Showing 87001 words to 90000 words out of 171903 words

Chapter 30 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

1405

hanashi jikinta? ..yanayin jin tsananin takaici ta girgiza kanta cikin jan ajiyan zuciya ta soma tuna cewa ba lefi bane dan tahana mutumin da be damu da needs dinta da lafyarta ba sai zallan sex.. dan haryau bataga abunda tay masa yay zafi har haka dayake kkrin shigo mata da macen da ake cewa zatazo ta kasheta ba.

Gani tayi koda ma ta yarje mishi ranar babu wani abunda zai sauya a tsakaninsu dan tabbas mace bazata iya sauya namijin da baida niyyar sauyuwa ba, kuma halama da duk da hakan zaizo ya yi auren ita ta tashi da jin radadi da takaicin jin batada wani daraja,kima ko amfani agaresa face ga kan shimfidarsa a duk lkcin dayakeson tarawa da ita, bayan bai damu da nata bukatun ba komi ma ya sameta ko oho.

Time to time haka shemau na lallashinta amma bata dena kuka mai sanyi ba har suka dawo gidan atare.

Hakanan shemau tay zaman diris ta dinga lallashin zuciyarta tana lallabata tareda bata karfin gwiwar cewa atare zasu yi abunda mutumin nan ya bata domin su cimma burinsu batare da wani tangarda ba.


******

Yau har dare ya soma rufawa victoria bata dawo gidanta ba, dan daga barin wajen aikinta direct ta wuce anguwar victoria island taje ta duba Jikin halisa mansa ananma sukasha hirarsu ta rayuwa mai saka dariya da kuma ban tausayi dan vicky bata taɓa dandana zafin cin amana da yaudara arayuwarta ba in halisa na faɗa mata yadda akeji har tsoro takeji makanta.

sosai zuciyar vickyn yay sanyi data samu yarhutu anan tare da kawarta halisa mansa, can da yamma suka shirya tsaf halisar ta rakata sukaje hotel din da nile yake suka duboshi atare.

Awajen nile din suka zauna hira har wajajen karfe 10 na dare kafin nan suka rabu bakaramin dadin zuwansu nile yaji aransa ba.

Dawowarta gidan kenan tazo ta samu ko ina yay shiru alaman kowa na bacci, batako tsaya neman inda mijinta yake ba kawai ta faɗa room dinta tareda zabge kayan jikinta ta shiga bathrum tay wanka da ruwan dumi.

Bayan ta fito agaban madubi ta zauna tana ta kallon kanta ganin kanta kyakyakwar mace kuma lafiyayya wanda ko sarki aka bashi ita da gudu zai saka hannu ya amsa yana godiya amma duk wai tarasa samun wann nitsuwar da ake samu na gidan aure.

Ko ayanzu ji take kamar tafi kowacce mace sanin cewa dadin aure bada ga kudi, ko daukaka,soyayya ko kayan duniya asalin dadinsa yake ba kacal, aure idan babu sexual compability and satisfaction to akwai babban matsala sabida wannin fanin shike gina sauran fannin jin dadin auren..

Sex a aure kamar gishiri da maggi ne a abinci wanda inbabushi sam bazaka gane taste din abincin dakake ci din ba komin kyawu da tsadar abincin kuwa.

In her heart she really really want her man to make mad love to her tanason taji yadda akeji kamar kowacce mace agidan mijinta..

Lumshe idonta tay jin dukkan gabobin jikinta na amsawa, ahankli take shafa cream dinta bisa wankakken fatar jikinta dakenan fresh and healthy tanashafawa kamar bazatay dan wata muguwar jarabar datakeji nacin ta ataciki.

Harta kammala shafa man ba acikin hayyacinta take ba dan kuwa tasan batada wanda zai kashe mata wann wutar jarabar dayake ci sosai akasarta wanda takejin kamar zai haukatata yanzu

Gyara fuskarta tay ya dadayin kyau sann ta fetsawa jikin nata turaren midnight oud mai sanyin qamshi tabi ta saukar da suman kanta ya zubo mata tun dagakan kafadarta har gadon bayanta.

Nannauyar ajiyar zuciyane ya kufce mata cikin dauriyar data saba ta miƙe tsaye zata nemi nitie ta saka kafin taje ta nemo sex toys dinta su rage mata zafi,batare da kulawa ba ta miƙe tsaye jin towel dinta ya subuce zai fadi kasa tay sauri zata caɓeshi sai ji tay hannun mutum ya rigata daukawa.

Tana daga ido taga mijinta ne prince femi haka kawai taji zuciyarta yay sanyi da tunanin he will atleast make love to her tonite ko irin gwadawar nan ma yay suga ko manhood din nasa ta soma warkewa.

Miƙewa tsaye tsirarar tay ta kyaleshi da taul din a rike a hannunsa tanamai kallonsa asalon jan hanklinsa dan dai tasan duk wani lfyayye namiji in yaganta haka bazai iya daurewa ba.

Yana daukar towel din ya miƙe tsaye dashi,wani takaitaccen kallo ya mata sann yabi ya dora mata towel din ajikinta.

Haushi ne yabi ya cikata ta rikoshi a susuce tace "Femiiii...femi Cmon are u still mad at me?...u wont even touch me sai kace kashi na zuba ajikina..Well i have sent my brother away for ur sake.

Juyowa yay ya riko hannayenta jin muryanta ya fara sauyawa izuwa na rauni da kuka, salon yaudara yafara shafa gefen fuskarta da sigar lallami yana cewa shushhh baby am not mad at you..Xatay magana yabi ya hade bakinsu waje guda yay kissing dinta sau daya ya zare bakinshi sann yace ina kikaje kika jima tun dazu nazo nan ina nemanki..cikin bude ido da lumshewa tace i was with halisa..ta rakani naje na duba nile a hotel..bakinta yake kalla kamar zai hadiyeta yabi ya susutar da fuskansa "baby kinje wajen nile shine baki fadamin ba, look that is what i want to talk to u about.

Tace what again femi menene kuma?ko cewa zakayi na koresa a lagos din..

Ya dada jawota jikinshi yana dariya a sigar lallami yace hakuri xan baki akan abunda ya faru jiya my baby..i knw ure mad at my decison and am sorry okay..baby..?

Salon dayay maganaan sosai ya kashe mata jiki, Dada lafewa ajikinshi tay
Tanamai turo baki "i still dont understand why u dont want us to have visitors wai meyasa ne?
,.. doguwar sumanta ya hau wasa dashi yana cewa is Bcos i want to protect you and am very jelous of my love. A mamaknce Tace har yan uwan mu na jinin ma kana kishi dasu? Ya gyada mata kai yace eh mana baby..sai batace komi ba..saukar kiss dinshi taji akan saman goshinta yanamai cewa "i am proud of you baby inason mace me biyayya da jin maganan mijinta ..and u knw what..dago kanta tay tana kallonsa yaja karan hancinta slightly snn yace"sakamakon abunda kikamin yasaka nakeson na gaya miki cewa i will take full responsibility of nile's stay in lagos. His hotel, his security, his wardrobe, his food and also zan na aika masa kudade kowani wata dan yana samun na kashewa.
Banason yay fushi dani yaga kamar banason ya zauna da yar uwansa, while i knw in my heart dat i love u soo much vicky...i love evrything about u baby.

Wani irin dadi vicky taji aranta ta kwace ajikinshi ahankli tana murna sosai ta rungumesa suka faɗa kan gadonta atare.

Nan Tafara kissing dinshi passionately yana dan maida mata martani wani irin azaban dadi tasoma ji ajikinta hartaci nasarar ciremai rigar nitynsa tana mai masa wasa da nipples dinshi tana tsotsewa ahankli sede ko uhm da uhm bayayi dan yafijin dadin namiji ya taɓasa akan mace, har vicky ta cire nonowarta dakanta ta sakamai abakinshi ya kama ya tsotsa kadan harta soma jin dadi jim kadan sai taji ya tureta akanshi ya miƙe tsaye.

Kamar zatay kuka ta zuba masa kwayar idanunta dake ci bal bal da ruwan tsananin sha'awar daya taso mata muryanta na rawa sosai tace femi, baby wats wrong why did u push me like dat..

Take ya sauya fuskarsa Ya rike kansa can ya dago yana kallonta cikin zare mata ido yace stop it vicky.. you know i dont have the strenght and the erection to fuck you..

Batasan sanda ta rarrafo harta baki bakin gadon tana kallonsa ba...
Femiii i i know but you can romance me femi..
U can finger me or do somthing to relieve me am going crazy i want you..

Wani irin jan mumfashinsa sama yay irin maganan na konashi din nan har muryansa na rawa yace u want me to fuck u?..tun bata amsashi ba a mugun tsawace "so what about me vicky? U knw what... ure so selfish. Dama Hakanan kuke ku mata kanku kawai kukasani, ke yanzu bakiyi tunanin nima inason ayi realiving dina ba sai naki jarabar kawai kikasani..
Innayi romancing dinki nikuma ya zanyi da kaina ko ce miki akayi ni ba namiji bane bazanji feelings ajikina in ina tabaki ba?..masifa ya haura mata dashi duk sai taji zuciyarta ya cunkushe.

Wani irin kuka ta fashe masa dashi batare da tasani ba.

Surutu da korafe korafe ya soma mata a salon gas lighting da shifting situations izuwa kanta yana nuna mata kamr irin cewa tafiye son kanta dayawa din nan.

He just make her look desperate and impatient with his words,yanuna mata irin ai a matse take da sex din har bata damu da wahalar da shi yake sha danashi rayuwar ba.

Ce mata yake wai shima irin dauriya da wahalar datakeyi shi yakeyi.. but he make it looks worst sabida yana hadawa da kalmomi mafi rauni tare da cusa mata aranta cewa yanajin fargaba da tsananin tsoron rasata da kishin jin cewa hala zata gaji da hakurin zama dashi ahaka ta nemi biyan bukatar wani namijin a waje.

Banda kuka babu abunda vicky takeyi agabansa ganin ta jawo towel dinta tana kkrin rufe jikinta ayanayin karayar zuciya da saka tausayi yasashi ya sassauto da acting din nasa ya zauna kusa da ita..nan da nan ya fara kakalo mata hawayen munafurci atake yana hawayen yana cewa Vicky am soo sorry i yelled at you.. dan Allah kiyi hakuri dani kidena kuka..ur tears its breaking my heart...

Cikin shessheka tare da jin tausayinshi aranta tace am sorry for being selfish femi..i promise i wont ask you again Allah ya baka lafiya

Sosai ta bashi tausayi aransa yabi ya rungumota jikinshi yahau rarrashinta Har sanda ya rudeta tay shiru ya tayata ta saka kayan baccinta kafin nan ya fita...

Bayan ficewarsa Wani sabuwar kukan ta fashe dashi tanajuyi akan gadonta tanajin kamar amaida hannun agogo baya izuwa lkcin da bata ma aureshi ba dan kuwa wann yanayin bakaramin nauyi yake mata aranta ba..

Juye juye kawai takey a dakin tanata tunanin makomar rayuwarta altho femi yace mata an bashi wani sabon magani yanasha duk da haka sai taji Kasa iya runtsawa sam.

Wajajen karfe daya na dare bayan ta amsa wani strange Email tadatagani a private email box dinta ta fice daga main room dinta tajeta dayan dakin ta fito da sex toys dinta tayi using dinsu suka dan rage mata zafi snn ta iyayin bacci.

Fannin shema'u ma kusan sai dare ta koma gidanta tana Allah Allah goben nan yay domin ta cire hadiza acikin wann damuwar datake ciki koba komi akwai tausayi dan hadiza kamar yar uwarta ce kamar yadda suke daukar kansu dukkan grp dinsu subiyar din nan da amana.
#SURAYYAHMS 08060712446
PLEASE AND PLEASE AYI SHARING DINSA...
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_


⏯️2️⃣1️⃣


Wajajen 11 na dare saura shema'u marafa ta dawo gidanta dake herbert marculay way lokacin mijinta engr mahmud harya gaji da jiranta ya fara bacci, tana turo kofar dakin ta hangoshi akan gadon can a matse ya rufe jikinshi da lallausar bargo tundaga sama har kasa alaman baccin daukarsa kawai tay badon yaso ba, ajiye jakarta kawai tay akan tabl snn tabi tacire takalminta a sulale cikin sanɗa tawuce bathrum din sharp sharp ta kimtsa kanta, snn ta dawo ta kwanta ajikinshi ta hau juje juye dan hnklinta da tunaninta sam ba'a waje guda yake ba tuna irin kalar tarwatsa taron mata dazasuyi gobe da ita da hadiza wajen tuntsirar da lamarin auren ramatu ex minister da Alhaj kyari acikin ruwan sanyi wanda hakan yasakata ta shiga saukar da murmushin mugunta dan tasani sarai aikin wann Alfa din bana wasa bane yanaci sosai.

Ta jima tana sake sake aranta dan tasan sai ta shiga rayuwar hadiza ta temaketa sosai kafin nan ta iya samun cikakken Amincewa tare da bban matsayi awajenta harta more dukiyar nata itama.

sai can data gaji da lissafi snn ta matso jikin mijinta ta mannu dashi sosai,lumshe idanunta tayi tana sauke ajiyan zuciya mai sanyi sanin cewa yakamata yau din ta bashi kulawarta ta musammn amma tuna cewa yana gajiyar da ita a duk sanda sukayi wata mu'amalar aure yasata jin bazata iya ba dan batason wani abunda zai kawo mata tsaiko a shirinsu na korar kishiya ita da kawarta hadiza maitama dan ta wann hanyar ne kawai zata samu wani matsayi na musammn a zuciyar hadiza.

Ahnkli ta dora kanta akan kirjinshi tabita dora hannunta jikinshi ta mamayeshi bada jimawa ba bacci mai nauyi ya dauketa, tun daga yanayin rungumar datayi masa acikin baccin zakasan cewa tana cikin kwanciyar hankli anata auren tare da kuma kwanciyar hanklin samun irin rayuwar datakeso din daga wajen mijin nata.

Washe gari da kyar ya tasheta dan suyi sallah amma kuma juyi kawai take bata farkan ba har ya dauro alwala ya wuce kasa izuwa masallaci domin gabatar da nashi sallahn asubahin, dan Al'adace agareshi a kowani asubahi in ya fice sallah daga nan yake zama yay karatun qur'ani snn yay morning azhkar dinsa har sai gari ya fara haske snn yake dawowa cikin gida, idan kuma bada wuri zai je aiki ba daga nan masallaci gidan motsa jiki yake wucewa, already ya riga ya saba duk sanda ya dawo cikin gidansa walau daga masjid ko daga gidan motsa jiki,kode ya tarar da shemau ta fice aiki ko tana shirin yin hakan sam bata fiye kulawa dashi ba as usual a koyaushe dai mai aikinsu hafsat ce take tarbansa.

Daga cikin masallacin ana kammala sallahn subhi engr na idar da Shafe adduoinsa yasa hannu ya dauki wayarsa ya hau rubutawa shemau sako dan daga nan wajen motsa jikin zai nufa.

Kwana biyu sam basa fiye spending time sosai ba aransa yana mugun son samun nitsuwa da ita koda bamai yawa ba.

karar bedside alarm ne ya tada shema'un daga Barci, agogon tajawo a kasale ta duba time taga har karfe shida dede mika hannu tay tanamai tattaba dayan gefenta wani uban sanyi taji aranta dataji har yanxu mijinta bai shigo ba dan asama sama cikin gigin bacci tajishi lkcin dayake tadata.

Agurguje ta miƙe ta shiga bathrum ta watso wanka tare da alwala tazo tay sallahn 5 secnds raka'a biyu agaggauce, nan ta koma jikin madubbi ta fara tsantsarawa kanta wani irin mayyar kwalliya wanda ya dauketa kusan minti talatin wanda tun kafin ta kammalashi ma bakaramin kyau tayi ba.

After 10 minutes da gama kwalliyar tabi ta kammala shirinta tsaf ta juyo zata dauki wayarta anan taga sakon daya turo mata awaya na cewa yana matsatsin bukatarta ma'ana yana bukatar yau ta dan bashi lkcinta..Wani irin lumshe ido tay snn ta budeshi ahankli dan ita din ma aranta tanajin matsatsin bukatartasa amma kuma bazata iya fasa zuwa mission dinta na tada gurmi ba dan tasan tabbas hadiza na cikin damuwa yau din nn sosai.

Saka hannu tay akan sakon ta danna delete dan karma yazo tacemai tagani, sauri take Tana shirin dauke kanta sai ta kalla key din sabuwar motar mijintan daya siyoshi a satin nan babbar DBX jeep me numfashi, hannu ta saka ta daukeshi jikinta harna bari tsabar murna ta jefa a jakarta tanata ayyana lissafi da nazari acikin ranta na irin lauyanci da narkewar da zatayi wa mijinta intaje ta dawo.


ƙarfe bakwai saura kwata shemaun ta fito tana taƙunta a hnkli all fashioned up acikin kayan data saka,taci uban kwalliyarta da launin jan janbaki tabi tasaka wata hadaɗɗiyar leshi baki mai stone work hannunta riƙe da drop bag na kamfanin fendi,

sai bi da kafafunta gently takeyi cikin catwalk kamar bazata taka kasa ba, hadadden takalman fendi din ne akafafunta dogaye suna kyalli,inta aje daya agaba sann tabishi da daya ahankli, dan bakaramin tsini talkamin yake dashi ba,a nitse cikin wata kalar daurin fuska ta iso ta kofar kitchen mamaki taji da bataji motsin hafsat anan ba.

Tunanin tashin hanklin da yarinyar take ciki jiya bai sakata tay wani nazari ba Dakin mai aikinsu din ta nifa direct tana jajjan tsaki wanda already zazzabi mai nauyi ya rufeta tun jiya da dare.

Dan tunda safe data kira kauyensu taji muryan mamanta a wani irin yanayi mai tada hankli saikuma bata kara samunsu awayar ba sabida babu wani netwk me kyau a kauyen nasu.

Tsananin damuwa da fargaba data cusa a ranta game da rashin lafiyar mahaifyartan yasata kasa samun cikakken bacci daga ta rufe idanunta zata hau mafarke mafarke munana masu matukar tsoratarwa.

Tun Asubahin farko data farka tay sallah kuka kawai takeyi tabi ta dukunkune kanta waje guda babu abunda takeji aranta face matukar son taje gida taga jikin mahaifiyarta da bataso ta rasu ta barta itakadai a duniya bacin bata da kowa sai ita.

Duk tsoron hafsat shine kar mamanta tamutu basuga juna ba wanda hakan ne ya galabaitata hade da zazzzabin data kwana dashi yasaka yau bata samu karfin tashi ta fito kitchen akan lkci ba..

Shemau na bude kofar dakin ta kalleta ahakan datake cikin mayuyacin yanayi dan ko iya dagowa kai ta kalle waya shigo din bata yi ba, tsaki mai sauti shemau taja tanamai kada kanta irin taji haushi anrainata din nan tasaba tana shigowa dakin hafsat take zabura ta rusuna mata kasa kamar baiwarta, ganin yau batay mata hakan ba ya bata haushi juyowa tay fuuuu aranta tana cewa lallai yarinyar nan tama samu waje..wato har karfe bakwai tana kwance akan gado uwa wata sarauniya tana sharban bacci ko? Toh ba a gida na ba kuwa..

Kitchen ta nufa neman ruwan zafi dan ta watsa mata da bata samu ba ta bude fridge ta dauko ruwan ice blocks masu sanyi sosai ta zubasu a bucket rubber ta zo dashi...

Hafsat na kwance a dukunkune batare a da ta hankara ba taji an watso mata ruwan kankanrar akanta daga sama har kasa kankarar suka fafaffadi mata ajiki, wani irin gigitaccen nishin daya taho a wahale data saki mai tsananin kangararwa har zaka dauka ko ta shide ne.

gigitaccen tsawar da shemau ta daka mata sanda hanjin cikinta suka hau rawa ahujajan ta dago kanta a rikice.

"Ki tashi Dan ubanki.
Nan gidan ubankine da zaki kwanta har karfe bakwai baki fito kin daurawa mutane abun karyawa ba..wani ubankin kikeyi akan gado

A mugun tsorace hafsat ta tashi ta rusuna kasa yanayin tsorara ta zube a gabanta jikinta na wani irin rawa rawa kamr kazar da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login