Showing 63001 words to 66000 words out of 155892 words

Chapter 22 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

462

duk yanda yaso da yacire duk wata damuwa da matsala aransa abun ya fasakara


Ba abunda yafi tsayamasa aransa irin furucin Mami nacewa In Khadijah tagama Makaranta zata maidata Garinsu ko ta aurar da ita shin hakan yana nufin tayi fushi dashine?

Kuma to meye matsayin Aurensa akanta?

Abunda yake tayi kenan yasak'a wancan ya kunci.


Ahaka Yaji ana niman ordern shigowa, nan yaba da ordern Habib ne yashigo yazauna Kujeran gefensa yana kallonsa "Man yadai? Tun jiya banganemakaba any problem?

Tab'e baki Kabir yayi gami da ajiyan Numfashi mai k'arfi yad'an kishingid'a acikin kujera, Habib ya d'anyi Murmushi.


"Yauwa Mami ce ta k'irani ashe Khadijah bata da lfy ne? Kabir ka bata Midicine mana.


Hararanshi Kabir yayi "a wani dalilin?

"Dalilin fanninkane kafini k'warewa a fagen.

"Eh amma ai wainda suka nimokan sunfika sanin hakan ko sokake inyi shishigi?

"Mamice fa tagayamin,

"Eh Mamin, watak'ila tafi yarda dakaine akaina.

"Amma Kb ai kaine....


"Shittt! Malam kaje kayi aikin ka kawai kar kasani aciki.

Habib yayi dariya sannan ya yagi takarda yazaro Biro a Aljihun Kb yana Rubutu d'an karkato kai Kabir yayi yana lek'awa ta wutsiyan ldo Habib d'in yake kallonsa yanagama Rubatawa ya mik'e Kabir ya ja tsaki "Amma dai bakasan mekakeyiba Midicine d'in da Mai hert Disease yakamata yasha kenan?

"Eh asanina shi yakamata Malam banson shishshigi.

"mtsss kb yakuma jan tsaki ya finciki takardan yayaga nan yashiga gayamasa Abunda zai Rubuta shikuma yana Rubutawa.

sai da Habib yanimo Maganin yakai ma Mami Sannan yadawo wajen Kb.

Alokacin har yawatsa Ruwa ya canza kaya, a k'ofan falo suka Had'u, sannan suka koma tare suka shiga Mota, Har sun fara tafiya Habib yajinjina kai "Gaskiiya yarinyannan tana jin jiki, Kb yayi kaman baijiba.



Can anjima ya nisa yana kalon Habib "kasan wai yarinyannane Mami ta had'amu da ita?

Habib ya gimtse Dariyansa yace "Wata yarinyafa?

"Wannan mai rawan kan tsiyannanman.



"Wai Nafisa kake fad'a?

Azafafe yace "Khadijah dai Nafisa kuma tana da rawan kai ne?

Habib ya shek'e da dariya yace "Af zancen yazo kunnenka kenan, yaushe kasamu labari? Ya ciro wayansa ya d'auko masa vidion Auren yace "gashi kaima ka shaida wlh Kb aurenku yayi Albarka kaga jama'a karkaso ka ganni Ranan wlh kaina sai huruwa yakeyi munzama manya, Kabir da ya k'ura ma waya ldo ko k'iftawa bayayi yanajin yanda sunasa yake tayawo a bakin mai shela abun daya k'ara bashi mamaki shine yanda yaga abokansa kaca2 a wajen amma arasa murum d'aya da zai gaya masa.

Dogon tsaki yaja ya wurgo masa wayan acinyansa, Gaskiya kai ba k'aramin Munafukibane shine ko a fuska baka tab'a nunaminba, Gaskiya angama dani yandama naji anata k'iran sunana ana had'awa da nata.

Hahh shiyasa a Ranan kak'irani kakw ta min dariyan iskanci kana hausa.


*Kuyi hak'uri da wannan wlh abubuwane suka sha kaina basonabane bana typing akan kari, sanna kuyi hak'uri da typing Errow masu k'irana awaya da masu min masdage a inbox nagode* 🀝🏻

Ummu fatima ce 😍😳
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣5⃣



*Nafisa*
Tunbayan da Kb yalallab'a Nafisa ya Maidata Gida, a Farfajiiyan Gidan ya hango Alhaji ya'u da Kila suna tattaunawa da Alama Maganan nasu Na sirrine.

Tare suka fito da Nafisa tashiga ciki shikuma ya isa inda suke azaune, tunkafin ya isa yaga yanayin Dadyn nasu ya canza sai mammatse ido yakeyi kaman Mara Gaskiya.

Kujeran da yake gefen Kila yajawo yazauna, yana Fuskantan Dady, yad'anyi k'asa da Kansa suka gaisa, ko kallon lnda Kila yake baiyiba yayi ma Dadyn Sallama ya fice, aguje ya figi Motan ya bad'e wajan da K'ura Maigadi ya bud'e masa yafita Alhaji Ya'u wanda yabi Motan da Mummunan Kallo ya dubi Kila.


"Anyah Yaronnan bai fahimci wani abuba? Shiyasa nace maka inzakazo wajena kadinga b'adda kama karink'a yinshiga na Mutunci yanda bawanda zaiganka awajena ya zargi wani Abun.

Kila ya kece da Dariya yana nuna Alhaji da Hanu "Alhaji ai kamala Afuska take ba arigaba lndai dan wanna banzanne da yazo yana wani Hura Hanci k'amshin Mutuwa ya jiyo, karakadamu tunda ya gagari Bindiga bazai gagari mai kwana Abuzuba.

Murmush Alhaji ya'u yayi sannan ya mik'e yana gyara Babban Rigansa, ya kalli Kila

"Ni zanshiga ciki Kila zan turo maka Kud'in kayi iya k'ok'arin ka komi yazama Normal kar asamu wata Matsala ko kad'an ne.


"ai Alhaji wanna karon Ko Kabir bai bak'unci Lahiraba, Malam Mai Buzu zai nakasashi yazamo bashi da Amfani, daga Haka ya shige Mota, Shikuma yayi cikin Gida.


Nafisa Kuwa tun fitanta a Motan Kb da kuka ta k'arasa Cikin Gida lokacin Mamanta tana kitchen, jin kukanta ne yasa tafito bashiri, tafara Tambayanta, tana kuka tana dukan Kujeran da take zaune take fad'in "Mama Kabir da Maminsa sunci Amanata duk jiransa da natayi yatashi Abanza, Aure! Aure
Akamasa, da sauri Mamanta ta Rufe mata Baki, "yanzu sai da akasamu Munafukin da ya gayamiki wannan Maganan, to bud'e kunnenki kiji, Kwanaki Dadyn ki yazomin da zancen wai... wai... Yaje wajen.... Fatima...take cemasa wai... Akwai wata yarinya..Aliya. da .. Iyayenta... Sukazo suka sameta.. Wai zai aureta... Ke intak'aice miki dai yanzu ba wannan maganan tuni naje wajan ... Malam anwatsar da zancen dama tana da saurayinta wai bayi da san'ane amma yanzu Ita Uwar kad'ad'in Fatima tasama masa aiki a Campanin Sugern Kabir.

Ki Kwantar da Hankalinki Kabir nakine ke kad'anki.

Nafisa ta kuma Rushewa da Kuka "Wlh Mami Wannan Bazan 'yar k'auyen da take gidan Matarsa ce, Nan ta kwashe duk yanda Mami ta gayamusu tafad'a.


Cike da tsoro Maman ta Rafka Salati tana tafa Hanu.

Dai2 Lokacin Dadyn ya zauna Fuskansa a murtuk'e yake kallon Nafisa dan yaji duk abunda ta fad'a.

"Nafisa d'ago ldonki kikalleni, Meyasa bazaki Hak'ura da Kabir ba ga samarukanki dayawa suna sonki da aure.

Da sauri tad'ago tana Kallonsa, "Dady wlh bazan iyaba inasonsa wlh sai nakashe yarinyannan kotawani Hali tafad'a tana wurgi da pillows d'in kujeru.

Ganin da yayi tana
Shirin Rikicemasa ne yasashi kwantar da Murya, "ya isa Nafisa inkinason Kabir bazan Hanaki aurensab, amma tunda Abun yazo da Haka zan d'aga aurenku daganan zuwa watanni biyu, sab'anin Sati Ukun da akasa.

Dai dai Lokacin komi ya zama Normal.

Sannan zanbaki abunda zakiba shi kitabbatar yaci, Muddin kinason Yazamo naki ke d'aya, Amma kinsan Hakan bazaiyiwuba har sai kin kwantar da Hankalinki, kinnuna baki damuba, Mamanta ta d'ora da kw'arai kuwa saikin had'a da Makirci, kafin aci Nasara, waye Kabir? Wlh namiki Alk'awari sai kin Mallaki Kabir fiye da Tunaninki.

Waro ldonta tayi tana sharan Hawayenta tace "Wlh zan iya Komeye kuma nima Nafison ad'aga auren harsai wannan Banzan takoma Gidan Ubanta, dan abun kunyanema ace wai na auri Mutum mai mata.

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Washi Gari ya kasance Laraba, wanda yadai2 da Ranan Kamun Sauda, da sassafe tazo dan duba jikin Khadijah, Bayan sun gaisa da Mami afalo kai tsaye d'akin iya tashiga, zaune tasamu Dijah abakin Gado ta jingina kanta a fuskan Gado, Har Sauda ta zauna agefenta bata saniba, saida ta tab'a kafad'anta kafin ta Kalleta, ta lumshe ldonta ta bud'e gami da sauk'e ajiyan Zuciya.

Sauda tace Khadija "Meyasa kikeson Jefa kanki cikin damuwane kinga fa ance dama kina da' matsalan zuciya baki ganin yawan tada ma kanki Hankali da tunanin da kikeyi zai Haddasamiki Motsawan ciwonki?


Sannan yawan Ganinki Hakan Agun Mami ba k'aramin tsahin Hankali take shigaba, Mami ta cancanci sakamako mai kyau a wurinki Khadijah inkiyi la'akari da so da k'aunan da ta nuna miki na zab'inki da tayi amtsayin abokiyar Rayuwan Tilon d'anta guda d'aya, ta tsallake Kaf Matan Familyn ta da na Familyn mijinta, ta zab'oki.

Dijah tasa Hanu ta share Hawayen da yagangaro mata ta gyara zama tana kallon Sauda,

"Aunty Sauda yaushe kika shigo?

"Yanzu na shigo, tun jiya nake sa Ran ganinki bangankiba nayi ta k'iran Wayanki akashe, na k'ira Mami shine take gayamin Abun da yake faruwa.

Ki kwantar da Hankalinki Khadijah kidaina sa damuwa aranki, Yaya Kabir Mutum ne Mai sauk'in kai da sanin yakamata Wlh zaki ji dad'in zama da shi Uwa Uba Allah yabaki Sirika ta Gari mai so da k'aunanki.


Dija tayi ajiyan zunciya tana k'ara Share Hawayen da yake bin Hancinta, tace " yau Mami tace min inna gama Makaranta na zata maidani Gidanmu, Sauda Ni Gidanmu zan tafi.

Wai nice za'ace Matan Kabir? Wlh bani so, Bani sonshi kaman yanda yace bayi sona yatsanane ni, nima na tsaneshi, yaje ya k'arata da Nafisansa kawai.

"Shi yace miki bayi sonki ya tsaneki?

"Eh jiya inajinsa acikin Gerding ina kwance anan bayan ya maidata gida, Shine da ta k'irashi awaya, yake cemata wai Shi dama tun asali ya tsaneni baya sona, lta zai aura. Ta k'arasa maganan tana sharan k'ollan da suka gangaromata.

Kuma nasha ji yana cewa bazai tab'a son wata mace aduniyaba bayan Maminsa, ko aure zaiyi to badai dan soba, wai shi bai ma yarda akwai wani soba bayan na d'a da Uwa.


Sauda tayi Murmushi "Habib yabani lbrn Irin Game d'in da kukayi tayi da Kbn naki tun farkon Had'uwanku, kuma duk games d'in ke kike Nasara k'arshe Har ya hak'ura, ya sara miki, Mai zai Hana ki Kwantar da Hankalinki Ku buga Game d'in k'arshe kigani na tabbata zakiyi Wining ni zan taimaka miki sosai Khadijah ki kwantar da Hankalinki, Zamanki Gidan Mijinki shine Kwanciyan Hankalin iyayen naki, kidaina Kallon wata Nafisa kedai ki Fuskanci Rayuwan Aurenki kawai.

Ko baya sonki yanzu, agaba zai soki, shi da Kansa wataran zai k'aryata furucinsa, zai yadda cewa bayan son d'a da Uwa Akwai wani Salon son na daban.

"Nifa Bana sonsa.

"Banyarda ba Khadija, Sau
nawa kike bani Labarin Abunda kike ganin Sunayi da Nafisa?
Inbaki sonshi ina Ruwanki?

Dijah ta turo baki "nifa Haushi kawai suke bani ai abunda sukeyi ne sam bai daceba"

Sauda ta kwashe da Dariya yanzu dai zo muje ki karya, dan Mami tace min baki Karya ba, Ga mai Gyaran jiki can tana jiranmu tare za amana komi k'arfe 4:00 za'aje kamun a can Distinatoin Hotel, kisaki jikinki wannan yana daga cikin plan d'inmu zan gaya miki sauran, ta rik'o Hanunta suka fito falo,

Mami tana ganinsu ta fara tafa Hanu Oyoyo Yarinya na ta warke, tana isa ta fad'a ajikinta tana Murmushi,

Mami ta Rungumota ko kefa My Khady, Amma har yanzu jikinki da zafi, barin kawomiki abun karyawanki ki karya kisha Magani da sauri Dijah ta mik'e "a'a Mami zan d'auko da Kaina.


Tea kawai ta Had'o tazo ta zauna tana d'an kurb'a ahankali.


Kabir ne yashigo Cikin takunsa na lsa yau shigan Manyan Kaya yayi na sky Blue d'in shadda sai Maik'o yakeyi ya Murza Hula zanna Bukar wanada aka sak'a da zare sky blue da dark Blue idonsa Manne yake da Farin Glass wanda kake iya Ganin fararen ldonsa fes daga tawajen glass d'in, ga wani Dadda d'an k'amshi da yake tashi ajikinsa.

Kallo d'aya Dijah ta masa ta yi k'asa da ldonta k'irjinta na Bugawa.


Fuskansa d'auke da Murmushi ya Zauna kusa da Mami dai2 lokacin ldonsa ya sauk'a kan Dija da take kurb'an tea ahankali sai tururi yakeyi, aransa yana mitan k'in bin dokan Likita da takeyi dan yana cikin dokan da akamata banda cin abu mai tsaban zafi.


"Inakwana yaya Kb Muryan Sauda ya ziyarci Kunnensa, ya dawo da Kallonsa gareta yad'an tab'e Baki Ashe dama kina nan ne Habib yake min wani dabara, Biyoshi kikayi dan tsaban Rashin Kunya ko?

"tad'an dara tace "Haba dai yaya Kb nanfa Gidanmunne kaga shi ya biyoni ba nina biyoshiba, watk'ila yaje Gidane akace masa lna nan,
Hararranta yayi "to sannu parot Inba biyoshi kikayiba me kikayi? Shida ya kwana anan, keda yanzu kika zo waye yabi wani?

"Wlh Bani daga cikin masu Bin maza gidajensu yaya Kb, wasu matan fa ma tarewa sukeyi a gidan samarukansu basu da shamaki a ko ina hatta da d'akin sa kullum suna nanik'e, "Hey Is Ok ya katseta yana Muzurai "Mawa kike mai da Magana haka?

Tana dariya tace "Sory yaya na.

Mami da take ta k'ok'arin Maida Dariyanta tace "Kabir ince aiki zaka tafi? Ai gara ka tashi kar ka makara.

Dija kam d'an Murmushin gefen baki tayi ta Mik'e da Cup d'inta, tashige d'akinta, Saida tasha maganinta mai gyaran jikin ta fara da lta, Suna cikin yi Sauda tashigo tana dariya,

Tace Khadija tak'ira Jamila ita zata musu kwlliya.

kafin yamma an yarfa musu tsantsararren Lalle da kitso, Jamilace ta tsantsara musu Kwalliya.

Dija tafito cikin fitet gawn d'in codeless pouple mai Silver, Head Sillver aka nad'a mata takalmi da Jakanta ma Silver, sark'a da warwaranta ma Silver. Tafito kenan Bintalo tashigo falon Baki Bud'e Bintalo take binta da kallo har ta k'araso inda take, ta rik'e Hanunta tana dariya Haba Matan Yaya Sani irin wannan Kallo.

"Ba dole inkallaba Khadija kinganki kuwa?

Bafa ke bace Amaryan irin wannan zak'ewa,

"Amaryance tabani wannan Dama, tafad'a suna zama abakin gadon lya,

Bintalo ta kalleta "Dija kinyi ciwo ne?

"Mhmm me kika gani?

"Naga Kind'an ramene.

"zamuyi maganan, yanzu Muje ki gaida Mami Bintalo Kinga ana ta tafiya, Af! Sory Aunty Binta zance, tana dariya suka fita,

4:00 dai2 su Dijah sukafito ajere da Amarya Sauda ba k'aramin kyau tayiba komi nata pink ne, Daf da zasu fito aka k'ira Dija awaya, haka suka fito su Uku agaba Amarya da k'awanta agefnta d'aya gefen kuma Jamila sai Dijah da take bayansu bayanta kad'an kuma Bintalo ce sai zabgamata Harara takeyi jin tana waya da Auwal, sai sauran jama'a dasuke tashiga Motoci, haka suka fito har bakin gate.

Kabir yana tsaye ajikin Mota shida Ango shigan Ash d'in dakakkiyar shadda Wanda Abbane yayo musu ordensu daga Dubai, sukayi hatta da aikin shaddan iri d'ayane huluna takalma duka iri d'aya, ba k'aramin kyau sukayiba, Gefensu Sani Suna d'an Magana akan yanda zasi tsara tafiyan sai Abokansu dasuke gefe suna bada Umurnin Motocin da za'a shiga.

Sani ne yayi ma Bintalo alama da tawagan Amarya Motansu zasu shiga.

nan suka nufi Motan d'agowan da Dijah tayine sukayi ldo Biyu da Kb wanda tun fitowanta ya murtuk'e Fuska yana Kallonta, abayansu ta tsaya tana cigaba da wayanta.

Sani ya bud'e Musu Mota suka fara Shiga, ahankali tad'an ti taku biyi tayi baya sannan tajuya ta nufi Motan wani abokin ango da tun fitowansu yake mata tayin Mota datazo tashiga su tafi.

Ke Khadijah! Taji an k'irata tana juyowa Sani yamata nuni datazo tashiga Motansu, sai da tad'anyi gajeren tsaki ta fara zuwa, Haryanzu ldon Dr Kb yana kanta k'are mata kallo yakeyi tundaga sama har k'asa, cikin matsanancin takaici nafarko kasancewanta Faran Mace anzana mata Bak'in Lalle daga can nesa shi zai fara d'aukan hankalin mutun zuwa gareta, na biyu Rigan jikinta ba k'aramin manneta yayiba ga Khadijah da Sharp na bugawa amujalla sanna ga d'an gyalantanma akafad'a kawai ta ratayashi, Uwa uba gawani Kwalliya da akamata nafad'a na Musali takalmita mai tsinine Sosai, sai k'ara yake yi duk inda ta taka, Ga Khadijah da wani irin tafiya mai matik'ar d'aukan Hankali, Ga wani sassayan turare da yake tashi ajikinta, kasancewan shine afarko tafi kusanci dashi a tsayuwan datayin, Har cikin k'wak'walwansa yakejin K'amshin.

Gani yake duk mazan gurin ma ita kad'ai suka zuba ma ldo, Sannanma da wa take lrin wannan waya da tun fitowanta har yanzu bata gamaba.??

Daga d'an nesa dasu tace ma Sani "Yaya Sani nayi mantuwane barin je ind'auko, yace "Ok barin kaisu sai indawo inkaiki da ragowan k'awayen naku, juyawa tayi batare datace komiba tayi cikin gida, Habib yad'an dunguri Kb "Man yadai?

"Mtss Dr Kb yaja guntun tsaki,

"zo mushiga Muje inyaso sai mudawo mu d'auketa Habib yafad'a da sigan zolaya.

Hararansa kawai yayi yashiga, Khadija data ke mak'ale tana lek'osu tana ganin sun tafi tafito tashige Motan Abokin Habib suka tafi.



*Anayinta Fa* πŸ€”
*Wai meke damun zuk'atan Ma'uratanne?*

Ummu Fatima ceπŸ€—
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*_Soyayya dad'i idan har dani zakuy inbaku wazana kalla Abayan Raiiiiiiii!!!!!!!!_* 🎢🎢🎡🎡 πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½πŸ’ƒπŸ½
_Gaskiya ina shiga matsanancin farin ciki ldan aka k'ira wayana nad'aga akacemin Masoyiyarki ce mai bin Noveld'inki, ................. Wannan Kalma yana Matik'ar Burgeni ko karantawa nayi nakan shiga cikin shauk'in kalma saboda haka na sadauk'ar da wanna page gaba d'ayansa gareku masoyana, Masu k'irana awaya da masu min Massage wlh nima ina Son ku Fatana a Kullum shine Allah ya sadamu daku a Firdausi_ 🀲🏻
Allah yabar k'auna🀝🏻

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 3⃣6⃣

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login