Showing 6001 words to 9000 words out of 155892 words
baki "nidai wlh baniso na warke ba Alluran da za'amin,
Tsayawa kawai yayi yana kallon bakinta ahankali yafara tunota yarinyannane marar kunya Wanda suka tab'a had'uwa arugan juma ta mishi rashin mutunci, tabbas biri yayi kama da mutum tunda tafarfad'o take masa kallon kamar tasanshi, wato shine data ganeshi take masa kallon raini haka? Tuno maganan da wani saurayi yagayamasa arugan yayi
*Dijah bukar med'ori kenan yarinyace maihankali sai dai akwaita datsiwa inkashiga hark'anta gashi bata da hak'uri, bata manta abu komi Kamata saita rama ko ta d'au fansa*
tsaki yaja yajuyamata baya ahankali yace k'arya ne yarinya kinyi kad'an baki kai kiyi wasa daniba yaushema aka haifeki? Ko can dakikamin nabarki, gani nayi bakikai intsaya yi da ke bane;
Baffa ya matso gaban Dr kB yace "likita don Allah kasallamemu tunda taji sauk'i murmushi yayi yanashafa k'irjinsa "OK Baba yau d'innan za'a sallameku insha Allah, yajuyo da kallonshi ga Dijah ya na mata dariyan mugunta gami da kallon zakisani,
Yakalli Alluran da yake hanunsa ya kuma kallonta yace "za'a k'arasa mata Alluranta "to kawai Baffa yace sannan yafita Dan yin sayyayan da yakesonyi yatafi dashi gida Cikin takunsa na izza ya matso daf da ita yahad'e fuska Yana kallon tsakiyan idonta, ya lashi lips d'insa meye ma sunanki? *Dijah k'aya* ko? Sunan da "yan k'auyenku suke k'iranki da shi, ya jijjiga kansa "kinga ikon Allah ko? kin tuna alokacin da kikamin rashin kunya a k'auyenku? Yau gashi Allah ya kawoki hanuna, ya juya ya fita Jim kad'an ya dawo da Allura ahanunsa, ina hannunkinan da yamin B'arna mik'o shi yafad'a yana zabga mata harara,
Dijah tuni ido ya raina fata Sai b'ari takeyi amma idonta bai huta da hararansaba, sai b'oye hannayenta takeyi tsakanin cinyoyinta, shi kuma yana tsaye k'yam kallonta kawai yakeyi
Ahaka Baffa ya traddasu, "yau likita anmata Alluranne ya tab'e baki tak'i amata kuma bazai yiwu asallameku ba amataba, Baffa ya matsota yadafa kanta haba mamata akamiki baunda yafi Allura zafi, bare Allura kiyi hak'uri amiki ya wuce muyi Mu tafi yau zaki ga innanki insha Allah, taso tasanar da Baffanta cewa Alluran zalunci zai mata bana gaskiya ba sai dai tasan Baffa bazai fahimcetaba don haka kawai ta fashe da kuka ya jima yana rarrashinta sannan ya kalli Dr KB da yake tsaye yana mata wani irin kallo "bismillah likita yimata mutafi matsowa yayi yana mata Alama da tabashi hanunta bayan da ta iya ta mik'o hanunta yana totson lips d'insa yace "atafin hanun za'ayi, Baffa kanshi Abun yabashi mamaki Allura a tafin hannu?
Bai kawo komi aranshiba ya zauna kan kujera yana kalle2 sauran marasa lfyn da suke sauran gadaje,
Cike da mugunta da son ganin gudun ruwan ta ya cakka mata Allura a tafin hanunta har waje biyu sannan ya koma gefe yana kallonta,
Azuciyansa yace bake baki da kunyaba? Kuma wai komi akamiki sai kin ramaba? Tom ina jiranki, ya jawo foldernta yayi rubuce2 aciki yace "shikenan Baba Akula da shan magani da dokan da akamata zata warke insha Allah, daga haka yafice batare da yaji daga Bakinsa ba,
Mama jummai ta shigo da sauri ta k'arasa wajen Dijah tadafa kafad'anta "haba Dijah keda yau zakije kiga mamanki meye naki na kuka? Kiyi shiru abinki maza zo muje kiyi wanka, tajata suka fita,
Kayanta da tazo dashi ajikinta tasaka Riga da zani farare k'al irin na fulani Baffa yana tsaye abakin k'ofa suka iso ita da mama jummai, sallama ta musu da fatan samun k'arin sauk'i
Baffa yace mata ta nuna ma Dijah office di'n likita ta mishi godiya, don d'azu yazo mata sallama tana wanka, taso tak'i zuwa sai dai bata saba yima Baffa musuba don haka tabita, da hanu mama jummai ta nuna mata office d'in ta wuce abunta,
a tsorace ta tura k'ofan ta shiga sai zaro ido takeyi yana zaune a cikin kujera yana aiki da lap top kallo d'aya yamata ya dakamata tsawa "ke "yar k'auye meya kawo ki nan wani irin harara ta bishi dashi batare da tace komiba, a fusace yafara danna k'ararrawan k'ira wasu masu sharane guda biyu suka shigo kufitar min da wannan abar anan sercatif problem ne da ita Ku mai data can layin mahaukata inaga daga can ta k'wace tazo, ai asaba'in suka d'auketa cak suka fita da ita sai tirje2 takeyi tana kuka amma sai da suaka kaita,
Wata nurse suka samu awajen tana zaune tana ganinsu ta mik'e tazo wajen tana tambaya, dayan matan tace "daga nan tafita garin yaya kuke barinsu suna fita office d'in Dr KB tashiga, nurse d'in ta kalleta cike da tausayi tace "gaskiya bansan da yarinyannan ananba inaga tun banzoba tafita, juyawa sukayi suka tafi abunsu, cike da tausayi nurse ta jawota itakuma sai kuka takeyi tana tirjewa, akan wani kujera ta zaunar da ita ta jawo ruwan Allura zata mata,
Cikin matsanan cin kuka ta durk'usa ak'asa hanunta na bari tace "don Allah sister kiyi hak'uri wlh ni ba mahaukaciya bace sharri akanmin wlh niba mahaukaciya bace, cak ta tsaya tana kallonta, Dijah ta rik'o hanunta Allah dagaske niba mahaukaciya bace Baffa na yana waje yana jirana, "kintabbata? dagaske kikeyi, wlh dagaskene sister inbaki yardaba muje kiga Baffa na zai miki bayani,
Nurse d'in tana rik'e da hanunta suka fito fuskanta sharaf da hawaye, Abunda ya bama Dijah mamki shine hango Baffa da Dr KB datayi, harshine ma yake nunama Baffa ita da alamuma yataya Baffan nimantane nurse dince tayi sallama tun kafin Su Amsa sallaman Dr KB yamata kallon don't say any thing, don haka shiru tayi batare da gane komiba,
Baffa ya kamo hanun Dijah yace " haba mamata da baki gane office d'in likitanba bazaki dawoba? Sai kije ki shige wani wuri kisani adamuwa? Ina ta nimanki,
Ya kalli nurse d'in yace "mungode ko, "bakomi tace sannan ta juya batare da tace komiba, tunda anyi waning nata
Dijah kan ko kallon inda KB yake batayiba ta wuce tayi gaba nan tabar Baffa sai godiya yakeyi ma Dr KB
*tofa wai kan meye tsakanin Dr KB da Dijah ne? Shin wani mataki yanzu Dijah zata dauka tunda ance ita bata barin ta kwana?*
*ku biyoni*
Taku *ummu fatima* ππ
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*DIJAH* *QAYA*
πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦
*BY ASMA'U GALADIMA*
π¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏπ¦πΏ
π¦ π¦
π¦ π¦ π¦ π¦
*MY* *NATION* π³π³π¬
*ISLAM MY RELIGION* ππ
_wata rana an atambayi Manson (S. A. W) "Mene ne Hak'uri ? Sai manzon Allah (S. A. W) yace " juriya kan bak'in ciki, yin raha ga mak'iya, Barin mummunan zato, cire Girman kai, karb'an uzuri agun da Kasan babu gaskiya, hak'uri a inda kakeda karfin ramawa, yafiya ma Wanda ya cuce ka, kyautatawa ga Wanda ya kyautata maka_ _(ya ubangiji kabamu ikon yin aiki da dai dai Ka gafartamana kura kuranmu)_
π *KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION* ..........βπ»
*page* 5β£
Tuk'i yake cike da nitsuwa yana bin k'ira'ar sheikh Abubakar shad'iri cikin suratul Namli, har ya iso gida, kai tsaye pert d'insa yanufa,
Akan wani kujera da akayi da sumunti wandayake farfajiyan waje ya hango Sani yana kishingid'e,
Cikin takunsa na isa da izza yak'araso wajensa, yasa hanu ya d'aga hulan da ya rufe fuskansa dashi "kai bacci kakemin anan? D'an k'aramin tsaki Sani yayi " dole kace hakaman tunda ka shanyani anan, murmushi kawai Kabir yayi yashige falonsa
Wanka yayi ya shirya cikin riga da wando na wani yadi milk mai laushi ya fito da hanu yayi ma Sani alamun yazo, suna daf da shiga pert d'in Mami Sani yace "wlh kunyan yanda kake sani muke k'arya ma mami nake ji
Haba oga meye amfanin kadinga hanamu fita dakai alhalin mami bata saniba,
Kabir yace "to wai Sani mezaku tsaremin ne? Duk Abunda Allah ya k'addara zai faru dani bawani mahaluk'i da ya isa ya hana,
Ni ka ganni kullum cikin Addu'a nake ba abunda zai samen insha Allah,
Ba wai cewa nayi zamu hana wani Abun yasamekaba amma ai atleast zamu kula da motarka dalilin da yakawoni garinnanfa kenan gadinka pls oga kabari mudinga take ma baya ko bakomi da muzaburar da mak'iyanka,
Murmushi kawai Kabir yayi batare dayace komiba suka shiga falon Mami,
Afalon suka tarar da Habib da Mum d'insa tare da Mami,
Mum tana ganinsa tace "yauwa Kabir gwanda da Allah yadawo da kai tun bantafiba, zoka zauna anan tanunamasa gefen da Habib yake zaune, nan yazauna yana sunkuyar da kai yana murmushi
Sani ya tsuguna ya gaidasu yafita mum takalli Kabir da Habib dasukayi tsilli tsilli da ido tace " kukuma abunda kukaje kuka aikata kenana?
Daga turaku zance sai kuje kuyi rashin arzik'i? Kuje kusa yarinya agaba kuna mata dariya da rainin hankali?
Mami da bata san me yafaruba, cikin rashin fahimta takalli mum zance kuma?
Nan mum ta zayyane mata duk yanda akayi Mami tahau tafa hanu tana salati mai had'e da dariya,
ai hajiya don bakisan waye Kabir bane shiyasa kikasashi cikin wannan hidima ai koda bakinsu ba d'aya bane indai da Kabir akaje to zance ya b'aci ba abunda ya iya kinganshinnan, sai shirme,
Mum tace "ai bakinsu d'ayama "yar wajen Aminiyatace hajiya sadiya naturasu dama Akwai wata k'awarta kusa dagidansu yarinya mai hankali shine nace dagana kuma suje kabir ya ganta
Shinefa uwar Amira tak'irani take shaidamin yanda akayi
Tam yanda kuka je kukayi shirirta haka zaku koma kuje ku gyara saurankuma inji wani abu nida kune Tafad'a tana mik'ewa bari mu wuce daman zani can gidan yaya ne nace barinzo mu gaisa kwana biyu
Naji dadi sosai, har bakin mota tarakota.
π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄π΄
Alhaji Ya'u ne k'anin mahaifin Kabir ne wanda suka had'a uba da shi, zaune atanka memen falonsa, tunaninsa d'aya shine yazayyi ya kawar da Kabir aduniya don ya mallake tarin dukiyan da mahaifinsa ya rasu yabar masa.
Tun Alhaji mahmud na Abba naraye k'anin nasa yake farautar dukiyansa duk da kawaici da kara gami da kyautatawan da yake masa, sosai yasha Alwashin ganin k'arshe yasha kai ma rayuwansa hari Amma Allah bai k'ddara mutuwansa ta hanunsaba.
Alhaji mahmud haifaffen jahar mai dugurine hark'an kasuwanci ne ya kawoshi jahar Adamawa, wanda Anan Allah yahad'ashi da Fatima bafulatanar asali ba b'ata lokaci akayi musu aure don dama Alokacin tagama karatunta,
Bayan shekaru uku da aurensu Allah yabasu da'nsu muhammad kabir, alokacinne ya dauketa ya kaita garinsu mai duguri don t mahaifiyarsa tace ya kawota tayi wankan gidan awajenta.
To awannan lokacinne ya'u yanuna sha'awan bin d'an'uwansa su dawo yola dazama, mahaifinsu malam Rabi'u wanda su kadai Allah ya baiwa don tun bayan haihuwan mahmud mahaifiyarsa bata ka'ra haihuwaba, mahaifiyar ya'u kuma tun bayan haihuwarsa ta tarasu ta barshi ahanun kishiyanta bata masa rik'on d'an kishiyaba tamishi rik'o tsakani da Allah.
Bayan sun dawo Adamawa dashine yasahi ahark'an kasuwancinsa inda ya bashi manajan kamfanoninsa sannan ya mishi aure ya bashi k'aton gid.
Tofa tundaga wannan lokaci da Alhaji ya'u ya fara tashen kud'i yaji yana son kawar da wansa don ya mallake duka dukiyansa kafin d'ansa ya taso kullum planing d'inda suke k'ullawa da matarsa kenan yanda zasu kau dashi aduniyan ma baki d'aya.
(Kai d'an Adam Allah yasa mufi k'arfin zuciyarmu, idan kabi ye ma son duniya ba abunda bazaka aikataba)
Mahmud bawan Allah shikuma duk tunaninsa shine yanda zai k'ara taimaka ma d'an'uwansa da dangin mahaifiyar sa, ahaka Allah yakarb'i ran mahaifinsu malam Rabi'u.
Fad'in tashin hankalin da suka shiga bazai yiwuba bayan sati bayanda Alhaji mahmud baiyiba akan yadawo da mahaifiyarasa kusa dashi fir tak'i tace yabarta kusa da "yan'uwanta,
Haka yadawo yabarta sai dai yana yawan ziyartanta akai akai.
Kabir yana da shekaru takwas Allah yaba Mami ciki, ai randa Balki matar ya'u taje ta gani ba k'aramin tashin hankali ta shiga tana dawowa ta sanar da mijinta ai shikamma kasa bacci yayi shawara tabashi akan suje gidan boka su sa ya zubar da cikin , sosai yaji dad'in shawaranta ba b'ata lokaci washi gari sukaje aka gama komi boka ya basu magani yace lalli susa mata a abunci bama zata sake haihuwanba.
(Iko sai Allah duniya abun mamaki)
Bayan Kabir yagama secondary ne Abbansa ya kaishi England anan ya karanci medicine alokacin Alhaji ya'u yana da yara biyu Aminu, da Nafisa yawanci idan yazo hutu anan yake samun Nafisa tazo wa Mami hutu Allah ya had'a jinin Nafisa da Kabir sosai tun alokacin duk dashi ba wani mai sake da yawa bane.
Bak'aramin kulawa da gata gami da soyyaya Kabir yake samuba awajen iyayensa, wanda hakan ba k'aramin k'iyyaya yak'arama Kabir ba awajen Alhaji ya'u
Sosai Alhaji mahmud yaci buri akan tilon d'ansa,
Wani hutun Kabir da ya k'arene Abbansa da kansa yatuk'ashi yakaishi air pot bayan ya masa "yan Nasihohin da yasaba masa ako da yaushe inzai koma makaranta sukayi sallama kowa da Abun da yake sak'awa aranshi na alhinin rabuwa.
Ahanyansa na dawowa yafito kwanan unguwansu kenan kasancewan gun ba mutane da yawa kawai yaji tayarsa ta sace, gangarawa yayi don yaga mai ke faruwa kafin ya bud'e motar yaji anrigashi wasu matasa ne su hud'u fuskokinsu a rufe suka bud'e suka shiga d'aya ya zauna agba ukun suka zauna abaya gaba d'ayansu suka saitashi da Bindigogi wanda yake zaune agban yace "Alhaji aikomu akayi mu kasheka amma kaga mu kud'i muke nima ba ruwanmu idankaga zaka fanshi kanka da kud'i sama da wanda Aka bamu mukasheka shikenan sai mubarka da ranka inkuma bazaka iyaba ashirye muke mu Bindige ka anan muyi tafiyarmu.
Murmishi yayi sosai saida hak'oransa suka bayyana yace "yanzu nid'innan har akwai wanda natsole ma ido?
Zai iya ba da kud'i akasheni?
Wanene wannan?
Don Allah ku gayaminshi,
Me nacimasa?
Me rayuwata ta tsaremasa?
Me yake nima da bazai samuba sai in bana duniya?
Alhaji kana b'ata mana lokaci da tambayoyin da bamu san Amsosinsuba, kafad'amana zaka bamu kud'inne?
Ko mu kasheka muje mukarb'i nashi?
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace "zan baku Amma don Allah kugayamin wanda ya aikoku?.
Tsawa ogansun yadaka mishi bazamu fad'a maka wanda ya yaturomuba,
"ok to nawa kuke so?
50 million atake ya d'auko chek ya rubuta ya basu,
Bayan tafiyansu yajima zaune acikin mota yana mamakin wannan Abu, daga bisni ya ja motar jiki ba k'arfi yanufi gida,
Afarfajiyan gidan yatarar da Alhaji ya'u yanata lissafa yanda zaishiga cikin d'akinsa ya d'auko decument d'insa na kadarorinsa, don jira kawai yake amasa waya ace masa gashi antsinci gawan d'an'uwansa.
Afirgice ya k'uramasa ido lokacin da aka bud'e masa gate ya shigo da mota har yayi perking ya fito ya nufoshi bai saniba tsaban firgici don yagama taget a yau zai mallaki dukiyansa gaba d'aya "Ya'u lfy kuwa naganka haka? Muryansa ta katsemishi tunani,
"A'a ba komi har ka kai Kabir d'inne? Eh kawai yabashi Amsa, "mushiga mana, "a'a zan wuce ind'uko yara a makaranta yau drivernsu bayanan yafad'a yana shiga mota,
Alhaji mahmud yaso ya fad'a wa matarsa abunda yafaru saidai baisan yadda zata d'auki abunba gudun kar yatayar mata da Hankali yasashi yin shiru da bakinsa bai fad'a ma kowaba sai dai ya duk'ufa da Addu'o'i ba dare ba rana.
"Allah sarki rayuwa, duk yadda ka kai da jindad'i ko wahala a duniya wata rana zai wuce, haka duk yadda ka kai da so ko k'in mutum watarana sai awayi gari bakanan ko shi bayanan.
Ahaka cutar ajali takama Alhaji mahmud yayi jinya na tsawon wata uku, sannan ya Amsa k'iran mahaliccinsa,
innalillahi wa inna ilaihirrraji'un Allahumma ajirni fi musibaty hazih wakhlifni khairan minha,
Abunda Mami take ta fad'a tana maimai tawa kenan lokacin da take rungume da gawan mijinta hawaye na d'iga d'is d'is akan fuskansa yana daga cikin wasiyyan da yamata kar tayi kukan da yasb'a ma shari'a bayan yabar duniya.
Mutuwar Alhaji mahmud ta girgiza illahirin garin Adamawa da kewayanta, don mutumne da ko had'uwa kukayi ahanya zaka bada lbrn nagarcaccen halinsa Akwaishi dakyauta, da tausayawa ma nak'asanshi aranan mutanen maiduguri suka iso har da Ayye mahaifiyarshi wayyo karkaso kaga koke2 agidan .
Yana da kwana uku Amininsa Alhaji jamil ya tafi England yazo da Kabir, tun ajirgi Zuciyan Kabir yake ta harbawa duk da dabara da tsarin da Alhaji jamil ya mishi, lokacin da suka shigo gidan komi yagama kuncemasa, hanun Habib abokinsa yakamo wanda yake d'a ma Alhaji jamil d'in cikin tashin hankali yake magana pls Habib tellme meke faruwa da mahaifana? Ina Dady da Mami na? Alhaji jamil yarik'oshi ya kaishi har gaban Mami kallo d'aya yayi ma Mami ganin yanda tadawo bak'aramin tashin hankali yaje fashiba,
Yadurk'usa ya kamo hanunta
Idonsa sunkad'a sunyi jazir "Mami Dady ne, ko shine yatafi ya barmu? Mami yanzu Dady ya..... Cikin kuka tasa hanunta ta rufe masa baki ta shiga masa nasiha mai ratsa zuciya.
Sai da Kabir yayi wata biyu, kafin yakoma da rad'ad'in rashin mahaifinshi.
*Mundawo lbr*
Yajima yana tunani sannan yak'ira wayan yaronsa kila,
bayan sun gaisa, yace "kila inason kazo muyi magana na k'arshe akan yaronnan, nagaji da wasa da hankalin da yaranka suke min,
wancan karon kud'i na baku mai yawa amma