Showing 45001 words to 48000 words out of 155892 words

Chapter 16 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

461

da ldonta yad'an washe ta yaye labulen Windown tana lek'a inda taji Hayaniyan yafi yawa, jibga2 Motoci ta gani aharaban Gidan sai sceuirity dasuka kewaye wata mota guda d'aya,

Cikin Isa yasako k'afansa yafito Fuskansa d'auke da Murmushi da Farin Ciki sai Hanu yake basu suna Gaisawa,

bata iya Hangoshi gaba d'aya Amma tayi Mamakin yanda yakoma.


Wucewa Gaba yayi Rataye da suit d'insa awuyansa, nan suka Rufa masa Baya, sauri yakeyi kaman zai tsaga k'asa Burinsa kawai yaganshi agaban Maminsa, ldonsa suga Mami ji yake kaman ya shekara goma baigantaba.



*Ummu fatima* 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹

*Fatan Alkhairi gareku Manyan mata*
*Maryam Ahmad paki*
*Fauxia m Bala*
*Ummu Nabil*
*mrs Makama*
*Mrs Mansur*
*Jidder*
*Aysha Bagudo*
*Maimuna matan Abdoulaye*
*Munira*
*Officail sa'adatu Alk'ali*
*Aysha Machika*
*Aunty Fauza*
*Matar tsoho*πŸ‘΄πŸ½ *yar Mutan kagara*

*Allah yak'ara muku Basira da Hazak'a* πŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌ


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬


🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣7⃣




Dai2 k'ofan shiga Falon Mami seceurityn suka tsaya, shi da Sani ne wanda yake rik'e da Breaf case d'insa suka k'arasa ciki a lokacin Mami tana zaune akan Sofa cikin koriyar atamfan Super Englsh Riga da zani, sai Murmushi takeyi tana Raba ido ta ina zata fara ganin Tilon d'an nata?


Zuba masa ido tayi bako k'iftawa Kabir!! Ta fad'a cike da Mamaki D'aya biyu uku ta fara k'irge da yatsunta azuciyanta, wai tanason ta tuno watanni nawane Rabonsa da ita? Da har ya canza irin haka, fatarsa ta murje tayi wani Haske na daban yad'an yi cika kad'an gashin jikinsa ya manne akan fatansa kaman irin larabawan Kuwait d'innan.



Agabanta ya durk'usa ya d'ora kansa akan gwiwan k'afanta yana Murza goshinsa akan k'afanta, yanajin wani irin so da k'aunan Mahaifiyartasa, Duk irin boren da Mami taso tamasa na jimawan da yayi bayan bai gayamataba kafin yatafi duk yakawu,

Farin cikin Ganinsa yamantar da ita komi,


Ta dinga shafa kansa tana Murmushi tsawon lokaci suna ahaka kafin yad'ago yana kallonta, ahankali ya furta "Mami!!.

Saikuma yasaki murmushi ya zauna dirshan kaman k'aramin yaro agabanta, Mamina Nayi missin naki.


"Nima Haka my lovley Son, daga wata uku saigaka kanason zarta wata shida Kabir?


Sunkuyar da kansa k'asa yayi yana Murmushi "kiyi Hak'uri My Mum wlh badaganibane.


"To shikenan ai tunda gaka Allah yadawomin da kai lfy Alhamdulillah Allah ya Albarkaci abunda da kasamu acan.


"Ameeen Mami na"

Sai alokacin Mami tad'ago ta kalli Sani da yake ta kallonsu yana Murmushi, Gaisheta yayi Ta Amsa cikin kulawa,

"Ya Fatima tana nan lfy? Mun kasa zuwa muga Gidan naku.

Kodayake ku kuka Hanamu zuwa sabida yawan sintirinku bakwa sati baka kawotaba, Amma ikon Allah so d'aya suka had'u da "yar'uwanta, duk zuwanta tana Makaranta,


Amma yanzu sun samu Hutu Insha Allah zankawota tamuku ini,

Yauwa ni yabatun karatuntane kullum Inason tambayanka sai inmanta yakamata kamaidata makaranta taci gaba da karatunta.

Sani yad'anshafi kansa "Eh dama wai Nursing school takeso, to kinsan yanayin makarantan bamusamu Form di'nbama to amma tunda Allah yadawo da oga zamu samu yanzu.


"Assha meyasa baka gayaminba ai dana samomuku tuntuni, Shikenannan yanzu kam tunda gashi aiko ba Admission za'asata a Aji, Nigeria kenan tafad'a tana dariya.

Kabir yad'an had'e Gira yana kallon Sani

"Malam tashi kafita kajirani awaje ina fitowa.

"Kabir yazaka koremin d'a? Bayan katafi Kabarni shida Habibne suke d'ebeminn kewanka, kullum suna tare dani.

"Shiyasama nace yafitan Mami Kusan kodayaushe inmuna waya yakancemin gashi Agidanki.


Yanzukuma yawani zo yasaki agaba da maganan matansa shi Adole ga mai Mata, Ni ansani agefe.


Sani yana dariya ya suri breaf case d'in yakalleshi "To inmutum yaji Haushi shima yayi matanmana.

"Gayamasa dai Sani Ga Amininsa Habib dai za'amasa Auren Dole wata mai kamawa.

Da Harar Kb ya raka Sani dayaketa Dariyan Maganan Mamin, har ya b'ace ma ganinsa, sannan yadawo da kallonsa ga Mami.

Dai2 lokacin Nafisa tafito daga d'akinta cikin Riga da sket English wears maijikin Roba ya matseta cif ajikinta tasha kwalliya kam afuskanta kamar Aljanna turare sai tashi yakeyi ajikinta kaman acampaninsa take.

Kallo d'aya Ya mata yad'auke kansa aransa yana tir da wannan shiga hak'ik'a yadawoda niyan Auren Nafisa don cika Burin mahaifiyansa, Amma sai ya d'auki Mataki akanta don yalura yanzu d'abi'unta suncanza, yanasane da Randa zai bar gari ahanyarsa ta zuwa air port yaganta amotan saurayi.

Cikin shock naganin yanda Kabir yadawo tak'araso zata fad'a jikinsa, Da dabara yad'anyi Zillo yakoma gefe ta fad'a jikin Mami mik'ewa yayi Hanunsa zube cikin Aljihun wandonsa yana d'an Murmushi "waike bakya Girmane? Nafisa kodayaushe Halinki irin nayara, ai yanzu kinwuce min Irin wannan oyoyo d'in.


Turo baki tayi ta kalli Mami, "Mami kinji irin Abundayake fad'ako?

Mami da Gaba d'aya kunyan furuncin Kabir yagama kamata Dariya tayi tana Kallonta Talura ita ko ajikinta bata ma Fahimci abunda yake nufiba.


"Rabu dashi danma yaga an damu dashine.


D'an tattaki kad'an yayi acikin Falon yanabin ko ina da Kallo yace "Mami Falonnan yayi kyau saidai kujerun Daining d'innan sunyi k'anana,

Tasowa Mami tayi tana kallon kujerun "kaidai kafi son Manyan Kujerune irin na pert d'inka amman wa innanma Sunyi Kabir, Kansa ya gyad'a zai sake magana.


Ta katseshi da kashiga kagaida Iya tukun sai kazo muci Abinci,

Murmushi yayi cikin jin dad'in tunamasa datayi tsohuwa Iya tana gidan,


"Barinje inwatsa Ruwa Mami kafin inzo kinsan Iya da surutu, yanzu sai ta rik'eni anan har dare banyi komiba.

"To kadai Hanzarta kar tayi fad'a dan tuntuni take tambayan ka.



Fitowan Dijah daga Wanka kenan, taji wayanta na Ruri ta d'auka tanasawa akunnenta baiko jira jin Sallamantaba yace "Ina waje inajiranki 'yanmata,

ajiye wayan tayi a fili tace yaya Sani kenan, sai kuma ta jinjina kai tana tunani wai ace suna Gari d'aya da Bintalo Amma su d'auki wannan lokaci basu ga junaba, tanason tace ma Mami zataje saidai batasan yadda Mamin zata Fahimci zancenba, shiyasa tayi shiru da bakinta.


Doguwar Rigan Atamfa tasaka blue mai had'e da bak'i da pink, Fuskanta ba kwalliya kasancewanta ba ma'abociya Kwalliya ba, Pawder ne kawai sai Lip glow da tashafa, ta d'auki bak'in mayafi mai stones Golden ajiki plat takalmi tasa bak'i tafito Hanunta Rik'e da wayanta tana tafiya kamar bazata taka k'asaba, ahankali tana dube2 ta inda zata ga Sani.


Yayi dai2 da Fitowan Kabir daga Falon Mami da niyan watsa Ruwa, ahankali idonsa ya sauk'a abayanta, Zuba ma Bayanta ido yayi cikin Rashin Sani yake k'arameta kallo karo na farko arayuwansa dayasa mace agabansa yaji yana sha'awan ta juyo ya kalleta, wa iyazubillah ya furta ahankali yana gargad'i ma zuciyansa, to idan matan Aure ce fa? Ai Hak'k'in zai maka yawa, wata zuciyan tagayamasa, Amma haryanzu yakasa d'auke Idonsa ba Abinma dayafi jan Hankalinsa irin tafiyan da takeyi.


Addababben k'amshin turaren dayak'i fita ahancintane tsawan lokaci tana mafarkin wannan turare shine ya ziyarci hancinta azahira, ahanakli ta juyo Bayanta, cikin sauri ya sunkuyar da Kansa, dan inyabari taga yana Kallonta yaci baya aganinsa koma wacece ita tayi kad'an yasaci Kallonta.



Itakuwa tana sauk'e idonta akan Fuskansa wani Jiri yaziyarceta dan Haka dasauri ta matsa ahanya cikin d'aukewan Numfashi tabashi Wuri.

shikuwa cikin zafin Nama ya wuceta batare da yako sake Kallon inda takeba, aganinshi wanda yayi d'azunma kuskure ne da sharrin Shed'an.


Binbayansa tayi da kallo zuciyanta sai harbawa yakeyi da sauri da sauri, har ya bud'e pert d'inshi ya shiga, yab'ace ma ganinta, tad'an jingina da wani Pilah awajen tana mai da Numfashi,


Sani ta hango ya bibayansa jimawa kad'an kuma ya fito dama shikam yaganta tun fitowanta, Gunta yak'araso kai tsaye,



Yadai Khadijah? Badai Bacci kk jiba dan tun zuwana nake tambayan Mami take cemin kina Bacci,



"Ba Bacci nakejiba to yana ganki haka? Ko jikin ne?

Ta sauk'e ajiyan zuciya,

"Nothing ya Bintalo? Bayan Hanunsa ya juya zai Buge bakinta ta zille tana Dariya, "Duka kuma yaya Sani?

"Iyi tunda Kunnenki bayajin Magana ai sai jikinki yagayamiki, sonawa na hanaki fad'an wannan Sunan?

"Oh sory Wlh mantawa nakeyi ya Aunty Binta?

"lfynta k'alau tana nan kullum sai tayi jajanki,

"Ayyah duk zuwanta bama had'uwa, yanzu ai Munyi Hutu zanzo muku kwana,

Kwana? Yafad'a yana zaro ido

"ke wayace miki ana kwana agidan Amare?

Bamu gayyacekiba, ininma dai kar muk'ine ace muna da bak'in Hali,

Dariya kawai tayi dan sam ba ta fahimci zancenba,

Dai2 lokacin Nafisa tafito k'amshin tirarentane yafara musu sallama kafin ta iso wani wulak'ancaccen kallo tabisu dashi, kafin ta wuce. Da ido Dijah ta Rakata.


Sashin Kb ta bud'e tashiga, Dijah ta tab'e baki ta kalli Sani shima Hanyan da Nafisan ta wuce yake kallo,


" Waini wannan wacece agidannan?

Sani yana Dariya yace "Gaskiya Kafin kayi fad'a da mutum kasan shi waye tukun, kinyi Tambaya me kyau.

Tahad'e Fuska ninace maka fad'a zanyi da ita?

"No tunda dai kinyi Tambaya kitsaya abaki Amsa

"Inajinka
"yauwa ita dai wannan d'in Sunanta Nafisa,

"Eh inaji ana fad'a

"yauwa 'yar k'anin Mahaifin Kb ne kuma mai niman Aurensa,


Zaro Ido Dijah tayi sosai tana kallonsa bako k'yaftawa, har ya sunkuyar da kai yad'ago tana cigaba da Kallon fuskansa.

"Yadai ko kina cikine?

Turo baki tayi kaman mai shirin yin kuka, tace "Allah yasauwak'e magananne dai yamin wani iri dama mace tana niman aure?

"Eh gashi kuma kingani,

"Kana nufin kacemin dama abinda yake kawota gidannan kennan?

"Iyi tsawon Lokaci tana binshi ya aureta yak'i Amma yanzu ya Amince zai Aureta, Nan yabata lbrn tun farko har zuwa yanzu.

Zuba ma k'ofan Ido Dijah tayi cike da Mamaki mai kashe jiki,

sai surutu Sani yake mata Amma bata fahimtan Komi, ta k'urama k'ofan Ido kaman maison Gano wani Abun.
Aranta kuwa ji take ta tsani Nafisan dama duk wata Mace mai Hali irin nata ita kam tanaga ci bayane Mace tabari Namiji ya fahimci wai tana sonsa. "mtssstt taja dogon tsaki.

Ganin bata cikin Nitsuwantane yasa ya sallameta ya tafi,

Tsawon Lokaci tana tsaye awajen tana abu d'aya.

cikin Rashin K'arfin gwiwa ta shige ciki d'akin Iya tashiga.

Alokacin iya tana Rik'e da k'ur'ani da k'aton Glass a idonta wanda yake k'aramata karfin ganin Rubutu daga dukkan Alamu ta idar da Sallahn Walhane, kan Gadonta ta haye jifa2 Kuma tana lek'a d'akin ta Window ko zataga Nafisan tafito amma shiru.

Aranta kuwa tuni tabasu wani matsayi na daban dan haka ta tashi zaune tana lek'e tana d'an mita aranta, guntun tsaki taja batare datasan yafitoba tace "Ashema 'yar lskace kike yi ma mutane kallon banza.

Tana shirin sake labulen kenan ta hangosu sunfito ajere, kowannensu Fuskansa d'auke da Murmushi, Nafisa tana magana shikuma gogan Murmushin kawai yakeyi kansa ak'asa da Alama ma Wanka yayi yana sanye da Jallabiya cottin mai guntu Hanu Ruwan k'asa kansa sai k'yalli yakeyi wani.

Dogon tsaki taja ta sake labulen ta koma ta kwanta.

Tana kallon slim taji sallamansu da sauri ta gyara rufan gyalenta ta juya musu baya.


*Ummu Fatima* 🀝🏻😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*UMMU FATIMA CE*πŸ‡³πŸ‡¬

*Jinjina Gareku da fatan Alkhairi*πŸ‘πŸ»πŸ€²πŸ»

*Halima Mk*
*Nasiba Gawo*
*Ummi ontop*
*Hadiza isyaku*
*miss Ayyush*
*Maman Aysha*
*Nafisa*
*Allah yak'ara Basira da d'aukaka* πŸ™πŸΌ

🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 2⃣8⃣


Fuskanshi d'auke da Murmushi mai cike da Farin ciki ya zauna agaban lya yana Fuskantan ta.


Rufe k'ur'anin tayi ta ajiye a gefe gami da zare Glass d'in Idonta tana kallonshi, Tana Murmshin farin ciki.

Photon d'anta ne yadawomata sak Kabir yake kama da Mahaifinsa,

"Tsohuwa Irin wannan kallonfa?

Ko kinzaci Malam ne yadawo,

"Kai kama isa ka kamo k'afan Malam, wayacemaka kallon ka nakeyi?

"OK to barin koma Inda na fito yafad'a yana k'ok'arin tashi.


Caraf lya takamo k'afansa tana Dariya "Yi Hak'uri Mai Gidana na Kaina, ai Yanzu Kaine sanyin Ido na Muhammad Khabir kai ka maye Gurbin Mahaifinka aguna ka maye Gurbin kakan ka Malam.

Muhammadu Kabiru Muhammadu mai suna dayawa, Muhammdu sunanka yafi K'arfin Arne,

Barka da Gani na Barka da Nasara Kabir, ta'ajiye Maganan a Raunane.


Murmushi Kabir yake tayi, cikin Tausayin Kakartasahi, ya kamo Hanunta irin wannan kirari Haka Iya Tukuicinki Umra Insha Allah dake zamu Umrannan,


"Kai nasamu Tukuici Mafi Girma Allah yayimaka Albarka yabaka mace tagari da zuri'a mai Albarka,


Nafisa maza k'iramin Uwanku inmata Albishir wannan Abun farinciki, kwanan nadawo gashi zankuma komawa tafad'a tana sharan k'walla, tana Kallon Nafisa da take d'an shan K'amshi.

"Gani nanma iya tun daga kitchen nake jiyo Addu'an ki meke Faruwa ne?


Kedai zauna kiji Fatima Kabiru zai mai dani Umra,

Mami ta zauna tana Dariya "ai wannan Dolensane ma Iya tun ba yauba yake saki ki taho wai kinzo tarbansa sai kizo yak'i dawowa.


Kabir ya gyara zama yana kallon Mami yace "to Mami wai me takeyi a Maiduguri? Wlh ni sonake ta dawo nan muzauna, nasha k'iranta awaya ina rok'onta tsohuwannan fir tak'i pls Mami kisa baki yak'arsa maganan da sigan rok'o.


Tun kafin Mami tayi magana lya tace "ai nagayamaka kabari sai kayi aure tukun sai inkoma gidanka na lna d'an d'ebe ma matarka kewa,

"Ok shikenan Yanzu sai bazaki komaba sai kijira in nayi Auren sai mukoma Gidan gaba d'aya.

"To yaushene Auren naka?

Ya sunkuyar da kai yana susa k'eya "ki Tambayi Mami Itace zatamin auren.

"lya Rabu dashi kawai Wai yana ba'a ne Amma ba'ansa zai tabbata Very soon.

Shida Abokinsa sunkasa tsayar da hankalinsu sufitar da mata suyi aure, shi abokin yanzu Auren Dole za'amasa kwanan nan.

Iya tace shima ai dakunbi nawa tuntuni da hakan kukamasa, Amma yanzuma bata b'aciba sai ahad'a dana Habibun kawai.


"Yauwa lya hakanma za'ayi indai yana son ki dawon, Mami tafad'a atak'aice. Nan suka fara magana akan maganan Auren nasa.

Kabir dai kansa yana sunkuye yana Duba massages d'insa na email.


Sallahn Azahar da aka k'irane yad'aga shi yatafi Masallaci.


Bashi ya dawoba sai da aka idar da sallahn lsha'i yana can yana fama da jama'a kala2 wayan Da Mami take tamasane yasa yashigo, shi da Habib, Dr Na'im da Sani, Mami tanazaune akan kujera.


Yana shigowa baiyarda sun had'a ido da Mamin ba, kai tsaye ya wuce Daining don yasan k'iran kenan.


Sune suka k'arasa suka gaidata sannan suka Haye Dainingd'in.



Kwanan Kabir Uku da dawowa, Dijah bata tab'a yarda sun zauna inuwa d'ayaba, duk yanda Mami taso sudinga cin Abinci a tare ta ware Kanta Dan Haka kawai take jin wani Haushinsu shi da Nafisa.


Ahankali ta lura Nafisa irin Matannane marasa kamun kai, la'akari datayi da irin Mannemasa da takeyi gashi Sam batasan girmama Nagaba da itaba,

Don Ko zuwa gaida lya batayi inka ganta ad'akin lya to tabi KB ne, Itama lyan tunda ta lura da halinta ta d'ibeta tawatsar acewanta Barewa batayi gudu d'anta yayi Rarrafeba.


Ko yauma tana Hango Su daga kitchen tana aiki Suna karyawa k'ok'arin bashi Abincin Abaki takeyi shikuma yana kaucewa, k'asa2 yake kallon Mami datayi kamar batasan da wanzuwansu agunba,

Ak'asan Ranta kuwa mamakin Halin da Nafisan ta koyo takeyi dondai tuntuni tasan irin son datakeyi ma Kabir amman dai bai Rufemata ldo har hakaba,


Gudu2 Kabir ya kamalla ya mik'e Dan so yake Yau ya lek'a wajen aiki,

"Mami Barin je
"To Allah ya kare
Nafisa ta tashi Itama tanayi ma Mami sallama wai zata gidansu sai da yamma tadawo.


"Khadijah! Mami ta Rafka mata k'ira,

Daga kitchen d'in ta fito tana Amsawa,
"Gani Mami,

Mami ta jefeta da Harara, ai sai kizo ki karya tunda Dodon naki ya fita.


Tad'an marairaice Fuska "Mami fa na k'oshine,

"OK munfara sa'insane bansani ba?


Jawo kujera tayi ta zauna ta d'ibi chiefs ta fara ci, Mami ta kalleta "Wai Meye tsakaninki da Kabir ne? Tunda yadawo naga kincanza kullum kina kitchen dakinga zamu ci Abinci sai ki tsiri wani aikin?


Turo Bakinta tayi tana yatsina Fuska "Mami wlh ni haka kawai na tsani 'yan iska, shiyasa bani son ganinsa shida wannan 'Yar Rainin Hankalin.

Zaro ido Mami tayi gami da rik'e Hab'a, 'yan iskafa kikace Khadijah iskancin me sukeyi?

Had'iye dankalin Bakinta tayi ta kurb'i Tea tana kallon Mami alamun zatayi Magana mai muhimmanci.

"Wlh Mami lskanci sukeyi baki Gani Harda ido sunayi, inayawan lek'asu ta Window Har maganan lskanci Sunayi Rananma inaji tanace masa wai kowani Numfashinta da sonsa takeyi shikuma yace mata wai Shi har Mafarkin Ranan aurensu yayi yana ta d'oki har antaru za ad'aura sai kuma aka fasa aka aura masa wata yarinyan da bai santaba.
Kinsan meye Mami?

Mami da har yanzu take Rik'e da Hab'a ta Girgiza kai.

Dijah tahad'iye yawu cike da takaici alamun Abun yabata Haushi sosai tace "Sokuwar kawai sai ta fashe da kuka takama Sambatu, Dijah ta mak'ale Murya ta dafe kanta tana koyon yanda taga Nafisan tayi, cikin Muryan Kuka "waiyo My Luve banji dad'in wannan mafarkin nakaba, Wlh da zai tabatta kowacece sai naga k'arshenta ina mai tabattarmaka zan iya kashe koma yar uban waye, duk wanda Ubanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login