Showing 54001 words to 57000 words out of 171903 words

Chapter 19 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

998

ta dauka tana jan tsaki,a walkance tace and who is this? Why have u called me kasame halisan ne?

Sai ya rasa me zaice kawai ya mikawa halisa wayar tana murmushi tace hello meenal
Nice fa nake kiranki.

Jin muryan halisa yasa ta mike tsaye ta sake muryanta tanamai cewa oh my god halsy...Wher have u been...i mean wher are u, "are u okay?...cikin yanayin nuna damuwa da ita ta fada.

Halisa tace dont worry am fine...am on my way, kina inane nazo na sameki naji ance kunzo gidana keda shema ko?

Tace eh..kizo office kawai ina nan zan jiraki..

Halisa tace okay snn ta katse wayar ta mikawa uztaz tare da umartan sa akan yakaita talba grop of companies.

Daga ta dayan bangaren kuwa cikin wani private hospital fadilace tazauna akan kujera kirjinta na bugawa sosai tana jiran likita ya fito ya gaya mata sakamakon gwaje gwajen dataje tay dan ta tabbatar da lafiyar kanta kafin ta tsunduma cikin sabuwar rayuwar data zabar makanta nan gaba

Dan tunda tay tunani me zurfi akan maganganun da halisa ta gaya mata snn likita ya fahimtar da ita komi ta gane cewa bata bukatar meenal a rayuwarta.

Yankewa tay akan is better ta bar aikin ta neme wata rayuwar awani waje inyaso daga baya zataje ta nemi mahaifyarta yafiya.

An riga an mata jinyar vagina dinta da hjy zee ta coccokala mata shi da fartsu,amma duk da haka saida tay wasu yan kwaje kwaje sabida tsorata da bayanin da likita ya mata akan cuttutukar da ake kamuwa dasu ta hanyar saduwa barkate batare da kwaroron rubber ba.

Izuwa yanzun dai tasan ta kwana da important client dinsu sunfi su 30 dats wanda sukayi asalin sex da ita,wanda suke jin tsoron ciwo suka sata ta shassha musu gabansu kam ma bazata iya kirgasu ba,lesbianism kuma first time dinta kenan da hjy zee.

Yaune likitan yace mata ta dawo dan jiya ya riga ya kirata a sabon layinta ya mata nasiha mai shiga jiki akan qarban qaddara da hakuri da halin rayuwa.

Zuciyarta kamar zai fashe take zauna harji take kamar numfashinta yana raguwa ta ciki tsabar fargaban abunda zatazo tagani a takardan sakamakon gwajin dan duk wata cuta dat is sexually related saida aka mata gwajinshi.

After like 10 min likita ya aika aka kirawota ta shigo cikin office ya nuna mata waje ta zauna tana kallonshi.

Calmy shima yake kallonta har saida yaga ta dan nitsu snn ya soma mata nasiha yanamai bata hakuri har saida kalamansa yasata fara hawaye sosai. Ji take Kanta ya mugun daurewa kanta na bugawa sosai amma dai ta daure ganin ya ciro takardan kwajin yana kallo..

Girgiza kansa yayi ahankli snn ya mika mata sakamakon hannunta na rawa ta karba, takai minti uku cikin tsoro jikinta na rawa rawa ta bude takardan ahankli tafara karantawa da dan karfi.

Acikin cutuka biyar manya manya da ake kamuwa dasu ta hanyar jiima'i kwata kwata guda biyune kacal babu ajikinta..

wanda take dasu din ta kafe da idanunta dake fidda ruwa sosai yana sauka akan takardan tuni har ya jikashi.

babban abunda ya fi tada mata hankli shine dataga wai ta kamu da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV.

Sam fadila Batasan sadda takardan ya sulale a hannunta ya fadi kasa ji tayi ta kasa daurewa ta dora hannunta akanta tay wani irin ihu mai tattare da birkitaccen kuka akasa ta fado rigijib cikin rikicewar tunani duk ta rasa inda zata saka kanta nan danan likitar ya sauko ya dauketa aka kaita counselling room shida dayan colleaque dinsa macen sunata danne ta suna bata baki....THIS IS A LONG PAGE 14 readmores, so I HOPE IS ENUF FOR u guys, SAI MUN SAKE HADUWA AND PLEASE AMIN SHARING AGROPS

_08060712446_
*SURAYYAHMS*
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
Hp palace

⏯️1️⃣2️⃣


Daga cikin private room na HIV counselling unit Wani irin kuka mai karfi fadila takeyi tamkar zata cire ranta doctocin biyu duka sun taru akanta suna rirriketa jikinta yay wani irin zafi sai jujjuya kanta gefe takeyi cikin rikicewar tunani tabi ta runtse idanunta gam gam dasuke fidda dumbin ruwan hawaye masu zafi tay tsamm da jiki jin Wai yau itace take dauke da cutar kanjamau? hakan datake nanatawa aranta yasata saki wani irin kakkarfan numfashi mai tattrre da firgici tabita dora hannu akai idonta a rufe cikin rudani tanamai cewa wayyo Allah na nashiga uku wayyo Kun cuceni kun cuceni Allah ya isa wayyo Allah na shiga uku.

Bakaramin tausayi tabawa likitocin ba ganin irin firgicewa da rudewar datayi tanata kuka.

Doctor sai Cewa yake malama Fadila kidena cewa kin shiga uku pls kiyi Addua ki furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun kidena cewa kin shiga uku babu kyau.

Bama jinshi take ba tana cikin yanayin firgici daya gama nakasata aranta tana jin ina ma ace mata mummuman mafarki takeyi ba agaske ba.

Izuwa yanzu takai k'ololuwa wjn tashin hankali da firgici, bacin kakkarwa bbu abinda jikinta keyi. Da kyar suka lallameta tay dan shiru, snn dayan docton tahau mata bayanin yadda za'a mata wasu kwaje kwajen co-infections kamar su tuberculosis da wasu kananan infections kmr su oral cancers snn a soma dorata akan maganin HIV na ARV
(Anti retro-viral Drugs).

Bisaga kwajin da aka mata Viral load dinta ya nuna cewa Da alama cutar ya dan jima ajikinta kimanin tsakanin wata 8 ko shekara daya ganewa ne kawai ba ayi da wuri ba.

A kasa kan bare floor Fadila ta zauna dabas kamar wacce ta samu tabin kwakwalwa sai hawaye dake sauko mata yuuu sam yaki daukewa, har iyanzu jin kanta take kamar a mafarki tana ta Allah Allah ta bude idanunta ace mata kawai mafarki take amma ina da alama qaddara ya riga ya riga fata.

Sunci kusan mintina sha biyar ahaka suna famar tausasar zuciyarta tare da bata karfin gwiwar amsar rayuwarta ahaka kafin nan da kyar fadila ta iya miƙewa tsaye, tace musu ta gode snn ta kama hanya ta fice a office din tanatafiya ahankli sosai kmr wacce ruwa ya kwasota tana share hawayenta da hannunta dan yadda kasan mutuwa aka mata haka yanayinta ya dawo.

Ita kanta Batasan yadda akayi ta isa bakin motar ta ba tsabar batacikin hayyacinta kafafuwanta taji suna rawa dakansu ta dafe jikin motar ta tsaya gabobin jikinta a mugun ragwabe, saida tay tsayuwar mintina biyu masu kyau tana sauke ajiyan zuciya kafin nan ta bude motar ahankli hannunta na rawa ta shiga ta zauna aciki cikin yanayin jimami.

Rife motar tay kriff snn ta kunna Ac takai shi can koluluwar karshe sanyi ya shiga busota duk dama batajin wani sassauci ajikinta, Kuka mai karfine ya sake kufce mata ta haɗa kanta kirif da steering motar tanayin kuka a zafafe jin kamar jijijiyoyin zuciyarta zasu tsinke a lkci guda.

Tsananin Duhun Baqin ciki tare da radadin ciwon da zucyarta yake mata yasaka ta rasa waye ma zata fara dorawa lefin wannn abun??? Shin Meenal talba ce ,ko ko mahaifiyarta ko ita kanta datayi wa meenal din makahuwar biyayya akan saɓon Allah daya jawo mata wann musibar da bazai taɓa rabuwa da rayuwarta ba.

This enuf, is a lifelong mental trauma..Hiv fa, Hiv?hiv of all sicknesses, shin Dukkan wayann tantiran karuwan da sauran mutane da sukeyin karuwanci da son ransu basu kamu da cutar kanjamau ba sai ita da ake tursasata takeyin shi na dole kuma ma bakoyaushe ba? Cewa take ita Metayi wa Allah ..Da karfi taja wani kakkarfan numfashi hummmmm tanajin tsananin zafi na tsaga mata zuciyarta sosai.

Wann wata iriyar musiba ce take bbiyar rayuwrsu, shin mutuwar da mahaifinta yay a yayinda yake aikata zina da matar makwbcinsu bai isheta abun kunya a fuskar duniya ba sai kuma ace gata da cutar kanjamau?...ta kara fashewa da kukan sosai tana cewa na shiga uku...na lalace wayyo Allahna pls How is dis fair to me...? Ita Dama can ba wani ilimin Addinin tay ba iyakacinta na sallahne dan ko datazo birni hajy nadia bata kula ta sakata a wani islamiya ba ilimi kawai aka bata na iya handling business sabida ta rika bautawa yarta meenal har iyakar karshen rayuwarta,.

Fadila sam bata gama sanin waye Allah ba bare ta gane babin karban qaddara mai kyau ko mara kyau bare har kuma taayi imani dashi,wanda hakan yasata ta fara tunanin hala Allah baiyima rayuwarta hukunci bisa adalci bane ayau da ya jarrabeta da wann cutar.

she was soo angry and furious da qaddarar da Allah ya dora mata tanajin kamar ta kashe kanta ta rabu da duniyan nan me gabaki daya..

Kukan fitan rai take tana ganin lallai Ubangijinta baya sonta,iyayenta da meenal kuma sun tsaneta gaba daya sun zalunce rayuwarta da suka sakata ta kamu da wann kazantacen cutar mai cike da kalubale na tsangwama da zubewar mutunci aciki.

Tasan inba dan son kudi irinna mahaifyrta ba da bazama ta san meenal ba bare hartakai wann matsayin datake ciki ayanzu.

Wani zuciyace ta debeta ta fixge motar a 360 tabar harabar asibitin aguje tahau kan titi tana tukin tanata kuka at same time kwakwalta na buga mata lissafin inda zata soma juye fushin dake kwarara asaman zucyarta..

Direct hanyar talba grop of companies ta nufa zuciyarta na tafasa dan harga Allah bata san mema zataje ta gayawa meenal din ba amma aynxu tafijin tsanarta fiye da komi arayuwarta.

Ta shararo tafiya kenan tana daf ta iso motarta ya fara alarming yanamai nuna mata cewa man ta ya kusa ya dauke, a dan dole yasata tay slow down ta lallaba motar ahankli har takai wani gidan mai da baifi minti 10 ba ne nisan su da kamfanin Amina talba ba.

Ahankli ta share hawayenta tana jan tsaki ranta yay baqi matuka da tsayuwar datayi dan Allah Allah take taganta agaban meenal talba ayanxu.

bude motar tayi ta sauko jikinta na rawa rawa ganin akwai layi dolene sai taja jira wayanda suke shan man agabanta.

Rufe motar tay ta dauki wayarta ta koma can gefe inda babu mutane kwata kwata, nan ta soma kirar layin mahaifiryata danma kartaje tay wani abunda zatayi dan danasanin da zaizo ya shafa harda tsakaninsu na har abada.

Hannunta na rawa ta rike wayar har saida ya soma ringing snn ta dora akan kunnenta tana daurawa kuwa batama san sanda aka dauki kirar ba sautin gundumammen muryan mahaifyarta tana mai kwararo mata ashariya daga can ne ya fargan da ita.

Bakinta na rawa tace salam Alaikum umma

Bata amsa ba tace "Shegiya Marar kunyar yarinya yar kutumar uba tsinanniya wanda bata gaji qashin arziki ba saina tsiya,..

wani irin runtse ido fadila tay jin zuciyarta na tafarfasa a kunnenta ta kuma jin,.."Dan durun uwarki gidan wani dan iskan kikaje da har kika saka hajiya nadiya ta dagamin hankli tana kirana tana cimin mutunci akan yarta hajya amina tace mata kin gudu kinbarmata aiki kwana biyu basu ganki a offis ba?nan ma bata barta ta amsa ba cikin azalzalan masifa tace...Wato fadila kin gwammaci kibi kafarki dan iskan ubanki kije dakin saurayi kuta iskancinku akan daki zauna kiyi aiki ki samo halak dinki ko? Wato cin gindi yafi miki aikin da zai ciyar dani da shegun yan uwanki da ubanki ya mutu ya barni dasu ko?kedai fadila bakida imani zuciyarki abakance take kamar na fir'auna.
shashasha kawai haihuwar asara yar iska,
..tou wallh baki isa ki tozartani kamar yadda ubanki ya tozarni ba...
"karyanki matsiyaciya,
Dama shiri nake zanzo har legas din naci kutumar ubanki keda matsiyacin saurayin naki shegiya kawai lalatacciya. Yanxun Uban me kika kira zaki gayamin marar kunya???.

Azuciye cikin rikicewa fadila tace Amma umma wann fa ba adalci bane ko amsa sallamata bakiyi zaki soma duramin irin wnn ashariya ni menayi? ni menayi? Bata san sanda kuka mai cin rai ya kufce mata ba.

Cikin bushe ido da fushi Umma lauratu Tace "An dura miki ashariya, nace kinci kutumar ubanki in kin isa ki tuntsireni da mari daga can insan kin botsare.

Fadila taja numfashi mai zafi kamar ranta zai fice ajikinta muryanta na rawa cikin hatsalallen kuka mai tattare da gajiya da fushi tace

Umma Koma me zan gaya maki ayanzu bazai yi tasiri a zuciyarki ba sabida tunda can ma kudi yafi miki ni, kin sayar dani wa mutanen da basu san darajar dan adam ba,snn kin goya musu baya suna yanke dukkan wata kazamar hukunci akan rayuwata.

Umma anan na kiraki sau bila adadin inamai gaya maki cewa suna sakani karuwanci amma kikace min gadon ubana ne in banyi ba a ina zaki same abincin da zaki bawa yan uwana..ko sau daya baki taba damuwa da illar abunda kike sakani ba..

Muryanta harna shasshakewa cikin kuka tace Toh gashi, ga..sh shi...tafashe da kuka sosai daya saka kirjin umma laure ya buga da karfi.

A tsawace cikin fargaba umma laure tace toh Gashi me?ke Da Allah jahila ki fadi karyan dake tafe dake kawai ai bazai wuce kicemin kinyi cikin shege ba Mtchewwww taja wani mahaukacin tsaki daya saka fadilan kara ragwabewa cikin kuka.

Da kyar ta tattaro kanta cikin dagon murya tace tou ba cikin shege bane umma asibiti naje ba gidan saurayi ba, yanzu haka likita yace cutar kanjamau ne ajikina.

Wani rambatsau Umma laure taji saukar maganan da wani irin sauri tace cutar kanjamau ajikinki fadila?

Fadila na kuka ta gyada kai.. jin umma laure tay wani irim shiru bayan wasu dakikai batace mata uffan ba.

Sai can cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya snn tace "toh ai wann qaddararki ce tunda ba wani dan uban ya saka maki ba..kece kika jajibo makanki. Ynxu da kike gayamin ni wata uwar zan miki? Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun amma fadila kin cuceni
Yanxu hajya taji wann maganar zata kuma amincewa kimata aiki ne? A ina kenan zamunq samun rufin asiri

Baki bude cikin daukewar kukan da yy cak a karsashe Fadila tace umma ashe bama tani kikeba tunanin kudi da wayanda suka jefani acikin halin dana nake ciki kikeyi???

Umma zatayi magana cikin tsareta tace
...umma mena taɓa maki a rayuwa da kika hade kai dasu kuka lalata min rayuwata..

Acikin sauri Tace daka min fadila kirufe min shaddar bakinki awajen. Ni ban lalata miki rayuwarki ba, harka ce ta ceto ranmu daga mutuwa, kuma kece babba yau inbaki fita duniya kin nemo kin bamu ba uban waye zai na bamu na sakawa abaki?ubanki bai barmu da gadon komi ba sai tsangwama da kyamata daga mutanen gari, Indan na ubankin zanbi aida yanzu haka dukkan mu gawawaki ne. Qaddararki ce ta zo miki ahaka, ni ban lalata maki rayuwarki ba.

Runtse idon fadila tay tanajin kamar zata yanke jiki ta fadi kasa tsabar jiri
Da rikicewar tunani.

A tunaninta kowacce uwa dolene zata girgiza intaji yarta acikin wann hali amma da alama nata uwar kam bata da daukeshi awani abu ba tukuna.

Maganganun halisan ne suka kuma dawowa mata, ahankli tana bude lumsashun idonta tace
Naji qaddarata ce kaka umma,amma ki sani bazan kara yin aiki a karkashin wayann mutanen ba inke baki damu da rayuwata ba ni bazan zauna in mutu ahaka ba kuma Allah saiya sakamin akan dukkan wanda suke da hannu akaina.


shewar umma laure ne ya katseta tana cewa lallai yaro yarone, yo ke fadila har wani rayuwa kike dashi na azo agani?
Dik inda zaki je a duniya tijarar da ubanki yay ma kadai ya isheki wallh.

Fadila tace Abunda baba ya aikata daban rayuwata daban ai Allah ma bazai kama ni da lefinsa ba.

Umma ta kuma yin dariya tace "gaskiyane Allah bazai kamaki da lefinsa ba shine zaije ya amsa laifukansa dakansa. Amma ki sani ZINA fa bashi ce. Duk sanda kayi sai anyi akan naka.. A irin halin mahaifinkun nan ai ku kadai bazaku iya biya masa bashinsa ba har jikokun sa sai sun biya wallhi. Ko ce miki akayi shidin ma bai rabawa ya'yan mutane cutar kanjamau dinbane?

Gaban fadila yay mummunan faduwa

umma laura tana dariya tace Heeheha ohh lallai, aini gata na miki fadila da bana zama in bude miki cikakken tarihin mahaifinki sabida tsabar kazantar dake cikinsa halama da ana gaya miki da tuni kin hadiye ranki kin mutu. Ke bari kiji ma, dalilin daya saka kika girma kikaga bana kwana dashi daki daya kenan tsawon lkcin nan,tun danayi cikinki ya gujeni yaje yana kwana da karuwai abayan gari, wallh bai dawo kauyen nan ba saida kudinshi ya kare ya dawo aikin gona ko wata daya baiyi ba wata yarinya yar shekara sha uku taje aika ajeji ya danneta yay mata fyade a gonar shinkafarsa,mai gari ya saka aka kamashi aka daure shi tun ina da cikinki harna haifeki ba afito dashi ba, to ajikin yar yarinyar nan aka san da cewa ubanki yana dauke da cutar kanjamau iyayen yarinya suka bar garin nan suna masu baqin ciki tare da tsine ma zuriarsa tun bai haifeku ba.

Har yau maganan daa uban yarinyar ya fada mini ya tsayamin araina fadila." Cike da kunci da baqinciki da ubanki ya qumsa masa ya dubeni da cikinki Yace min In sha Allahu duk wani abunda zan haifa sai Allah ya jarrabe abun da irin Jarabtar da ubanki ya dorawa yar yarsa. Kuma har sukabar garin nan basu yafe masa ba.

Tun alkcin nima na raba hanyana dashi amma kinga da me gari ya rasu ya samu ya fito daga gidan yari wallh bashine ya hanasa cigaba da yaɗa cutar nan wa matan da basusan yana dashi ba. Yanzu haka rabi daga cikin kannenki suna dauke dashi sabida uwayensu dayayi ciki dasu awaje basu san yana dauke da cutar ba.

Danko na yi shelarsa agari ba jina akeyi ba ana zaton zafin kishine yasaka nake cewa mijina yana da kanjamau sabida duk matar da suke biye masa suyi iskancin tare yana basu kudi sosai. Yo ke waye da zaki tuhume wasu akan dan kin kamu da cutar da ubanki ya riga ya rabawa mata sunfi akirga anan kauyen?

Ni aganina wanm lamarin qaddarare ne saiya sameki, ke kadaice yata a duniya dan haka ki nitsu kije kibawa su hajya hakuri kicigaba da zuwa wajen aikinki bama sai sun ji cewa kina dauke da cutar ba bare su koreki inyaso idan kikaga dama saiki dauki fansarki akan wanda suka saka maki ciwon in kuma kin hakura shikenan ohon miki dai.

Nide damuwata shine ki samu ki basu hakuri kina turo mana kudi dan kinsan dake kawai muka dogara anan kauyen babu mai tausayin mu bare hulda damu, ki aje maganan kanjamau agefe kawai kiyi abunda zai ficceki.

Cikin rasa na cewa Fadila
Ta katse wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login