Showing 12001 words to 15000 words out of 171903 words

Chapter 5 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

758

da tashin hankli hade da rudanin ganin du ahaka marar miisaltuwa...

Jikinta na rawa ta karaso wajensu tana tafiya hankli tanamai kuresu da idanu dan ta karance expression din datake gani a fuskokinsu.

Tana isowa daf ta dube idon meenal kai tsaye..
Muryanta a sanyaye tace
"Meenal, what truth?.

Shiru meenal din tay kanta na kallon kasa sam taki ta haɗe ido da halisar dan itakadai tasan irin bugawar da zuciyarta yakeyi a dede wann lkcin da guilt na sanin cewa itace sila.

A dan rude Halisa ta sake gown din nata kasa jelarsa ya bazu snn ta fara ja da baya a ragwabe kuma ahankli tanayi tana dan duban fuskokinsu duka, gani tayi cikinsu daga mai kawar da kai gefe sai me sunkuyar da nashi can kasa jikin vicky kuwa rawa jikinta yake har yanzu,wani runtse ido halisa tay dan already aranta tasan wani abu mummuna ne ya faru da ita.

cikin murya mai cike da tashin hankli tace "shiru zakumin bazaku fadamin ba?..

Shema'u tay kamar zata bude baki cikin sauri meenal ta mata alama akan tayi shiru aka bar halisa da binsu da kallo

Daga nan inda take tsaye tana hawaye ta dubi hadiza da idanunta ya kawo ruwa alaman tana cikin yanayin rauni tasan itace kawai zata iya fallasa abun cikin sauki nan ta soma rokonta tana hawaye sosai tace "Hadiza dan Girman Allah Dan darajar mahaifyarki ki gayamin meke faruwa..

Hawayen Hadiza tuni ya sauko zirrrr,numfashi taja zatay magana vicky ta rikota tanamai ce mata no adiza. Snn ta juya tace Halisa pls calm down okay.

A masife tace NO!! "Dont tell me to calm down vicky just tell me what is going on"..ku fadamin mana,..meye haka kuke min? A rikice cikin kuka mai cike da rauni da kuma razana ta fada numfashinta na hawa sama sosai yana sauƙa dakyar.

Da wani irin sauri kuma a ragwabe meenal ta karaso wajenta ta dafo kafadunta a sigar lallashi
Tanamai cewa "halisa zamu gaya miki..but i need you to calm down.

Kallon meenal din tay snn Tace but am calm..oh u think am not calm? Na zauna tun safe ina jiranshi da weding gown a church har kusan karfe sha biyu da rabi saura baizo ba and u still think am not calm..wani irin kwantar da hanklina da hakuri kuke son nayi. Nide Kawai ku fadamin meyene banason iskanci.

Masifa tahau musu amma da Meenal ta fara kuka sosai sai kuma taji tsoro me tsanani ya kuma lullubeta...

duk dama tana cikin halin fushi mai tsanani da zach amma tunani daya takeyi aranta gamedashi..gani take kamar wani abune ya sameshi na hatsari ko mutuwa ko kuma wata yar matsalace ya tsaresa a wani waje.

Kallon meenal ta dingayi tanata kuka batasan da cewa guilty consience ne kawai yake kwaranya acikin zuciyarta ba..

Tana daga idanunta sama sai kuma taga sauran kawayen nata suma sunakan share nasu hawayen jikin su duk yay sanyi. Wani irin bufff bufff taji zuciyarta na harbawa kamr this minute zai dauke cakk

akan hannun vicky dake rawa sosai idanunta ya kuma sauka take taji Wani sanyi ya lullumeta ta juyo a kangare ta dube meenal dake daf da ita tana kuka, muryanta a kakkarye tace mmmm mee...meee..menal, mmmmmmmmeenal
"Is zach dead??? Ya mutu ne..did he die??tun meenal bata amsa ba ta fasa ihu cikin birkicewa da zaucewar hankali nan ta cakumota tana ta jijjigata a rikice tanacewa please tell me mutuwa yay? Meenal bata iya cewa komi ba sai kukan da takeyi duk tsoro ya cikata ta ciki, Da sauri sauran kawayen sukazo suka rirrikesu.

Lkcin kowa na cikin wani yanayin da basu iya danne baqincikinsu ba

Halisa tana shirin yankewa ta fadi kasa vicky ta rikota dan rikice musutayi gaba daya zata suma duk tunaninta mutuwa zach yay kawai shiyasa ake boye mata

Ganin haka yasa Hadiza tasa kuka mai dan karfi acikin rudani ta dubesu duka snn tace in babu wanda zai fada mata nide zan gaya mata ta huta da wann azaban

Da sauri Meenal ta dago kai "tace a'a hadiza..dani mukayi magana da zach dan haka zaifi dacewa halisa taji komi daga bakina.

Jin hakan ya dawo da halisa hayyacinta kadan nan ta miƙe tsaye ajikin vicky da shemau dasu suka rirriketa dan babu karfi ajikinta ko kadan.

Bakinta na rawa tace ohj thank god meenal kin yi magana da zach? Where is he..what happen.

Meenal din ce ta karaso daf kusa da ita snn ta riko hannunta suna masu kallon juna..

kame kame goma da ashirin sai da tayi acikin zuciyarta dan kallon kwayar idanunta da halisa takeyi gwanin ban tausayo yasaka taji aranta kamar bata kyauta mata ba.

bayan ta gamsar da ita cewa zach na raye nan tafara mata bayanin abunda ya wakana a wayarsu da sukayi dashi.

Sede nan ma Iya abunda ta gayawa sauran kawayen shine ta kuma gayawa halisa cewa zach yace yay tunani yaga bazai iya auren mace irinta ba.

Wayann kalmomi da meenal' tace mata zach ya furta saida halisa ta memetashi a brain dinta bila adadin tanata neman yuwar dalilinsu da kuma mafarinsu dan tasan dai zach baisanta da wani mugun hali ba, iyaka ace yasanta ne a matsayin mace mai kamun kai mai neman nakanta mai kuma kudin kanta, sann tana da kyau tana da aji tana da hali ta iya hulda da jama'a sosai, yo wani namiji ne zaice bazai iya auren mace irinta ba? Wann karya, Lefin me tay masa shine asalin amsar datake nema ayanxu.

Rudani da baqin ciki mai tsanani atake suka lullubeta.

Hatta Duniyar daukewa cak tay wa halisa ta tsaya cak akan kafafunta tanata kallon bakin meenal dake fidda mata bayanai mafi muni da saka karsashi, tuni kwakwarlta yadenajin motsin komi harna tsawon mintina goma dan ji take kamar gangan jikinta yana yawo a iska a can sama dan kwata kwata kurwanta baya tare da gangan jikinta a wannn lkcin.

Baqin ciki mai cike da tukiki da karsashi shiyake tsagata tun daga tsakar kanta har ixuwa jijiyar jininta yanamai mata yawo a sassan jiki yana kuma mamayar kowani lungu da saƙo na jikinta da kwakwalta.

Duk sai ta rasa awani duniya take dan jira take ace mata mafarki takeyi

Ahnkli Ta fixge jikin ta ajikin kowa ta tsaya a tsakiyarsu cak kamar an dasata..jiri da duhu take suka rufeta.

Tsabar yadda xuciyarta da kwaakwalta yake tafasa da baqin ciki bata iya yin komi ba saida ta dau minti goma masu kyau in shock dan ko motsawa wani sassan jiikinta baya iyayi.

Iyakar Munanan qaddarorin da suka gudana a Rayuwar ta gaba daya sune suka hau mata ziriya acikin kwayar idanunta da kwalrta tana kallonsu daya bayan daya kamar wani film.

Acikin zuciyarta dake bugawa kamar zai fatso waje take cewa "Laifina na ne.. its all my fault..laifi na ne..dan kuwa babu wani abu na farinciki daya ke raɓata saina baqin ciki,i knw that nothing good will ever happen to me in this life amma haka na rufe idona nabiyewa zuciyata na amshi soyayyar zach inata tunanin samun sauki da rayuwata mai dadi awajenshi.

Nabashi dukan yardata da zuciyata..na so shi so na haqiqa wanda babu na biyunshi a duniyar soyayya,dan tun bayan rasuwar mahaifina da mahaifyata ban karayi wa wani dan adam irin wannan soyayyar ba.

Maybe i am born to suffer and dwell in pain

Maybe ubangijin daya halicceni baya kaunata.

Datatuna irin baqar azabar datasha da rayuwa bayan rasuwar iyayenta atake taji Wani irin gulluton abu mai nauyi ya shaketa a kirjinta tanajin tsitttt tsittt kamar jijiyon zuciyan zasu tsinki haka taji sunata tsananin zafi sun kuma kameta taciki.

Lumshe idanunta tay sosaiiii jin kawayenta na kuka agafenta sosai

Sai kuma tausayinsu ya kamata, gani take kamar yauma itace silar digawa ma zuciyoyinsu baqin ciki da tashin hankli.

A tunaninta duk wanda ya rabeta dolene yay baqin ciki sabida haka Allah ya halicce da munanan qaddarori.

Cike da dauriya Juyowa tay tana kallonsu ganin mamaki dake kwaranya akan fuskansu ganin halisa bata yanki jiki ta fadi kasa ko ta suma musu ba.

Hawayenta masu sanyi suna sauka muryanta a sanyaye sosai ahankli tace musu"its Okay, ni na dauka wani abune ya sameshi ashe ashe wai
Zach Ya duba ne yagani cewa ban dace dashi ba, ragwabben murmushi ne ya kufce mata bazata, gyada kanta tayi cikin tukikin rudani snn tace..ders no big deal. Lets just...call dis weding off ...kowa yaje gida ya huta.

Kawayen nata Zasuyi magana ta hade ranta cikin dakatar dasu in a subconsious mind wanda kusan kowa awajen yasan bata cikin hayyacinta,hawayen ma duk ta gogeshi a fixge cikin zafin nama tace shema,vicky, hadiza, and meenal, girls... ku make sure kun rabawa kowa souveniers and all the food we got kafin mubar nan wajen.

A raunane hadiza tace akan me? Halisa why r u doing this to urself,..take a break. ure in pain...

Ranta a bace yasa bata tsaya taji karshen zancen hadizar ba ta juyo tace and so what if am in pain dijaa..am use to it..pain is part of my life now.
Inde har kuna tare da ni dari bisa dari toh kuyi abunda nace muku kawai mubar nan wajen. This respectable pppl waited for hours for my weding to take place bai kamata ace mubarsu su tafi haka empty handed da taqaici ba..

Vicky tace and what about u ?

Tace im fine, zan jiraku anan..i just need my space right now pls u guys shud understand me.

Shiru sukayi sai can snn kowa tahau share hawayenta hadiza tace lets go guys.

Vicky da shemau sun taso meenal tace ita zata zauna tare da halisa amma haka firr halusa taki ta amince mata hakanan ta hakura ta bisu suka kyaleta ita kadai awajen

"U think she is going to be okay ayadda muka kyaleta ita dayan nan..?

Hadiza ce tay wann tambayar

Meenal tace ni nasan halisa..mace ce jaruma mai karfin zuciya da kuma hakuri.

Tunda kikaga ta umarce mu muyi hakan bana tantama she is going to control her emotions.

Gyada kai hadiza tay sai basu kara cewa junansu komi suka wuce direct stalls din souvernier da wajen harhada abincin

Within 30 min shemau da hadiza suka saka aka yi good packaging na kayattaun abincin dale wajen aka zuzzba su a hadadun a take aways.

Meenal da vicky kuwa tuni suka gama da wajen masu sourvenir jakuna da tsarabar biki masu tsada aciki, dake suna da list din iyakar bakin da suka gayyata abun bai wahalar da su koya ci musu lokci ba, sai yan dedeku wanda a radin kansu suka zo wajen duk suma an providing musu nasu tak aways din

Bayan an kammala komi aka baza ma'aikata sula soma rabo mutane nata mamaki ganin cewa ba a daura aure ba amma ana raba musu kayayyakin tsarabar biki.

Ana daf da karewa meenal ta saci jiki batare da sanin kowa ba ta koma domin duba amarya halisa..

Tana ficewa acikin church acikin sauri da sassarafa ta karaso baya inda halisar take..kanta ne ya sara ganinta a yanaynin da bata taaɓa ganinta aciki ba.

Tsantsar Soyayyar datakeyi ma zach a zuciyarta shine yake neman ya zautar mata da kwakwalwa aynzu
Sai huhh huhh take tana furzan iska da karfi sosai alaman iskan ma yamata kadan.

Tun bayan tafiyarsu take ta kakalo tunanin tana lisafin abunda ta masa a rayuwa da zai saka mata da haka bayan soyayya mai tsafta da dadi dake wanzuwa a tsakaninsu.

A ragwabe ta kasance kafafuwar duk sunyi sanyi sunamasu kasa iya daukarta,zama tay daɓas a kasa ayayin da ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta hawayena zubowa daga cikin kwayar idanunta masu tsananin zafi da ciwo marar misaltawa ..

mental depression da anxiety yasaka ta kame jikinta kamar wacce take kkrin zaucewa

Har meenal ta karaso wajen kallonta kawai takeyi, ahankli ta rusuna daf da ita dan da alaman ma bataji motsin isowarta ba.


Saukr Hannun meenal din kawai taji ta dago kai suka hade ido yanayinta sodai ya razana meenal din muryanta a ragwabe tace "Halisa..

Tsareta tay da wani irin raunatattece ragwabben murmushi tare da cewa "har kun gama ne?

Meenal bata iya cewa komi ba ta gyada mata kai..

Hannu ta mika mata alaman ta dagota sama
Babu musu ta aikata hakan suka miƙe tsaye

Jiri sosai ke dawainiya da ita,duhu duhu kawai take gani agabanta amma haka ta daure tace meenal lets go the church.

Meenal tace mezakiyi a church halisa muje gida mana halisa.

Hawayenta ne
suka sauko tace a'a..
Sanin kanki ne bana tsoron fuskartar wani qalubale ma rayuwata koda kuwa baqin ciki ne ya cikeshi. Sabida ni mutanen nan sukazo dan haka abunda ya dace kawai zan aikata.

Meke nan zaki aikata halisa..did u realise dat akwai yan jarida da bloggers awajen.

Halisa tace and so what meenal..trust me
Am not going to do anything stupid..

Meeenal batace komi ba ta rrikota suka taho ahankli har izuwa cikin church din.

Already lkcin waje ya kaure da cece kuce jamaa ana ta tambaye tambaye ana neman amsa.

Tsayawa halisa tay alan alter tanata kallonsu ayayin da ta hanaa kowa matsowa kusa da ita.

Nan da nan Attention din kowa ya koma kanta ganin yanayinta da ya gaza boye halin tashin hankli da baqin ciki datake cikii

Nannauyar ajiyar zciiya ta sauke, snn tay murmushi tana kallon dumbin mutanem da suka dominta, da kalaman Godiya masu tausasa zuciya ta soma baza takaitaccen jawabinta.

Daga bisani ta dan babbasu hakurin zaman jira data sakasu sukayi, bayan nan cikin dauriya sosai ta hau sanar dasu in formal and calming manner ba araunace ba, "cewa tayi auren ta bazai yuwa ayau ba batare da ta furta musu dalili ba, ta kare da cewa tanay wa kowa fatar ya koma gidansa lfiya.

Tunda ta kammala furta hakan church din ya guntse da wani irin surutu na fitar haankli kowa na neman amsa

"why why meya faru whats going on.

Wani irin kallon juna Uncle dinta kawu karami da matarsa mama G sukayi wa junansu dan dama a hatsale suke da dan tsarabar da aka basu bayan sunga manyan mutane an basu mai yawa mai tsoka sukuwa da ba a gayyata ambasu wasu abubuwa na yaku bayi kuma aganinsu sunfi karfin abasu iya wannan.

Kawu karami ne ya soma mikewa tsaye yana zage zage da bakai ba gindi yana wani huci yana cewa aikin banza aikin wofi..duk baqin cikinsa da basu hadu da ango sun aiwatar da cikar burinsu na samun kudi da masauki awajensa ba.

Sanin cewa yan jarida zasu mata cha yasaka meenal da hadiza suka zagayeta suna bata cikakken tsaro ayayinda shemau da vicky suka kirawo attention na security aka soma matching din jama'a izuwa waje.

Kusan acikin rudani kowa ya bar harabar church din, wasu na harsashen matsala aka samu daga ango,wasu tausayin halisan kawai sukeji aransu, wasu kuma takaici ne ya lullubesu na bata lkcin su anan da sukayi.

Bakaramin drama akayi da media ba sede aka kusan watsa musu tear gas snn aka samu kwancyar hnkli ahakan ma sun nanike a gate suna neman amsar tambayonsu abakin halisa.

Within 10 min church ya zama daga su saisu kafin kace wani abu halisa ta ragwabe akasar alter dan ji tay kamar duk wani karfi daya rage mata a gangan jikinta ya gushe, is like yanzu ne ma datay hakan takejin mugun radadin zafin rasa zach da kuma tozarcin daya faru da ita yana me mamayeta sosai.

A hannu a hannu kawayenta suka ririkota domin sukaita mota.

Meenal da vcky ne suka shiga motar tare dabita suna danne mata kirjinta sabida hauhwan da nunfashinta yakeyi ayayin da su hadiza suka hau binsu abaya

Ana bude musu gate din church din mutane suka bi bayan motocin su yuuuu kallo da kuma maganganu.

Lokcin halisa batasan ina hanklinta yake bama.

Hadadden Gidan hadiza dake kan hanyar Victoria Arobieke street no 305 a anguwar lekki suka wuce da ita direct dan nan yafi tsatsauran security dan ita minister of petroleum resources take aura.

Duk da haka suna isa kofar gate wasu jounalist din har sun iso suna neman tada hayaniya,tun ba abude musu gate ba suka wawuso kansu da tambayoyi kala kala game da rushewar auren halisa,abayan su kawu karami ne da matarsa ta gama zugashi akan sam bai isa suyi biyu babu ba.

Sun kashe kudin motarsu tundaga benue sunzo amma ba aure babu cikar burinsu borance masa tay snn tace masa sede suzo su amshi salalan kudadensu da sukayi asararshi awajen zuwa auren halisa inba haka ba seta kashe shi dan itama bashukan mutane taciyo dan suzo.

Bakaramin Tsoron mamam G kawu karami yakeji ba,tun daga bakin gate din gidan hadizar security sukayi ca akan yan jarida.

anata kkrin bude musu gate su shige ciki kenan saiga kawu karami ya taho da mugum gudu kamar wani mahaukaci haryana tumbul yanata ihu yana cewa wallahi ba'a isa ba. Uba nake awajen halisa ba a isa arainani ba kee Halisa keee halisa.

Da yarensu na idoma ya soma ce mata ta sauka kasa ta same shi suyi magana tun kafun nan ya soma tona mata asiri.

Ya memeta hakan yafi sau biyar kuma da ihu yakeyi yan jarida kuwa sai daukarsa sukeyi

Halisa Tana layi amma ahaka ta tsinkayo mummunan Muryansa ahankli ta mike ajikinsu meenal tana jin jiri jiri muryanta asanyaye tace musu abarsa ya karaso tanason taji meke tafe dashi..

Hakan yasaka duka kawayen sukayi parking motocinsu abakin gate dan su tsaya mata har halisar ta sauko daga cikin motar a hankli

Sakeshi akayi ya taho yana wani huchi yana fiffixgewa.

Cikin rada mata a kunne Meenal tace halisa pls dont speak da karfi kuyi maganan ma kawai ayarenku kinga media suna daukarku.

Gyada mata kai halisa tay ta tsaya kafin nan kawu karamin ya isota cikin bunƙasa yana wani fadi yana hura hanci kamar bijimin kauye.
Atayani sharing izuwa grps please dats all am asking👏🏻

To join my postin grp caht me 08060712446
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_


⏯️4️⃣

Hade kwayar ido da halisa sukayi da kawu karami atake yasa taji tsananin rauni ya dada lu'llumeta.
Duk dama ta tsaneshi aranta amma he is her only family right now dan bata da kowa a duniya face shi.

Kawu karami yana mugun kama da asalin mahaifinta kamar an tsaga kara each time taganshi sai taji aranta kamar mahaifintan ne ya dawo.

Tsayawa datay agabansa yasaka zuciyarta tuni ya dadaa zurfafa cikin rauni da neman agaji, Ji take inama ace ya rungumota jikinshi a sigar lallashi, ita koda kalma dayana rarrashin ya gaya mata koda zataji sanyi acikin ranta Musmn Ayau take dada jin tsananin kewar iyayenta da suka rasu tuntuni wanda shine yake dada kuntatta ma ruhinta da zuciyarta ayau bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login