Showing 33001 words to 36000 words out of 171903 words

Chapter 12 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

764

sauri zaata shiga Ta hangosa yana kkron tahowa wajenta da sauri cikin sassarfa.

Atunaninsa hutuwar datace masa zatayi bacci kawai hala zatayi.

budan baki yay zai mata magana ganin ta dakatar dashi da hannu yasaka yay shiru. Kunna motar tay sann ta dubeshi ta ciki tanamai cewa ka bude min gate malam liman.

Jikinshi a sanyaye yaje ya bude irin mummunan fixgar motar dayaga tayi saida ya yakoma da baya a rude yana salati da karfi.. ko mint biyu bai karayi ba yaga keyanta acan hartakai kan titi tana sharara wani uban gudu akan hanyar.

Da sauri ya koma gidan yana shiga room dinsa ya dau wayarsa ya hau bugawa uztaz kira kusan miscalls tara ya masa bai dauka ba sai ana karshen ya dauka hankli atashe yace salam Alaikum malam liman

Jin muryansa wani iri yasaka malam liman yace wa alaikusalam uztaz lafiya kuwa.

Yace ina kuwa lfya na farka da tashin hankli munata neman madam bamu ganta ba.

Cikin katseshi malam liman yace wata madan din?...uztaz ya ja tsaki a kufule kaji wani shirme dama can wata madam muke dashi banda miss halisa mansa?, Zai magana ya tsaresa a masife kai malam liman in baka da abun fadi ni zan shiga gari ynxu nemanta securityn mu duk sun fita amma bazan iya zaman jiransu ba gaskiya.

Agaggauce ya fada Yana shirin katse wayar cikin sauri Malam liman yace dakata uztaz,yace toh menen kuma fadi da sauri..yace dama na kira na gaya maka ne cewa madam fa tun karfe hudu na asubahi ta dawo gidan nan tacemin hutawa zatayi, ynzu ma na kiraka ne in gaya maka cewa ta kara ficewa kuma kamar naga bata cikin hayyacinta dan Allah kayi kkri kaje ka nemota kar taje tay hatsari ko wani abu yaje ya sameta.

Bakin Uztaz na rawa sosai yace dagaske kakeyi malam liman???
..tunkan ya amsashi yace tohh to nagode kashe wayar kawai ina zuwa.

Yana katse wayar ya fice acikin asbitin da uban sauri ya fita can waje ya nemo abun hawa ya wuce gidan agaggauce.

Already security sun riga sun bazama hanya ana neman halisa sanin cewa da motarta ta fita..

Ita kuwa ta baya tabi inda babu hanya mai kyau within 40 min max ta fito awani sharbaben anguwan masu kudi anan ta inda kyafaffen gidan hadiza yake wato anguwar lekki.

Wani coner na daban ta dauka nan ma tay tafiya me dan nisa kafin ta iske hadadden mansion din zach..

Nunfashinta dake kkrin daukewa cak ta dedeta snn ta Rage kudin motar gani datay kamar ana kkrin bude gate din.

Ahankli ta soma tahowa tun ma bata iso daf ba taga gate din abude anata kkrin loda wasu heavy luggages abayan booth din wata black range rover.

Kirjinta na bugawa ta rasa menene takeji gabaki daya dan wani irin tsinkewa da faduwar gaba mai tsanani ne suka rufeta a lkci guda sai taji kamr ta rasa nitsuwarta ne ma gabaki daya. Jikinta atake yahau karkarwa shikadansa.

Tanakaiwa daf da gate din tun batagai ga horn ba idanunta yaci karo da siffar wata budurwa a tsaye farace sollll sosai kamar ba yar kasar nigeria ba daf da motar zach din ana kkrin bude mata domin ta zauna aciki, a daskare halisa ta kuresu da idanu, sai wani rigima take ta sako dark green silky gown iya kan cinyarta, rabin nonowarta na waje tasha uban heels ga wani kwalliyar kece raini da ta zubawa fuskarta.

Hawaye yuuuu suke sauka da ga idanuwan halisa izuwa kasa, ji tay kamar notinan kanta na kwancewa, dan Harga Allah halisa batasan yadda akayi ta iya danne tsananin azaban kishin dataji ya cakke zuciyarta ayanzu ba.

Kkrin saukowa take da sauri jikinta na rawa taga wai harsun kammala sun fito, gani tayi sun dau kan hanyar dake gabanta dake ita ta baya ta fito da alaman basu ganta ba.


Sauri tay ta isa gaban megida,muryanta na rawa tace hey, ya juyo a tsorace ganin itace jikin shi sai yay sanyi.

Goo...good morning maam..akwaita da iya danne zuciyarta sosai dan haka calmly tace masa morning, da harshen turanci tacemai zach ne awaccn motar?
Bai iya mata karya ba ya gyada kansa sabbin hawaye yaga yana sauko mata sai yaji ta bashi tausyi sosai..
tace can you Please tell me where he is heading to..

Yace Airpot maa.
Muryanta na kukan tana kkrin danneshi amma ina kukan yaci karfinta ta ciki, ahankli Tace but I tot he is in london?..

Mai gadi yace eh amma jiya yazo deben kayansa yaune dai zai koma .

Batare da ta kalleshi ba Tace okay thanks. Kafin ya amsata Ta juya da gudu ta koma motar tawani wainashi da mugun gudu ta shiga binsu abaya.

Kukan datake dannewa ta sakeshi a fili tanayi kamar dama jira take a ballo matashi .

Aranta Ta mugun yarda da zach, yaukoma wacece acikin motarsa tare dashi tabbas yau ta dandanwa zuciyarta wutar kishi mai zafi da radaddi.

Dake sun mata nisa yasaka baima lura da cewa tana biyosu ba

Ita kuwa gudun data sharo dashi yasa harta kusa cimmasun dan daga inda take tana iya hango bayan motarsu.


Daga ta bangaren uztaz kuwa yana sauka abakin gate ya gamu da malam liman atsaye,agaggauce yahau tambayarsa shikuwa bai boye masa komi ba ya gaggaya masa abunda ya lura dashi.

Cikin sauri uztaz ya shige cikin gidan ganin falonta is intact yasa ya wuce cikin dakinta direct.

Yana bude kofar idanuwansa suka sauka akan fasasshen castle din nan daya rugaje akasa daganan ya soma fahimtar komi..

Da mugun gudu ya sauko kasa yana salati nan danan ya zari key din wata sport car na kamfanin camaro mai falfala uban gudu ya fice da ita yay hanyar lekki.

Koda ya isa kofar gidan zach da kyar mai gadinsa ya kulashi,..

Jin cewa airpot duka suka nufa yasaka shima yay nan acikin gaggawa.



6:30 am na safiya on the dot yay masu zach a farfajiyan fili safaran jiragen sama na murtala muhammad intnl airpot lagos.

Shi din mai kudin gaske ne dan haka baiya bin kowani irin jirgi saita haya,dan haka sashin su aka wuce dasu kai tsaye
Inda jirginsa zai tashi dashi around 6:45am shikadansa aciki.

Budurwan dayazo da ita tun daga london danta dan ragemai ciwon kewar halisa yasaka aka tsaya domin a sauketa Adaf wajen shiga asalin normal entrance wanda harya saka an kama mata first class flight dazata koma london din dashi around 7 am itama.

Motarsu na tsayawa awajen cak sai ga na halisa ya karaso.

Daga cikin motar kuwa banda kkrin shawo kan zach da nonowarta babu abunda budurwan nan takeyi, dan kuwa jiya ya bata mamaki bana wasa ba.

Atunaninta ya daukota ne danya kwana yana sex da ita amma sai taga duk hakan bai faru ba, yaxo gidansa da itane kawai dan baison ya kasance shikadai ne a gidansa dats full of halisa's true love and memories bare haryakaiga ya shiga wani hali na tunanin abunda yay mata a matsayin cin amana ko mugunta.

Suna sauka abakin kofar shiga ya dan jingina da motarsa yanaa mai sanarda ita cewa ya riga ya tura mata kudaden service dinta, wani Rungumar bazata budurwan ta sakar masa tanamai shishege masa
Tanamai ce mishi cikin kunne da sexy voice nata" Are u sure u dont want my company in dat plane?...miskillalan murmushin gamsuwa dakansa yay najin babu wata macen data isa ta rudar dashi. Ya turata ahankli hannunsu sarkafe da juna yace mata "no am fine"..Sosai budurwan taji wani iri, ganin tanata kallonshi yasaka yay murmushi tare da sauke mata karamin kiss agefen kuncinta. Ahankli yace go..i work with time.

Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi tace okay goodluck to you sir and thanks for the money

Baice komi ba harta ja luggage dinta ta bashi baya, yana dago idanuwansa sama karaf sukaci karo da ruwan kwayar idanun halisa dake da cikke da tsananin kishi data zubamai bata ko kiftawa.

Wani irin shocking yaji yabi jikinshi atake ya mamayeshi yanamai masa ziriya tun dagakan tsakar kansa har izuwa kafafunsa da suka tsaya cak agabanta basa iya ko motsawa.

Yanayinta dayagani yasaka jikinsa ya mugun mutuwa yanjin wani yarr ajikinshi na yanyameshi.

wani irin kallon juna sukeyi da tsumayi mai ragbarwar cikin yanayi mai ciwo da zafi marar fasaltuwa, thousands od words going tru deir minds at the same time,

jikin halisa na rawa sosai ganin yadda zach ya lumshe idanunsa ya kuma budesu, Duk sun juya atake sun dawo ruwan jaaa, ..ahankli ta ke kallonsa da idanuwanta da sukayi jaaaa din itama sosai wanda tsabar kuka har sun dan kumbura sun sauya mata kamanni, jin bazai iya tsayawa kallonta ahaka ba yasaka ya fixge nashi idanun acikin nata da karfi cikin sauke ajiyar zuciya da basarwa ya juya agaggauce ya nufi hanyar private entrance dinsa inda jirginsa ke jiran shi.

Securities dinsa sunkai su biyar take suka wani rufamai baya suna masi biyedashi, sai sauri yake yana tafiya yana duban agogonsa yana kallon time da ya rage masa wanda baifi nan da minti goma jirginsa ya tashi ba.

Da kyar halisa ta fixge kanta acikin ruwan kishi dayagama sasssare mata sassan gabobin jiki.

Binsu tahauyi cikin gaggawa godiyan Allah da babu hayaniyar mutane awajen duba da private area ne .

Sunanshi take kira tana tahowa da sauri sauri jin zuciyarta na bugawa da tsananin karfi kamr zai ballo waje.

Gabaki daya rauni ya gama nakasata, she cant even hold on anymore kuka takeyi ahakli kamar yar karamar yarinyar datake bibiyar mahaifyarta ayayin datake guje mata.

Zach...zach..wait...
Li..sten... Zach pls wait!!

Hakan take maimatawa da disashen muryanta mai tafe da kuka

Yanajinta amma hakan baisaka yaji aransa da ya dakata ba, itama bata fasa ba harta isko su daf securities dinsa ne suka juyo suka rirriketa.

Hakan yay mata ciwo bana wasa ba. Cikin birkicewa da kuka ta fara daka musu tsawa .
"Hey, What are doing
How dare u touch me, Get off me..dont touch me. Zachhhhhh..pleasse.
Ta karashe cikin kuka sosai.

Zuciyarsa kamar zai tsage haka yakejin ciwon kukan nata aransa, sede wani irin taurin zuciya yake dashi, iya tausayi da rauni halisa tasakamai ayanzu amma kuma...

Har ya kama handle na no go area zai shige ciki sai yaji gabaki daya ya kasa yin hakan.. dan yasan in ya shiga nan ya rabu da halisa kenan na har abada .

Juyowa yay ahankli yaganta acan tanata kuka tana kokowa da securities dinsa duk ta rikice tanason tanayi magana dashi.

Dawowa yasomayi ahankli batare dayasan yay hakan ba, halisa tana daga kai yay kamar zai koma ta kwala ihun sunansa cikin kuka tace "Zach, zach please dont go.. just listen to me...once .. this once. .
Nayi maka alkwri after this bazaka sake gani na a inda kake ba..

Lumshe idanuwansa yay tsam jin hakan daya diro masa abazata yakuma tsaga kahon zuciyarsa kamar wuka.

A tunaninsa halisa is here to beg him to come back to her...which yasan bazai taɓa yin haka ba.

Saide cewa datayi bayan yau bazata kara zuwa inda yake ba yasaka shi jin tsananin ciwo da kuma muguwar zumudin son jin meke tafe da ita..

Dedeta numfashinsa da nitsuwarsa yay snn yay hannu wa securiteis dinsa suka kyaleta.

Tsayuwar cak tay tanata sauke wasu irin tagwayen gajiyayun numfashi masu azaban nauyi.. yana tsammani yaga ta taho da gudu tazo ta zube akan kafarta agabansa dan yaji dadi gaya mata abunda ke ransa amma sai yaganta tana tsaye

Dedeta kanta tay snn ta hau share hawayenta saida ta share fuskarta tasssss ya zamo babu dison hawayen kafin ta sauke ajiyan zuciya cikin wata nitsuwar da bata san dashi ba ta tako ahankli har ta iso gabansa.

Kallon juna suka shigayi kirjinsu duka na bugawa da wani irin karfi.

Ta budi baki kenan zatay masa magana cikin dakatar da ita yace

...."5 minutes". Say what eva u want say and just leave.

Yanayin daya fadi hakan yay mata ciwo amma ta basar tana duban cikin idanunshi, fuskarta a dore sosai .."tace i have nothing to say to u coward; ure the one who have sumtin to tell me..
zach what is happening i dersve some xplanations.

Shiru yay nadan wasu lkci dan kuwa Zuciya da Karfin gwiwar dayagani a idanuwanta yasashi jin kansa na tafasa ta ciki da rauni da kuma tsoro.

Just 2mint ago she was weak and crying and shaking amma yanzu ynzu harta shanye duka hakan ta dawo masa tamkar wata dutse wanda bbu dandanin abunda yake girgizata.

Wani Tsawa ta dakamai a bazata wanda saida ya dawo dashi cikin hayyacinshi daga duniyar mamakin daya lula ciki

Nace Kafadamin abunda ka gayawa meenal da bakinka..tell me u never loved me..and i am not the woman you ever wnted to marry..kafada min yanzu, agabana, idan ba haka..........

Cikin katseta a karsashe yace Idan ba haka ba meye? What will u do girl? ...tace ohh, nothing! Except that u will never have this chance in ur life again and u will regret it.

Cike da zafin nama yace ya isa haka,..im not scared of anything.

Tace goood..then tell me

Hannunsa ya dungule da karfi snn Ya lumshe idanunsa sosai sai can snnn ya budesu tareda zubasu acikin nata, wani irin tausayinta yaji yafara magana acikin nitsuwa.

Yace Babu wani abu danaso araina dayafi minke halisa..u were perfect. .kuma Nayi tsammanin zan samu rayuwar danake buri atattare dakke,Sede hakan bazaiyu ba..
Rayuwarki na da can danawa ba iri daya bane.
Altho I am not scared to live with ur past..but what about my future???.
What about my familys reputations..my own reputations..

Cikin katseshi Adan daskare takoma baya murynta na rawa Tace ".....my past?..a...a ina kasan past dina...did u knw dat u dont own a right to my past..meya kawoshi cikin wann maganan..which past are you talking about...

Ta karashe maganan acikin rudani mai yawa hakan yay saurin sanar da shi cewa meenal batagaya mata gaskiya ba kenan.

Shikuwa Bai boye mata ba ya soma gaya mata tun daga yadda kawunta yake sakata karuwancin dole dan ta siyar musu da kayan tallarsu, kwana da ita da kawun yayi da cikin datay masa kuma ta zubar, da kazamin rayuwar datayi a lagos wanda tayisu dan ta samu na cin abinci wajen kwana da na biyan kudin makarnta.

"But it seems like shafin kazantar kawai akafi rero masa batare da ansanar dashi dalilanta na shiga cikin wann irin rayuwar ba..

Bai daukesa wani mintina biyar ba ya gama mata bayani game da abubuwan da meenal talba tafada mishi akanta batare daya ambato sunanta acikn bayanyin ba

A daskare take kallon bakinshi har ya kammala yay shiru jin wani irin girmammen mamaki na rifeta yana kuma tsilleta tsaffffff tun daga kan kafafuwarta, ji tay kamar a mafarkine zach ya bankado cafta cafta na littafin rayuwanta yana kuma yi yana rufa rufa baya son kama sunan kowa aciki.

Juyin duniyan nan tay dan ya gaya mata inda yaji wann labarin amma ce mata yake babu amfanin fada mata hakan kwata kwta..

Yace mata shi baida lkcin tsayawa yin wata doguwar magana da ita, kawai dai bazai iya auren ta bane ahaka..badon kansa ba saidan yaransa da familynsa da mutuncinsa.

Maganan nasa ya sosa mata ranta tare da mata ciwo bana wasa ba.

rufe idonta tay snn tace Zach saiyau na amince da cewa baka taɓa kaunata ba tunda dai qaddarata da ya wuce ne zai saka ka walakntani snn ka tozartani aranar aurenmu.

Yace halisa karkice min haka..i have my own life too. kuma nine nake da ikon tsara abunda ya dace da rayuwata

Tace kuma bakasan ban dace dakai bako sai aranan aurenmu? Ahankli cikin sauke ajiyar zuciya tace mishi " ..dats not fair..

Wani irin Shiru yay baice mata komi ba sai yanzu yakejin aransa kamar bai kyauta mata ba.

Kanta na kallon can kasa aftr some minute taja numfashi, ahankl ta dago kanta ta kalleshi wani ragwabben murmushi ta sakar masa daya raunata masa zuciya fiye da komi

Tana murmushin tace 'Okay,..its fine..lets say ur reason is validated. Zach i wish u all the best..ta sake sunkuyar dakanta tanajin zafi sosai, ta kuma dagowa tana murmushi snn tace in ur life..Good bye zach!!!

Tana fadin hakan ta juya a nitse zata barshi anan atsaye, harta fara tafiya da wani irin shauki mai tattare da rauni taji an fixgota baya.

Zach din ne ya fixgota jikinshi idanuwansa sun dada yin ja kamr zasu fidda wuta..Yace iya abunda zakice min kenan Halisa..all the best in my life?..murmushi tayi mai yawa snn tace what do you xpect? Kasa magana yay yanata kallon cikin kwayar idanunta dan a duk sanda namiji yaso rabuwa da mace yaga bata zautu tanason ta mutu akansa ba toh dolene wani abu daga ego nashi saiya raunatu.

Normally maza sukanyi tunanin cewa muddin suka samu wata babban gurbi na dasa soyayyarsu a zuciyar mace to koda zasu tozarta ta bazata taɓa iya rayuwa babu su ba.

Zach yasha tsananin mamakin karfin zuciya da irin calmness din dke tattare da halisa awann lkcin.. He tot mental maturity is for men not men. He was wrong!!! And He hate to be wrong!!!

Da karfi yace Halisa tambayar ki nakeyi.

Da karfi ta kwace kanta anashi tace i askd u too dama me kake tsammni

Yace really. Cikin katse shi tana murmushi tace
Tace yeah..kaine kace
Min rayuwarka yana da tsari kuma na fahimceka
Nima Nay maka fatan alheri. So, Now is left for me to go and find sumone who can love me truly including my past .

Ahankli ya wani irin lumshe idanuwansa jikinshi a mugun sanyaye sede kafin nan ya bude idon halisa hartayi nisa.

Yafi minti goma atsaye awajen kamar andasahi yanamai hangen bayanta da idonshi da sai aynzu suka soma zubar da ruwan hawaye sosai.

Ji yake kamar ya fice aguje yaje ya tarota amma ina bazai taba iya aikata hakan ba..
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe snn ya zaro glass dake aljihunsa gaban rigansa ya saka akan idanuwansa ya juya aggauace ya shiga jirgi.

Yana zama captain din ya fara shirin lula su sama saidai har iyanzu zach hawayen ciwon rabuwa da halisa yake saukewa sam sam kwakwalsa bai dawo masa daidai ba.


Halisa na ficewa a airpot din tun kan takaiga motar ta taji jikinta ya mata nauyi atake atake zazzabi mai zafi ya kuma rufeta.

Ta dora hannu akan murfin motan kenan taji jiri mai karfi ya kwasheta zatayi baya ta fadi kasa saiga uztaz ya karaso a gurguje yazo ya tareta..

He was right der yana hangen lokcin da halisa take tattaunawa da zach din sede shi baije kusa dasu ba ya jiratane ata waje

Tana sume suka iso asibitin aka kara bata gado, allura doc ahmed ya mata snn aka dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login