Showing 33001 words to 36000 words out of 155892 words

Chapter 12 - Dijah Qaya Book 1 Hausa Novel Complete

22 Dec 2024

442

tajata suka shiga ciki,

Lokacin Bintalo tagama ma Mami shinfid'a a d'akin da yake gefen nasu, tare suka kwana da Dijah,


Washi gari da safene tabasu tsaraban datazo dashi kayan kwalliya sosai ta had'a wasu Dijah sannan tayi d'inki ma Inna da Baffa Harda buhun shinkafa, taliya da sauransu sosai Baffa yayi fad'a nacewan shibayison tadinga d'awainiya haka duk abunda zaiyi na Kabir Don Allah yamasa, itama tace badon Kb takawo musuba,

Yau Mami ita kad'ai ta shiga sashinsu Kb sunjima dukansu sun shan Hira takalli Sani tace "yarona naga kaman bakinka akwai magana ya sunkuyar dakai yana dariya sannan yadago ya kalli Kabir "mnn dama yace zai gayamiki,

"Zaigayamin me? Mami ta tambaya tana kallon Kb Kabir ya kwashe da dariya yace "wlh Sani baka da kunya ko kad'an,

Mami waifa yarinyan gidan nan yakeso tunjiya yadameni wai ingayamiki kisanar da iyayenta shine yakasa Hak'urin yajira infad'a miki,

Mami tace "Alhamdulillah naji dad'i sosai daga ke shirin "yanta kanka da kanka tun banmaka na dole ba

Khadijah yake so? Yarinya mai Hankali ga nitsuwa,

Kabir yad'an Had'e rai "Haba dai Mami mezaiyi da wannan Mahaukaciyan yarinyan? Fatima yake fad'a

Mami tarik'e hab'a Khadijahn ce Mahaukaciyan? Kabir Allah yanunamin gwananka aduniyannan, ta kalli Sani "Insha Allah zan nimamaka izini awajen mahaifinta daga haka ta fice,

Koda tasami Baffa da maganan Fatima yayi farin ciki sosai saidai yasanar da ita tana da manemi zai samu magabatansa da maganan yaji,

Kwanan Mami biyu ta koma duk da Kb ne yasata tak'ara d'ayan amma datazo tafiya bak'aramin damuwa yayiba, haka tayi ta lalkabashi kaman wani jariri,


Ahankali cikin ikon Allah K'afan Kb yasamu sauk'i sosai dan yanzu da k'afansa yake fita yaje masallaci yadawo, saidai d'an d'ingishi dayakeyi, Ganin haka yasa Sani yatafi gida duba Mahaifiyarsa, anan yabar Kb dagashi sai Iro,

Muje zuwa masoya Dijah k'aya yanzufa aka fara




*Ummu Fatima ce*😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*MY NATION*πŸ‡³πŸ‡¬







🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š



*page* 1⃣8⃣




Abun Duniya duk ya taru ya dami Alhaji Ya'u yarasa inda zaisa kansa har yanzu mafarkinsa yak'i yazama gaskiya,


Bashi da buri aduniya daya wuce ya mallaki Dukiyan Kabir amma abun yaci tura, ada yana ganin kashe Kabir shine masalaha saidai yanzu yana ganin yayi wauta dayawa,

ayanzu dai gashi ya halaka Kabir Amma Haryanzu burinsa bai cikaba, baisamu koda takarda d'ayaba na dukiyan, sannan Mamin da yakeso ya aura aikin boka yak'i tasiri akanta Ga yaranshi guda biyu dayaci burin suyi karatu Su zamo Abun kwatance abu yagagara, Aminu kam yagama lalacewa da shaye2 ga Nafisa tak'i karatun dayakashe mak'udan kud'i dantayi yanzu tazama saidai wannan samarin ya d'auketa wancan yad'auketa, wani abun Haushinma akan idonsa,

Inyace tafito da Miji tace KB take jira tunda haryanzu ba aji labarin mutuwansaba.

Wani hucin iska ya furzar, zuciyansa kaman wuta, dan takaici,

Wayansa yad'auka yayi d'an danne2 sannan yakara akunnensa, cikin fad'a yake magana, "Nacuceka ko kacuceni kai kace zaka samomin Boka yamin aiki danaje wajen Fatima duk abunda nace tayi zatayi,

kasani naje nasameta nace takawomin duk wani duccument na Kabir, sai gashi yayanta yashigo maganan har da shirin makani akotu, shiru yayi na d'an lokaci Sannan yace no yanzudai kawai so nake akashe Alhaji Musa yayanta inkungama dashi Fatima bazata gagareniba tunda angama da Kabir daga Haka ya ajiye wayan yanajin k'warin gwiwa,

🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴

Yau take Alhamis, matasa maza da Mata suna ta shirye shiryen Gobe juma'a Ranane da aka tanadar da wasannin Al'adun FULANI kala kala, Wanda k'ak'anan Rugan dasuke kewaye dasu suke zuwa ayi dasu.


Tun jiya Iro yakeba KB labarin yanda ake gudanar da wasan.

Kud'i sosai KB yabashi don yin nashi.


Tun da aka dawo daga Masallacin juma'a Kabir yake zaune akan kujeran Roba a k'ofan gida cikin kwalliyan shadda sky blue, Da Bak'ar Hula da tasha kari, bak'aramin kyau yayiba, shiyasa yawancin Masu Wucewa suke shagala da kallon sa.


Shikam Kallon yafara isansa don Haka ya mik'e da nufin shiga Gida,

Dai dai lokacin Baffa ya iso akan kekensa.

Da sauri Kabir ya matsoshi yana masa sannu.

Cike da fara'a Baffa ya amsa, yad'ora da "naji dad'in ganinka anan Likita,

Yanzu mukayi waya da Hajiya, take cemun wai ka matsa akan wai zaka koma asatinnan,

Cikin girmamawa Kabir yace "Wallahi kuwa Baffa Asibitin danake aiki Suna da buk'ata na Sosai kasancewan gaba d'ayan Asibitin babu Wanda yakaranci fannin dana karanta,
Tun barina wajen ba Wanda yamaye Gurbina Har yanzu saidai afita waje,

Shiyasa nakeson inkoma tunda naji sauk'i,
.
Baffa ya jinjina kai bank'i makaba Kabir sai dai zuwan Kawunka na kwanan nan yatabbatar min da cewa zaka d'an zauna anan dai dai agama gano masu Hanu cikin abumda aka maka,

Kayi Hak'uri kaji nasan dole kagaji kodon yanayin Rayiwanku tasha banban danamu.

Meya hana d'an'uwanka dawowane?

"Mahaifiyar shi ce bataji dad'iba, Anma da sauk'i inaga Gobe ko jibi zai zo insha Allah.

Baffah yace "Ayyah Allah yabata lafiya.
Dai dai lokacin Dijah tafito zata shiga Gidansu Jebu, Baffa yace "yauwa Ga Dijah kuje ta nuna maka Gari, inaga zaman waje d'ayane ya dameka,

Daga haka ya shige ciki yabarsu anan,

Kabir Sam baiji dad'iba aransa, Dan baya k'aunan abunda zai had'a Inuwansu da Dijah,

Itakam sosai tashagaltu da kallon kb ba k'aramin kyau yamataba, Ahankali Kabir yad'ago ya kalleta, ya maida idonsa k'asa, ga yarinya har yarinya kyau da kyan fasali, duk Allah yabata Ga sweet voice, Sai Hatsabibanci,

Sake Binta da kallo yakeyi kayan FULANI ne ajikinta dark blue fuskanta ba wani kwalliya daga powdar sai kwalli sai d'an jam bakin da tashafa.

Cikin kasallaliyan Murya tace masa "Mutafi, sake kallonta yayi jin voice d'in datayi maganan dashi,

wuce wa tayi yabi bayanta, ajere suke tafiya ahankali kaman masu niman wani abu ak'asa.


Sund'anyi tafiya kad'an ya zauna akan Dutsi agindin wani Bishiya, danshi sam baiyarda da Dijah ba yasan k'aramin aikintane ta cusashi wani gurin.


Saida tad'anyi nisa sannan ta lura da baya bayanta.

Can tahangonshi zaune yana Kallon masu wucewa, "Lallaima wannan gayen ya rainani wallahi badon kar yab'ata Baffa yamin fad'aba da tafiyana nayi, tafad'a tana dawowa, agabanshi ta tsaya tana mishi wani kallo, Ganin bai ko kalli inda take bane yasata matsoshi, tace "katashi mutafi wallahi ko inyi tafiyana, kab'ata ba Ruwana dondai nan ba birnibane,

ai bata rufe bakiba ta hango kuliya yana zuwa inda suke wayyo Allah na!! Tafad'a atsorace ta juya zata gudu, cikin zafi ya cafkota yadawo da ita gabanshi, jikinta na b'ari tace "Don Allah kasakeni intafi wallahi banison kule, ta juya tana kallon kullen har yanzu gun yake zuwa, ta juyo ta kalli Kabir Murmushi yakeyi alamun zai mata mugunta, tahad'a Hununta Biyu tana matsan k'olla "Don Allah d'an Birni kayi hak'uri kasakeni in tafi, wani Murmushin muguntan yakumayi
"Waye d'an Birni?
Bakisan sunana bane? Ko rashin kunya?,

Kayi Hak'uri Don Allah Likita, tajuya daf da ita taga kullen yanashirin tab'ata wani k'ara tasake tayo kanshi Ganin tana shirin Hawa jikinsane yasa yad'agata cak ya d'orata kan wani k'aton Dutse, ya matsa da baya yana kakkab'e Hanunsa yana kallonta sai b'ari takeyi tana d'angale k'afafunta, Arayuwan Dijah kokun kulle taji sai hankalinta yatashi bare taganshi ido da ido, batayi auneba kawai taga Kb yad'auki kullen ahanunsa yana nufota, ihu tasaka tana shirin fad'owa akan Dutse da sauri ya tareta da hanunsa d'aya, yagyara mata zama yana rik'e da damtsen hanunta, d'ayan Hanunkuma yana rik'e da kullen, daga ita har kullen sai zare ido sukeyi

Cike da tsoro tafara magiya
"Don Allah yaya Likita kayi Hak'uri,

Saketa yayi ya Ajiye kullen ak'asa yana Dariya mai sauti "ta ina nazama yayanki? Dani yayanki ne Khadijah dana jima da b'ab'b'alaki,

Yazaro hankachef a Aljihunsa yana goge Hannayensa yana kallonta kuka takeyi tsakaninta da Allah, hankalinta bajikin kullen da takwanta luf ajikin dutsin tana wasa da takalmin Kb da yake k'afansa,

Yaja tsaki ke ga shegen tsoro kamar farar kura ga kuma rashin kunya, yanzu duk ina wannan tsiwanki yaje?

Tasa bayan hanunta tanashare hawayen da yake ta zirya akan fuskanta tace "Kayi Hak'uri yaya Likita wallahi bazan sakeba don Allah kakoreshi intafi gida Bacci nake ji,

Yana dariya yace to goge hawayenki tas inkinason inkoreshi ba musu takama bakin Hijabinta ta goge fuskanta, ya kalli fuskanta yayi jazur yace
"Meyasa ne ke bakya kwalliya kamana na "yanmatan garinnan? Shiru tayi tana sheshshek'a,
"Inbaki ban Amsaba zan d'aukota insamiki acikin Riganki,

Da sauri tace "nikawai bani son kwalliyane bayi burgeni,

Yatab'e baki "Ok masifa da Rashin kunyane kawai yake Burgeki?
Talangab'ar da kanta tace "
Nifa bana Masifa,

"to meyasa agarinnan ake cemiki Dijah k'aya?

"Nima haka naji suna fad'amin tun ina k'ara amma ba a fad'a a idona sai abayan idona, tad'an had'e rai wallahi duk yarinyan da tacenin Dijah k'aya sai nafasa mata baki.

Don Allah yaya kakoreshi intafi bacci nake ji tafad'a cikin sanyi murya,

Ya kalleta duk takoma kalan tausayi haka kawai yaji wani iri a zuciyansa,

"Niba yayanki bane nagaya miki Sunana Kabir inbaki saniba, kuma ba gida zamu komaba can wajen wasannan zamuje inason ganin wasan da za'ayi,

Gyad'a kanta tayi da sauri tace to yaya bazan komaba, dariya Kabir yayi har yana d'an sunkuyawa, jiyake kaman su tabbata ahaka ganin yanda takoma sosai game d'in yamasa.




*Tofah πŸ˜†πŸ€” yau Dijah ce daba Kb hak'uri? Hardace masa yaya? Gashi tace masa bazata sakeba anya kuwa dagske yaci bulus kenan? Kubiyoni danjin yanda zasuje dandali* πŸ˜‚

*Ummu Fatima* 😘
πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*DIJAH* *QAYA*

πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹
*BY ASMA'U GALADIMA*
πŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏπŸ¦‹πŸŒΏ

πŸ¦‹ πŸ¦‹
πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹ πŸ¦‹


*Ummu Fatima*πŸ‡³πŸ‡¬



🌈 *KAINUWA WRITTES ASSOCIATION*.......πŸ–Š


*page* 1⃣9⃣


Juya bayansa yayi yad'anyi taku biyu sannan yajuyo yana lasan lips d'insa yana Murmushi,

Yana kallon yanda gaba d'aya jikinta yake b'ari ga wani zufa da yakebinta Ganin bayi da niyan koran kulen ya sauk'o da irtane yasa ta daddage iya k'arfinta tasaki wani irin k'aran dayasa kulen ta tashi ta arce,

Cikin hanzari ya iso gabanta tana shirin fad'owa yacafeta yamayar da ita, zata sake k'walla wani k'aran yasa Hanunsa ya rufe mata baki,

Yanunata da yatsa kika kuskura kika k'ara min ihu ahanan ba abunda zai hana ban wurga magen nan cikin bakinkiba, ya cire hanunsa daga Bakinta, yana hararanta,


"Don Allah yaya kayi Hak'uri ka saukeni Mutafi, nagayamaka bazan sakeba Allah daga yau nadaina duk abunda nakeyi,

"Tam maza share hawayanki da zufan gaba d'aya, yafad'a yana sauk'ar da ita,

Ya mik'amata Hankachef takarb'a ta goge fuskanta suka tafi,

Daga d'an nesa yatsaya yana hango abunda sukeyi a filin, ba irin wara idonsa da baiyiba amma bai hango Dijah ba, hayaniyan gurinne yamasa yawa danhaka ya juya tacan bayan fili yatafi,

tundaga Nesa yahango Dijah ita da Lado tana tsugune ta tusa kanta atsakanin cinyoyinta ta danne Hijabinta dak'afafunta, Lado kuma ya d'an rank'wfo yana mata magana.

Dogon tsaki kabir yaja aranshi sai mita yakeyi ta yaya za'abar yarinya k'arama kaman wannan tana sauraran namiji? Ba dolema tarink'a rawan kaiba, wata k'ilama su suke koyamata abunda takeyinnan, yasake jan tsaki ya juya haka kawai yaji zuciyansa namasa zafi, gangarawa yayi can bakin kogi ya zauna akan wani itace, yana wurga k'ananan duwatsu acikin Ruwa.

Daga ta bayansa yaji motsin k'afa ahankali ya juya suka had'a ido da Dijah da Jebu, dawo da kansa yayi kan abunda yakeyi harsuka k'araso,

Aciki ya amsa gaisuwan Jebu, ko kallonsu baiyiba, harsuka gaji suka koma, yajima agun yana zaune daga bisani yad'auko wayansa a Aljuhu Sani yakeson yak'ira don d'azu yaga text d'insa Wai may be yadawo ayau,

Yana shirin k'iransa Wayan Mami ya shigo sai da yamurmusa ya d'auka bayan sun gama gausuwa tace "zakabari zuwa next Month d'inko?

Yad'an shagwab'e murya yana kwantar da Murya pls Mami aduba uzurina, kinsanfa akwai cus d'in da zanyi a England kuma inaga tafiyanmun bazai wuce nanda da three weaks ba pls Mami yafad'a in a cool voice.


"shikenan Kabir bazan hanaka dawowaba insha Allah ina zuwa asatinnan mudawo tare,


Wani ajiyan zuciya ya sauk'e mai nauyi yace "To my Mum nagode sosai dakika fahimceni, Allah yakaimu,

"yauwa sai maganan Sani da yarinyannan na tambayi mahaifinta awaya akan maganan damukayi dashi nacewa zai tintub'i iayen yaron fa yake nimanta, yanzu yace ba matsala kawai aturo, kai yanzu me kagani?

Kabir ya zaro ido kaman yana gabanta yace "Mami batayi k'aramaba kuwa ace yanzu za amata aure?

Mami tace "Matsalana dakai kenan Kabir mantawa nayi namaka maganan yo ai ko Khadija k'anwar Fatima batayi kad'anba amata aure balle kuma takwarata.


"Habadai Mami kidaina sa wannan yarinyan alisaffi,

"to shikenan Kabir nidai yanzu zan gayama su Yaya sukai musu Sadaki kawai kuma kai zaka bayar,

yayi Murmushi "karkidamu Mami hatta kayan auren da gidan dazasu zauna nad'auki nauyi zanbayar, "To Allah yasaka maka da Alkhairi,

Daga haka suka ajiye wayan, mik'ewa yayi dashirin tafiya yahango Dijah zaune jikin bishiya

Ta jingina kanta da bishiyan tana bacci, d'abi'an Dijah kenan indai zatayi kuka to tabbas zatayi Bacci, taso tatafi gida sai dai tana tunanin kar ta tafi Kabir yakasa komawa Gida πŸ˜†

Ragowan Dutsen dayake Hanunsa ya wurgeta dashi, firgit ta tashi tana sosa wajen ya harareta "oya tashi mutafi, daga haka ya juya ta tashi tabi bayansa,


"Khadijah taji ya k'ira sunanta ahankali tad'ago ta kalleshi,

shid'inma itan yake kallo, ya tab'e baki yace "wai mekike gaya ma samarukanki insun zo Hira wajenki?

Mai da kanta tayi tana kallon k'asa batasake d'agowa ta kalleshiba, shima bai kuma cewa komiba,

can anjima yaga ta kalleshi tayi murmushin da baisan nameyeba, Sannan yaga ta sunkuya ta d'auki k'aton Dutse a hanunta sam bai kawo komi aransaba, duk da Murmushin dayaga tanayi ahaka harsukazo kusa da gida,

da sauri Dijah ta k'arasa Jikin wata k'atuwar Bishiyan Kuka ta tsaya awajen tana dariya, kallonta kawai yakeyi har yak'araso wajen yana shirin tambayanta kotasamu matsalan k'wak'walwa ne,

Dutsen da yake Hanunta ta saiti Gidan Zuma da yake kan Bishiya ta wurgesu dashi, ta tsula da mugun gudu tashige cikin Gida, haba ai kan kaceme zuma sun taso gadangadan wajen Kb suka yo ga wani adabbaben turaren dayake tashi ajikinsa, ga k'afansa har yanzu batagama dawowa Normal ba,
Tashin HankaliπŸ€”

Gudu yafara mai kama da sassarfa, Sake fitowa tayi daga cikin gidan tatsaya abakin k'ofa tana tafi "Gurgu sai katsere, Gurgu sai katsere,

dai dai lokacin Motan sani tafaka awajen ganin haka yasa ta juya ta koma batare da yagantaba.

cikin zafin nama Sani ya Bud'e motan Kabir yashiga ya rufe baiyi auneba yaji Harbin ahanunsa Runtse ido yayi yana yarfe Hanun ya jingina kansa ajikin seat d'in motan yanajin yanda harbin yake ratsashi Sani ya had'a hannayensa yakashe zuman k'waya d'aya data biyoshi, yana kallon Kabir, yace

"Sory garin yaya Kb? Tunda nazo garinnan bantab'a ganin zumannan sun tashiba, ko turaren kane yad'agosu?


Bud'e idonsa kawai yayi ta glass d'in Motan yake ganin yanda zuman suke shawagi awajen batare da yace komiba,


Ahaka Baffah yafito daga cikin gida zai shiga gari dukansu suka fito Kabir yana goye da Hannayensa abaya suka k'arasa suna masa sannu,


"a Sani kadawone? Ya kabaro mai jikin?

"a jiki Alhamdulillah,

"to Allah yak'ara mata lfy
"Ameen,

Kallon Kabir yayi "yace Kabir har kundawone?

"Eh Nadawo ind'an hutane ya fad'a yana shafa kanshi,

"to barka inace dai ba wani matsala?

Sani yace Zumace ta harbeshi Baffa,

"Subahanallahi garin yaya Kabir? Yarane suka tab'osu ko? Dondai basu tashi hakanan,

Sunkuyar da kansa yayi tabbas da yasan Sani zai fad'a daya kwab'eshi,

Yana d'an murmushi ya kalli Baffa "nad'an zaunane ak'asan Bishiya watak'ila k'arfin da turarena yake dashine yasa,

"Ayyah to sannu barin dubomaka magani kashafa.


Tundaga wannan Rana Kabir yayi saranda wa Dijah yayarda da kirarin da mutanen garinsu suke mata, ya k'ara mata matsayi sosai awajen Hatsabibanci, yak'udura aransa bazai sake shiga sabgantaba,

To ab'angaren Dijahn itama hakane saida takoma gida gaba d'aya taji kunya yakamata sam taji bata ji dad'iba can kuma taturo baki ita kad'ai tace "to shima wayace ya shunamin Mage? Wlh inyasake nima Ramawa zanyi, ko da dare yayi bata yarda takaimusu Abinciba Bintalo ce takai tea d'in sama da tadafa wa Jebu tabayar takai masa wasan b'uya suka dinga yi sosai.



*Rayuwa kenan* yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login