Showing 132001 words to 135000 words out of 171903 words

Chapter 45 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

796

amma ke dakike yar uwansa kece zakina Bashi dama yana jefa kansa acikin hatsari na abokan banza?

Are u even aware that young men living in the same house is toxic? Idan nile yabi abokinsa ya fara shaye shaye fa,ko yafara jansa suna kwana da karuwai?? That lucio or wateva, can be a gay, or a thief or drug dealer i just dont like him around nile.

Tsabar ranta ya baci da ihun dayake mata akai cikin tsaresa da tsawa tace "Ur likes does not matter sabida rayuwar kanina ne bana ka ba so you cant control his life like dis femi..Tsabar abun yaci mata rai hawaye kawai ta zage tanayi agabansa muryanta har na rawa rawa tace yanxu akan wann maganan da baifi muyi shi acikin fahimtar juna ba kake min irin wann tsawar?

Da gadara a muryansa yace "Na isa ne..zan kuma miki magana a duk yadda na ga dama bcos i am the man here. Iya abunda nace miki kiyi shine kawai zakiyi..

A zuciye Tace in banyi ba mai zaka iyayi me zaifuru femi? Ina de fitar dani zakayi agidan nan..do it do it mana...ka fitar dani ko ynxu dan alkcin ne zaka gane cewa Ur everything is worthless to me.. dan da arxikina ka ganni ka aure ni iyayena kuma ba matsiyata bane bare kace kaine ka musu komi rayuwar kanina ne kawai bazan kyaleka kayi controlling dinsa batare da wani kwakwaran dalili ba..so u can go to hell..do ur worst, ka fitar da uwarka agidan nan ma bare ni? Bata hankara ba taji saukar maruka har biyu tasss tasss akan fuskarta saida ta kusa kifewa kasa agigice.

Jikinsa har na bari jamar zai tattakata ya matso kusa da ita yana diri yace how dare u talk about my mother..ke ki shiga hanklinki fa.. this is a warning to u vicky tunda kince rainani zakiyi then fine...aje ahaka..nile da abokinsa zasu zauna tare amma karda ki yadda na sake naganin ki agidan sa koda a mafarki ne.

I forbid you frm going der tunda ke bakida da hankli ni ai ina dashi. I think i will just talk to ur mother directly regarding his safety.

Yana fadin hakan ya kama hanyarsa fuuu ya fita ya barta cikin wani irin yanayi na hajijiya dan tunda ta zube kasa kuka kawai takeyi har aka kira asubahi bata iya runtse idanunta ba.

Gaba daya ta rasa ma'anan borin dayay mata yanxu she dint even realise cewa its just an emotional manipulation.

ya zafafa maganan ne dan ya dorata a matsayin me laifi dan ace yana iya bakin kkrinsa akanta da yan uwanta itace kawai bata gani.

Tunda ya barta anan bai sake waiwayota inda take ba da kyar bacci ya kwasheta da asuba ta farka da wani irin zazzabi tare da jiri wanda hakan ya jawo bata iya fita wajen aikinta yau ba.

Ko awa biyu batay da kwanciyar ba Karar wayarta ya tadata a firgiceta farka ta jawo wayar da kyar batare da ta duba waye bane ta saka a kunnenta ahankli tace "Hello?

firgita ta mikie zaune dan da wani irin muryan bacin rai mahaifyartan ta tare dashi tanamai cewa zata tona musu asiri.

Duk bayanin da vicky take kkrin mata bajinta takeyi ba dan jiya acikin daren femi ya kirata har yana kuka.

Yace mata vicky tana masa gori snn tana nuna masa cewa shi ba jagora bane ga rayuwar kaninta nile, ya juya maganan yace ai beisan lucion bane shiyasa ta tanbaya amma vicky tazo taci masa mutunci harda zagin maman shi, yace musu sei abunda taga dama take masa agidan
..ya gugguduma karya wanda yasaka iyayen vickyn suka amince dashi sosai...

Washe gari da sassafe yabi ya turo musu da makudan kamar wanda baiyason kudin yanamai kuma basu hakuri akan karsu yi ma yaransu fada akansa.

Bakaramin tausayinsa sukaji ba aganinsu femi is doing too much for vicky amma bata gani.

Kalar masifa da bakaken magana da mahaifyarta ta gaya mata akan wann maganan har saida taji zazzabi ya rufeta.

Kuka kawai ta wuni tanayi akan gadonta harta soma tunanin cewa bazata ma kara zuwa gidan nile din ba tunda yanzu iyayenta sun nuna mata cewa sun fi amincewa da zantukan mijinta akan nata.

Mahaifin nasu shine ya kira nile ya masa fadan akan daya duba lamari femi da zuciya daya sedei dayake yana mugun son danshi a matsayinsa na dan auta shikan lallami ne yafi yawa atanashi fannin basumasa fada sosai kamr yadda sukama vicky ba.

Ata fannin Femin kuwa dake yasan be kulla gaskiya ba tun dayay ma vicky hakan da sassafe ya zille yajeshi hutun wucen gadi a abuja wajen dadironsa chief okoro.


Ata fannin engr kuwa tunda yaji shiru hajy bata dawo ba adan dolensa ya koma ga hafsat datake kuka ajikin radadin ciwon rashin mahaifyarta ga rudewar sabuwar aure da aka mata ma bazata
Ga makudan yunwa dayagama nakasa ta.

Da kyar ya lallameta da dukkan haqurinsa har tadan sha shayin da snack din aka kawo musu dakin, sede tana shan shayin batakai rabi ba cikinta ya dinga murdawa haka ta dinga kwaxa masa amai seda duk yabi ya rude ya rasa yadda zaiyi da ita gashi dare ya nitsa gidan yay shiiru sukadaine suka rage wanda basu kwanta bacci ba.

haka ya lallame zuciyarsa ya kuma cire kunya aransa gabaki daya yafara kulawa da ita sosai, nan yay moping floor din snn ya dawo ya temaka mata ta cire kayan jikinta duka ya mata wanka da ruwan dumi snn ta sauya izuwa towel ya wanke mata fuskarta da bakinta ya dawo da ita kan gadon ya kwantar da ita.

Itade a sama sama take jin abunda yake mata kanta na juyawa bisa gajimare, Lokcin alluran ne kawai yana famar wainata bata cikin hayyacinta ma bata san meyake faruwa da ita ba.

Zaman diris yy agefenta yana bata baki har bacci ya dan saceta ta kwanto ajikinshi nan da nan duminta ya mamayeshi kafin kace wani abu ya samu ya runtsa kadan.

Bacci suka kwasha Har wajajen karfe shida da rabi saura na safiya basu farka ba. Dan juye juyen datakeyi ajikinshi da sunan ummanta yasaka ya firgita ya tashi yanata kallonta ashagale ganin towel din gabaki daya ya zame daga kan kirjinta .

Cikin lymshe ido da budewa yay sauri wajen zare jikinshi anata kafin nan ya gyara mata zaman towel dinta ya dada gyara mata kwanciyarta ya mike tsaye ya shiga bathrom da sauri sauri yay alwala ya fito.

Ahankli ya fice a dakin batare da sannin kowa ba dan duk abubuwan daya faru ajiyan cikin daren sune suketa dawowa masa a idanunsa har bai tabbatar makansa ko zai iya sake hade ido da yarinyar ba... daga masallaci bai dawo tanan ba ya wuce gidansa direct yana isa dakin shemau ya nufa ya samu tanakan sharban baccinta hanklinta akwance.

Karasowa yay ya tasheta dan tay sallah suna hade ido ta wani gallara mai harara acikin gigin baccin tacemasa taji..yana ficewa tay banza da shi ta cigaba da sheka baccinta. Shima bai wani jima da kwanciya anasa dakin ba wani nannauyar baccin gajiya tay awon gaba dashi...
SHARE .
[2/8, 11:31 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB*_


BY SURAYYAHMS.

BONUS PAGE FOR ALL COMENTERS❤️💋
The same morning 6:am

Karfe 6 na safe halisa ta farka a hankali ta buɗe idonta tareda saukarwa akan littafin da Dr khalid yabata dake yashe agefen pillown datake kwance domin tana karantawa idan zatay bacci akowani rana..

..maida sanyayyun idanunta tayi tana dada lumshewa cikin tuno da abubuwan data tsinta acikin littafin jiya. Ta kusa 6mn a haka sannan ta ƙara budesu a hankali tanamai furzar da iskan bakinta tana turo sulbabben kafafunta saman floor din room din tanamai ƙara sauke ajiyar zuciya tareda tura hannayenta cikin lallausa kuma kwantacciyar baqin sumar kan ta daya barbazu tana murzawa a hankali sannan ta tashi zaune ahankli.

kayan bacci ne ajikinta Dark leafy green colour masu kyau da taushi kallo daya zakamar kasan tsadadde ne mai daukar hankali.

Da kayan ajikinta ta sauko Direct toilet ta nufa tana dan jan ƙaramin tsaki dan har yanzun kanta bai bar mata ciwo inta farka a bacci ba, da shi take kwantawa da kuma shi take tashi gashi sam batason ciwon kai ko kadan.

Ta kusa shafe kusan 40mn a toilet tana wanka daure da bathrobe ta fito sai dan handtowel tana tsatsane ruwan dake makale a jikinta.

Direct gaban vanity table tanufa ta zauna tare da jona hand drywr ta fara drying din sumarta..

Taci kusan mintina talatin akai tana famar tattalashi da mayukan gyara Bayan ta gamane ta sharce sumar ta kamashi duka baya sai kyali yake da daukar ido dan har da spray din gashi mai qamshi duk yau ta daure ta fetsa masa shi sannan ta fara shafama jikinta lotion da creams masu kyau da bada fuska kariya daga hasken rana ko ina ajikinta sai da yaji bayan ta gama shafe jikin nata ta samu wata pink matte powder ta dan murzama kyakkyawar fuskarta snn ta shafa ma labban bakinta glassy gloss Tay lining dinsa dan kadan..

Kallonta kanta tay acikin madubin sai taga still kamar ba ita din bace data sani. dan aydda take rayuwarta adacan kafin zach ya shigo ciki awajen kwalliya ma kawai takan yi awa guda tana aikin tsantsarawa fuskarta bare kuma wajen saka hadaddun kaya classy and stylish Wanda duk inda ta wulga mata da maza duk sai an juyo ankalleta tsabar iya dressing din nata shiyasa alokacin datay sana'ar modeling bakaramin suna tayi ba.

Sede ayanxu neman ma shaukin yin hakan takeyi a zuciyarta inda gabaki daya ta rasashi.

Hatta tsayawa yin kwalliyar na neman gagaranta dan saita fara sai taji mummunan kasala yana sauka mata agabobin ajikinta hakama kwata kwata batajin sha'awar yin wani dressing mai nauyi.

Kallon kanta take a mirrorn tana tunowa da maganan da Dr khalid din yay mata jiya, she knew she can't dwel in her past thinking about all the things that hurt her. duk dama abunda zach yay mata shine silar da yatsokalo mata dukkan wani abu mummuna data binnesu abaya.

Duk sanda take kallon kanta agaban madubi haka kawai sai taji ranta yay mummunan baci. Daga baya kuma sai ta rasa haushin kanta takeji koko na abunda ya faru da ita amma yaudin seta cize bata kyale zuciyatta ya raya mata hakan ba.

Duk wani abunda Dr khalid ya gaya mata jiya a asibitin shi ta dinga tunawa aranta, sede kalamansan sunyi karancin tasiri a zciyarta domin brain dinta yana samun saukine wajen fassara kalamai masu manya manyan ma'anoni.

She feels like she need sumting stronger and fiercer, in form of words ko actions, kawaide tanason wanda zai gaya mata wani abunda ba ta taɓa rarrashin kanta dashi ba ko wani bai taɓa gaya mata irin kalmn a duniyan nan ba.

Daga bisani kamar an tsikareta ta miƙe tsaye tay gefen gadonta ta dauko littafin nan sann ta wuce kan lallausar couch dinta dashi.

Tun jiya data dawo daga hidimar hadiza iya rubutun Dr asim khan kawai take karantawa akan yanayin tunanin dan Adam amma ta lura kamar da akwai citations na wasu authors din aciki dan haka take so dubawa aranta gani take kamar in littafin bazai mata wani amfani ba ajiyewa kawai zatayi ta soma neman wani mafita.

Mikewa tay tana tafiya kamar dawisu dan halisa Doguwar mace ce mai daradaren hazel eyes ga kuma hanci har baka Masha Allah,gashin idonta da na girarta kamar ta saka na kanti dan idan har baka santa ba sai kace kullum sai ta saka ma idanunta eye lashes.

Kwayar idanun nata is dark brown in colour mai mai aciki dan har wasu ce mata suke me vampire eyes..

daga ita sai bathrobe dinta ajikinta ta zauna a nitse akan black couch din tare da bude chapter seven na littafin direct dede inda taga wani sabuwar topic mai taken "female and fragility" dukkan nitsuwarta ta tattara akai tana kkrin karantawa.

Author din bai gabatar dakansa a farkon shafin ba amma ya bar sako wa duk wata ƴa macen datake cikin yanayin kunci da rauni.

Idanuwanta ta zuba akan sakon kamr wa ita kawai aka rubuta, nan da nan zuciyarta yahau karanta mata kalamomin anitse kuma ahankli sosai
_Dear, my Fragile heart_
(Yake zuciya mai rauni)
_Here are some lessons i learned about my life_ .(ga wasu darusun dana koya daga cikin rayuwata) kisani:

"Kowani dakikanin numfashi dakike shaka a duniya lokacin kine yake karewa ko kinyi amfani dashi ahanya me kyau ko bakiyi ba...

"Kowa zai mutu, kema zaki mutu, har da wanda kika sani da wanda baki sani ba. Lokcin mutuwa ne kawai baki sani ba.

"Akwai Abubuwan da kudinki bazai taɓa siya miki su ba.. kamar lafiya, soyayya da kuma farin ciki da kwanciyar hankli.

"Dan kinyi imani da Allah bashine zai hana Allah ya jarabbeki da kunci da kuma rashi ba....
jarabawarsa soyayya ce me girma...( Yakan iya zamowa miki Kariya, ko hani da abune wanda baidace dakei ba, ko Allah zai baki wanda yafishi alheri )

Murmushi halisa tay adede nan wajen ta dada nutsuwa akan rubutun tanamai cigaba da dubawa cos is making alot of sense to her a matsayinta na wacce batada cikakken ilimi akan babin imani da qaddara a addinance.

Cigaba da dubawa tay kalma nagaba yace

"Dukkan abunda kike so a duniyar nan daga inda kike har izuwa wani lkci mai nisa akwaishi yana jiranki...amma in naki ne zaizo shi dakansa ya sameki, ko ke zakije dakanki kisameshi komin nisansa.

"Sa'a tare da Qaddara mai kyau takan iya zamowa jigon rayuwar mugun mutum, haka ma wahallen rayuwa da qaddara mafi muni yakan iya faruwa da mutumin kirki sosai.

Love is the greatest gift of all...

Anan ta tsaya da karatun Batare da tacigaba da karantawa ba ta kure rubutun da idanunta tanamai sauke ajiyan zuciya mai nauyi acikin yanayin tunanin makomar rayuwarta cikin sanyin yanayi...

"Good things can happen to bad people and bad things can happen to good ppl is actually the most relatable word acikin wann write up din dayafi shigewa mata har cikin bargon kashinta.

Mafi akasarin lokuta tasha tambayar kanta shin metayi wa Allah da qaddarorin rayuwarta ya kasance mai wuya da tsauri.

But with this words she understand that maybe haka law of nature yake bawai akanta ita daya bane hakan yake faruwa tunda har an rubutashi.

Ta jima azaune tana nanata wasu daga cikin kalaman a brain nata musmmn data fara gane cewa kamar each time she stays in pain chance dinta na neman makanta farin ciki kawai take batawa dan ta lura kamar babu wani wanda zai iya bata abunda take nema a duniyan nan wanda shine kwnciiyar hankli.

Karanta chapter 7 din nan sosai ya jefa brain dinta acikin tunanin rayuwarta all over again and again kofofin brain nata nayin tunani da suka dan toshe a sanadiyar karsashin damuwar datake fana dashi ahankli suka fara buduwa tanamai kkrin amfani dasu.

Da sauri ta kuma bude littafin zata juya shafi na gaba sai taji karar knocking daga bakin kofar dakin nata

Kallon kofar tay duk da ma tasan waye ne amma sai data dan nitsu After like 5 min tace"
..Yes come in".

Uztaz ne ya bayyana cikin shirinsa na bakaken co-operate suit yasha wanki da guga kamar kullum ..Idanunsa masu sanyi ya zuba mata da alaman yasha mamakin ganinta a zaune da littafi a hannunta alaman tana karantawa.

Yana sauke karamin murmushi Yace gud morning maam kin tashi lafiya?

Ahnkli ta kallesa fuska ba yabo ba fallasa Tace gud morning, and what do we have today..

cikin gyaran murya yce "your Breakfast is ready den zamuje muga likita by 9:30 Snn yau akwai general meeting a office na kamfani tare da manyan share holders na kamfaninkina mansa cosmetics dana takalma da kuma clothing materials.

Batace mishi komi ba har ya ciro Wani file daga wata jaka daya riko ya mika mata yanamai cewa "maam i think this woman is upto sumting.

Ahnkli ta kai idanunta ta sauke akan file din snn ta budeshi ta karanta kadan tanata kallon hoton matar, can ta dago ta kallesa tace ..."Mrs florence ogumka?

Yace yes maam..

Juyowa tay a nitse snn tace mishi.. Meke faruwa??

Yace maam, wann matar Itace take insisting cewa sai kin zo wajen meeting din da za'ayi yau, snn tay broadcasting sakonni to all the members of board na kamfani ta kuma kira media house amma nace mata baki da lafiya sede kamr bata fahimci hakan danace mata ba.

Halisa ta dauke kanta cikin ayyana wasu abubuwa aranta sai can tace Tana damunka da tambayoyi akaina ko?

Dan Shiru cikin son ya boye mata details din yace "yes.but forget about her ma'am kananan magana ne kawai na mata da be shafe aikin mu ba karki damu evrything is under control now.

Karamin Murmushi ta saki snn ta mike tsaye da file din a hannunta, tace uztaz kenan...uve truly done enuf for me. Amma basai ka daukar min wann cin kashi ba dan bazaka taba fahimtar halin wasu matan ba

Mrs florence ogumka is well knwn igbo business woman, ta taɓa auren mahaifin zach basu jima ba ya rasu so bata haihu dashi ba,tun ranar da tasan muna soyayya da step son dinta take sakamin ido sabida tasan zach yana da kazamin kudi wanda mahaifinsa ya bar masa gado da nashi shikansa.

She believe all my money is a scam..karamar yarinya dani da babban kamfani..infact Tana daya daga cikin matayen da suke ganin cewa budurwa kamana wacce bata da asali bazata iya neman halak dinta ba sai inta bada kanta ma maza. Kudin mahaifin zach da bata samu gado aciki ba shine bata son ni in auresa in haihu dashi in samu...but wann ba damuwata ba amma nasan sirrikanta akaina sosai.

Yanxu da aurena ya fasu dashi so take kawai ta batawa kamfanina suna snn ta kunyartar dani agaban other investors namu awajen meeting by asking me alot of personal questions about my broken weding with her ex step son zach

tanason ta shirya labarin karya snn ta gayama duniya cewa akan kwadayin kudi zach kawai ya rabu dani..,
then,she wll watch me loose my integrity, my company will also loose its value. Intergral investors Zasuce da kudin karuwanci na gina shi. Kaga idan na raunatu na fadi kasa sai ita ta saye kamfanin gabaki daya ya dawo nata.

Nannauyar ajiyar zucya ne ya kufcewa uztaz cike da mamakin jin ahakan daga gareta yace nima nayi tunanin hakan sabida tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login