Showing 21001 words to 24000 words out of 155892 words

Chapter 8 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

461

ta rafka tagumi,
Asanyaye Dijah ta iso ta tsiguna agefe,
"wai Dijah meyasa ne baki jin magana, ban hanaki tsayuwa bayan kuntaso daga makarantaba? Wai yau harkece da fad'a akan saurayi Dijah? Yaushema kk kula Lado? Yaron da sai yazo yayi aika so goma baki fitaba, naga ko sunansa aka fad'a sai kin b'ata rai, shine don tsaban iyawa harda tare "yar mutane akanshi,
Wani irin kunya mai tsananine ya rufe Dijah, ji take kaman k'asa ya tsage tashiga ada tasan Bintalo takan rufa mata asiri, kotayi wani abun awaje batacika fad'a agida ba tabbasa da tasan Bintalo zata mata haka bazata bari taji ba, wani irin zufa taji yana bin jikinta, tsaban takaici sai kawai tasaki kuka,
Sosai Bintalo tayi nadaman fad'a ma inna da tayi, musamman ma yanda taga Dijah tana kuka, ba makawa tasan bashi taci awajen ta sai dai fatanta Allah yasa kar Dijah ta mata mummunan ramuwa,
Kuka takeyi bil hak'k'i ahaka Baffa ya shigo yasameta dasauri, ta tashi ta rik'e kekensa "Sannu da dawowa Baffa tagad'a tana share hawaye, Ran Baffa bak'aramin b'aci yayiba, Don in Akwai Abunda Yatsana kukan Dijah ne,
Tana sauk'e kayan Abincin da ya shigo dashi akan keke tana kukanta, har tagama sauk'ewa,


Hanunta yakamo rai b'ace yanufi inda Inna take,
"me kukayi mata? Ya tambayi inna yana mata wani irin kallo, aza bure Dijah take kallon inna tana juya kanta, inna ta fahimci Dijah bataso Baffa yaji, murmushi tayi "katambayeta tayi maka bayani da kanta, Bak'in halintane inaga ya motsa,


Nan dai yayi ta fad'an dayasaba sai da yayi yagaji don kansa,

Ya shiga d'aki Inna tace "ki wuce kije kicire kayan makarantan kizo ki kwashi Abincin Bak'innan kikai musu,


Su biyune ad'akin Kabir da Habib, suna Hiransu Habib yana rik'e da Hanun KB yana d'an matsamasa,

Ta shigo da tray d'in Abinci tunda ta shawo kwanan d'akin Kb yake Kallonta, sallama tayi Habib ne kawai ya Amsa, ta dire tray d'in a gefe ta d'ago ta kalli Habib akunyace tace ina wuni, lfy Beatiful girl yana murmushi,
Ta juyo ga kabir "inawuni, caraf idonsu suka had'u, Dam taji k'irjinta ya buga ta tsaya baki bud'e tana kallonsa yamurtuk'e fuska yana hararanta, yace "Malama Kallon ya isa haka ko, ai sai kitashi ki k'ara wuta, dama d'an k'auye ako ina sai yanuna k'auyancinsa, bandahaka meye Abun kallon?, mtss yaja Dogon tsaki, cikin zafin Nama ta mik'e saida tafita tasa takalmin ta tayi taku Biyu ta juyo Rik'e da kunkuminta, ta zabga mishi Hararan sama da k'asa sannan taja tsaki ta tafi, Habib ya kece da dariya har yana rik'e ciki shi kuma gogan ji yake kamar zuciyansa tafito din takaici, arayuwansa yatsani raini,






*Tofah Anya KB kasan waye Dijah kuwa? πŸ€” ka takalota kuma kace bakason raini?* 😳







Ku biyoni


*Ummu fatima* πŸ‡³πŸ‡¬
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣3⃣


Sai bayan la'asar sosai, su Uncle Musa suka dawo,

K'aton Generator suka sayo Da kayan Electronic, irinsu, fanka, frich Tv, lokacin da motar ta tsayane wani d'an makocinsu Saurayi mai suna Iro yazo ya dinga shigar musu da kayan sannan yatayasu gyara wajen, capet suka malala d'akin sanna suka sa k'atuwar katifa Gado huta da kujerun Roba guda Hud'u, Basu bar garinba saida aka gama shirya komi,

Har makanike aka k'ira ya had'a Generator yasa Tv yasa Dish, aka kunna frich Iro ya jera Ruwan faro aciki da sauran Drinks kala2,

Tuni Gurin yayi fes kaman ba acikin Rugan juma ba, Iro kam sake baki yayi yana bin d'akin da kallo aranshi yace "lallai Ni'ima na birni, jinyanma bazai iyayi hakaba sai sunmayar da d'akin irin nasu,


Sai wajen Daf Magriba, suka musu sallama sukatafi,


Saida akayi sallahn Isha'i suka isa uncle Musa wajen Mami ya wuce kai tsaye,

Nafisa ya samu a falo ta kifa kanta ajikin kujera, sallamansa ne yasa ta d'ago kanta, tagaishi tace "barin k'ira Mamin, da kai ya amsa mata ta haye sama jim kad'an Mami tazo, "Yaya shigowan dare kukayine? "wlh kuwa nasan kin matsu kiji lbrn d'anki, dariya kawai tayi
Shima dariyan yakeyi yazauna suka gaisa, "ya me jikin dai? "jiki Alhamdulillahi,
Nan ya gayamata duk yanda akayi, sannan ya d'ora da "wannan kaman "yar wajen Ya'un nanane ko? "Eh Nafisa ba itace, "inafatan baki sanar da ita ansamu Kabir ba "Bangayamataba amma yanda tad'aga hankilinta naso ingayamata "to kar kifara nagayamiki akwai binceken da mukeyi, abunda yasa nace inkundawo inason magana dakai,
"Dama Alhaji Ya'u ne ya matsamin akan maganan Campani Wai anrufe acount d'in Campanin kullum yana gidannan jiya karkaga irin Haukan dayamin yau kuma tun safe yazo wai Nafisa ta koma gida tunda tak'i karatu nayi ta bashi hak'uri bai saurarenba ita kuma tak'i ta koma, dariya yayi yana gyad'a kai yace "yasake tambayanki Kabir?
"cemin yayi yabayar ayi istihara indai Kabir na raye nan da sati zai bayyana inkuma bai bayyanaba, to ya mutu,
mik'ewa Uncle Musa yayi yana Dariya, yace inyasake miki maganan campani kice yasameni da maganan, sannan maganan yarinya, baruwanki in yamatsa takoma naki ido, duk da Mami bata fahimci komiba, ta karb'i shawaran yayan nata don ta lura kwanann Alhaji Ya'u yana nima yacanza Hali,

Washi Gari da safe Mami ta fita ta shiga side d'in KB, zama tayi akan kujera sannan tak'ira wayan Habib alokacin ya ciro sabuwar wayan Kabir acaji yana samasa layi, yana d'auka gaisuwa kawai sukayi yaba ma Kb, jin muryan Mami ne yasashi ya lumshi ido ya bud'e jiyake kaman ya rufe ido ya bud'e yaganshi agaban maminsa, ba k'atamin kewanta yayiba, jin sauk'an nunfaahinsane yasa tayi dariya, "Helo Kabir murmushi yayi yace "Mamina kina lfy?
"Lfy lau Kabir ya jikinnaka?
"Alhamdulillah Mami na,
"to Allah yabaka lfy Kabir d'in Mami,
"Ameen wai jibi za'a kunce Mami kisani a Addu'a Allah yasa akunce a sa'a,
"To Kabir Addu'a kam kullum yinta mukeyi sai dai ak'ara,
Wai yaushe Habib zaidawone?
"wai yace sai nan da sati biyu,
"a'a yaushe za'ayi haka kai baka zuwa aiki shima bayazuwa?
Munyi waya da Sani zaizo ya karb'i shi inyaso inya dawo sai yadinga zuwa a weekend yana dubaka,
"to Mami Allah ya kaimu Nagode,

Dahaka sukayi sallama ya mik'a masa wayan yayi masa bayanin yanda sukayi da Mami,

Sallama sukaji anayi, Habibne ya amsa ta d'aga labulen tashigo cikin nitsiwa ta tsuguna tagai dashi, ta kalli Kabir "ya jikin? Yana murmushi ya Amsa da Alhamdulillah,


Ta mik'e zata fita yace "Mmn nace ba, dawowa tayi ta tsuguna tana kallonsa, Meye Sunanki ne?
"Sunana Bintalo,
"Bintalo kuma? Wani irin sunane haka?
"Fatima, zaro ido yayi waje yana kallonta asalin sunanki kenan tomeye alak'an wannan Babban suna da Bintalo, Fatima sunan Mamatace, Habib yace "Daga Fatima suka mayar dashi Binta daga Binta kuma shine akasake cewa Bintalo, Kabir yace "Ayyah mai sunan Mami ta kar ki sake cewa Sunanki Bintalo kinji
Sunanki Fatima Babban sunane dake, to tace ta mik'e tana tattara kwanukan dasuka karya fasu, Habib yace "ina k'anwan kinnan? Meye sunanta? "Dijah, tana gida "ok inkinshiga kice ina gaisheta, "to daga haka ta fito awajen wanke wanke tasamu Dijah ta kad'a kumfa sai shek'eshi takeyi fa cup kaman mai sai saita shayi,
Bintalo ta zauna agefe tana kallonta dama inzasuyi wanke wanke Dijah ce take wanke wa Bintalo tana d'aurayewa, don kozatayi ya Dijah bazata bata wanke wanba,
Ganin bata da niyan fara wankewan ne yasa tace "Dijah ki bar wasannan haka ki fara wankewa zamuje d'ibo Ruwafa,
Dijah ta Murgud'a baki "Bazanyinba ina Ruwanki dani?
"Da Ruwana inbazakiyiba kibani Inyi nawa intashi, Hararanta kawai Dijah tayi tacigaba da wasanta, ganin haka yasa Bintalo ta d'auko omo ta kad'a kumfanta zatayi wanke waken, Dijah kuma tace bata iya jiba,

Da k'afanta tabuge kumfan tazubar, Bintalo tajawo wanda take wasan dashi zatayi wanke wanken, Dijah ta d'auke nandai kokuwa ya kaure, kai kai, suka jiyo muryan Inna abayansu, Rik'o Hanun Dijah tayi tana tambayan meya had'asu, Dijah tana hak'i tace "wai don tace min zata aikeni wajen Ila nace bazan jeba shine kawai ta dakeni, cikin tashin Hankali Bintalo ta zaro ido ta dafe k'irjinta, "Ni? Ni zakiyima sharri?
"Eh mana ba sharribane jiyama inaji dayazo Hira kinace masa kina sonsa cikin zafin nama da b'acin rai Bintalo takai ma bakinta bugu, kokuwa suka sake kaurewa dashi Inna ta Rabasu Bintalo ta fashe da kuka tana kallon Inna "wlh Inna k'arya takemin
"Ba karyabane Inna rananma har wasik'a ta rubutamishi yanzu haka yana jakanta,

wayyo Bintalo kaman tayi hauka tsaban kunya gami da takaici uwa uba tanaganin kaman inna tana mata kallon shikenan kinzama "yar iska,

tana share hawaye tace "Wlh Inna sharri takemin

Inna tace "wuce kitafi abunki kibarta tayi wanke wanke ita kad'ai, inna takalli Dijah tana jijjiga kai Dijah Allah dai ya shiryar dake Addu'an danake miki kenan kullum nabaki minti biyu kacal kiyi ki tashi awurinnan ku d'bo Ruwa, daga haka ta wuce d'akinta,


Sauri sauri Dijah tayi tagama, ta shiga d'akin kwanansu ita da Bintalo, alokacin Bintalo tana Assigment d'inta da aka basu, Dijah ta tsaya mata akai

"kitashi muje d'ibo Ruwan, Bintalo bata kulataba tasake magana, Bintalo ta zab gamata Harara bazanjeba, uwarmarasa kunya, Da k'arfi Dijah tace "Inna ga Bintalo tana k'irga k'waryan tarunta, wai tace ita da guda goma sun mata kad'an,

azuciye Bintalo ta tashi ta Cafko Dijah, Inna tana jinsu tayi kaman bata jiba,

Sarai tagane cewa Dijah tana rama Abunda Bintalo tazo tafad'a ne randa ta tare Larito akan Lado,

Inna rik'e hab'a tayi
"oh ni jikan Adamu naga takaina ayi yarinya da nacin fad'a, wai ba'a isa ayima Dijah abu ta hak'uraba sai ta rama? Aidai Baffanki mai goyamiki bayan bayanan bari dai inbarki da Bintalon yaukam kin k'urota,
Tanajin tana ihu amma har yanzu bakinta bai mutuba, sai k'ara wasu sharrin takeyi,

Ahaka kuma take k'iran sunan Inna
"bazan zoba
Dijah saikin ji jiki, ke ba k'arfin kobo sai tsiwa da karad'i

Saida Inna ta fahimci Dijah taji jiki sosai tukun taje rabiya, don dai Dijah ko agun sa'anninta bakintane ke cetonta, indai k'arfine to bata da na ko sisi,

Ahakanma da k'yar Inna ta fitar da ita ad'akin don kafewa tayi da magana wai sai ta rama.

Har ga Allah badun Inna tana tunanin kar Baffa ya shigo yanzuba da tabarsu ta d'an k'ara dakata don ta lura har yanzu bakinta bai mutuba, kuka tayi kaman zatayi yaya har sai da Inna ta koma rarrashinta ta kwantar da ita akan cinyanta da k'yar tasamu tayi shiru ahaka Barci ya d'auketa, Inna ta kalleta sai jan zuciya takeyi, ta girgiza kai tana murmushi, . "Dijah am Allah ya shiryeki, anan ta zamar da kanta ta kwantar da ita ta tashi,


Yaune Kabir yake da sati Guda d'aurinsa,
Bayan Baffa ya shigo gida ya shiga shashin su Kb da niyan gaishesu kaman yanda yasaba,

Bayan sungaisa ne Habib yace ma Baffah, yau zai koma bakin aikinsa Sannan suna sa ran ayaune Sani zai zo Baffa yace "To Allah yakiyaye hanya shima yau za'a kunce d'aurin,

Ya kalli Kabir yana mik'ewa Yace " anjima Dijah zata zo ta kuncemaka d'ori nizanje can wani k'auye gaida Abokin mahaifina,

"Ah Baffa itama Dijahn ta iya hark'an d'orine Habib ya tambya don ya kula Kabir ya harzuk'a sosai da jin Wai Dijah ce zata kuncemasa d'ori
Baffah yace "Eh ai takanyi d'orinma ta iya sosai wano lokacinma nata yakan fi nawan kyau, daga Haka Baffa ya fita
Habib ya saci kallon Kb sai wani had'a rai yakeyi sai k'unshe dariya yakeyi,
"yadai kb?
Kb yaja dogon tsaki wanna "yar rainain hankalinne zata kuncenin k'afa?


" Kai dai wlh kad'au zafi da yarinyan nanne nibanga matsalantaba wlh ni inajin dad'in hira da ita, wani uban hara kb ya masa Habib yafita yana dariya "barin sayo kati abakin hanya,

Wanka tayi ta fito cikin doguwan Riga na atamfa yellow d'nkwali kawai ta d'aura, tafito tasaka hijabi ta d'auki maganin da Baffa yabata tashafa ma Kb,

Da sallama ta shiga d'akin aciki ya ansamata, tunda ta shigo yake mata kallon wulakanci,

"wai ke baki san k'aidan sallma bane? Dakin yi salkam baki jiran abaki izini, mtsss yaja tsaki,
Turo bakinta tayi ta tsuguna agabanshi, "Baffa ne yace inkunce maka k'afa kallonta kawai yakeyi baice mata komiba, ta ajiye maganin ta matso, da k'arfi ta rik'o k'afan
Ahsh ya furta yana rintse idonsa ta fara kuncewa k'afan sai b'ari yakeyi, ta d'ago ta kalleshi, "af ashe kai ragone? Kodayake wannan kad'anne da aikin "yan birni ba abunda suka iya sai raki da ragwantaka,
Inkasan zaka b'atamin lokaci kawai inje unk'ira gardawa jaruman "yan k'auye su ruk'eka,

Tunda ta fara maganan kallonta kawai yakeyi baya ko rintsawa,

Ji yake kaman ya kifamata mari da gangan tafara jan igiyan da d'an k'arfi bai san likacin da ya dafe hanuntaba ta d'ago suka kafe juna da ido wani abu kb yakeji namasa Yawo tunda ga d'an yatsansa,

Zame hanunta tayi ta fita sai gata tadawo da wasu k'atti bak'aramin mamaki Kb yayi ba to wainnanfa?

Aibaigama tunaniba yaji tace ku damk'eshi sosai Don Allah sama da sati biyu kenan ankasa kuncewa, amma fa sai kunyi dagaske,

Kb baiyi auneba sai ji yayi su rirrik'eshi ta baya, suna masa sannu Dijah tayi murmushin Mugunta, ta tsuguna tafara kuncemasa ahankali,

Haka Kb yanaji yana gani da yad'anyi motsi k'attinnan zasu sake damk'eshi ahaka har tagama kunce duka k'afafun, dai2 lokacin kuma su Habib suka shigo shida Iro,

Cikin mamaki Habib yake binsu da kallo, Dijah tace musu "shikenan mungode,
Suka sakeshi sai sannu suke jeromasa gamida Allah yabada lfy,
Tsananin takaicine yahana Kb yin koda motsine binsu yakeyi da kallo har suka fice sannan yadawo da kallonsa ga Dijah da take gaida Habib cike da ladabi kaman da gaske binta yayi da kallo har tafita, sannan ta dawo da baya tana masa wani kallon rainin Hankali "inka d'an huta zanzo inshafamaka wannan maganin daga haka ta fice,

Habib ya matsoshi yana kallon k'afan
"Man wai sai da aka rik'ekane aka kunce?
Haba kai kuwa katsaya aka d'aurama balle kucewa?


🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣

*ummu fatimac* πŸ‡³πŸ‡¬
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login