Showing 90001 words to 93000 words out of 171903 words

Chapter 31 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

777

tsamo daga ruwan randa, kusan a rude tabi ta kame jikinta sosai jin sanyin kankaran na ratsa mata gangan jikinta bana wasa ba.

Magana take son yi amma zazzabin sosai yaci karfinta tana budar baki hawayene suka dinga saukowa daga idanuwanta kamar ruwa

Acikin dauriyar da batasan daga ina ya tason mata ba tace Hajiya Dan darajar iyayenki ki dan bani kudin aikina naje na duba umma na a kauye wallhi batada lafiya sosai.

Babu imani ko tausayi shemau ta watsa mata mari saida ta kifar da ita.

"In baki kudi kin bani ajiyarsu ce? Ko nice na daurawa uwar taki ciwon datake fama dashi .ai ciwon kenan bazai wuci na talauci da kwadayin abun duniya ba. Wato na baki kudina a baqas kije ki kaimata kuyi danashar ku dashi nikuma kibarno da aikina a gidana ko?
Wallh tallahi inkinga na baki kudi to lokcin biyan albashinki yay ne amma haka kurum bazan fadawa yaudararen karyan ciwon da uwarki takeyi dan ta cimin kudina ba. Toh Bazan bayarba inyaso In ban bada kudin ba ta mutu..

Sosai hafsat ta fashe da kuka mai mugun rauni kanta na kallon kasa hawayenta na zubowa sosai.

"Mtwsss kefa jaka ce...toh wa ubanwa kike zubda ruwan hawaye anan,.. mtchewww, nace Bacci aka kawoki kiyi a gidan nan ko aiki?...

Kafin hafsat tay magana harta dungureta da karfi

"matsiyaciya kawai ba sabon ba anzo birni anji laushin katifa an kime hakarkari ana baccin lalaci to wallh ba agida na ba. Zaki tashi kihau aiki ko sai naci ubanki.

A daddafe hafsat ta miƙe dan Tsabar jirin dake tafe da ita har duhu duhu kawai take gani ga wani irin zafi da jikinta yay sosai.

Bata hankara ba ji tay an cakumota an turata waje ke da Allah kiyi abu da jikinki Mijina yanzu zai dawo daga wajen motsa jikinsa dan haka ki tabbata kin hadamai ruwan wankansa yanzu, kiyimai breakfast snn kin gyara mai dakinsa.

Bakinta da muryanta duka na bari tace toh hajiya.

Batare da bata lkci ba shemau ta fice tabarta awajen. Tun fitarta hafsat take kuka ahankli harta kama aikin bata dena zubar hawaye ba.


hadaddiyar motar mijin nata bude shige ciki ta hakimce a gidan baya,
yau driver ne zai kaita direct gidan hadizar ta nufa zasuje su fara shirin abubuwan da Alfa ya basu akan lkci.

wani tafkaken spec ta maka akan fuskartan tana tajan tsaki ita kadai dan tunda ta shiga motar babu abinda takeyi sai gudun kirar mijinta awaya. duk iya cijewarshi a kwana biyun nan danya nuna mata baya tsoron ta amma abun yana neman yaci tura cos right now data fito zata tafin ma harji take kmr she is not soo scared nd worried akan yadda zaiyi reacting afterall shine yake sonta sosai ba itace take kaunarsa har can can ba.


******
Bangaren vicky kuwa tun asubahin farko data farka daga bacci take gaban computer dinta tana aikin danne danne dan bata fiyeson cusawa ranta damuwar aurenta data kwana dashi a zuciyarta ba.

Maganganun da mijin nata ya gaggaya mata jiyan ya tsaya mata aranta duk tabi ta rasa menene mafita guda daya, zuciyarta yana cikin yanayin karyewa da damuwa najin cewa ita da samun wata kulawa awajensa har sai ya samu cikakkken sauki..

Ynxu babban damuwarta shine when, how soon, dan koda bata fada a fili ba itakanta tasani sarai cewa zuciyarta ya soma gajiya da rashin samun kulawa tare da biyar bukata daga wajen mijinta femi.

Ta dauki tsawon lokci tana aiki a website dinta na kasuwanci at same time tana exchanging email da kamfanin da suke kawo mata kayan kwalliya daga America duba da yawan masu neman products din datake kawowar yanxun sun ragu sabida rashin nitsuwar datake dan fama dashi kwana biyu.

Wajajen karfe shida da rabi na safiya bayanta kammala duba shafinta kenan irin sakon dataga ni jiyan ya sake shigowa mata.

Bude email din tay ta karanta sakon ganin an rubuta _"Hi mysterious soul, your enigmatic vibes have sparked my curiosity. So, Shall we exchange secrets and create a story only we know?"_ Batare da ta amsa sakon ba tabi kan information din ta dudduba amma bata fahimce komi game da sender din ba duk dama aranta tasan namiji ne, itade babban abunda ya bata mamaki shine yadda akayi wann sender din ya samu private email dinta wanda bakowa ne yake dashi ba sai mutane masu muhimmanci sosai.

Tunani kala kala sun bijiro mata aranta ganin zata iya Bata lkcinta akai yasaka ta basar ta miƙe tsaye tareda wucewa wajen wanka domin ta wuce makaranta..


Yau tun sassafe Dr khalid yake sauraron sako daga wajen Dr Asim game da halisa mansa amma sai shiru baiga komi ba,Yau tun dayazo office din yake zafafa bincike akan lamarin rayuwarta Gabaki daya saiya kasa zaman waje guda,izuwa yanzu ya bincika har yasan da cewa halisa macece mai zaman kanta kuma ta tara kudi sosai tay suna,

snn yasan da cewa matsalar daya faru tsakaninta da wanda zai aureta ne ya jefata acikin wann halin, he wants to get to know her better ta inda zai more game dinsa akanta sosai tunda kowa yasan mata suna fama da rauni sosai ayayin da suke tafiyar da rayuwarsu sukadai batare da wani nasu ba

A kwakwalrsa kallon A lonely mysterious lady with Unknwn past and dark stories yake mata

Dan haka da yuwar akwai qamshin nasara bisa plans dinsa daya tsara wajen shigewa cikin rayuwarta da kutse.

Babu wani tantama ko shakku yasan bazai daukesa doguwar lokci wajen samun kan haliisa a tafin hannunsa ba.

Koda ya duba irin makudan kudi da sunan datayi sosai lamarinta ya tsaya mai a rai..dan aranshi yasan he can use her to get her money ta hanyar aurenta a sirrance da zimman bata kulawar data rasashi a rayuwa, toh inhar ya auretan yagama lasar zumanta yasan babu abunda zaiyi da ita sede ya billo ta hanyar black mailing inta tunda tay suna sosai,..

Yasan hala kafin lkcin ta fada cikin soyayyarshi bazata iya karawa dashi ba, so iyakaci ne akarshe ace zata ta kashe kanta da kanta shknan case dinta is closed kenan har abada, and since bai samu wani information akan familynta ko yan uwanta ba kenan inta mutu shine zai gaji arzikinta batare da wani ya sakamai ido ba.

Wayannn plans din ya dinga hadawa aransa
minti kadan zai bude computer yahau duba messages ko ya kira sectary ya tambaya ko Dr Asim ya shigo.

Duk wata nitsuwarsa ya tafi izuwa kan case din halisan, ga wata ubar shaarwata dayakeji aransa dan da siffar halisar ya kwana a idanuwanshi jiya ko iya runtsawa mai kyau baiyi ba.

Daga Abuja kuwa Dr asim dagangan yakisam ya waiwayota lagos bare ya kulashi dan already ya riga da ya fahimce inda ya dosa duk dama basai plan din nasa na yaudara babba bane yake shiryawa akanta.

Yadai san ganin halisar ne yasaka Gabaki daya dr khalid yabi ya rude harya hakura da aikinsu na Abuja..

Yau koda suka hadu da Dr khaleel zancen halisar kawai yake masa in sun zauna hira,aransa so yake lallai ya cusama khaleel son aiki akanta aganinsa she needs him more than khalid,.

Khaleel kuwa bakaramin tsanar jin sunanta yay aransa ba daurewa kawai yake dan yana girmama dr Asim din sosai.

Tunda ya soma bashi labarinta Baice masa komi ba dan har mamaki yake wai doc Asim da iliminsa na sanin yanayin hali da tunanin dan adam amma wai har yana iya danganta halisa da mace mai sanyin nitsuwa da hankali.

irin kallon da khaleel yakema dr Asim din shine na irin wanda Baisan asalin halin halisan bane shiyasa haryake yabonta haka .

Tare suke zuwa wajen aikin da suka budeshi a babban asibitin Abuja duk ransa a dagule take taciki dan Bisaga dukkan Alamu ya lura cewa kusan dolene Dr Asim ya dawo dashi lagos in few days time domin ya duba lamarin yarinyar nan daya mugun tsana.


**************
Tunda shemau ta bar gidanta, jikin hafsat ya tsananta da zafin zazzabi sosai dan tsabar tsoron muguntar shemaun datakeji bata iya samun damar cire jikakken rigarta data jikamatashi da ruwan kankanra ba.

Aikin gidan kawai ta fada kai tanayi hawayenta na zubowa tana tunowa da jikin mahaifyarta jikinta banda rawa kar kar kar babu abunda yakeyi..

Gashi dokace kowacce rana sai tabi kowanni falo acikin falukansu manya guda ukun nan ta share tay mopping ta sakamai turaren qamshi.

Hakama duk dakuna sha biyu dake gidan zata wanke toilets dinsu evryday koyay datti ko baiyi ba, snn ta mopping floor both ciki da waje tayi Abinci tabita kimtsa kitchen din. In mijin shemau ya dawo daga aiki shima haka zatamai komi kamar dan karamin yaro.

Ayar shekarunta dabai wuce sha biyar zuwa sha shida ba bakaramin galabaita tay a hannun uwargijiyarta shema'u izuwa ynzu ba,..

Koda shike an sha gaya musu cewa masu aiki basa jimawa agidan suke guduwa. Akwai kudi kam amma akwai bauta.

Da kyar da wahala tay ma engr breakfst ta zuba masa a mazubi takai dinning table ta aje snn ta kammala tsaftace falokan duka uku wansa kamin ta kammala wani irin numfashi take ja mai tafe da azaban zafin zazzabi da tsoro, jin kamar numfashin nata na neman yankewa yasata hakura da aiyukan sauran dakunan ta yanke hukuncin kawai zata gyarawa mijin shemau iya room dinsa kafin ya dawo daga motsa jiki.

A daddafe ta isa dakin batare da tasan inda cikakken hankalinta yake ba..

Hannunta na ɓari ta yaye bargon kan gadon ta hau gyarawa tana sauke nishi da kyar dan gabaki daya gabobin jikinta yay sanyi batajin karfi ajikinta ko kadan,tunanin halin da mahaifyarta take ciki yasaka tun jiya bata iya saka komi acikinta ba

Da kyar ta kammala tsaftace room din sann ta wuce toilet dinsa zata wanke, toilet brush ta dauka tafara wanke toilet din dashi kenan taji cikinta ya murdata.

Tamke cikin nata tay jin radadin murdawar dayakeyi yana dada hautsina mata hanji.
Batare da tay aune ba wata amai mai tafe da kakari mai karfi ya soma fitowa daga bakinta yana kkrin zubowa akan floor

zubewa akan gwiwanta tayi kafin nan ta kai bakinta cikin toilet din tafara gwazawa aciki kamar ranta zai fita.

Tsananin damuwa da rikicewar tunani hadi da tsabar dacin da aman yazo dashi yasata fashewa da wata ragwabbabiyar kuka mai tsuma da kara duk gidan saida ya dauka da radadin sautin kukan nata.

Bude kofa aka yi dagata bayanta babu zato ba tsammani wanda tayi zaton baya nan din ne ya leƙo.

Gudun dayay a mill machine yasaka shi ya cire jacket din rigarsa ya bar kansa da armless din datake ciki wadanda take bayyana siffar manyan damatsansa da cikakken halittar kasaitaccen kirjinsa wanda ke lullube cikin shara-shara armless ta Ralph Lauren din da shot dinsa baki.

Da mamakin jin kukan nata yake karasowa cikin toilet din da sauri sauri Ita kuwa tanajin sautin takunsa abayanta wani mummunan tsorone ya kara rufeta awajen tanajin kamar tay fifika ta bace daga wajen cikin gaggawa.

Ɓari takeyi kamar zata rikito kasa ta tamke jikin toilet seat din sosai danta samu karfi, sede dan tsabar tsoro batasan sanda hannunta data dafa jikin toilet seat din ya soma zamewa dakansa ba,..

bata wani kammala fidda aman daga cikinta ba amma haka ta komar dashi da karfi tay sauri zata miƙe ta yi flushing nasa tana miƙewa tsaye jiri mai karfi ya kwasheta tayi luiiii cikin yanayin sumewa zata rikito kasa kan tiles, tsoron karta fadi ta buga kanta akan toilet seat yasaka yay saurin tarota jikinshi...

Kansa a mugun daure yake kallonta ayayin da idanuwanta ke rifuwa dakansu ahankli, gani yay jikinta gabaki daya ajike da ruwan sanyi ga wani irin zafin zazzafi daya lullubeta wanda yasan koda shine bazai iya daure mishi ba.

Tempureturenta is extremely boiling hot

Dada rikota jikinshi yay yanayin jikinsun na gamutsuwa atake taja wani irin wahalallen numfashi daga nan bata kara motsi ba.


Daukarta cak yay cikin rasa yadda zai yi da ita ya shimfidata akan gadonsa snn ya koma bathroom din da gudu ya kunne ruwan zafi ya debo ruwan kadan a bucket ya surkashi izuwa lum lum sann ya zura karamin towel aciki ayanayin tsorata ya jika towel din tareda zubewa gabanta ya matseshi ruwan ya dan ragu snn ya soma daddanawa ajikinta tun daga kan fuskarta har izuwa kan kirjinta yabi har tafin kafafunta yana daddanawa.

Yafi minti ashirin yana aikin mata hakan koda ta dan farfado bata iya bude idanunta ba, sai surutayya kawai take tanayi tana kuka me ban tausayi cikin zafin zazzabi tana kiran sunan mahaifyarta tana me bata hakuri akan rashin zuwanta da batayi akan lokaci ta duba lafiyarta ba..umma na kiyi hakuri zanzo dan Allah karki mutu ki barni, umma dan darajar muhammadu rasulillahi karki mutu kibarni. Yadda zaka san ta mummunan cusa abun aranta har jajjan zuciyarta take kamar mai ciwon tabun hankli alokaci guda idanun egnr yabi ya tara ruwan tausayinta sosai.

Duk a cikin bayaninta ya fahimci cewa kamar damuwar rashin lafiyar mahaifyarta ne fall acikin ranta,.

Towel din ya cigaba da danna mata kafin nan zafin jikin nata ya ragu sosai amma bata farfado fully ba.

Zama yay agefen gadon yanata mamakin yadda hakan ya faru da ita dan jiya da daddare lafiya kalau yaganta tana ayyukanta kamar yadda ta saba duk dama yana lura da kamar ba acikin hayyacinta take ba..

Kallo daya yay mata ganin hawayen dake kwance akan fuskarta yasashi dadajin mugun tausayinta aranshi yanata wondering yadda takeji gashi duk ta jike jikinta da ruwan sanyi dan Bakaramin tausayi ta bashi ba.

Shide a iya zamansu agidan kallon shiru shiru me hankli yake mata kullum yarinya ce da baata damu da abun duniya ba, dan baima san metake ciki da rayuwarta ba iyakaci tay serving dinsa ta masa sauran ayyukan daya shafesa shikenan wani abu na raini ko cin mutunci bai taɓa giftawa tsakaninsu ba duk dama sosai ya fahimci cewa tana matsanancin jin tsoron matarsa shema'u.


Dakin da suka kwana da shemaun ya nufa domin ya tambayeta kota san wani bayani gameda maganganun da hafsat din takeyi akan halin rashin lfyar da mahaifyarta take ciki, ganin babu kowa acikin room din yasakashi ya ciro wayarsa daga aljihunsa agaggauce ya soma danna mata kira.

Kusan sau biyar yana kirarta amma bata daga ba, can kasa ya sauka yana jin ransa na sosuwa sosai tuna cewa ya umarceta akan da ta jirashi ya dawo kafin ta fita. He truly loves shema'u kuma yasan zai iya daukar kowanni irin hali datake masa amma arayuwarsa ya mugun tsanar ayi disrespecting dinsa.

Daga tsakiyar babban falonsun ya tsaya ya cigaba da kirar layinta tana gani amma bata dauka ba, duk tunaninta ya dawo gidan ne zai bukaceta gashi ita bazata iya bari show din gidan hadiza ya wuceta ba. Ayanzu bata bukatar komi sama da samun cikakken amincewa da yardan Hadiza dan tasan ata hakane kawai zata iya yagar rabon arzikin mijinta ajikinta itama.


After few minutes hafsat ta farka kanta na juyawa da jiri sosai ganin kanta a inda tasan batada damar kasancewa aciki.

Nishi take saukewa slowly har ta dan samu nitsuwa daga nan cikin minti biyu rak taji saukowar dumi mai yawa ta cikin pants dinta, Abu kamar wasa ta dan janye jikinta ta duba,jinin period din tane ya fara zuba har gashi yayi staining masa kan gadon nasa sosai.

Ahankli ta Lunshe idanunta sabbin hawaye na zubo mata, aranta tace na shiga uku, arikice batare da tasan me zatay ba saita mike tsaye a rude,.kara tsorata tay ganin yadda jini yay ma dede inda ta kwanta akan gadon kaca kaca, hannu ta dora aka tana cewa wayyo Allah na na shiga uku innalillahi wa inna ilaaihi rajiun kafin ta ce zata yaye zanin gadon har tayi waje dashi Sai Kyat taji alaman bude kofarsa. Bari jikinta ya hau yi Dan Batasan sanda ta dira kan gadon da sauri ta koma ta zauna akan jinin ba.

Ransa a bace yake dan haka Ko kallo na biyu baiyi mata ba,amma daga yanayin yadda yake kkrin danne mood dinsa tasan yanada tausayi sosai.

cijewa tayi duk hnkalinta baiya jikinta dan hatta zafin ciwon cikin ma ta dena kulashi. Tunanin yadda zata soma masa bayani takeyi duk ta kasa motsawa.

Yana karasowa kanta ya daga ido ya kalleta kafin ya budi baki yay mata tambaya atake ta soma rera masa kuka sosai

Cikin kukan tasoma cewa Ogah Dan Allah kayi hakuri. Dan Allah karka koreni kayi hakuri bada gangan nayi hakan ba

Tsaban rawan da jikinta keyi sai abun ya bashi mamaki aransa Yace Ikon Allah What is this?yabi ya kafe ta da idonshi yana lura sosai da yanayinta na post traumatic stress.

Da kyar tadena kukan tayi masa shiru snn ta rike cikinta ta jin jinin na dada bulbulawa,hawayen da take saukewa yuuu ne suka fara razana shi Sanda ya lura da ita sosai snn ya fahinci yanayin da take ciki na matsalar barkewan jinin al'ada.

Domin ya dada tabbatarwa yasashi yace mata "Get up...daga inda yake ya furta mata hakan

Girgiza kai tayi ta cigaba da cewa dan Allah kayi hakuri..

Yace hafsat
U can't get up?

Sama sama take jin turanci dake zaman lagos yakansasu suna tsintar me ake cewa, gyadamai kai tay cikin sabon kuka tace yes sir am soryy sir Ciki na kemin ciwo wallh dan Allah kayi hakuri.

shiruuu yay yana ta kallota tana kuka,it took him a while kafin yasoma tambayarta asalin halin datake ciki.

Batagayamai komi gane da ukubar da matarsa take gumsa mata ba, Nan ta fara fayyace masa halin da mahaifyarta take ciki na tsananin jinya kuma bata bukace komi daga gareta ba face ta ganta ido da ido. Sede Tsabar tsoron shemau datakeji bata iya gaya masa cewa har ta nemi alfarman hakan shemaun ne ta hanata tafiya gidan ba.

Yaga wautarta sosai amma dake tabashi tausayi sai baice mata komi ba, kuma ya dauke kai yay kamar ma baisan tay stain ba.

Komawa kan kujerar sa yayi ya zauna ya na latsa wayarsa, In not less than 10 minutes suna zaune sai sukaji knocking abakin door.

Wani irin hadiyar yawon azaban tsoro hafsat taja duk a tunaninta shemaun ce ta dawo.

Gani tay ya tashi da kansa ya bude kofar bataga wanda yazo ba har ya juyo da ledojin shopping a hannunsa manya guda biyu

Batare da ya kalleta ba ya aje matasu akusa da ita snn sai ya juya ya fita ya barta adakin nasa.

Da wani irin Kallo kawai tabi closed door din kafin nan daure ta bude park din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login