Showing 108001 words to 111000 words out of 171903 words

Chapter 37 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

1010

havent u tell me dat before sai yau
shin wann wacce irin hukuncin zalunci knn kika yanke mata ynxu Inkece mahaifiyarki take cikin wani hali zaki tsaya neman izinin wani kafin kikai mata dauki?

Cikin katsesa da jin haushin maganan tace A'a mahmud karda ka sake ka kawo mahaifyta acikin wann maganan, akan me, akan me zakana hada uwata da wata jahila kuma matsiyaciyar mata..Daga fadan gaskiya shine kawai zaka juyo da maganan akaina...Ai gara ma da ta tafin inba haka ba wallahy yau da sai tamin cikakken bayanin yaushe tacemin uwarta bata da lfiya na hanata banda sharri kaima ai bakasan komi akan maganan ba

Calmly Yace Kece dai bakisan asalin gaskiyar ba sabida ni kuwa naga gaskiyar da idanuna snn ni nace mata taje gida ta kulada jikin mahaifiyarta..

Tace "ohh munafurcin data hadamin awajenka kenan dan ka bata izini ta tafi Toh wallh ni bazan dauka ba..kaima karka sake min haka akan me? akan me zaka yanke wann hukunci batare da sanni na ba? Mahmud nine fa nasaka aka kawomin ita nan gidan tanamin aiki bakai ba dan haka bana son shishshigin nan da kakemin banaso mtsw.

Batare da ya kula masifar datakemai ba
Yace inhar mahaifyrta ta samu saukin jikin nata zata dawo ta cigaba da aikinta agidan nan..

A hatsale ta Wani irin watso mai harara tay tace 'what me kace?? Ta dawo ina,..dauke kansa yay bai kulata ba tace amma dai ba gidan nan ba ko..fuskarsa a dore yace agidan nan mana shemau,..wani irin dariya ta fashe masa dashi na rainin hankali, Hahahaha lallai ma mahmud ai tun da ta tafi ya kare mata kenan .wallh wallh munafukarnan bazata dawo min gidana ba.

Yace da kike ficewarki wajen kawayenki a yadda kika ga dama nataba tuhumarki ko na tsareki?

Shiru tay bata amsa shi ba ta dauke kanta cikin fushi ranta na tafasa dashi bana wasa ba.

Yace no no nunamin kike kina da full independece din kanki,..but this is my house shemau. So i will also decide who ever stays here kamar yadda u also decide for urself when ever u want to go out to ur frends

Tace Mahmud kenan, i knw sabida abunda ya faru jiya kake fadin hakan dan kawai ka neme ni ban baka hadinkai ba shiyasa kake neman ka gayamin magana akan mai aiki, toh ana dolene! ni sauri nakeyi, kuma harsaida na isa gidan hadizan kafin nan nake ganin sakonka.

Muryansa kasa kasa yace wann ai duk ya wuce tunda bayau aka afara ba. Batun yarinyar nan ne nace zata dawo bakin aikinta and dat is final....

Tace haba mahmud kai waye, wallh baka isa ka kawo min wacce banaso agidan nan ba..

Baice komi ba ya juya zai bar wajen ranta a bace ta sha gabansa tana huci tace "ina zakaje?

Yace zanje na gayawa mammy duk wani abunda ya faru inyaso sai kije gidanku kiyi mata cikakken bayani akan hana yarinya zuwa jikin mahafyrta da kikayi and also explain to her why bazata dawo bakin aikinta ba.

Shema'u dake kallon bakinsa shekeke taji kamar zata fashe masa da kuka jin ya ambace sunan mahaifyarta mammy datake mugun jin tsoro acikin maganan.

wani mahaukacin hatsalallen tsakine ya kufce a bakinta, muryanta a shake cikin dakamai tsawa tace Bakomi,do as u please nide bada yawon bakina zaka dawo da ita nan gidan ba,..mahmud nagaya maka bana sonta ana dolene da zakace zakaje ka hadanii da mamy?kace kawai Dama can kana da niyyar kai karana gidanmu kuma wallh zakasan wacce zatana kulawa da bukatunka agidan nan amma bani ba what nonsense....a mugun fusace ta bar wajen tanajan masa tsaki mai sauti sosai tana tfya tana rusa masifa

Yarinya ta tafi gidan ubanta amma Sai kace dole sai ta dawo..toh wallh babu ruwana aciki ko ta dawo sede tana maka aiki amma bamani ba tunda har makirci za'a kullamin.

Yana tsaye daga wajen har ta wuce room dinta ta dauko key din sabuwar motarsa data dauka jiya tazo ta jefa masa ajikinsa snn ta koma dakinta cikin fushi daga nan bata kara fitowa ba har ya shirya kansa tsaf ya fita da jin zafin irin rashin kunyar data masan aransa...

Daga nan wajen mahaifyarsa kawai ya nufa shikadansa yanamai tuka sabon motar tasa ahnkli.

Mahaifyar tasa sananniyar philantropist ce Wacce tay fice wajen aikin bada agaji da miƙa temakon gaggawa wa yara marasa galihu da marayu,gidan hajiya badiatu shagari na cikin anguwar victoria Island inda halisa mansa take da zama da akwai nisa sosai tsakanin anguwar nasu dan haka ya samu isashen lokacin yin nazari gameda abunda zai furta mata akan lamarin hafsat da mahaifyartan dan ta teimakesu ta kuma bashi shawara tunda yagama lura kamar shemau km bazata kula wann zancen ba.


Wajajen Karfe takwas da rabi saura Halisa ta bude idanunta ahnkli tanamai karewa dakin nata kallo.
Tunanin iyayenta data kwana dashi ta sake farkawa jin ko ina ajikinta kamar an mata duka.

Kwana biyun nan Da kyar take iya bacci, inta samu tay kuma dakyar take fixgar kanta daga baccin dan ko ta kwanta da wuri ne batajin kamar baccin na isarta sosai. Saukowa tay daga kan gadon ahnkli batare da jira ba ta zabge rigar baccin dake jikinta tare da warware suman kanta gabaki daya duka suka sauko mata akan kafadunta,
Farisol din towel ta daura a kirjinta snn ta shiga bathrum ta hada ruwan wanka mai dumi tare da lumewa ciki..


Ta kusa shafe minti 30 aciki snn ta fito dauke da handtowel ahannunta tanamai tsantsane suman kanta, towel din dake daure a kirjinta ta cire ta sauyashi da wata farar comfy bathrobe wanda atake yahau dumama mata jiki,.gaban vanity table ta isa ta zauna tare da jona handryer tafara drying suman kanta saida takai mintina ashirin masu kyau tana gyarashi da mayuka masu qamshi sann ta tattarashi in a soft bun tay light nude make up wanda inbawai ka kureta da idanun sosai ba bazaka gane tay kwaliya ba saidai ma kace natural beautynta kenan.

Bata wani jima agaban mirrorn ba aka fara knocking mata kofa, as usual ustz ne ya taho sanar da ita cewa lkcin karyawanta yay, batare da bata lkci ba ta sauko kasa daga ita sai robe din ta samu har ya jera mata her favourite cinnamon pancake da fresh mango juice da akayi shi da ginger da kuma low sugar. yana kammala serving inta ya koma daki ya ciro mata kayan da zata saka ya jera matashi kafin nan ya dawo ya samu tanacin abincin ahankli.

dake ita ba gwanar son zaki bane sai taji dadin abincin abakinta sosai bayan ta kammala taje room dinta ta dauki kayan daya ciro matan ta kalla cikin kyabe baki snn ta cire bathrobe din ta hau sakawa ajikinta

After few minutes ta sauko tana tafiya ahankli sanye da Marigold and dark brown colour maxi gown dinta from house of escada wanda shibai je mata har kasa ba snn bai kasance dan guntu ba. Dogayen heels ta saka masu aji na kamfanin mahnolo blank kalarsa kalar marigold din dake jikin kayan inda Sulɓabbun kafafunta dasuke nan chocolate masu sheqi suke murza taku bisa floor din ahnkli.

Satar kallon ta uztaz yakeyi ganin kalar dark brown weave cap din ta saka dayay marching sosai da kalar kayan nata, suna hade ido tay masa wata sassanyar murmushi tare da dora wata farar gilashi dats very classy a idanunta wanda daga ganinsa kasan bana yara bane jikinsa dauke yake da tambarin kamfanin Rayban snn bakaramin kyau yayi mata ba.

Qamshin turarenta na zebra rasasi data hadashi da latttafa oil ya haukata wajen da wani irin dadaddar qamshi mai asalin shiga jiki tare da tsaga hanyoyin jini dake isar da saƙo har cikin madigar kwakwalwa.

Shikansa uztaz din kkrin dauke kansa yakeyi with all his calmness dan babu wani abunata da bazai iya burge idanun kowani irin lfiyayyen namiji ba.

Ita kuwa a Lokuta da dama kallon dan uwan jini kawai take ma uztaz bana mai aikin gida ba shiyasa sam bata saka komi aranta insuna tare.

Jakarta ya amsa tare da wayoyinta ya rike mata
Cikin dedeta nitsuwarsa yana dan murmushi yace shall we? Ahankli tace masa yes..kofar ya bude mata tana fita ya kashe wutar gidan tare da kulle kofar da keys, kafin ya dawo yazo ya samu harta bude mota ta shiga tana jirarsa aciki.

baiyi wata wata ba ya aje dukwani tarkacenta agefe snn yajasu a Lexus jeep dinta mai tsada kalarsa dark maroon wanda dashi suka bar harabar gidan izuwa nisa premier hosptal dake anguwar lekki.

Ahnkli ta umarcesa daya tukata bada sauri ba.
Dan she dont want to be early kuma bata son tajeta very late ayadda take daukar kanta da eminence she knws she have to maintain her class and value.

Tasan ire iren private consultations irin haka yana farawa ne daga yadda ka dauki kanka agaban doctor dinka. dan haka ta umarce uztaz daya tafi dasu ahankli dan ta samu daman yin nazari akan iya abunda yakamata ta furta musu a fili game da rayuwarta.

Cikin kankanin lkci takammala wann lissafin

Bata wani fiye son wakoki ba amma dake wayoyinta kaf na gaba tare dashi yasata soma maida hanklinta akan wakar daya kunna mata na jericho by iniko.

Baitukar cikin wakar ta dinga nazarta jin yadda rayuwa yake tafiya mata kamar an rero wakar ne domin ita, har suka kai ixuwa bakin asibitin bata ma lura ba, har saida ya kashe motar ta dawo hayyacinta tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya.


Daga cikin asibitin kuwa tun wajajen karfe bakwai na safe Dr khalid ya taho yake zaune akan chair na offce dinsa yana karasa yan shirye shiryen da zaiyi.

Tun dazu daya zauna babu abunda yakeyi sai nazarin assessment na trauma din dake damun halisa wanda dr ahmed jimada ya riga yay report akai ya aje musu domin suyi amfani dashi a matakin treatment din halisa na farko.

Duk wani labarin abunda ya jawo halisa ta shiga wann halin ya karanta a file din kuma ya fahimce su sosai, altho yay bincike akanta tun bayau ba kuma ya gane cewa depression din tun tana karama ta taso dashi, a game da batun rugujewar aurnta kuma yaji labarin komi daya faru iya sunan saurayin nata ne haryau bai sani ba.

Allah Allah yake halisa ta iso asibitin ya soma jin labarin daga bakinta kafin nan ya santa inda zai shige mata..

Dan Yasha cin karo da Ire iren yan mata irinta masu kudi saidai basu da wani karfin zuciya da basirar yin doguwar tunani musmmn idan suka shiga wani hali.

barazana da wahalhalun dake tafe da rayuwarsu yasaka suke zamowa raunatattu masu neman dauki da sauki kusan kullum a matse suke wajen neman sauki ma ransu wanda hakan yake sawa suke bada kansu wa maza cikin sauki batare da sunyi doguwar nazari ba.


Tun asubahi ya tashi ya hau shiryawa ya kmtsa kansa suman kansa yasha gyara yana baza kyalli
yau din bakaramin kyau yay ba dan tamkar wanda zaije ya ga budurwarsa dasuka jima basu hadu ba ya sako wata hadaddiyar black suit na kamfanin gucii wanda bazaka iya krga yawan turare masu tayar da mutsamutsan sha'awar mace daya fesa masa ba.

A tunaninsa kwakwalwar mata duk layi daya suke aiki gani yake kamar halisa a tafin hannunsa take zuwa da wuri dayay yay tsammanin zatazo ne akan lkci, sede rashin ganinta alkcin dayy tsammani shiyahau bashi impression na cewa hala sai ya dage kafin yayi duk yadda yakaga dama da ita sanin cewa da yuwar cewa bazata dauki duk wani abunda ya zantar mata out of deprecy ba.


As usual uztaz yana buɗe mata kofar motar saida ta dau mintina kamar biyar aciki sann ta sauke kafafunta kasa suka taɓa kasa, ahankli ta sauke ajiyan zuciya ajere harsau uku sann ta miƙamai hannunta ya tallafota bisa kan kafarta tadan tsaya cikin dedeta nitsuwarta dayake neman kufce mata

Dan a Duk sanda ta fuskance inda taron jama'a suke sai taji hanklinta yay mummunn tashi....gani take kamar haryau kallon "the dumped bride" ake mata kamar yadda wasu mutanen suke tagging dinta dashi akafafen sada zumunta.

Kwana biyu har misali taga ake kafawa da ita indirectly a wasu reality shows din musammn ma wanda ya dangance hira akan relationshp na cin amana da yaudara.

Dan wasu cewa suke dolene yakasance da akwai babban dalilin dayasaka zach yay ma halisa haka aranar auren su saidai majorityn mutane gani suke kamr lefinna halisa ne sabida ita macece kuma sananniya ce acikin duniyarmu, wanda ya zamto muddin mace tayi wani abuna abun alfahari ko tayi kudi kusan kowani mahuluki zai ambaceta da sunan watsatsiya ko tantiriya.

Our societies belive that women cannot make it witou a man, shiyasa duk sanda mace ta jajirce tay abun kanta ko tay kudi n kanta toh dolene taci karo da kulabalai masu girma da nauyi.


Tun bayan faruwar rugujewar auren halisa babu wanda ya damu dayasan lefin zach aciki saidai na halisar, wanda shiyasa akafi saka ma duk wani motsinta ido tare da kahon zuƙa haryau mutane basuki suji cikakken bayanin lamarin daga bakinta ba


Tunda ta sauko kasa gabanta yake ta faduwa ganin yadda dedekun mutanen dake wajen suka soma nunata da baki.

Uztaz ne ya matso daf da ita riƙe da jakarta ganin duk ta razana da idanun dake bibiyrta,...cikin kara mata karfin giwa yace maam muje ciki,rmber is my job to protect u, ahnkli ta daga ido ta kallesa yace mata ure brave and Am here for you.

Gyadamai kai tay kafin nan ta amshi jakar ta zaro karar taɓarta ta kunnashi da ligher ta zuƙa kadan sann ta dada toshewa da spec dinta ta fara tafiya ahankli yana tafe daf da ita..

Tafiya take gabanta na faduwa amma dake tabar datake zuƙar yana distracting mind dinta sai ya zamto bazaka fahimce cewa a razane da idanun jama'a take ba.

Har can sama uztaz ya kaita daf bakin kofar office din Dr khalid ta amshi jakarta ahannnsa shikuma ya karbe tabar dake bakin nata ya rike mata, tana kallonsa yana nemi waje ya zauna daf da bakin kofa akan wani waiting chair alaman yana jiranta tagama ta fito.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin nan tay kncking after Like 3 mints aka bata izinin shigowa, ahnkli ta bude kofar inda qamshin turaren nata yafara bugar ramin hancinshi.

Suna haɗe ido ya miƙe a zumbur kamar yaga fatalwa snn ya fara jefo mata murmushi.

Tun bata zauna ba cikin sanyin murya tana kallonsa daga can tacemai "Hello doctor!!!!
Can i come in???

Cike da i ii na ayanayinsa
Yace H..h..hi miss halisa,
..Please come in nd have a seat.

Batare da tay masa musu ba ta karaso ciki a nitse, sai kallonta yakeyi kamar zai hadiyeta, harta ta nemi waje ta zauna tana fuskarnsa bai dawo hayyacinsa ba.

At this point sosai gabanta yake faduwa ganin irin rudewar da dr khalid yay, da alaman bai san ya ruden ba dan Gabaki daya idanunsa naga kan kyakkwan fuskarta izuwa kan kirjinta ne duk tabi ta rasa menene yake kallo.

Tana sauke gyaran murya shima ya jawo kujeransa ya zauna tare da dasa mata shanyayyun mayaudaran idanunsa a nata.

Ganin yanata jefo mata friendly smiles itakuwa fuskarta kamar ba asake yake ba yasaka yadan kame tare da Maƙe muryansa salon rigima da shan qamshi,yace ure welcome once again.
Ammm Allow me to formally introduce myself.,i am doctor khalidi bankole the only senior therapist in this hospital. So ina fatan zaki bani cikakken hadin kai domin mu shawo kan matsalar nan taki...

Bayabo ba fallasa halisa tace "its okay. We can proceed doctor!

Bude file dinta yay kamar abun arziki after few minutes ya dago kai yana dubanta..

Ahnkli yace mata please relax ki sake jikinki, kiyi imagining cewa bada mutum kike magana ba da robot ne. This will hepl u achieve some sense of security, sai ya dada duba files din yace miss halisa ure famous, u were a model and u own big companies kinga kenan ur story is definatly a news to the media. Amma inaso kisani cewa ni khalid ina tare da ke,we wll fight this together at the end of the session Zakiga inda komi zai zo miki acikin sauki..

Halisa batacemai uffan ba ta gyada masa kai like ders nothing new about his statement.

After assesing tru her files Next level na jinyar shine education and cognitive behavioural model.

Ya rike wasu file ahannunsa snn ya kalleta yana murmushi mai sanyi yace zan iya maki wasu yan tambayoyi????

Nervously Tace yes sure
Dan wann fannin ne yake dan saka mata fargaba.

Jacket din rigarsa ya cire tare da ratayawa ajikin cliff snn ya mike tsye da file din a hannunsa yace walk with me please.

Mikewa tay acikin nitsuwa snn ta jera tare da shi suka nufi wani corridor dagata cikin office din wanda upstairs ne daga jin shirun da wajen ya dauka kasan babu kowa aciki peaceful environment ne wanda yake basu damar suyi magana da client dinsu acikin nitsuwa da sirri.

Suna tafiya ya fara mata Bayani gameda cognitive behavioural model din shikansa, ayayinda yake fahimtar da ita cewa sunayin hakan ne sabida a gano ire iren tunannika da suke jefata ga shigewa cikin wani mummunan hali na damuwa wanda bata san yana faruwa da ita ba.

Lallausar kujeru ne ash colour guda uku da wall decors bakake masu kyau sai center table da fridge acikin dakin da wasu jajayen flowers masu daukar idanu.

Daya daga cikin kujerun ya umarceta ta zauna kafin nan ya dauko wine botle da glasses ya zuba musu kada kadan snn ya jerasu akan table din.

Tambayar daya fara mata shiyasa tadago kai ahnkli ta kallesa jin yace mata me take fara tunawa kafin tay bacci da bayan ta farka a bacci.

Shiru tay na dan wasu lokuta cikin nazari dan ita kanta bata taɓa tsayawa tay duba da hakan ba sede tabbas tana sane dacewa a duk sanda zatayi bacci iyayenta kawai take tunowa haka zalika inta farka sune take tunowa wanda hakanne yake cusawa zuciyarta rauni bana wasa ba....

Ta kallesa muryanta ba yabo ba fallasa tace mishi bana tuna kowa awayann lokutan face iyayena...

Yi Yay kamar baisan kan labarin rayuwarta ba curiosly yace Why dont u call or go and see them.

Wani irin nauyi taji ya dira mata akan Kirjinta ahnkli ta shanyeshi sann tace

"They died when i was 7!

yaudararren numfashi yaja tareda yin wani lambar cikin son nuna mata yana tare da ita a sigar tausayawa snn yace..ohhh i am sorry abt that!

Tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login