Showing 93001 words to 96000 words out of 155892 words

Chapter 32 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

457

tsiyaya masa Kunun Aya, takaimasa bakinsa, yana kurb'a ya lumshe ido yana kallonta, ya had'iye yace "waye yayi wannan Drink d'in? So sweet haka, Murmushi tayi wanda yasa Kb ya shagaltu sosai da kallonta, aranshi kuwa Mamaki yayi wannan shine karo na farko da tayi murmushi ita dashi duk da bai gama tantacewa dashi tayi kokuma wani abun ta tunaba,

Hanunta ya Matsa, "Tell me mana,
"Nice
"waya koya miki?
"Aunty Binta
"Gud anma yayi dad'i sosai nima zaki koyamin, ta tashi taje ta d'auko masa Magungunansa yasha, yabata pracetamol yace tasha,

Ahankali Kabir yadinga janta da Hira har akayi k'iran Magriba suna wajan yayi Alola yayi yace yau zai gwada zuwa masallaci, itama tayi nata har akayi isha'i bai dawoba, tayi wanka ta sa kayan bacci, tasa Hijabi ta shiga kitchen ta bud'e kulan da da'zu Mami ta kawomata guda biyu fefesuf d'in kajine tace mata d'aya nata d'aya na Kb ana ta zauna tafara ci sam test d'in natan bai mataba ji take kaman akwai wani abu aciki gashi Mami tace ta cinyeshi tas kar taba kb, anma inyabar nashi zata iya ci, haka tayi ta d'urawa sannan ta d'auko wani magani a goran da shansa yazama mata jiki dan tun zuwanta Mami take bata wai maganin rigakafin ciwon ciki haka dai take shansa tunda taji zumane aciki,

Tana fitowa ta wanke bakinta, tafito ta bud'e sif tana gyara kayan ciki ya shigo, yazauna abakin gado yana danne2 waya,

Tagama ta rufe ta d'auki blancket da pillow takai falo, kallo kawai yabita dashi, tana zaune a falon taki anbuga k'ofa taje ta karb'o musu Abinci inji Mami, ta'ajiye sannan tashiga d'akin Akishingid'e tasamu Kb idonsa alumshe, "Likita ga Abincinka, a falo yad'an zaro ldo "Falo? Ai daga inda akayi lsha'i bana zama afalo tsoro nakeji dan nasha jin ana dariya, Ranan kamma susan Kule akamin da natashi zan gudu aka k'aramin da Rank'washi, tundaga lokacin bana gangancin zaman falon, ki d'aukomin Abincin pls yafad'a da sigan tsoro,

Khadijah wanda tunfara Maganansa take b'ari jin yace ta d'aukomasa, ai dagudu tayo jikinsa ta rushe da kuka,

"wlh bazanjeba saidai kar kaci Abincin wato ni inje su shek'eniki ko? Yan b'oye dariyansa, yace "inaga ke bazasumiki komiba, k'ara rik'eshi tayi, "Allah saidai kaje,


"Ok barinyi Addu'a sai ind'auko, tana zaune yashigo da sauri yana zare ido ya ajiye kayan Abincin,


"Sunmaka dariyanne?
"a'a nadaiji kaman Motsine, zama yayi yaci Abincinsa tana zaune abakin gado tana kallonsa, har yagam yaje yayi wanka yazo yayi shirin kwanciya,

Yana hawa gadon ta sauk'a baice mata komiba ya kwanta ya lullub'u wayansa ya d'auka yana danne2 yanaganin ta fara gyangyad'i ya kuna audio na kukan Kuliya yayi saurin turawa k'asan gado, ai asba'in ta ware idonta tadaka tsalle tahaye Ruwan cikinsa, d'ago kai yayi fuska ad'aure "Meye Hakan Khadijah? Lfy kuwa?
"Kuliya... Likita... Kuliya ad'akinnan nashiga uku, tasaki kuka, Rungumota yayi yasata cikin Bargon yana fad'in "Yasalaam nima naji kota ina tashigo oho?


Saida yaji ta manne ajikinsa, ya tura hanu yayi stoping audion, yanajin yanda k'irjinta yake bugawa da sauri2 ya kashe hasken d'akin yana d'an wasa da hanunsa abayanta har bacci mai dad'i yayi gaba dasu,


K'iran k'arshe na asubah ya farkar da shi agaggauce ya tashi yashiga toilet yayi Alola zaune yaganta akan gadon tana zaro ldo

"Likita kafitar da kulen
"Eh cikin dare na bud'e mata k'ofa tafita, yafad'a yana saka jallabiya da sauri yafita dan yakusan Makara,


Saida gari ya fara Haske yadawo, afalo yasameta tana shara yakama hanunta yashiga da ita kai tsaye gado yakaisu zatayi Magana ya manne Bakinsa danata ahankali yake tsotson Lips d'inta har bacci ya d'aukesu, wurin 11:00 ta tashi agggauce tashiga kitchen ta had'a musu abun kari tafito tagyare gidan tas ko ina k'amshi ke tashi tayi wanka tayi kwalliya cikin doguwar Rigan shadda dark blue da akamasa aiki da light blue zare, sark'a da 'yan kunne Gold tasaka tafita dan zuwa gaida Mami ta d'anjima awajen kafin tadawo a falo tasameshi har yayi wanka yana sanye da dark blue jeans da ligth blue d'in shirt mai dogon Hanu, da hanu yakitota ta k'araso jikinsa, "ina kikaje?
"Wajen Mami,
"da izininwa?
Shiru tayi tana wasa da zoben hanunsa da yarik'eta dashi.
"Karkisake fita bada izininaba, kinji?
Ta gyad'a Kanta
"kin karya? Ta girgixa kanta
"Ok d'auko, mu karya,

Bayan sun gama tana kitchen tad'anji hayaniya Alaman wasu sunshigo falon, lek'owa tayi taga Uncle, Habib ,Mami, Abban Habib da Sani, Fitowa tayi cikin nitsuwa ta durk'usa gaidasu, sannan ta mik'e Uncle yace "Zauna Khadijah ai zuwan nakine,

Dam taji gabanta ya yanke, ta koma ta zauna kanta ak'asa, Uncle yayi gyaran Murya, wannan daga office d'in Ss yake, yanuna wani matashi dake zaune kusa da Sani sai yanzu ta ganshi,

Yacigaba akan Maganan gubannan da Kabir yaci, dama anbari ne sai yasmu k'arfin jikinsa, to yanzu Aluamdulillah yad'an warware dan haka daga yau za'acigaba da bincike har agano kan abun yanzu haka daga office d'in muke Nafisa da iyayenta suna can, bincike ya nuna cewa ke kika karb'o caked'in daga gun da akayi, kinga kenan bincike ya hau kanki, shiyasa mukazo da shi dan sun buk'aci ganinki a office d'in dan ki amsa tambayoyin da zasu miki,


Cikin tashin ahankali Dijah ta d'ago ido duk sun kad'a sun rine, suka had'a ido da Kabir wanda tashin hankalin fuskansa yafi nata, kai yad'an girgiza mata ahankali alamun kar ta nuna damuwa,

Uncle yace "karkidamu Khadijah tambayace kawai za'a miki, ki amsa, kinji,

Kabir yadawo da kallonsa ga ss d'in da idonsa kekan Dijah wani bak'in cikine yaji ya kamashi, yayi mugun b'ata Rai yace "Uncle ina niman Alfarma abarta nan da kwana biyu inna dad'a jin k'arfin jikina zan kawota da kaina, ss d'in yace "No Ranka ya dad'e kabari akaita yanzu bawani abu mai wahala bane duk wa inda akae tuhuman yanzu haka suna can har da ita wacce tayi abun, azafafe Kb yace "wlh ba inda za'aje da ita malam badakai nayi maganaba, nace zan kawota jibi inzaku iya bari zuwa jibin to inbazaku iyaba kuna iya watsi da case d'in tunda akaina keyi anma wlh ayanzu ba mai fita da Khadijah,

"I'm sory sir wannan case d'in bazai tab'a yiwuwa awatsar dashiba koda kace bakason ayi yanxu hak'k'inmu ne muyi yanda mukaso,


Kb zai sake Magana Mami tamishi tsawa "ya isa Kabir ba hayaniya mukace kamanaba pls abi abun ahankali,

ta kalli ss d'in "kuyi hak'uri zuwa jibin kaman yanda yanima,

"Ok Ranki ya dad'e kinsan ban isa inje insamu oga da wannan maganaba saidai in zaki k'irashi,

"Kar kadamu zan maje da kaina inmasa bayani, Abban Habi yace "Shikenanma hakan zaifi, "kai Kabir jibin k'arfe nawa zamu jiraka,?
"1:00
"baka isaba bazamu kai har d'aya awjenba, duk abunda kukeyi katabbatar kun iso 9:00 daga haka Ya mik'e

"mujenku,
Gaba d'ayansu suka fita,

Kabir ya kalli Dijah har yanzu kanta asunkuye, yace "zo Khadijah bata d'agoba bare yasa ran zata zo, ya matsota ya d'ago kanta hawaye yajik'e mata fuska, yad'an yatsina fuska, "To yanzu meye abun kukan? Ke sam kuka baya miki wahala, k'wace fuskanta tayi takalleshi "Dole kace haka tunda kun had'a baki kunsani cikin case, wlh Allah yana kallo zai bimin kadi,



D'an ciza lips d'insa yayi yana jin zafin furucinta, ya jawota jikinsa,

"Duk k'iyayyana dake Khadijah bazan miki hakaba, to innayi meye ribaana? Kidaina zargina mana pls banji dad'in wannan maganaba, yana share mata haye yana d'an murmushin k'arfin Hali dan yanaga tabbas shima anyi amfani dashi saidai sam shi bai gane ta ina abun yazoba, duk dahaka yanaga bai dace tagayamasa hakaba

Ta zille ahanunsa zata tashi, ya kuma rungumota jikinsa, yafara shinshinta, ji yayi yana niman ya susuce, ahankali ya d'ago fuskanta suka zuba ido ma Juna,


"Khadijah idan kinje karki nuna alamun tsoro ko damuwa afuskanki wlh wannan ba k'aramin case bane, ki ware kiyi bayani iya abunda kika sani, Allah yana taare dake,


"yana tare da masoyiyar kanma ai Malam nika k'yaleni kar kawani min dad'in baki, meyasa kukace inkarb'o? Baku da k'afane? Tsakani da Allah inba shiriba, meye nasani cikin shirginku ina mak'iyiyarku, kusan Ranan yin abun naku,

akunnena naji kanacewa *Natsani wannan yarjnyan kuma har Abada bazan sotaba, tsarina da nata ba d'ayabane,*

itakuwa baki da baki tacemin wlh sai taga bayana muddin tana numfashi sai na toxarta,

To dan me zakusani cikin shirginku? Inba dama had'in baki kukayiba? Sau nawa kana cewa Mami ta mayar dani garinmu? To ai inba ta mayar dani adad'in raiba yanzu Allah yakawo hanyan tafiyana, nima nagaji da Rayiwan gidannan, nayi Alk'awarin duk randa nabarshi sai nayi sujudishukri, yanda katsaneni bakason Ganina nima Likita basonka nakeyiba, kanacin Albarkacin Masoyiyata Mami ne kawai.


Dafe kai Kabir yayi yaji gari na juya masa up side down, tuni kansa yadinga sarawa, yanajin kukanta acikin k'wak'walwansa,



*K'ak'a sara k'ak'a ga Akuya ga kura* 😡😲😲😲😲😲


*Ummu Fatimace* 😘😘😘
[8/7, 6:26 AM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


5⃣0⃣


Zubamata ido yayi kaman soko yake kallon kukanta gwanin tausayi, sunan Baffa da innanta take k'ira,



Yana rik'e da Kansa ya mik'o Hanu zai jawota tayi saurin zillewa baiyi Nasaran kamotaba, ta kife kanta ajikin kujera, tana sheshshek'a,



Ya matsota ya Rungumota da duka Hannayensa, ya kwantar da ita akan Damtsen Hanunsa, ya kalleta gaba d'aya fuskanta yayi jaa, ta gama fita ahayyacinta, yama Rasa ta ina zai fara Rarrashinta, dan haka yafara d'an Hura mata iska a fuskanta, ta mik'o Hanunta zata ture Bakinsa, caraf ya rik'e ya tsunta biyu abakinsa, yana tsotsansu a hankali yana kallon k'wayan idonta da suka fara Lumshewa, yasa Hanu yana sharemata Hawaye a hankali kaman mai tab'a kan ciwo, sai da yagama sharemata tas ya maida Hanunsa kanta, yana kwantar da gashin kanta, yana cigaba da tsotsan yatsunta, yana lumshe ldo, wani irin pilling yakeji na tasomasa ahankali, jin yanda take sauk'e ajiyan zuciyane yatabbatar masa da cewa tayi Bacci, tsawon lokaci yana ahaka sannan ya zare Hanunta a bakinsa, yana cigaba da shafa kanta aransa yana tunani, Dama haka Mata suke da Rikicin Ganganci? Ko dai Khadijah ce kawai hakan dayake dama ita Halinta dabanne?, indai kuwa haka duka Mata suke lallai zama dasu matsalane, shi yaushe zai iya irin wannan fitina, Shima yaushe yagama Rarrashin kansa?


Kallonta yakuma yayi sai sauk'e ajiyan zuciya takeyi acikin Baccin tana k'ara lafewa ajikinsa, yashafi kumatunta Ahankali yana 'yar Murmushi, "Khadijah Case! Yanzu kinsani dole sai nafita nimomiki Magani, dan wannan kuka dole ciwonki ya tashi, Why? Why Khadijah, ya fad'a ahankali yana kwantar da ita, akan pillow ahankali yana tsoron kar tatashi,



Ya tashi ya shiga Bed Room, wanka yayi sannan ya d'auko Maganinsa yasha ya fita, yana shirin sa key ya bud'e Mota, Mamy ta shigo tsayawa yayi yana kallon Motan Har driver yayi perking, ta bud'e tafito, ahankali yake takowa har ya isota, kallonsa tayi anitse, yace "Mami Sannu da dawowa,
"yauwa Sannu Kabir! Lfy dai ko? Ta tambayeshi cike da kulawa, yad'an shafa kansa yana d'an Murmushi, "lfy Mami,
"Anyah Kuwa Nagankane duk awani firgice Kabir, inazakaje? Naga kana k'ok'arin Bud'e mota?
D'an gyara tsayuwa yayi yana kallonta,
"tun fitanku Mami, Khadihah take ta Kuka, sai yanzu Bacci ya d'auketa, shine zanje nan phermarcynmu nimomata Magani, dan na wajena ya k'are, d'an jinjina kai Mami tayi hakanan taji duk tausayinsu yakamata, tad'an ja Numfashi, "To Amma ai da ka aika aka karb'o Kabir dan kaima har yanzu jikinka ba wani k'arfi yayiba,
"No Kar kidamu Mami daganan ba inda zanje zandawo, to shikenan kasa driver yakaika, baison Musun yayi yawa dan haka ya Amince badon yasoba, yaso ace shi kad'ai yaja motan ya tafi,


Har ya dawo bata farkaba, dan haka ajiye maganin yayi ya fita ya shiga wajen Mami,


Daf Mariba ya shigo, azaune yatarar da ita tak'ura ma T.v ido sai sauk'e ajiyan zuciya take da Alama yanzu ta tashi, Tsayawa yayi akanta hanunsa soke cikin Aljihunsa, yazuba mata ldo yana nazartan yanayin Numfashinta, ta d'auki d'an kwalinta ta d'aura ta tashi batare da ta kalleshiba, binta da ido yayi har ta shige Bedroom, ya tab'e Baki gami da jan Numfashi ya zauna akan Kujera ya d'auki Remot yana canza tasaha,


Yana Kallon CNN yaji ana k'iran Magrib ya Rage volume d'in T.Vn Sanna ya shiga bayan Gidan Falo yayi Alola, ya tafi Massallaci,


Yana idarwa ya dawo, sab'anin yanda yasaba sai anyi lsha'i, da Sallamansa ya shiga bed room, Khadijah tana zaune kan sallahya, ta kifa kanta ajikin Gado,


Daf da ita ya zauna abakin Gado ya d'ago kanta ya kalli Fuskanta, Hawaye na bin Hancinta, ya zare Hijabin ya ajiye agefe, Ahankali yak'ira Sunanta,

D'agowa tayi ba tare data Amsaba, ya Girgiza kansa, "Haba Khadijah meyasa baki jin Rarrashi da ban Hak'uri? ya zamo k'asa suna Fuskanta Juna, yaci gaba, "indai wai dan Maganan Office d'in C l D da akace zakije dan Amsa tanbayoyine bakiso, indai shi yake saki irin wannan Kuka Na janye Maganan Zuwan naki, ki kwantar da Hankali ba inda zakije koda hakan yana nufin za'amin wani Hukuncine zan d'auka, pls is Ok, kukan ya isa hakanan, ya k'arashe yana Murza 'yan yatsunta,



K'wace Hanunta tayi tana hararansa,
"Danme zaka hana cikan Burinku akaina? Bayan wannan shine plan d'inku, bana buk'atan ka hanani zuwa Koma inane, koda hakan yana nufin salwantan Rainane zan je, daganan kai da Masoyiyarka sai ku dafa shinkafar Murna,



Bak'aramin zafin Magananta Kb yajiba har cikin Ransa,


K'ank'antar da idonsa yayi cikin zafin Rai yace "Ke Khadijah kar kiga ina lallab'aki kiyi tunanin kinsamu wata dama na Rashin kunyane da zaki zage kina gayamin magana haka,


Wacece ke? Da har zanyi wani buri akanki? Ko kina tsammani akwai wata manufa da nake dashi akanki wanda sai ta wannan Hanya zan cin mata?


In baki saniba kisani tsawon Rayuwata bani da wani abokin Hamayyan da natab'a kusantansa da sharri sai dai ni amun, ki iya Ma Bakinki, kar kiga ina lallab'aki dalilai biyu yasa hakan nafrko ur are My peciant na biyu, so nake in sauk'e nauyin da Mahaifiyata ta d'oramin banda haka ba wani dalili,


Ya d'anja fasali sannan ya kuma kallonta, ya d'an sassauta murya "inkuma dan zamanki anane yasa kike niman d'agamin Hankali Khadijah barin k'ira Mami sai kikoma gurinta indai hakan zai saki daina d'aga Hankalinki, ya fad'a yana lalumo Waya,


D'a Jim tayi tana tunani, Sannan ta dafe Hanunsa da yake Rik'e da Wayan tana sheshshek'a ya d'ago suna kallon juna d'an ciza gefen lip d'inta na k'asa tayi idonta taf Hawaye, tana girgiza kanta Ahankali tanason tayi Magana amma takasa dan duk abunda za'ayi sam bata son tasako Mami aciki, wani lrin tausayinta yaji yana ratsashi ta ko ina, ya ajiye wayan agefe ya jawota jikinsa, "Wlh Khadijah bani da Hanu cikin cutar da ke kiyarda dani kuma na miki Alk'awari insha Allah bazan bari ki cutuba, Banason Kuka arayuwana ko k'aramin yaro banson inga yana Kuka, pls take it Easy, ba abun tada Hankalibane.



Yayi shiru yana Kallonta So yake yaga ta saki ranta, wani dabarane ya zomasa dan yasan da haka zai sha kanta, yad'anyi Murmushi yana Kallonta yace

"Ga wani Albishir game da Baffanki, yasa bakinsa dai2 kunnenta ya fad'amata wani Magana, ta d'ago ta kalleshi tana Murmushi da gaske Likita? D'agamata Gira yayi yanajin wani abu nayawo cikin jikinsa, wanda yarasa gane meye, wani irin Murmushi tayi ta kwanta ajikinsa, ahankali tace "Kayi Hak'uri bazan sakeba da mamaki ya lek'a fuskanta, yanason tabbatar da cewa Khadijahnce kuwa tayi Maganan, har yanzu Fuskanta na d'auke da Murmushi aransa yayi tunanin wani lrin sone haka Khadijah takeyi ma Baffanta,


"Ina zuwa yace sannan ya fita ya dawo da Kwalin fresh milk ya tsiyaya mata ta sha sannan ya b'alli Maganinta yabata, Ya tashi ya tafi massalaci dan anyi k'iran isha'i, bayan ya idar sai da yaje ya sallami Mami kaman yanda yasaba, yadawo alokacin Khadijah har tayi wanka tayi shirin Bacci tana zaune ak'asa, Shima shirin yayi sannan ya had'a Alluranta yana zaune abakin gado yace "Khadijah Bismillah, ta zaro ido "Gaskiya Likita bazakamin Alluraba pls banso wlh, kallonta yakeyi yasani yanzu abune mai sauk'i tafara masa Kuka dan haka ya ajiye Alluran, yace "to shikenan inbakiso zo kiji, ba Musu ta taso, d'an nesa dashi ta zauna, ya kwanto da ita jikinsa yana d'an Romace d'inta, ayanzu ta saba da irin wa innan Abun nashi,
dan haka ta lafe ajikinsa, cikin dabara ya janye Riganta ba ta ankaraba sai jin shigan Allura tayi ta zabura zata sa ihu ya had'e bakinshi da nata, tsawon lokaci kafin ya ajiye Alluran ya gyaramata kwanciya ya rufa musu Bargo.




*Ummu Fatima ce* 😘

[8/9, 9:11 AM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login