Showing 123001 words to 126000 words out of 171903 words

Chapter 42 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

792

yay yana sussukunyar dakansa kasa cikin jimami kamar yadda magajiya ta zayyana masa yayi snn yazo ya tardasu a wajen yanajin me suke cewa.

Alhaj aliyu ne ya dubesa snn ya karkda kai yace yawwa malam mudi tunda ka dawo sai ayi hkri amance komi ka mana jagora izuwa kauyenku domin ayi mata duk abunda yakamata.

Da mamakin su mudi Bai musu musu ba aka hau shirya komi dashi aka dauko gawarta aka saka acikin motar asibiti daga drivern sai mudi, engr mahmud kuma ya dauko Hajya badiatu tare da hafsat din sai Alhaj aliyu dake bibiyarsu abaya.

Tun ahanya mudi ya kikkira sauran yan uwansa ya zayyana musu komi da harshen yarensu sabida karma driver yaji me suke kullawa.

Daga can kuwa Sunajin zancen kudi atake jikinsu ya fara rawa babu sanya suka soma kulle kullen yadda zasu yi su yage rabonsu ajikin wayannan mutanen dan koda anbarsu a kauyen da hansatun sunsan ba riketa zasuyi ba gara taje duk inda zataje kawai dan suhuta maransu da jarabar gulman jama'a


Tafiyar Awa daya yakaisu har cikin kauyen Direct akayi da gawar gidan mijinta, Sann aka arranging masu wanketa da shiryata kamar yadda addini ya tanadar babu wani jinkiri aka mata sallah aka kaita makwancinta..

Hajiya badiatu taso ace hansatu ta zauna tay makokin mahaifyarta koda na kwana uku ne amma lura da tsananin jahilci da tsana dake kewaye da zuciyar yan uwan mahaifinta yasaka ta yanke hukuncin kawai ta tafi da ita asalin gidan mijinta dake Abuja dan hutune da businesses dinta kawai yake kawota lagos, manyan foundations dinta kuma yafi karfine a kano da kaduna da zamfara state.

Kawunan hafsan kudi kawai suka nuna suna so abasu kota halin kaka dan harta gadonta ma saida suka ce ba nata bane, inji babban wan mahaifinta yace ai gida da filin kofar gidansun ma duk ya cinye acikin basukan da suke bin iyayenta harma suna neman kari akai bayan hansatu da dedeku acikin mutanen gari sunsan duk karya sukeyi basa bin dan uwansu ko asi.

Case aka dingayi hajy badiatu nata kkrin kwatowa hafsa hakkinta amma Rantsuwar da suka dingayi akai yasaka engr yace abar musu shi,
Hatta yar dubu uku da dari biyar da suka kara akaima duk ya dauka ya basu snn aka dawo da tattaunawa kan batun makomar rayuwar hafsa.

Ko ajikinsu suka tsunduma ciniki dasu kamar wata yar akuya zasu siyar..

Dan Adam bazai taɓa sanin amfani da darajar da iyayensa suke dashi ba musmmn in suna raye sai a ranar da akace masa babu su a duniyar, ranar ne zai asalin fahimtar cewa baida wani gata ko mutunci bare kuma security face na kulawar iyayen nan nasa.


Yadda yayun mahaifin hafsatu suke tsaurara zancen hana tafiyar Shikansa mudi saida ya matukar sha mamakin yadda suka shirya makirci adan kankanin lkci.

Babban yayan su mai suna dogara yace inhar kungiyar marayu ne zata dauki hansatu saidai a biyasu kudade ko ahada harda sauran yayansu marayu da uwayensu mata suka mutu akaisu binnin suma

Dake hajya badiatu tasan halayyar dan kauye tuni ta ja gefe ta kira awaya dominta shawarce mijinta,..sun jima suna magana sai can suka kammala snn ta nemi tayi ganawar sirri da hafsat din.

Koda ta shige cikin dakin a dukunkune ta sameta kwance akan tabarman mahaifyar tata tana wani irin rawar ɗari zazzabi mai zafi ya rufeta.


Daga waje kuwa Engrn mahmud ne a zaune tare da abokinsa alhj aliyu agindin wani bishiya inda ake karban gaisuwar mamaciya, caraf sai ga kirar mahaifinsa ya shigo.

Ciro wayar yay daga aljihunsa dan Bai sha mamakin ganin kirar ba sabida yasan hala mahaifyarsa ce ta gaya masa komi shiyasa ya kira domin yaji ba'asi.

Ajiyar zuciya engr ya sauke sann ya kara wayar a kunnensa cike da girmamawa ya rusuna kai kamar wanda mahaifin nasa yake gabansa, muryan mahaifin nasa ya tsunkayo yana cewa asalmu alaikum..yace wa Alaiksalam Abu an wuni lfya?.. Daga ta dayan bangaren mahaifin nasa yace masa lafya kalau alhamdullh mahmud ya kuma akaji da hakurin wann matar data rasu??

Yace hakuri Alhamdullh.

babu yabo ba fallasa yace toh Allah ya jikinta ya mata rahma, Allah ya saka namu in taxo tazo mana da sauki.

yace Ameen ya rabbi."

"kuma da kuka tsayawa wann marainiyar yarinya Allah ya baku lada ya dora muku shi a mizani.
Engr yana amsashi acikin jimantawa yace hmmmm mutuwa nasiha ce mahmuda.Toh wann sai ya zame maka ishara, ka kuma sani bawai Allah bayason wann yar yarinya bane ya dauke mata gatan ta a duniya, dukkan mu yan adam a bisa kan hanyar jarabawa muke rayuwa, Allah yay mata hakane dan ya jarabeta ta, kaima da ka taimaka mata ba ikonka bane Allah ne ya nufa zaka samu wann ladar.

Engr yace hakane abu

Daga nan Nasiha masu shiga jiki ya dinga jero masa akan qaddara yana kawo ayoyi da hadisai da kisosi har kaman zai sakashi fidda hawaye.

Bayan ya gama kashe mai jiki sai ya danyi shiru
snn yace mahaifiyarka ta fayyace min duk abunda ake ciki da yan uwan uban yarinyar, kai kuma me kace akan haka!

Ahankli engr Yace Abu dama duk wani abunda ya shafi karatunta nace zan dau nauyi tunda hjy tace zata dauketa a karkashin kungiyarta na marayu

Yace toh madallah amma dai kaji batun kawu nan nata kasan fa shi mutumin kauye kamar taɓababe yake yanzu akan wann abun saiga sun mata hassada sun hanata samun wnn alherin daga tattare daku,
toh nidai atunani tunda ba haramun bane ai ko kai zaka iya temakawa ta dawo karkashinka gabaki daya inyaso kawai sai arabata dasu tunda zaman nata dasu ba alheri bane. mahmuda kayi tunani wann jihadi ne babba, kuma shi aure ai nufin Allah ne inda Allah be nufa ba bazamu ma kawo tunaninsa aranmu ba..toh zai iya yuwa wata babban kyauta ce da Allah ya karkato maka dashi kai din baka lura ba.

Cike da rashin fahimtar furuncin nasa engr yace Toh abu aure kuma bangane abunda ake nufi ba?..

Kai tsaye mahaifin nasa yace masa ina nufin tunda ba haramun bane kai me zai hana ka auri yarinyar...
ka fahimceni ni ba tursasa maka hakan nakeson nayi ba kuma bance sai kamin hakan dole ba amma a matsayina na mahaifinka inaga hakan ne dede. Koba dan komi ba kayi dan Allah dan ka ceto rayuwar marainyar nan daga halaka dan muddin kuka barta a hannun wayann bakusan wani irin mummunan rayuwa zata fada aciki nan gaba ba.

ATake Engr ya cire hularsa yahau fifita jin wata zazzafar zufa na karyo masa, gabaki daya yaji zuciyarsa da kwaklsa ta cirke sai yaji yakasa furta wata kalma sai kame kame dayakeyi shikadansa aransa batare da yasan me zaice ba.

Dada kwantar da murya Mahaifinsan yay yanamai cewa karka damu mahmuda nasan kai ɗa ne mai hankli da biyayya dankace min bazaka yi ba ai ba wani abu bane dama shawara kawai nake baka akan abunda zai ficce ka har Agaban ubangiji..babu wani soyayyar da zan nuna maka a duniya face in bida kai ta hanyar da zai kaika ga samun kyakkwan karshe.

Zuciyar engr na bugawa cikin neman dedetu makansa yace "Hakane Abu..hakan ma yay, In sha Allah koda umarni kabani zanbi bare kuma shawara me kyau kabani namaka alkwari in sha Allah hakan za'ayi nagode Allah ya kara girma yasa agama ibada lafiya.

Murmushi mahaifin nasa yay snn yace Allah yay maka albarka mahmuda
...Allah ya tsare bayanka da gabanka snn yasaka wann aure da zakayi ya zamu alheri gareka duniya da lahira.

Muryansa ararrabe Yace Ameen Abu... amma inason amin alfarma nayi dan nazari akai kadan sabida...bai barsa ya kammala zancen ba yana dan murmushi yace dakata mana malam ai duk munyi lissafin wann Mungama magana da ni da mahaifyarka,munsan baka shirya ba dan haka ne ma tacemin koda an daura auren bazata tare agidanka ynxu ba harsai ta gama mata yan shirye shiryenta by then ma an dan samu fahintar juna kaga inka shirya kaita gidanka willingly sai ka zo ka dauketa ku tare acan. Tare da sauke ajiyar zcya yace toh masha Allah hakan yay dama abunda nake so ince kenan.

Mahaifin nasa yace Toh inda akwai wani Abu dai zaka iya gaya mata ai alfarma muke nema awajenka mahmuda duk wani abunda kake so in sha Allah zamu duba.

Yace a'a Abu karka damu in sha Allah zanyi duk abunda kukace din.

Albarka ya dinga sakamai kafin nan ya katse kirar.

Daga nn Komawa yay ya jingina kansa ajikin motarsa ahankli yake furta lahawla wala kuwwata illa billah... hasbiyallah wa neemal wakeel...dan kwata kwata baisan meyakeji aransa ba sabida baiyi tsammnin hukuncin da iyayensa zasu yanke akansa ba kenan.

Wani bangaren zuciyarsa yana ma abun kallon saukakka wani bngaren kuma tunamasa da rikicin shemau yakeyi dan yasan abune me wuyar dauka awajenta barinma ace mata yar aikin suce, dan yasan bakaramin wutar balai bane zai huru agidansa wanda hala zai iya jawowa ya rasa matarsa dayake matukar kauna.

And He does not want to hurt shemau in anyway sabida yana sonta aransa bana wasa ba sedei ata wani fannin kuma bazai taba iya butulcewa ko ya saɓawa umarnin iyayensa ba har abada dan haka ya samo masa kamar dolene ma ya amshi batun auren nan.

atake yaji kansa ya cirke abun na neman tay masa nauyi, zuciyarsa na neman toshewa da tunanin wata mafita...

sake sake yakei aransa har saida abokinsa aliyu ya dan taɓa kafadunsa kafin nan yadan dawo hayyacinshi wanda kallo daya yay masa ya gane cewa ba lafiya.

Yace abokina Meyafaru ko baba ne kuma ba lafiya?

Cikin lumshe ido da budewa engr yace lfyarsa kalau yana saudi arabiya ma.. yace ma zai kiraka anjima....ynxu de wata magana mukayi dashi da take son dagamin hankli.

Alhj Aliyu Yace sirri ne ko zan iya ji?

Yace no bawani abun sirri bane aliyu...kawai cewa yay wai na amince a auramin yarinyar dan mubata daman rayuwa. Nikuma Na amsa mishi na amince amma kai abun na min nauyi a zuciyata gaskiya..i just dnt feel like its a right decision for me now
..wallh akwai matsala a
Aliyu...yadda baba ya kawo zancen rike yarinyar nan tamkar yabani Amanarta ne, amma kuma matata ta gida fa bazata taɓa fahimtar haka ba karshe ma tafara zargina tunda kaga aiki yarinyar take mana.

Alhj aliyu yy murmushi mai sanyi yace haba mahmud wallh ure overthinking it, i knw yin aure gatsau nada wuyar dauka, amma wann ai ba wani abun tashin hankli bane, inde akan fitinar mace ne duk zaizo ya wuce amma farinciki da albakan iyayenka akanka is priceless mahmud, ni ynzu da ace mahaifina na raye i wont mind doing anything for him wallh ko a bola aka tsinceta yacemin na aura zan aura badon komi ba saidan sabida nasan duk duniya sune zasu cigaba da tsayamin alkcin da bani da komi sann sukadai ne kawai zan saɓa musu inyi babban asara tunda aljannata akarkashin kafafunsu yake bana matata ba.

Think about it aynxu ahaka inda ace wani abu zai same arzikinka macen dakake ikirarin kanaso itace zata fara azabtar dakai wata ma rabuwa dakai zatay atake
Dan haka a shawarce ni banga wani abu aciki ba
Just calm down and think about yadda abun zai kasance.

Engr Yace haka ne amma Aliyu still dis is not easy as u said. I mean taya zan fara gayama shemau cewa nayi aure just like that ....i think is not fair kuma inajin nauyin ince ma baba a daga auren
Zuwa wani lkci..aiko Addini baice in zakama mace kishiya ka mata a sigar da zai daga mata hankli ba.

Aliyu yace hmm zaku tare da yarinyar ne ynxu?

Yace a'a....bana tunanin hakan just yet sabida za a sakata a makaranta a can Abuja..im talking about the future, kasan dei dolene shema'u tasan nayi aure wata rana sabida dolene inzo na hadasu susan juna.

Aliyu yace toh dont tell her just yet mana tunda bayanzu zaku tare ba
..ka dai tsaya kayita tunanin hanyoyi mafi sauki da zaka fito mata maybe hala kasamu wata yar maslaha da zata billo maka acikin wayann lokutan.

Engr Yace toh nasan hakan zaiyu, tunda mama ne tace zata riketa for the main time amma ina tsoron wani abu yaje south wallh dan shemau bata da sauki ko kadan

Murmushi Aliyu yy yace tunda ba da niyyar cutar da ita kayi ba nothing will go south.. kawai kayi Adalci snn ka kula da yarinyar koba dan komi ba bakasan albarkan dake tattare da ita ba.

Suna cikin wann hirar aka zo aka kirawosu lokcin hajy badiatu tay iya bakin kkrinta wajen lallama hafsa dan ta aure danta
Sede da kyar da wahala hafsat din ta amince badan komi ba saidan mummunan tsoron shemau datakeji aranta sedei jin hajy tace mata agidanta na Abuja zata zauna yasaka taji dan dama dama amma ko kadan aranta bason auren takeyi ba kawai dan bata da yadda ta iyane.

Koda aka baje magana Kawunanan nata sun sha baqar mamaki jin cewa baqin nasu sunce zasu amshi auren hansatu atake.

Sede aransu gani suke kamar auren bogine ake nema dan wani dan birni ne zai aure yar kauyen tukuf irin nasu wanda batay ilimi ba kuma ma marainiya??

Hakan yasaka basu wani dau abun da muhinnnci sosai ba.

Daga lkcin da aka binne mahaifiyar hansatun izuwa karfe biyar na yamman ranan aka kammala komi dan uwan mahaifin engr dake zama a kano shi yazo har kauyen ya wakilce auren dake tsakanin jigawa da kanon baki da hanci ne.

Duk wata al'ada ta aure anyi, Nan aka kawo dubu Dari biyar sadakin hafsa aka basu, Nan ma sukay kutunkutun suka hana hafsa ganin sadakinta sukace ai sadakin nasu ne tunda sune ubanninta.

Da yamma lis aka daura auren akofar me garin kauyen, ana kammalawa basu wani ɓata lkcinsu ba suka bar garin inda har suka fita a kauyen suka nufi gidan alhj aliyu asalin cikin garin jigawa hafsatu bata dena kukan rudani da baqin cikin yadda rayuwarta ya juya mata a lkci guda ba.

Anan sukayi magrib da ishai matar alhj Aliyun ta musu tarban mutunci da mutuntawa sosai, matar tasa mai suna murjanatu cikakkiyar bahaushiyar kano ce yar babban gida datasan darajar dan adam dan ko kadan bata raina yanayin dataga hafsa ba. Koda ta bawa hjy badiatu masauki bata zauna ba,nan da nan ta jawo hafsa suka wuce ciki tamata jagora tay wanka da sabulai masu qamshi ta fidda dauda kyanta ya dada fitowa sarari, hafsa ba fara bace snn bazaka kasaata a layin bakake ba amma wani irin narkakken natural beauty take dashi wanda fuskrta sam baya bukatr wani kwalliya.

Idanuwanta yan dedei ne farare sol gata da shatin saje baki dake nuna alaman yawan suma da Allah ya albarkaceta dashi, girarta ma acike yake tam snn tana da doguwar hanci mai kmr pencil da dan karamin bakinta pink colour me shatin baki kamar an zana mata da gazal, bazaka kuma ce da ita mai kiba ko tsiriya ba dake tana da diri na lafiyayyar budurwa mai fitinannen kyau mai kuma ban sha'awa kana kallonta kaga zubin bafulatanar jeji futuk.

sabuwar abaya mai kyau matar aliyu ta bata da inner wears new pant da bra ta saka ajikinta duk dama sam taki sakewa da su bare taci abinci.

Aliyu da matarsa Sunyi sunyi akan su kwana musu agidan amma haka engr yace sam, shidai yayi musu alkwari cewa zai kawo musu ita ziyara inkomi ya lafa musu in the future.

Suna zaune suna dan hira hafsa na tare da hjy badiatu ata ciki dan haryanxu jimamin mahafyarta takeyi.

Nan da nan Engr yay booking musu jirgin karfe 8:30pm na dare amma basu samu ba sai aka maida musu shi 9.30pm wanda ya saka suka dada samun hutu kadan.


Dagata fannin victoria kuwa tun kafin dare yay nisa ta isa sabuwar estate din mijinta ya kama ma dan uwanta nile.

Tun tana parking motarta a haraba ta dinga kallon wajen tana mamaki ganin yadda aka sankamawa gidan security camera ta ko ta ina.

Bata kawo komi aranta ba harta sauka ta karaso gaban apartmnt din nile tay knckng abakin door din after few min wani saurayi yazo ya bude mata kofar ta shigo ciki

Cike da girmamawa gayen yace mata "Gud evening sister vicky..Ta kallesa da fuskar rashin sani atakaice snn tace 'evening young man am here to see nile and who are you?...

Tun bai bude baki ba saiga nile din yana saukowa daga matakala
As usual looking breathtaking sassnyar murmushinsa mai ratsa zuciya bisa kan fuskarsa yana kallonta direct da sanyayyun ruwan idanunsa. Atake ta daga kai itama tana kallonsa sabida yanada wani irin fitinannen kyaune na fitar hankli.

sanye yake da armless shirt baki da 3qtr shot na kamfanin puma wani irin fresh kafarsa yay acikin lallausar roam about sleepers din da ya zura akafafunsa na kamfanin fenty.

Har ya karaso kasa gabanta bata dauke idanunta akansa ba har saida taji saukar lallausar labbansa agefen kuncinta yanamai cewa hey sis,.. hannunsa ta kama izuwa nata tanacewa Hi Darling "Whats up..ahnkli tace and who is this? Yace ohhh..Gefen abokin nasa ya dawo yana murmushi snn yace this is my friend lucio..kin tunashi tare muka fara scndry schl back in the days,
sumtimes muna canada tare.. He is my gee, even mum and dad knws him very well.

Yana maganan vicky ta kure gayen da idanu sai can kafin nan ta tunasa tafara dago fuskarsa na yaranta tace ohh okay lucio wilson.. The model guy right?

Lucio yana murmushi yace yes sister vicky its me.

Tace lu willy???

Dariya suka fashe dashi jin ta ambacesa da sunansa na yaranta.

Lallai an girma da ahanya naganka ma ai bazan gane ka ba, well is
Nice seeing again lucio

Yace thanks sister vicky. well, am on my out zanje na karbo mana abinci me kikeso kici sai na taho miki dashi.

Tace nothing dear ba jimawa zanyi ba, yanzu zan koma gida.

yace okay bye then daga nan ya fice yabasu waje

Nan Ta juyo kan nile tanata kallonsa kafin nan ta nemi waje ta xauna akan lallausar sofar dake falon, nan shima yazo ya zauna kusa da ita yay shiru.

Tace Ehen kacemun nazo wajenka cikin gaggawa sann nazo kuma kamin shiru..i even tot it was emergency hanklina duk ya fara tashi kawai sainazo naganka looking all fresh and good bama abunda ke damunka a duniyan nan face ka dagamin hankli.

Yace nooo sister vicky ba haka Bane. Dagaske akwai abunda yasaka nake nemekin kuma yana da muhimmnci.

Tace okay am all ears.
Gayamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login