Showing 21001 words to 24000 words out of 171903 words

Chapter 8 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

760

tarukucen mutane agidan nata ba.



Ata dayan bangaren kuwa Wannan gida na meenal talba ya shahara ne sabida tsantsar kyaunsa da yadda aka kawata gaban sa da shuke shuken fulawowi masu ratsa hasken idanu,sai kuma uban tashen kima da mutunci da mijinta Dr Alhaj khaleel Abubukar yake dashi. He is a 35yr old millonaire and a medical Doctor. Vibrant, Young and handsome gashi sam baison hayaniya arayuwarshi. Shidin cikakken dan garin maiduguri ne yaren kanuri.


A jikin babban whitish gate din shiga cikin gidan nasu aka manna silver bell plate mai bala'in dauke ido anrubuta 4033 residence.

Yadda tawaje yake a kawace da shuke shuke hakama cikin gidan yake koina an tsarasa ne cikin tsafta da kwarewa dan haka mikakkiyar hanya guda daya ne zai kaika har cikin harabar gidan dake dauke da wata wadatacceyiyar parking space da aka jera kala kalan motoci na zamani.

Asalin main building din yana tsaye cur a tsakiya ne, gidan akwai filli sosai dan zaka iya zagayeshi gabaki daya hartacan bayansa batare da kakai bangon sa ba,sai ya kasance filin daketa bayan gidan yafi na gaban gidan yawa alaman su mutane ne da ke bukatar sirri a personal life dinsu.

Dik wani kele kelen Swimming pools da karamin relaxation outdoor palors da main garage da Duk Wani abu na shakatawarsu Duk anan abaya suka zuba bata gaban gidan ba..

Cikin gidan kuwa bangare hudu kacal yake dashi.

Shashe na farko na dauke da 2 rooms and a big palor masu kyau fadi da kuma yelwa.

anan shashin farko Meenal talba take da zama, Dayan bangaren shima iri dayane da nata Sedei mijinta Dr khaleel ne ke zama aciki kowa dai acikin su na da personal space nasa da room dinsa, dan meenal talba din wata iriyar murdaddiyar mace ce agidanta sam bata taɓa amincewa wai suyi sharing room da mijinta ba.

sai sauran rooms guda biyu din da suka rage ake barsu kamar quest rooms dayan room din anyishi tsarin dakin mai aiki ne amma mjinta yaki sam akawo mata me aikin sabida yasan tana da mummnan zargi aranta sosai.

Dayan room din kuma anyishi ne a design din dakin bacci da falo mai kyau musammn dan in baqo na jini ne ko na kusa da su sosai yazo.


Main palon su an kerasa ne da set din kujeru uku guda shida bakwai given a total of 18 luxurious chairs, bangare guda na wasu mahaukatan milk colour turkish royal chairs ne masu golden crown,dayan bangaren kuma wasu mahaukatan cozy lush sofas ne wanda aka kera design dinsu da silk nd velvet sai Italian sofas masu kalar brizzle brown throw pillows.

kujerun nasu sunyi matukar kawata gidan sabida da bold colours aka tsarasu, komi na cikin gidan tsaddade ne me daraja,wani irin sanyi mai dadi dake fitowa daga airmores din falon wanda shine ya kame jikin bangon falon ya sakamai yanayi me kwance gajiya sosai ajikin dan adam.

Meenal talɓa ce ta siya gidan gabaki dayansa da kudinta dan gidan da halisa ta siya a victoria island ya mugun tsaya mata arai,.tay hakan ne danta kwaco kanta daga boyayyar kishin kawarta halisa dataji ya kamata na irin daukakar datake cin karo dashi, tunda suka taso aranta sam batay tsammanin har halisa zata miƙe ta zamo cikakkeyr mace me sa'a a duniya ba, Duk dama siyan gidan datayin shiyayi silar da haryau surukunanta suke samun matsala da ita.

Hasalima a dangin mijinta babu wanda yake zuwa gidan ko ya mata magana hatta iyayenshi.

Matsalar ya soma ne ayayin da suke shirye shiryen aurensu da mijinta Dr khaleel, wann shahararren gidan nasu ya zaɓa ne zai siya da kudinshi domin ya sakata aciki, sede girman kai, hassada da son nuna isa yasaka meenal talba taje ta rigashi siyen gidan at a double price domin kawai cikar burinta da kuma son asaka gidan nasu a sunanta bana mijinta ba.

Meenal tana wani irin jiji dakanta tana kuma baza alfahari sosai da dumbin dukiyarta na gado hadi da cewa mahaifiyarta ta tarbiyantar da ita ne awani siga na sakalci da nuna mata ita watace a duniyan nan.

Meenal ta taso ne acikin narkakken daula dan haka tarbiya da iya girmama dan adam yay karanci a kwakwlwarta, arayuwarta ita kanta kawai tasani bata son wani mutum yay wani abu arayuwarsa face saida amincewarta.

She is a very controling lady, And an Emotional blackmailer. Meenal Kwararriyar Macijiyar sari ka noke ce, Zata iya tsula maka mugunta abayan idonka amma sai tazo gabanka tayi maka kuka ta nuna a duniyar Allah nan tana dare dakai dari bisa dari.

Itade muddin rayuwanka bai tsaya a iya matsayin data ajeka ba toh tabbas sai tasan hanyar da zatayi ta rabaka da Abun da bataso aranta din.

Tanada wani irin boyayyar mugun hali najin cewa duk wanda yake tare da ita dolene yakasance a kasan ta karde a fita da wani abu sann kowama yay rayuwarsa akan bisa tsarinta ba akan nashi ba.

Duk wani abun farinciki ko daukaka idan ya sameka inhar abun bai gamsheta ba toh komin shakuwarrku saitay kkri ta ruguza abun a boye. Snn haryau bbu wanda ya fahimci wann hali nata sabida yadda ta mugun kwarancewa a wajen saka fuska biyu، iyakar mahaifyarta datake dora ta akan komi itake ke lura da wann mugun halin nata.

Gidan da suke ciki da mijinta a yanzu haka nata ne, koda khaleel ya nuna bacin ransa lkcin dataje ta siye gidan sai tanuna mishi tsabar sonshi datakeyine yasa ta siya musu amma bada wani manufa ba, iyayen mijin nata kuwa sun ji baqin cikin hakan da tayi dan mahaifiyarsa ta riga ta fahimce kamr meenal din so take ta zamo itace me controlling din gidan khaleel amma bashi ba.

Anyi tashin hankli sosai kafin aurensu, da chan ma kamar za'a fasa auren amma abune da Allah ya qaddara.

Haka iyayensa sukayi hakuri suka amshe karereyin ta na cewa so ne ya jawo ta siye gidan dansu zauna aciki..

Sedai ba awani jima da yin aurensun ba Doc khaleel ya fahimce komi daga cikin munanan halayyar meenal talba.
Domin kuwa karamin sabani in ya shiga tsakaninsu haka zata bushe idonta ta soma masa gori tanamai cewa in bazai bi abunda take so ba ya fita mata agida ai bada kudinshi ta siya ba. Tay masa munanan gori irin haka a farkon aurensu yafi sau a kirga.

Intaga yay fushi zai fice sai kuma sauya kalar tausayi harta kame kafafunshi tayi ta kukan fitan rai tana wani irin rikitaccen birgima akasa tanamai bashi hakuri tana cewa sharrin shedan ne.

Haka Doc khaleel yayita fama da ita musmmn a farko farkon aurensu har abun yazo yabi jikinshi ya soma danne zuciyarsa akanta yana hakuri da ita sosai.

Sosai ya fahimce cewa Baida cikakken iko akan matarsa meenal iyakar abunda tayi niyya shi takeyi agidan bata damu da hakkinshi na aure ko wasu abubuwan da yake so aransa ba.

Iya abunda ke cusa mai tausayi aransa shine sanin cewa meenal tana mutuwar sonshi aranta bana wasa ba, inkomai zai kasance masa karya a duniya amma son da meenal take masa shikansa yasan na gaskiya ne, duk sanda yace su rabu koda a wasu ne to babu shakka abubuwa mumunana ne yake biyowa baya. Sau tarin yawa yaso ya rabu da ita din tunma kafin aurensu amma meenal intaji hakaan rikicewa takeyi, takaiga hatta poison saida tasha dan ta mutu akansa. Tabbas Zata iyayin komi domin mijinta amma saukar da kai da biyayya ne kawai bazata taɓa iya mashi ba.


*********
Tun barinsu asibiti meenal take juya tunani dayawa aranta, 4:30pm dede driver ya iso da ita bakin gate ya danna horn mai gadi ya taho a guje yana kkrin budewa, dagata glass din windon motar ta hango motar mijinta Dr khaleel atake fuskarta ya sauya tahau yamtsusahi acan kasar wuyarta taja wani irin takurarren tsaki.

"Barka da zuwa hajiya
Allah ya temakeki.Allah ya tsareki..."

Mai gadi ne ke miƙo gaisuwa cikin rusunawa da girmamawa amma ko kallo bai isheta bare ta amsashi.

Saida driver yy daf da zai shiga ciki snn tace stop a dakilance cak ya tsaya awajen.

Glass taja ta wurga wa me gadin wani irin kaskantacce kallo baisan lkcin daya sunkuyar da kansa kasa ba.

Dauke kai tay sann tace
"Kai me gadi..Yaushe Doctor ya dawo gidan nan??

Bakinsa na bari bari ya budi baki yace Allah ya temaki ki hajiya ai Baima fi mintina 20 da shigowarsa ba.

Daga nan batacemai komi ba ta maida glass din motar ta rufe sann ta umarce driver daya juya yakaita office dinta kawai
Dan aranta tasan dolene in tashiga ciki zasu samu matsala dashi aranta tasani sarai dolene mijinta yanemi ya bukaceta duba da kwananta goma sha bakwai kenan tana can gidan halisa suna shirye shiryen biki hade da kwana biyu da sukayi a asibiti..

and if ders one thing she hates very much shi ne sex a aure. A nata ra'ayin
Gani take kamar yawan bawa namiji sex shiyake kawo raini tsakanin miji da matarsa. Besides tafison ana kwana da itane ayayin da take bukatar hakan bawai idan mijinta yana bukace ba.

Meenal is a chronic feminist at heart dan bata fotowa fili ta fada amma kuma tsarin rayuwartan bisa akan haka yake tafiya ba karya .

Itadin irin matayen nan ne da suke da ra'ayin cewa mace da namiji have equal right, in zatay girki shima dole yayi, in zai gaisheta zata gaishe shi, in zata kwana dashi dolene sai tayi ra'ayi. Awajen ta namiji ba shugabanta bane bare kuma tay jagora da shi, yadda zaiyi yadda yakeso da rayuwarsa haka itama zatayi da nata rayuwar but deep down inside her heart she still expects him shidin ya kasance tamkar wani bawanta, as handsome and rich as he is awajenta babbanabun alfaharine agareta taga tana juyashi sosai, so take ya saukar mata da kai ta mulkeshi while he humble down and worship her needs and desires as his wife a duk lkcin datake son haka...
Atayani sharing izuwa grps grps da kuke ciki please.

08060712446 chat surayyahms direct.
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_


⏯️6️⃣

Kananan tsaki mai tafe da takaici meenal ta dinga jerowa akan hanyarsu ta barin herbert marculay street na anguwar nasu,duk tagaji jikinta nayi mata nauyi nauyi amma batajin tana bukatar wani hutu,nan da nan ta umarce driverta ya wuce da ita inda babban companyn business na mahaifinta daya rasu yake dake itake take juya komi yanxu...

munafikar motartance ta shigo harabar babban gininsu na Talba group of companies,wajen masha Allah,irin doguwar gidan saman nan ne mai hawa sama da talatin, suna shigowa cikin harabar kamfanin wayarta ya hau ruri batare data dauka ba sede yay kusa katsewa snn ta dauka ta kara a kunnenta.

Driver cikin suit dinsa daya yafi kama da na security shi ya fito ya bude mata kofar car din, tun kafin ta juyo da kyau ta kallesa Hannunta rike da tsaddaden wine colour iphone dinta sai waya take calmly kamar ba itace take jajjan tsakin nan ba.

A lokacin kusan Kowani ma'aikaci ya tsaya still ne ana jiran ta, wajajen after 5mints ta aje kafar ta a kasa ahankli...akan wata 5 inches higheel shoes take taku daddaya ana biye da ita da sauran tarkacen ta cikin juya bountiful body structun ta mai daukar hankali.

Masu aikinta ne ajere sun tsaya cikin formal work dresses dinsu ana miko mata gaisuwa duk dama mamakine a akan fuskarsu ganin ta shigo office yau a kurarren lokaci.

Tafiyan ta take As usual ko kallo basu isheta ba bare ta amsa gaisuwan nasu da suke jefo mata, a cikin kwanciyan hankali take takunnata har ta shiga cikin Babban office dinta dayagaji da haduwa.

Jakarta ta soma ajiyewa snn tasauke karamin ajiyan zuciya tana zama akan soft leather chair dinta wani wayar ya kara shigo mata,takai mintina talatin tana amsa wayar daya sake shigowa din anan ma har ta kammala bata daga ido sama ta kalle files din dake gaban desk dinta ba.

Sauke wayar datayi ke da wuya tadauki office telephone ta buga waya cikin muryan ta na gadara tace ma female seceteryn ta akan shigo ciki marmaza" ,ba tare da ta jira amsarta bama ta katse wayar ta dangwalashi snn ta mike tsaye tanata kallon kan teburin dake ciki da takardu na ayyuka dake jiran dubawarta da saka hannunta akai.

In not less than 3 minutes aka turo kofa sai dai mutane biyu ne suka shigo kusan a tare

Hajiya zainab magajiya wato babban business partner dinta da mumynta ta hadasu sai sectarynta fadila sum sum tana tahowa abayanta.

Dan takaitaccen kallo meenal din tabi su da shi snn ta dauke kanta ta nemi waje ta zauna cikin kamewa tana watsama fadilar mummunn kallo.

Hajy zainb batace komi ta sama ma kanta wajen zama itama tana bin fadilar da mugayen kallo na kurilla kowani lungu da sako na jikin fadila sai data kalleshi tsaf tsaf

Sai snn tace hajya meenal talba?

Meenal ta dago kai fuskarta ba asake ba cikin sauke ajiyar zuciya tace "Barka da shigowa hajya magajiya..ganinki ai yafimini ganin gwamna aynzu,..ashe dama kina kusa dani kika kirani awaya.

Hajy zainab tay murmushi tace dont mind me. Kinsan batun harkan kudi ba wasa
....tana fadin haka ta juya ta kalli fadila sama da kasa ganinta kyakkwanr budurwa danya sharaf nononta dumu dumu a sama sun tsaya cur tana hango cikarsu daga cikin rigar suit dake jikinta wani irin balamin asirtaccen ajiyan zuciyane ya kufce mata tabi tay control cikin shan qamshi snn tace" "ita Wann kuma wata kuchaka ce haka meenal,
Tunkan meenal ta amsa tay wani rau da ido tana dada checking din fadilar da gefen idonta..wani irin shocking na sha'awa taji na mata yawo a jinin jiki..ta wani kame numfashinta ta ciki"so whats she doing here duk ta ishi mutane fa da kallon kauyanci..".

Kafin meenal ta dago kai ta amsa akaro na biyu taji sautin good evening maam..Da barin jiki cikin daburcewa fadilan tafada tana dan kame kame. Take meenal din ta dauke wuta tanamai kallonta a kyamace tace "pls dont speak!!!!!

Ta kalli hajya zainab muryanta a shake tace "Itace lazy sectary na danake gayamaki shirmen datayi min dazu..

Hajya tay rolling idanunta cikin wani irin yanayin kisisina snn tace ohhhh..

Da masifa meenal ta rufe fadila.

"wai meye nakeji manager na gayamin wai haryanzu karfe biyar na yamma na neman gaucewa amma wai baku kammala ayyukan ku ba?...

Cikin yanayin gyara tsayuwa Fadila tace

"Ammm.."Am sorry ma'am,dama munata jiranki ne kizo kiyi signing wasu takardu since last 2 weeks..and our calls have not been picked by u shiyasama bamuyi aiki akan wasu files din ba..sorry maam.. ta fada a ladabce tana dan rusuna kai a tsorace.

Cikin kwaiwayon muryanta Meenal tace yen yen yen yen our calls have not been picked by u.. mtchewww Wann din har wani dalili ne? .And so what in ban picking calls dinku ba..,how dare u distub me while am preparing for my best friend weding..and why are u interogating me like dis,wato nice zan bar abunda ke gaba sabida picking calls dinki ko are u mad?..who the hell did u think u are girl?wani tsawa ta daka mata tare da wurga mata files dayawa a kasa snn ta koma ta harde hannu sannan tayi jim tana binta da banzayen kallo.

Ahnkli fadila ta rusuna tana kwashewa jikinta a sanyaye sosai.

...cikin azzalzalan masifa meenal tace ki tattara tasss kisan yadda zaki yi dasu, duk wani investor dake wajen ki tabbata kin dawomin dashi kan harka since is ur fault da lokaci ya kure mana. I dont care what u have to do, just do it. inma karuwanci zakije kiyi inma mutuwa zakiyi i dont care..All i care about is my business.
Tafada tana watsa mata harara masu zafn gaske.

Fadila ta rasa meke mata dadi idanunta atake suka ciko da ruwan hawaye sosai,cos how isit her fault bayan ta yi iya bakin kkrinta hasali meenal din itace ake jira ta saka hannunta akai amma batazo ba taje bikin halisa so tayaya kenan yanzu komi ya dawo lefinta.

Da kyar ta shanye kukan takaici da gajiya dake kkrin shakureta snn ta miƙe tsaye da files din hannu tay shiru batace mata uffan ba.

"U think u can come here and play around with my business don kinga ana yaba ki kin iya aiki ko?
Toh wallh Muddin bakiyi abunda nace miki kiyi ba korarki zanyi.

Hade ido sukai da fadilar tawani ja doguwar tsaki tace mata "jaka kawai doluwa. Agaggauce fadilar ta dauke idanunta tay dashi can kasan zuciyarta na mata susa.

Daga nan shiru tay kanta na kallon kasan bata sake ko motsi ba, har sanda zucyarta yadanyi sanyi cikin tunowa da wani abu aranta yasa ta sauke ajiyan zuciya snn ahankli tace pls am sorry maam..kiyi hakuri dan Allah...a sulale cikin sanyin jiki tabi ta tsuguna har kan gwiwar ta tana rokon meenal...

tabbas farida ta fi kowa jajircewa wajen bi da manyan contracts dinsu duk da some of the rude and arrogant business men and inverstors din basu mata da dadi, wasu har tayin karuwanci suna mata,wasu su zageta tas wasu subita da maganan banza shiyasa in abun ya ishe saita ta dan cire hannunta akan aikin ta barwa meenal din abunta duk dama tasan zatasha buhun barkonon masifa da kuma baqaqen maganganu.

Hajy magajiya sai kallon fadila take tanajan tsaki while aranta jarabbiyr shaawar yarinyar ne ya gama rikitata sosai، sai can snn tace" sorry for urself, kinci sa'a ma kina da What it takes kinemo abunda ogarki tace if not da koninan da saina saka ankoreki yau.

kan fadila na kasa bata ma fahimce me take nufi ba tanadi kan basu hakuri bata damu da mesuke cewa ba,babban damuwarta aynzu shine yadda zata aikta abunda meenal ta umarceta tayi na shawo kan investors wayanda jinkirin yasa suka janye.

She have no one att all da zai tsaya mata duba da mahaifiyar meenal dince dakanta ta siyota a kauye da kudade a wajen mahaifyarta tazo birni ta sakata tay karatu bayan ta kammala snn a kawota nan tanayi wa yarta meenal aiki.

Fadila batada katabus arayuwanta bare tacewa dan tamkar amatsayin baiwa take musu, dan haka komi da meenal tace mata dolene tayishi komin muninshi dan bata saurara mata ko kadan.


Bayan tulin cin fuska da Banzayen maganganun su da kyar hajiya magajiya ta rokawa fadila arziki tanamai cewa kibani ita muje gidana na kawai tamin wani aiki intana da wayo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login