Showing 96001 words to 99000 words out of 171903 words
an kunnata itadai godiyar kawai take zubo masa tare da adduoi batare da tasan metake furtawa bama.
bai wani kulata ba ya maida hnklinsa kan lokci ganin karfe uku aka nema na rana.
Ahankli yace mata ina waje. Snn ya fita.
Acikin sauri ta miƙe ta wuce dakinta babu bata lkci tafara tattara kayanta ajaka tana kukan murnan jin zata sake ganawa da mahaifarta ahankli tana kuma murmushin amsa mata adduarta da Allah yayi dan haryanzu bata gama dawowa cikin hayyacinta ba.
Within 10 minutes ta sauko rungume da jakarta ta rufe kanta da wani tsohon mayafi,kallo daya ya mata ya dauke kansa ya bude door din daya daga cikin motocinsa dake paker a tsakar gidan ya shiga gidan gaba snn ya bude mata itama ta shigo ciki.
Basu jima ba suka dau hanyar Aiport bayan tamasa cikakken bayanin inda kauyensun yake acan agarin jigawa, koda suka isa filin jirgi banda kalle kalle babu abunda hafsa takeyi jin kanta na juyawa kamr na wacce zata zauce da kauyanci dan tunda aka haifeta bata taɓa giftawa ta hanyar tashar jirgin kasa ba.
Wani babban office aka kaisu inda wani farin mutum sanye da uniform fari yake zaune, bayan sun gaisa da engr itama ta gaishe sa da sanyin murya gefe taja ta rakube tana daga tsaye tana kallonsu har suka kammala wata yar magana da harshen turanci sann yace mata tabiyosa su tafi, abaya abaya ta dinga binsa har suka kai cikin jirgi..lkcin banda bugawa da karfi babu abunda kirjinta yakeyi har aka kai kan seat dinta aka bata wajen zama,a sudade ta zauna kmr me jin tsoron wajen zaman tabi ta kame jikinta duba da yadda kowa yake mata kallon bakauyiya .
Da kyar da wuya ta iya kakalowa kanta nitsuwa ta sunkuyar da kanta can kasa ganin duk wajen babu wani mai kama da ita. daga nan baifi tafiyar awa da yan mintina ba jirginsu ya sauka a dutse intl airpot inda ya amshi motar dayay booking awajen ajiya suka kama hanyar izuwa kauyen nasu dake da dan nesa da garin jigawa.
Duk dama ransa a cunkushe yake da lamarin shema'u baisa ya dena tausayawa halin da hafsat din ta shiga ciki ba musmn ganinta yar karamar.
Aransa bai taɓa tsammanin cewa dan hutun daya samu domin yahuta tare da matarsa zai kasance masa a wann yanayin ba sede arayuwarsa bai taɓa yin danasanin taimakon nakasa dashi.
Wajajen karfe hudu na yamma suka iso cikin wata kwarabbiyar hanya mai dauke da jan kasa dake babban jeep yake ja sosai kurar hanyar ta bude jikin motarsa.
acikin dan wani sukukun kauye suka billa wanda baifi a kirga mutanen cikinta ba, hausawa ne da fulanin tashi suke gauraye awajen suna rayuwansu cikeda rashin neman ilimi da tsananin talauci.
Wanda karancin temakon gwamnati da rashin kayan more rayuwa yasaka matayen suke yawan mutuwa ayayin haihuwa,hakanne ya jawo suke da yawan marayu da yara marasa galihu dayawa Wanda basu da uwayen da zasu rainesu daga sunkai shekaru hudu izuwa biyar za'a kaisu aikin gona, ko almajiranci ko aikin bauta irinsu wankau ko mai aikin gida ko na shago,in namiji ne koyay dako ko achaba acan wasu garuruwan masu nisan tsiya danma karsuna gudowa gida.
Zuciyar hafsat har kamar zai zauce da murna tsabar farincikin datakeji dataga kauyensu.
Mamaki ya dingaji aransa ganin duk wani kunyar datakeji ta kawar tana masa jagora ixuwa lungun da zai shiga...
Acan kusan karshen anguwa gidan nasu yake
Dan karamin gidane da aka zagayeshi da karare, tsabar talauci ko darajar samun kofa bataci ba yarwata tsohuwar tsommace data yayyage tay dukundukun aka rufe kofar gidan dashi tun daga waje kana iya hango cikin gidan.
Lkcin Inkaga yadda hafsat take dagokai tanamai washe baki zaka rantse ba itace takecikin matsanacin ciwo da damuwan nan ba.
Sunayin parking agaban gidan A nitse ta juyo ta kalleshi tacemai "Alhaj mun iso. Kallo ya karewa gidan nasu Baice mata komi ya gyada mata kai tareda bude lock din motar sann yace mata ta saukata shiga ciki tukuna zaishigo daga baya...
Batay mai musu ba ta sauƙa da kullin kayanta a hannunta, tanajin kafarta akasa wani irin shaukin son ganin mahaifyrta ne ya lullumeta, nan ta zuba aguje ta nufi cikin gidan nasu da murna tunkafin ya dago kai harta bude labulen nasu ta shige ciki..
Dakin mahaifyar tata ta burmu ciki dan ko labule bai ci darajar samu ba a wangale haka yake a fili.
Tana kaiwa tsakiyar dakin ta hango maman nata yashe akasa akan tabarma jikinta duk ya kangare bata iya motsi bare tay magana ga wani irin warin rashin wanka daya gamutse dakin..
Idanun hafsa na fitar da ruwan hawaye ta soma kirar sunan ta a ragwabe tana karasowa ciki" umma umma hansatu ce
Umma gani nan na dawo
Ahankli Har ta iso gabanta ta rusuna gwiwowinta kasa ta kamota jikinta ta rungumenta sosai iya abunda take furtawa kenan acikin gunjin kuka..
Wani irin tari mai fitowa da kyar umman nata tafarayi tana kkrin tashi jin muryan yar tata kamar acikin mafarki.
"Acikin wata iriyar nakasashiyar murya datay kamar na wance zata mutu ta soma cewa "Hansai?Allahu akbar ashe da rabon zan ganki kafin Na mutu..hawaye ne suka soma sauko mata tanakan tari tace na dauka mutuwa zanyi hansatu hala sede kizo ki kalli kabarina amma tunda kinzo Alhamdullh nagodewa Allah ko aynxu zan iya mut...t...uwa...
Acikin tari me karfi ta karashe maganan. Tana cewa hansatu ki yafe ni, kiyafeni..
Lkcin Jikin hafsa rawa yakeyi tanajin kamar notinan kanta suna ku cewa, wani irin azababben kuka mai kara ta fashe dashi acikin yanayin tsorata da gigicewar hankli me tsanani.
Umma dan Allah Dan Annabi karki mutu ki barni umma dan Allah kiyi hakuri karki mutu..
Wayoo Allah na na higa uku umma in wani lefi na maki ki yafemin kar daga zuwana kicemin zaki mutu..wallh hajiyata ce ta hanani zuwa wajenki na roketa kudin aikina amma tace bazata bani ba, wallh ba kin xuwa nayi ba umma. Ummana dan Allah ki yi hakuri, dan Allah karki mutu kibarni.
Wani irin raunataccen Kuka mai kara takeyi tanata memeta wayann maganganun acikin kukan nata,shikansa engr baisan lokcin da kururuwar tata mai cike da gaucewar hankli ya sakashi ya shigo cikin gidan babu shiri ba.
Tsayuwar cak yay daga bakin kofar dakin yanata kallonsu yana kuma jin abubuwan datake fada wanda yaso ya shigar dashi rudewa.
Kenan shema'u ta san da wann maganar amma tay shiru bata turo yarinyar nan gida tazo tay jinyar mahaifyarta ba
Salati ne ya kufce masa tare da shafa fuskarsa dayay ahankli yaname furta innalillahi wa inna ilahi rajiun kasar wuyarsa jikinsa atake tay mugun sanyi..
Cos All he saw was an immensed fear of being alone daya ke tsagawa a cikin razanannen sautin muryan karamar yarinyar nan.
Kukan datakeyi sam ba acikin hayyacinta takeyin shi ba, tunawa da yadda rayuwarta nan gaba zai kasance ne idan aka barta ita kadai a duniyan da ba uwa babu uba.
Take tahau tunawa da cewa itace silar mutuwar mahaifinta hamma Aliyu a dacan asakamakon gwagwarmayansa na son yaga ya sakata a makaranta tay karatu. sedei tun burinsa na hakan bai cika ba haka yan uwansa suka ji haushinsa suka taru suka lashe shi a maita.
Da kyar engr ya Tattaro nitsuwarsa ya karaso cikin dakin cikin karfin hali ya bambare hafsa daga jikin mahaifyarta sann ya soma mata tambaya ina mahaifinta yake ko yan uwanta dan taje ta kira masa wani muharrami sabida akai mahaifyata asibiti cikin gaggawa.
"...Dake ba acikin hayyacinta take ba bai dauketa wani mintin biyar wajen fayyace masa halin datake ciki ba.
Tace babana ya rasu da jimawa..yan uwan babana sun gujemu dani da ummah ne kawai muke rayuwarmu,ita kuma bata da cikakken lafiya,shiyasa tabada ni wa magajiya aka kaini legas dan ina aiki ina samo mana kudin rufawa kanmu asiri.
Alhaji Dan Allah dan darajar iyayenka ka taimaka min kar ummana ta rasu wallh bani da kowa a duniyan sai ita.
Duk ya rasa meke masa dadi ganin rikicewar da yarinyar tay..
Baiyi kasa agwiwa ba ya tayata suka dauko mahaifyartan suka sakata a motarshi.
Fizgar motar yay cikin sauri suka bar kauyen izuwa nearby public hospital ganinsa me kudi
Yasaka aka tarbesu da sauri tarban mutunci aka bata gado tare da saka mata ruwa. Hafsat ke tare da mamanta agefe tanata adduar Allah ya taimaka mata ta farka daga sumewar datayi.
Shikuwa tunda ya fice waje baiyu wata wata ba yakira few contacts dinsa daya sani acikin garin jigawa nan aka masa arranging motar emergency daga general hospital jigawa.
Kafinsu iso daga cikin garin jigawa already har mahafiyar tata ta sha ledar ruwa yakai guda sha shida, agaggauce aka dauketa izuwa cikin garin direct aka kaita emergency inda za'a ceto ranta cikin gaggawa.
Suna tsaye daga waje hankalinta sam baya jikinta shikuwa yanata satan kallonta ganin ta kasa tsaye ta kasa zanne.
Aransa gani yake kamar bai dace ya mata tambayoyi game da abunda dazun yaji tana cewa ba, wani zuciyar kuwa ce masa yake zai iya yuwa tsoron shemau yasata taki ta gaya masa gaskiyar maganan..inhar yana son ya san menene asalin gaskiya to dolene ya tambayeta acikin wann hali na rauni datake ciki yanzu hala bazata iya boye masa komi ba.
**********
Daga ta dayan bangaren kuwa sai kusan Wajajen bayan la'asar aka kammala daurin auren Alhaj kyari da amaryansa honourable Hajiya ramatu bukar ex minister of foreing affairs wanda ba ayishi a bayyane ba kamar yadda bokarta ya gindaya mata.
Hudu da rabi na yamma nayi aka kawo amarya.
Daidaikun matan ne suka fito tare da amarya cike da nuna tattali,a lokacin hamshakan kawayenta na harkan siyasa da ayarinsu ne suka sauya sautin iskan gidan hadiza da zazzakar sautin gudansu me karfi da zaƙi wanda kamar da gayya sukeyinshi ba.
Amarya har ila yau sanye take da cotton white lace an rufe mata fuska da tsaddaden mayafi mai sheki assorted with expensive swrasvoki stones hannayen ta sunji asalin jan kumshi duk inda suka wulga da ita tana fida wani irin azaban qamshi ahaka har sukayi cikin gidan da ita.
Duka duka Lokaci kalilan suka deba suna xaga wajen dukansu yan kawo amarya kowa yana raha ana sam barka,daga nan Har sashin amarya aka bi aka mata ban kwana cike da farinciki bayan nan kowa ya wuce mota domin a maidasu masaukinsu.
Itace a lullube luf zaune a tsakiyar fankacecen queen sized italian bed din dakin.
Babbar aminiyarta hajiya hasana ta dafa kafadunta cikin wata iriyar rangwadi tace toh Amarya ramatu zamu tafi...Allah ya bada zaman lpya.
Jawota ramatun tay suka dan yi wata magana kasa kasa acikin kunne.
Cikin jadaddawa hasanan tace toh
Kawata karki wasa, ki dira ma aiki kawai, ki kuma tabbata alhaji yana shigowa dakin nan ko be nemeki ba ke kinemeshi dan aikin boka ya fara aiki akansa sosai, kema kinsan ai bazama ya kawoki gidan nan ba kifara fidda wancan shegiyar yarinyar yau yau kafin ki share hanyar debar arxiki da matsayi.
Murya kasa kasa ramatu tace "Au har kuma sai kin nanata min ne? Ai ni a shirye nake shiyasa basai anjira dare yayi zamuyi harkan nan ba yana shigowa yanxun zakiga aiki da cikawa. Kin sanni wallh bani da imani, gagararrun mata nawa ne nayi fatali dasu a uwa duniya bare kuma karamar yarinya kamar Hadiza meitama banza da ita kusan sa'ar yar cikina. Kedai kije ki huta gobe zakiji yadda komi ya kasance.
cike dajin dadi hasana tace shegiyar kaya aikinki na kyau, ai dama Babban goro sai magogin ƙarfe tun asali irin gidan daya kamata ace kin kama kenan bana tsoffin stake holders ba.
Tace Kedai bari kawata ai inkinga nabar gidan nan to na sharewa kaina hanyar wata zazzafar siyasace, Ke nifa so nake nan da sati na gaba ya soma sokani acikin harkansa ta man fetur na kasa dan nafara kwashar rabona ina riftawa ciki toh kaf dinku kawayena sai na nema muku wajen ci.
Wani irin shewa hasana tay tabi ta rangwada guda mai karfi suna masu kwashewa da dariyar mugunta
Heheheheh ramatu kice da zafinki kika zo.
Tace bari kawai kede sai kinjini...
Suna kammala zantar da hakan saiga kanwar ramatun ta shigo yi mata sallama itama, itade Tun isowarsu gidan ta kasa boye damuwarta wajen nuna zakewa da tambayar shin ina kishiyar yar uwa tata take? dake kusan dukan su basu taba ganin ta a fili ba, ita kam ko da sau daya ne tana so ta gan ta da idanunta dan taje gida tabada labarinta ganin Tunda suka zo gidan ba ace musu komi game da ita ba kuma ko yanxu ma ance musu tana nan acikin gidan a sashenta.
Abun ya dan dameta amma dayake anyi bikin agaggauce ne babu wata hayaniya sai ake yawan danne tsegumi,cikin son tada zancen tace Adda ramatu gashi har zamu wuce kishiyarki bata fito ba bare muganta adan gaggaisa,kakkaurar tsaki ramatun taja batace mata uffan ba.
Hasanan ce tace."Yo me ne aciki dan anyi biki har munzo kishiya bata fito ba? rashin fitowar ta ai Alheri ne agaremu.
Zata kara wata maganan ramatu tace ke da Allah kin fiye son gulma uwarki ce da sai kin ganta? Hassana sata agaba ku tafi ni karta batamin rai
Kanwar tata batace uffan ba ta dauki gyalenta tana cewa Allah baki haquri amarya muntafi..
Suna ficewa ramatu ta sauke ajiyan zuciya tare da yaye mayafin kanta tanamai dada bajewa akan gadontan.
Wayarta ta dauko tana duba sakonin bokanta tanamai sake nanata su.
Tsaki taja tare da jefar da wayar agefe duk ji take kamar Alhajin bazai shigo akan lkci ba.
Bayan nan ana neman wajajen shida na yamma saura shi kadanshi ya taho gida yanzu an manyata so there is less need for all fomalities na angonci, shiyasa tun da yamma aka sa masu kulawa da tsare tsaren biki suka sallame kawayen amarya da masu kawota gidan da goma na arziki.
Daga shigansa gidan nasa shashin hadiza ya fara kuskokai dan har saida aka daura aure kafin nan ya dawo hayyacinshi ya tuna da cewa baima sanar da ita cewa aurensa yayiwu acikin gaggawa haka ba.
Yana saka kafarsa a site dinta kuwa yaji kanshi yayi wani mummunan sarawa sabida warin hayakin maganin hana aikin ramatu ci akansa datariga tayi,wani dishi dishi yake gani inda ya tsinkayo muryan Babbar mai aikin ta wato iya sharifat, a ladabce ta rusuna ta gaishe shi tare bashi labarin cewa hadiza ta bada umarni akan cewa duk wani mai himman ganin ta ya bari sai da safe bata son ganin kowa yanzu.
Har Ya budi baki zaiyi magana wani irin sarawa kanshi ya dadayi sanda ya dafe goshinsa,daga nan bai gane komi shikansa baisan ya akayi ya sallame ta ya juya yabar wajen ba.
Yana tafiya kuwa iyaaa sharifat ta isar da sakon ta ciki inda hadizan take zaune...
Har tana batar kalma ta durkusa gaban su...
"Hajiya alhajin ya koma....
Lkcin Wani wal wal din walkiyar ababen hannu dana wuya ne kawai yake haska wuyarsu ita da shema'u suna zaune acikin shigarsu ta alfarma.
Hadizar ce a zaune akan babban kujera na farko shema'u na agefe duk sun yi kyam suna faman shan qamshi dan duk wata hayaniyar guda a kunnensu akayi.
Gabaki daya ran hadiza a dagule yake dan tsabar tsanar datayiwa kishiya fitar da magana ma gagararta yayi.
tsaban iya kaskntarwa ko kallo shemau bata iya maida ma iya sharifat ba bare ta samu amsar ta
Sai Cahn dataga dama sai ta juyo,Maganan ma takanyi shi ne kasan fatar bakin taf kamar bazatayi ba.
tace ke da Allah ki tashi ki bishi ki tabbata ya shige sashinsa bayan yayi mintina goma aciki sai ki dawo ki gayamin.
Da barin jiki tace toh cikin ladabi ta mike ta fice after 11 minutes ta dawo tace musu eh yana ciki..
Gyada kai kawai hadiza tayi suka sallameta ta tafi.
Tana barin wajen shemau tay marmaza ta mike hurjan jan tare da sake mayafin ta cikin azama..tace hadiza tashi muje ki shirya kanki kema zama bai kamaki ba.
Babu wani bata lokaci Cikin dakinta suka nufa ba Inda shemau ta fito da wata jaka daga kasar gado wanda bata tsaya bude shi complet bama ta zaro wasu fararen yadunan likkafi matsu karfi ta shiga warware su
agabanta hadiza ta tube tsindir ta nade ta da kayan tsaf izuwa dunduniyar kafafun ta.
Cikin sauri Tace "Durkusa acan ta mata nuni da tsakiyar fankaccen gadon ta dayaji jan kyalli daga gani ba tambaya kasan shima na tsafi ne.
A durkushe hadiza tasaka gwiwon ta a tsakiyar gadon inda shemau ta ciro karamin kwarya mai dauke da kwai ta rufe idanun ta tsam tana tofe tofen harufan sihiri aciki.
Bayan minti 2 ta bude idanuwan ta Kwaryan ta aje a tsakar kan hadiza tabi ta rage wutar dakin zuwa dim inda fuskokin su kawai ake iya ganewa.
Wasu ayoyin sihiri da alfa ya basu suka dinga karantowa, A hankali hadiza take maimaitawa Muryanta har na rarrabewa,alamu sun nuna kusan dukkan imaninta tasa take rerawa fuskn ta dauke da yanayi mai nuna matukar yardan da tayi wa abunda takeyin.
Basu tsaya ba har sanda suka kai aya sanda kwaryan dake kanta
Dakan shi ya bule dakin da wani irin hayaki mai raxanarwa..
Kwan shemau ta ciro ta mikawa hadiza tana kamawa ta fasashi acikin kwaryan.
Ganin komi ya kammala sai ta dauko karamin karrrawa tana bugawa gyelen gyelen a gefen kunnen ta na hagu da dama. Nan suka faffadi bukatunsu akn ramatu
Cewa take ka tafiyar da ita kamar iska mai tsananin karfi da bai da matsaya sai madakatan karshen rayuwar sa.Ta tafi,ta kurmance kar ta tsaya har abadan abada.
sannan duka suka rufe ido suna mai rike hannun juna,Ko secnd basuyi ba Wani iska mai tsananin sanyi ya shiga ratsa su, bat kwaryan ya bace a dakin jim kadan komi ya washe kamar ba ayi komi anan ba.
Cikin sauri hadiza ta sauko suka nannade bedsheet din ta mika ma kawarta shemau
Lkci Shemau take kallo tana cewa toh Nidai baxan fito gobe ba sai ki tsaya kisha kallo.
Hadiza tace toh ai sai kije ki huta goben zamuyi magana
Shemau tace toh Ni ma zan wuce kedai kisan yadda xakiyi nagaya maki bana son asaka mana ido yi zakiy kamar bakisan komi ba
Tsaki kawai hadiza taja tace wallh bana shayin su Ohon musu tunda ni suka so su taba.
Shemau tace Allah sa tana fita a karo na farko ta mutu.
Hadiza bata ce uffan ba, har shemau taja mayafin
ta takama hanyar bude kofa,tsayuwar scnds tayi.
Tace..to nidai na tafi sai kinjini,hadiza na amsawa ta rufe mata kofar ta fice mai gaba daya agidan....
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS