanfashin da suka tare motan da nake ciki lokacin da nafito daga wajen Boka, dan karb'o miki Maganin da zaki Mallaki Kabir da kuma wanda Zamu kashe Uwarsa da matarsa, cikin k'araji Nafisa ta sake Rufe Bakin Maman tana fad'in "K'aryane Mama xafin ciwone yasaki wannan Maganganun, Dan Allah kiyi shiru,


Mami tayi Murmushi ta janye Hanun Nafisa tana kallon indonta da tsoro da tashin hankali ya bayyana a cikinsu k'arara,


Ta Girgiza kai a hankali tace "Karkiji tsorona ko kunyana Nafisa, Allah shine abun tsoro da kunyan sab'amishi ni bani da wuta bani da Aljannanhn saku, Allah ke da wannan, Sannan nayi imani ba wanda ya isa katse Rayuwata har sai Allah ya kawo k'arshen Rayuwata,


Ta koma ta zauna a hankali akan kujera tana cigaba da kallon Nafisa da zufa ke fitomata,


"Tuni nasan abunda ke gudana atsakaninku Nafisa, sai dai ni ke nafi ji, Ba itaba, Dan ita ta girma kece da sauran Barka yanzu dai halin da Mahaifiyarkin takeciki kad'ai ya isheki Isahara, ki hak'ura haka ki mik'a lamarinki ma Ubangijinki, dan kitsira duniya da lahira, Ta mik'e tana fad'in nixan tafi Allah yabata lfy kidage da Addu'a shine mafitanmu yanzu zan turo wacce zata zauna da ita ke ki koma gida ki huta haka kinji? Allah yabata lfy, kasa cewa komi Nafisa tayi tabita da kallo har ta fice sannan ta dawo da kallonta ga Mamanta da taci gaba da Baccinta,


Tana shirin zama Dadynta ya shigo da Sallamansa, duk ya Rame ya fita a hayyacinsa, yaja kujera ya zauna, ba tare da ya tambayi me jikiba,

Yafara fad'a, "Kingani ko? Kinga irinta ko Nafisa? Ga abinda Sakarcin Uwanki ya janyomana sai da nahanaku Maganan sa Gubannan kukak'i ji, Yanzu kinga zasu kai kotu, k'arshenta kuma prison dakuyi, meyasa kika biyemata?



Wani irin kuka Nafisa ta rushe dashi tamarasa kukan me d'aya zatayi, ji take kaman zuciyarta zata fito waje dan damuwa da ya cikata, cikin tashin Hankali ya dafe kanshi yana jin kukan 'yar tashi har cikin Ransa,

Can dai ya mik'e ya k'arasa kusanta yana lallashinta da k'yar ya samu tayi shiru, yace nasan mezanyi, wasan ya kusa ya k'are gaba d'aya, daga Haka ya fice,

********


Kaiwa da kawowa Dr Kb yake tayi a d'akinsa cikin damuwa yana sanye da Rigan Bacci, can wani tunani ya zo masa, da sauri ya nufi Drowern gadonsa ya janyo ya dinga birkitawa cikin sa'a yasamu abunda yake nima, ya d'auka gami da sake d'an Murmushi, ya fita, taku yake cike da k'arfin gwiwa, har ya isa, yasa key d'in ya murd'a, sai da yasaki wani k'ak'k'arfan ajiyan zuciya, gami da Murmushi, a hanakali yake takawa yana bim illahirin Palourn da kallo ga wani daddad'an k'amshi dake yawo a hancinsa, ko ina tsaf gwanin sha'awa, ba k'aramin Missing sashin yayiba da mai sashin gaba d'aya,

Bed Room ya nufa yana tafiya yana kalle2 can ya hangota kwance a saman Kujera hanunta rik'e da remot, ta matse d'an k'aramin pillown kujeran a tsakanin k'afafunta, da zumud'i ya k'arasa ya durk'usa daf fuskanta, har suna musayan Numfashi, jin k'anshinta yakeyi har cikin k'wak'wakwansa, yana zaga jikinsa, Rigane mai Hanun Best da gajeren wando masu taushi jajaye ajikinta, Cikinta ya bayyana Sosai a cikin Rigan, yad'anyi Murmushi yana kallon hanunta dake Rik'e da Remot d'in da alama tana cikin canja tashane Baccin ya sureta, yasa hanu ya cire Remot d'in gami da Mannamata pick a saman lips d'inta, ahankali ya furta "Imissed U so Much my Luvly Wife, ya kashe T.vn da wutan d'akin ya zo ya d'auketa a hankali yake tafiya, har ya shige Bed Room d'in ya kwantar da ita akan gado ya tage Hasken d'akin ya saura sai na jikin gado, ya kwanta suna Fuskantan Juna, ya rungumeta ajikinsa, a tare suka saki wani irin ajiyan zuciya, ya lumshe ido yana shak'an k'amshin jikinta da yayi tsananin kewansa, jin wani irin yanayi da tajima rabon da taji ajikintane, yasa ta fara mutsu2 tana tureshi shikuma sai dad'a shiga jikinta yakeyi,


Ta bud'e idonta a tsorace ta tashi ta zauna tana mutstsike idon, ganin Kb tayi ya k'uramata ido, yanayinsa gaba d'aya ya canza, sai juya kai yake idonsa jazur, Rai a b'ace tace "lfy?


Ya had'a Hannayensa Biyu yana Girgiza kai,
"Pls Khadijah horon ya isa haka, kin hukuntani da yawa akan laifin da ba nawaba, ki taimakeni kiji tausayina, yanzu kibani a k'alla 10 Minuts daga baya sai muyi magana kinsan komi Khadijah wlh ba laifina bane, ki taimakeni nayi missing naki da yawa pls, ya k'arashe kaman zaiyi kuka yana jawota jikinsa, taso ta bijiremasa sai dai tana tuna laifin da zatayi ma Ubangijinta, dan haka kawai ta fashe da kuka ya jawota jikinsa gami da tura bakinsa cikin nata yana tsotsa kaman zautacce,



Sosai Ma'auratan suka nuna ma junansu irin Missing juna da sukayi,

*********

Kabir ya Rungume Khadijah tsam a k'irjinsa yana kallon fuskanta, "My Luv meyasa kikadinga Rufemin k'ofa kikak'i barina in zo gareki? Sai yau na tuna ina da master key da zai iya bud'emin k'ofanki, koda da makuli ajiki ta ciki, yafad'a yana shafa cikinta,

D'an hararansa tayi tana bugun k'irjinsa, ta turo baki, "to ba kai bane,

Ya kamo lips d'inta da bakinsa ya dinga tsotsa, da k'yar ta k'waci bakinta ganin yana shirin sake rikicewa,

Dukansu suka saki dariya, yace "Gaskiya nayi missing naki da yawa babyna, keda my Little baby, yafad'a yana shafa cikinta,



"muma munyi Missing naka Honey lokaci guda ka gujemu ka juya mana baya ba tare da munmaka komiba,

Yad'an ciza lips d'insa yana jin zafin abunda ya faru abaya, yana shafa bayanta yace "Kiyi hak'uri Babyna kinsan cewa da gangan bazanmuku hakaba, anma insha Allah da Izinin Allah ba wani shaid'anin da zai kuma shiga tsakaninmu, tabbas abaya mun d'anyi sakaci da Addu'o'i anma yanzu nagano lllan hakan bazan kuma yarda hakan ya faruba, ki yafemin kinji?,


Tasa hanu tana shafa gashin k'irjinsa tana murmushi zuciyanta cike da farin ciki, taja Hancinsa, "O'o sai ka goyeni in hak'ura, da sauri ya tashi ya juyo baynasa, " Bismillah indai hakan zai sa ki huce ki hak'ura zo ingoyaki Luver na,


Tasowa tayi tana dariya ta haye bayansa ya dinga zaga d'akin da ita suna dariya, daga bisani yazo ya direta akan gadon yana haki,

"Gaskiya kuna da nauyi 'yan mata anyah kuwa ku biyune kawai? Kai inaga kun kai uku Gobe in Allah ya kaimu zan bincika ingani, inaga twince ne anan ya fad'a yana shafa cikinta,

Ta dafe Hanunsa tana tura baki "Ni dai gaskiya ina tsoron haihuwan twince ance suna da wahala,

"waya gayamiki? Basu da wani wahala, inkinci sa'ama kukansune zai d'agaki daga barci namiki labour da haihuwan,

Dijah ta zaro ido, kamin labour da Haihuwan kuma? Likita dama ana hakane?

Ya d'an had'e Rai alaman Gaskiya yace "K'warai kuwa to barin baki lbrn Maman twince Nurse d'innan da muke aiki tare matar Dr Na'im, Ranan muna Round da ita, bayan mungama sai naji tana cema Nusaiba k'awarta tanajin Bacci, Sai ta shiga Office ta kwanta bacci, ni kuma dana dawo Office d'ina sai na samu Dr Na'im a zaune yana ta zufa, dana tambayeshi meyafaru? Sai yacemin wai nak'uda yakeyi, nazaci wasane, can najimiki d'an banza yayi Ihu, na shareshi kaman bansan meyakeyiba, naci gaba da aikina, sai kawai naga ya tashi ya fita, sai gashi yazo da twince, ashe da gaske shi yamata Labourn itakuma ta haifomasa su, Dijah ta kwashe da Dariya ganin yanda ya dage yanason Raina mata Hankali, tace "Ashe Dr Na'im d'innan d'an baiwane, KB yayi Fuska "ke ni nafishi k'ok'ari Zakiga ranan namu ko motsi bazanyiba zamu haifo namu, tace dagaske? Yad'aga gira k'warai, ta k'ank'ameshi tana murna, tace "shiyasa nake Sonka Likitana, Allah yabamu har 'yan Ukuma, shima Rungumeta yayi yana ta zabga dariya batare da ta fahimci dariyan da yakeyiba,


Haka suka dinga hira da shewa gaba d'aya sun mance da darene, har sai da sukaji ana assalatu, Kb ya zaro ido,

"Ke kiga yanda kika hanamu Bacci Baby,

Dijah ta tura Baki tana Hararansa, Allah kaine ka hanamu Bacci, ta juya baya ta Rufe ido, "Ni dai barinyi Baccina,

Yana Murmushi ya jawota ya d'agata,
"Ai baki isa yin Bacci yanzuba My Luve sai kinyi Sallah,


Yana rik'e da Hanunta har bayi, su kayi wanka suka d'auro Alola, sai da yayi Raka'atanil fajir ya wuce masallaci,

Akwance ya dawo ya samu Dijah, tana shirin yin Bacci,

Saida ya zare jallabiyansa kafin ya d'agota, yana Rik'e da Hanunta, ya kaita Dining ya jawo kujera ya zaunar da ita, sai da yakai mata Pick a kumatunta ya kalleta gami da d'aga Gira yace "Give me Two Minuts Baby,


Dijah ta lank'washe kai gami da tattare Fuska kaman zatayi Kuka tace "pls Honey wlh Bacci nakeji, ya kashemata ido,

Gami da kwab'e fuska kaman yandatayi ya lank'washe Murya, yace "Only 2 Minuts fa Baby, Bai sauraretaba ya shiga kitchen, acikin Mintunan da basufi biyun ba ya Soya k'oy gami da dafa Ruwan tea mai kayan k'amshi ya fito da su, ya dire a gabanta, yahad'a mata tea ya saisaita, Sannan ya zauna ya turomata gabanta, da ido yamata alama da Bismillah, ta kalleshi ta kwashe da dariya har tana rik'e ciki, sai zufa yakeyi kaman wanda ya dafa wani Abu mai tsaban wahala,


Ya d'an had'e gira yana hararanta,
"Kinsan Allah zan fasa tayaki haihuwan ke kad'anki zaki haife yaranki, ta d'an sassauta dariyanta, tace "Sory Nawan naga yanda kayi zufane kaman wanda yayi dakan sakwara,

"Mhmm kisha tean kije ki kwanta, Kar kisani inmakara a Office, yafad'a yana kai Cup d'in Bakinta,


Saida ya tabbatar ta k'oshi ya rik'e hanunta takaita har Kan Beed d'inta, sai da ta kwanta yajamata Bargo, yayi kissing goshinta yace, "inkingama Baccinki kimin nawa kinji Baby, Na tafi,

Ta Lumshe ido tana kallonsa tace,
"Allah ya kiyaye, Allah yabada sa'a Honeyna,

Sai da yaja numfashi mai sanyi, yace "Ameen Khadijah na, ina sonki Babyna Allah yabarmin ke, yafad'a yana kashe ido, Sannan ya fita,



Cikin sauri yake shiri, yana d'aura Belt d'insa yaji sheshshek'an Kuka a bayansa,


A hankali ya juya, Nafisa ya gani tsaye ta Jingina kanta da jikin k'ofa, ta koma kalan tausayi, Kamar wata Mutuniyar Kirki, mai da Kansa yayi yana cigaba da shirinsa,


Ta tako a hankali ta k'araso ta tsaya a agabansa, cikin sauri ya k'arasa abunda yakeyi ya d'auki Brief Case d'insa, ya rab'a Gefenta Zai fita,

Ta saki wani irin Kuka mai cin rai da yasa Kabir sake kallonta bai shiryaba, wani irin matsanancin tausayinta yaji aransa, ba sai angayamakaba zaka gano tsantsan damuwa atare da ita wanda ya haddasamata Mugun Rama kaman wacce ta shekara tana jinya, idonta sun kumbura Fulu fulu sunyi jazur wanda zai tabbatarmaka da irin kukan da taci da rashin bacci da tayi,


Sosai yakeson ya danne Tausayintan, danso yake yamata Horo mai tsanani dan ta kiyaye abunda ta Aikata nan gaba, ya juya zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login