Showing 102001 words to 105000 words out of 155892 words

Chapter 35 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

473

dan baza'a rasa abunda za'ayi agidanba, inyaso zuwa jibi kuna cikin gidanku, Allah yasanya Allhairi, gaba d'aya jiyayi jikinsa ta mutu sai kace bashi da kansa ya k'ak'alo auren kuma yake d'okiba,


"yace Dan Allah Mami amin uzuri ad'aura auren abarta agida ahankali sai agyara gidan ta tare pls Mami kar kice a'a,

Kallonsa Mami takeyi sosai yabata mamaki,

Iya tace "shikenan ai kaida ita gidanku d'aya dan haka sai kasamu Uban naku da maganan duk yanda kukayi shikenan,


Ajiyan zuciya yayi zai magana Mami tace "Tashi katafi Kabir kayi yanda akace, banson Musu, tashi yayi kaman wanda baida laka ya fita,


Ya k'arasa kusa da Dijah lokacin har ta fara bacci juyawa yayi ya kalli k'ofan d'akin lya, ya d'an tab'a kumatunta ahankali yake k'iran sunanta, ta bud'e idonta yakama hanunnta yana kalle2 kaman mara gaskiya, suka fita,


Washi gari Misalin k'arfe sha d'aya aka d'aura auren *Muhammd Kabir Mahmud* da
*Nafisa Zakariyyah* ak'ofan Gidan Alhaji ya'u sosai abokann Kb sukayi mamakin rashin ganinshi awajen d'aurin auren

Shikuwa mutumin sam yama manta da maganan auren dan tun dawowansa daga masallaci yaja Dijah suka kwanta sai dai tana ganin yayi bacci ta zare jikinta tafito tafara aikinta, na had'a break da gyaran gida.




*Tofa yau dai burin Nafisa ya cika jama'a* 😁


Wai yazata kayane??? πŸ™„πŸ€­πŸ€”


*Taku Ummu Fatima ce* 😘😍
[8/15, 8:15 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


5⃣4⃣



Rasa yanda zaiyi da ita yayi, kallon Fuskanta kawai yakeyi yanda ta galabaita tafita hayyacinta, ahankali ya dinga tab'a kumatunta yana k'iran Sunanta, da k'yar ta bud'e Wahallallun indonta ta kalleshi, ya lura gaba d'ayan jikinta asake yake ta inda ko yatsanta bata iya motsawa yanda ya kamata, K'ok'arin d'agata yayi nan idonta suka kuma rufewa, ahankali ya maidaita ya kwantar cikin damuwa, Gaba d'aya yarasa yanda zaiyi da ita,

sai kaiwa da kawowa yake tsakanin palour da Bed room,


Daga baya kawai yayi sashin Mami abakin k'ofa yayi sallama lokacin tana rik'e da littafin Add'u'o'i, bayan ta amsane tamasa izinin shigowa, ahankali yaturo k'ofan ya shigo ta ajiye Littafin tana binshi da kallo dan Rabon da taganshi da sassafe haka har ta manta,


d'an gefenta ya zauna yana gaisheta cikin yanayin Rashin Gaskiya, Sai da ta Amsa tace lfy kuwa Kabir? Naganka haka,


D'an girgiza kansa yayi yana sosa bayan wiyansa yace "Nothing...

Kai ta jinjina tana fad'in "oiright,

tafita ta shiga kitchen dan shirya abin Break,

tashi yayi yabi bayanta ya kalleta k'asa2 yace "mhnn Sannu da aiki Mami, juyowa tayi ta kalleshi da d'an mamaki sai kawai ta amsa,


Wucewa d'akin iya yayi itama zaune yasameta tana lazimi ya zauna yana gaisheta,

rik'e baki tayi "Lallai Kabir yau idonka kenan? Da sassafennan?

Had'e Rai yayi,

"Ina gaisheki lya to ki amsamana kafin kiyi k'orafin tab'e Baki tayi

"a'ayo naga abunda najima banganiba, badole inyi tambayaba?

Mik'ewa kawai yayi dan yasan tunda tafara wannan surutun inma yagayamata abunda ke tafe dashi sai ta tara masa Mutane,


Fitowa yayi yakuma Gifta Mami akitchen yafita, yakoma sashen ya d'an tattab'ata anma ina Wannan wani irin Baccine? Ya tambayi kansa,


tunanin k'iran Habib yayi dan shine Likitan da yashafi Matsalolin Mata anma yasan inyak'irashi yau tashi ta sameshi, dan haka ya hak'ura sai yarfe Hanu yake cike da Damuwa ya kuma fita,

Wata Nurs ce ta fad'omasa arai ya ciro waya da niyan k'iranta, tsaban damuwa yak'ira Mami bai tashi ankaraba sai dayaji muryanta tana fad'in "Helo Kabir wthat is wrong with u??


"Mnnm Ina kwana Mami abunda yatsinci bakinsa da fad'a kenan,

tsananin mamaki ne yahanata Amsawa tabi wayan da kallo, tabbas taga damuwa afuskan d'an nata kuma ta fuskanci abun mai nauyin gaskene da yake kunyan sanar da ita saidai ita ta alak'anta abunda aurenshi da Nafisa, may be akwai wani abunda suka shirya shikuma yake jin nauyin sanar da ita,


D'aga kafad'unta tayi na intayi wari maji,

Komawa kitchen tayi har tagama break d'in tafito kaima iya nata anan sukayi kicib'us dashi wannan karon tashin hankalinsa yafi bayyana,


Hanunshi Mami ta rik'e har d'akin iya ta'ajiye Abincin sannan ta kalleshi,

"Kabir wai meke faruwane sanar dani duk duniya baka da abokiyar sirri kamana fad'amin kar kab'oyemin,


Sauk'ar da kansa yayi yana Shafa k'eyansa cikin in ina yace "Mnnn Mami dama ... Dama .. Khadijah ce, "lnnalillahi wainna ilaihirrajiun, lya da take fitowa daga bayi ta katseshi, cikin damuwa Mami tace "Meyasameta? tana lna? Da hanu ya musu ishara da pert d'insa, ahanzarce Mami ta shige lya ta rufa mata baya, tana fad'in

"habakai Biri yayi kama da mutum wannan sintiri daka dingayi bana banzaba,


Bak'aramin k'ara rud'ewa Mami tayiba lokacin da tayi arba da Dijah shame2 cikin bargo, ahankali ta taka gaban gadon ta yaye blancket d'in,

kai kawai ta jijjiga tafito da niyan d'auko wayanta a falo tasamu gogan sai muzurai yake da idonsa kaman yaci kud'in aika, yana ganinta yayi saurin ajiye idonsa ak'asa wani matsanancin kunyane ya lullb'eshi Mami kam har ta kai bakin k'ofa tanabin d'an nata da kallon Mamaki,


Iya ta lek'o ta k'irashi a kasalance ya shiga, ta harareshi "Anma Kabiru kabani Mamaki ka iya b'arna amma baka iya gyaraba? Kana matsayin Likita kayi lrin wannan aika2 anma ka kasa gyarawa, yanxu tun da naji k'aran yarinyannan ba wani taimakon dakamata haka kabarta tun daren jiya har xuwa yanzu? Kai ga sakali ko? ta k'arashe tana kallonsa rik'e da baki, Kabir dagaba d'aya ya lula cikin damuwa sai juya kai kawai yakeyi yana kallon Dijah da take tajuya ldo basai angayama lrin halin Kunyan datake cikiba duk da yanayin da take ciki na Wahala,


"Shiga bayi kahad'a Ruwa mai zafi ba musu yashige ya had'a Ya fito, lya tace "to maza taimaka mata ka kaita kasata aciki shirmammu sakalu kawai, daga haka tafita ta zauna afalo,
Nanfa Malam kb ya nad'e k'afan wando yashiga aikinda iya tasashi,


jimawa can Mami ta shigo da Dr Husna, yayi dai2 da fitowan Kabir daga bedroom d'in baiyarda yahad'a ido da Mamiba yaje can gefe yatsaya, Nan Mami tayima Dr lzinin shiga, can anjima tafito rik'e da Baki ta kalli Mami tace "Hajiya wai *Fyad'e* akayima yarinyannane? Kome? Abinfa yayi yawa,


Da ldo Mami tamata ishara da inda Kb yake tsaye,


Jinjina kai Dr Husna tayi harxata koma ciki tafasa ta k'arasa inda yake tsaye kaman ankafashi zufa sai binjikinsa yake ji yake kaman k'asa ya tsage yashiga, murya k'asa2 tace "Haba Yarona kaifa likitane baikamata kanuna k'arfi haka ma matarkaba koda tamaka gardamanee sai kaduba yarintanta, pls dan Allah kakiyaye gaba, karkasakemata haka, yanzu kanimo mana kayan aiki za'amata d'inki nan tagayamasa abunda take buk'ata yafita,


Bai wani d'auki lokaciba yadawo saidai baisamesu ananba dan haka yakai sashen Mami,

Mamin kawai yasamu afalo yana sosa kai ya mik'amata itakan kallon Mamakin abunda ya aikata kawai takemasa, Anyah Kabir d'intane ko ancanzashine,


Yana fita sashensa yakoma, har angyara d'akin an canja bedshit d'in fad'awa yayi akan gadon yana maida Numfashi,

Sai kallon ldon Maminsa da tayi ta hukuntashi dasu yakeyi yayi juyi ya rungumo pillow,
" Just 2 hours only fa Mami, "mtsss raguwa kawai yafad'a yana lumshe ldo,


Su Dijah anji jiki 😁

ba ita tagane kantaba har sai kusan magriba bayan Alluran Baccin da Likita tamata kafin tamata d'inki,

Sosai Gambo take bata kulawa, matan da Mami ta samo dan kula da ita dan ta lura dukansu biyu maidata suruka sukayi, basu yarda idonsu ya had'u danata,


Sai bayan isha'i Mami tashigo akan sallaya tasamu Dijah tana shan pape suoup d'in kaza, ganin yanda take sinne kaine yasa ta fita tana murmushi, sai alokcin ta tuno Kb ko abun karyawa bata bashiba, kuma yananan agidan tasani bai fitaba, Wayanta ta d'aga tak'irashi tace masa yazo, bai b'ata lokaciba wajen zuwa,

nan ta gabatar masa da Abinci ta fita,

Sosai yasake yaci ya k'oshi, dan tun safi ruwan tea ne kawai acikinsa, Mami tadawo dai2 lokacin yagama, kallon juna suka shigayi ta k'asan ido,

atunaninsa zata masa fad'an abunda yayi shiyasa ya tank'washe k'afa yana sauraro, itakam Mami dariya yaso yabata yau ga Kabir najin kunyanta sai Abubuwa yake kaman Maraya,


Ganin tashiga wani sabgantane yasashi mik'ewa yanamata sai da Safe, dahaka sukayi sallam ya fito sai kallon d'akin Dijah yakeyi har ya fice,

bayan yagama duk abunda yasabane kafin kwanciyansa, ya kwanta, anma wani abu maikama da kewa ya addabeshi,

juyi yake tayi tundaga farkon Gado har k'arshensa, ya rungumo pillows anma ba sauk'i da k'yar bacci yayi gaba dashi,


Bayan sati d'aya Dijah ta ware fes kaman ba itaba, saidai har zuwa yanzu basuyi ido biyu da Kb ba, dan sam bata fitowa, yayi2 yasamu yaganta abu yagagara,

sai kuma daga baya ya tuhumi kansa wai ina Ruwanshi da itane,

yau Lahadi da sassafe Sani yayi waya ma Mami cewa Bintalo ta kwana a Asibiti tana labour anma har yanzu bata haihuba, suna gama waya Mami ta fita batare da tasanar da kowa ba ta tafi asibiti,


Da misalin 10:00 na safe Kb ya shigo gaida Mami, nan yatar da batanan,

ya juya har zai fita yadawo ahankali ya tura k'ofan d'akin Dijah ya shiga, alokacin tana zaune da waya ahanunta tana chert,

yanda tagama gayunta kenan cikin Riga da wando na jeans sake baki kawai yayi yana kallonta dan bai tab'a ganinta da irin dressing d'inba, d'ago kan da zatayi sukayi ido hud'u dashi yana takowa, arazane ta tashi zata gudu, sai kuma tarasa inda zata shiga, dan haka kawai ta fara kuka tana ja da baya

hard'e Hanunsa yayi ak'irjinsa yana kallonta da d'an Murmushi, har takai bango ya tako ya k'araso, tsugunawa tayi tan girgiza kai "Dan Allah Likita kayi hak'uri wlh nibance komiba, ya tsuguna aganbanta yana Murmushi, yace "Haba Khadijah kebakiyi missing d'inaba? Meye abun gudu ajikina kaman kinga wani Dodo? Me kiketsoro game dani? Ya fad'a yan shirin rik'o Hanunta, janye hanun tayi tana magiyan ya barta,


"Allah Khadijah ba abunda zanmiki nazone kawai inga lfynki, kiyarda dani pls ki kwantar da hankalinki, ya Rungumota Jikinsa yana Murmushi sauk'e ajiyan zuciya sukayi a tare ya kalleta, yajikin naki?


D'an turo baki tayi tace "Ni lfyna k'alau,

Kintabbata? Kodai in bincika ingani da kaina ya fad'a yana kashemata ido, da siririn murmushi a fuskansa,


*Yau nasan kun gaji da karatunma* 😜


*Ummu Fatima ce* 😘
[8/16, 5:35 PM] Ummu Fatyma: πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ¦‹πŸ¦‹



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


5⃣5⃣


K'ok'arin zamewa takeyi duk da yanayin da takejinta ajikinsa, kaman tayi missing nashi,



Yak'ara rik'ota, tace nifa "Ba inda yakemin ciwo, kasakeni zanje gaida lya ne,

"Ok to barin Maimaita, Azabure tace "mene?
"fyd'en mana,
Idonta taf da Hawaye ta kalleshi "Nifa bancemaka d'an.is.. Sai kuma tayi shiru, d'agota yayi suka haura gado, Nan Dijah tasa kuka, "ni wlh bance komiba,

Yad'ora hanunsa kan bakinta "Shittttt ai nagayamiki zaki iya cigaba da k'irana d'an iska yanzu,

Tana girgiza kai tace "wlw bazan sakeba, dariya yayi sosai ganin yanda take ta zare ldo cike da tsoro,

Dan Allah Likita kayi ha.... Bai bari ta idaba ya rufe bakinta danashi,

Sosai yauma ta d'and'ana kud'anta ahanunsa, tayi kuka har ta gaji, shikan mutumin tunda yasamu biyan buk'ata, ya juyamata baya, lumshe idonsa yayi yana sauraron kukanta, daga bisani ya juyo ya Rungumota jikinsa yana shafa Gashin kanta,




"Sory Khadijah daina kukan hakan kinji, bazan sakeba, cikin zolaya yace "in Mami ta dawo kar kice mata namiki fyad'e kinji, da sauri ta d'aga kanta alaman to yana Murmushi yatashi yashiga toilet, ya had'amata Ruwan zafi kaman yanda Ranan lya tasaashi,

ya fito kenan ya hango Dijah daf da k'ofa zata gudu da sauri ya sha gabanta gami da kamota, "Ina kuma zakije?

"Babu ta fad'a da sauri, tana ture Hanunsa "Dan Allah Dr Kayi Hak'uri wlh Dazafi, mutuwa zanyi, dariya ne yakusan k'wacemasa, dan ya lura Hak'urin na gaske yau take bashi, ba na shak'iyancin da tasaba,


Hanunta ya kamo har cikin bayan gidan gami da nuna mata Ruwan yace shiga kiyi wanka Khadijah ba abunda zai saki Mutu,

"To ba kaibane kajimin ciwoba,

"No yau ban jin miki ciwoba, shiga kiji, badan tasoba, dan tsoronsa kawai tayi abunda yace,


Ya fito da niyan shima ya kwab'e yaje suyi wankan tare yaji anbud'e Gate, labulen Window ya bud'e nan ya hango motan Mami, da Sauri ya maida kayansa ya lek'o bayi yace Ma Dijah inkin shirya kizo pert d'ina inbaki magani,




"tou tace dasauri, ya rufo k'ofan yana dariya yafita aransa yace "Ashe akwai abunda zai kashe wannan tsiwa da gautsin bakinkin, kizama mai ladabi?

Kicib'us sukayi da Mami afalo, nan ya k'ak'alo yaudarraren Murmushi yana sosa kai,

"Sannu da dawowa Mami ta, Harara ta dinga binsa dashi, da yasa ya shiga taitayinsa,

"Meya kaika d'akin Khadijah?
"Mnn yanzu shigowana Mami naje d'akinki bangankiba, shine naje tambayanta ina kikaje? Naga yau ba Ranan aikibane, ban gantaba ma, inaga tana wanka,

"Katabbata?
"i'm serious Mami,

"Mnm mnn fa Kabir kafita ahanyana kar inmaka tsiyafa, yayi k'asa da kansa yace "kiyi hak'uri Mami dagaske nakeyi, daga haka ya wuce ta bishi da harara tayi k'wafa,

Sai da yafita yayi dariya yana shafa kansa, "Oh KB yaushe kafara lya k'arya? Yafad'a yana tura k'ofan pert d'insa,

tsaye yasamu Nafisa agaban sif d'insa cikin tashin hankali, d'an turus yayi yana kallonta,

ta juyo suna kallon juna, Rai ajagule tace "KB kayan wata Banzan nagani a Sif d'inka? Tun kan yabata Amsa ldonta yakai kan Mirow cikin tashin hankali ta k'arasa tana kallon Cusmetic na Mata, "Kabir kana nufin kacemin wancan Banzance ta dawo d'akinnan? Ko me? Wlh bazai yiwuba wannan wani irin cin Amana ne bazaiyiwuba Kabir, ta k'arashe tana fatali da kayan gaban Mirrow, Ahanzarce ya rik'o hanunta, yana binta da wani irin kalo,


"Nafisa meyasa bakison zaman lfyane? Meyasa yanzu kk sake bakinki kina gayamin magana son ranki? Me ma yakawo har kike min Bincike har closet d'ina?

Fincike hanunta tayi "dole kace hakamana, tunda anci amanata nimafa matarkace ina da hakki na aure akanka, wlh bazaiyiwu inzuba ido irin na baya azalunceniba, bazaiyiwuba,


Cikin tsawa Kb yace "Ke da Allah can Rufemin Baki da maganakin marar ma'ana awajen= kebama abun kunya bane aji irin wannan magana abakinki, yaushema kikasan wani hak'k'in Aure? Inbanda Rashin kunya, mtsss yaja tsaki ya shige bayi,

nan ta kife akan gado tana kuka ga wani addabbaben kishi da takeji ga bak'in Maganan da Kb yagayamata, ga matsalanta datazo dashi, tanan awajen tana Rizgan kuka ya fito daga wanka, shirinsa yayi ko kallon inda take baiyiba, k'ananan kaya blue black jeans da shirt fari mai gidan daran blue, ba k'aramin kyau yayiba, ya feshe jikinsa da turare, ya d'auki wayansa yaga wajen 8 missed call Sani da Habib suka masa, key d'in Motansa ya d'auka yana dailing no. Habib yafita, Kuka Nafisa tasake rushewa dashi ta tashi tabi bayansa, tafad'a ajikinsa yana wayan yad'agota yazauna sannan yazaunar daita akan cinyasa yana wasa da yatsunta yana girgizamata kai Alaman tayi shiru, kwanciya luf tayi ajikinsa tana wasa da hanunsa da yarik'e yatsunta dashi, Har suka gama wayan ya ajiye gami da d'agota,


Kallonsa tayi tana share hawayen fuskanta tace "Kb kadaina Sona ne?


Yaja kumatunta "Halinkine banaso Nafisa, banason hayaniya kinsani,

"Maganafa nazo muyi dakai shine kaketamin fad'a

"Dakinso muyi magana ta fahimta bada haka zakizomimba, taya zakidinga k'ok'arin yimin tsawa da tuhuma kaman d'anki? Ina Ruwanki da min Bincike a d'aki?

Badun nakai zuciyana nesabama da zanekima nayi, ya fad'a yana dan gware goshinta,


Hawayene ya gangaromata yasa yatsunsa biyu ya share shikenan daina kukan fad'amin meke tafe dake Mata ta?

"Kabir tsakaninka da Allah ka kwanta da yarinyannan d'an had'e fuska yayi "kinga inbazaki fad'i abun da ke tafe dakeba sauk'amin jirana akeyi inada petian a Asibiti, banason Shirmen banza,

"Anmafa kai kamin Alk'awarin haka bazai faruba atsakaninku,

"K'arya kikeyi bamu tab'a wannan hiran dakeba, Kuma banason kidinga kawomin irin wannan Magana, koda wasa, lnason yazama wannan shine Rana nak'arshe da zaki sakemin wata magana akan yarinyannan kinaji?

Cikin tsananin b'acin Rai tace "to shikenan dama Dady ne yace wai shi har yanzu bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login