Showing 42001 words to 45000 words out of 171903 words
kife wasu yan iskan irinsa basu lalata ƴayan sa ba sabida abun ai kamar bashi ne..humm amma dai kin bibiya kinji inda gidan saurayin nata yake kuwa? Karma ya kasheta da cin gindi azo a sakani a salalar tsiya ohh ni nadiya na shiga uku..ai na manta shafff cewa ubanta ma ashe gindin wata matar aka cire gawansa.
Arazane da labarin meenal tace kai mummy kamar ya ya mutu a gindin mace, mekenan ya kasheshi dadin gindin ko wuya?tafi karfinsa ne.
Hajiya nadiya tace a'a yadda dai naji ance wai yaje ya danne matar kwabcinsa ne toh ashe mijinta yay musu asirin makalewa dake ya jima yanajin labarin cewa sunayin sex din bayan idonsa,ashe wai yanama zargin cewa yayan nasa da ita kaf na baban fadilar ne bana shi ba.
Meenal da bata taba jin wnn labarin game da fadila ba cikin mamaki tace ikon Allah ji wani kazamin rayuwa Tirrr.."ni ina zan san gidan saurayinta mummy..ni walhh ko kallo bata isheni bama ashe ashe dai da jinin karuwanci ajikinta no wonder mana Hajy zainb tacemin wajen saurayi ta nufa hala tuntuni taga siffar karuwai ne ajikinta.
Hajya nadia ta dan yi shiru sai can tace toh kidai kwantar da hanklinki Amina koma ina fadila ta shige zatama dawo ai..nima in sha Allah xuwa anjima jirginmu zai taso amma a Abuja zan sauka, maybe if i get the chance zanzo na dubaki cikin satin nan..rmbr we have alot to talk about.
Meenal tace okay mumy i cant wait to see you wallh abubuwa sun fara min yawa a lagos din nan yanxu. I just need a good break!
Hajya tay dariya tace dont worry my baby zanzo ai, zamuje waccan beach din mu huta mu biyunmu Nasan da akwai maganganu abakinki.
Meenal tana murmushi tace toh shikenn mumy sai kinzo din.
Daf Hajiya Zata katse wayar cikin sauri ta tsareta. "Mum... mumy wait...wait....
tace yes menene kuma meenal?
Fuska a dan kwabe Tace mum bakifa ko tambaye yanayin jikin halisa ba, cm'n Dats not fair ke kam ma hala harkin mance da sha'aninta ko.
Baki bude Hajya tace auuuu, so sorry wallh mancewa nayi..toh ya jikin nata? I tot she is depressed and brain strucked ko hartaji sauki ne... haka kawai taji dariya ya subuce mata saita karashe maganan tana yar karamar dariya hmmm lamarin da bai shafeka ba ko ajikinka ta kyabe baki.
Ahankli meenal ta lumshe ido sann ta bude tace mumy kenan kema ai kinsan wacece halisa, she is the strongest woman ive ever knwn,ita ba irin wayann matayen bane masu yawan cusa damuwar duniya aransu. Tuni har ta warke abunta ta dawo gida.
Amamakance sosai hajya tace wowwww ikon Allah, really?..tabb lallai tay kkri fa..ni ai daukawa nayi tana can ayashe akan gado tanata murkususu cikin ciwon zuciya aiku yaran zamanin ne akwaiku da son cusa lamarin maza aranku shiyasa bakuda daraja wajensu sam.
Wani hummmm meenal ta sauke nannauyar ajiyan zuciya batace komi ba tay kwafa.
Hankli adan tashe hajya nadiya tace A'a What is wrong kuma Ko na fadi wani abu marar kyau ne..
Cikin sauke ajiyar numfashi Meenal tace A'a..ko daya, Dama already Doctor Ahmed jimada yacemin she is depressd ,dan lkcin da za'a sallameta nayi magana dashi privately dan nasan condition dinta, shine yakecemin wai halisa tana fama da emotional trauma da kuma chronic depression a brain dinta so harma ya tura request wajen wani babban therapist dake qasar waje wai sunan shi Dr Asim khan, yacemin in ya amsashi zai hadasu asoma mata jinyar depression dinta. amma aikinsan halisa ita bata barin hakan ya durkusar mata da rayuwarta so magani kawai ya bamu ynxu yace a rika bata tana sha akai akai kafin dr Asim din ya taho
Hajya data nitsu tana jinta harta kammala maganan,atakaice cikin sauke ajiyan zuciya tace toh hakan yay dats good.
Amma ya maganan shi saurayin nata zach dayay dumping nata kunyi wata magana dashi kuwa..
Nifa tsorona kar azo amata jinya yaga ta warke ta dawo dede ya soma bibiyarta, inkaji "khan" kam kasan indian doctor ne kuma wallh sun kwarance akan harkan kiwon lfiya, halisa tana warkewa wann karamin aiki ne awajen namiji ya biyota...kinsan inhar zach ya shiga hayyacinsa ya dawomata toh zai dawone da karfinsa wallh asirinki ne xai fara tonuwa.
Meenal Ta lumshe ido jin gabanta na faduwa, tace pls mum forget it, kina kashe min jiki wallh,zach fa ba dawowa zaiyi ba.
I mean koya dawo ma halisa ba kara kulashi zatayi ba. Nan ta hau bata labarin abunda ya faru da kuma yadda halisa take zargin ko matar kawunta ne ta aikata mata hakan.
Bakaramin sanyi da kuma mamaki hajy nadiya tasha da zach ya rufawa meenal asiri ba.
Meenal tace " kinsan dazu mune muka kaita gidanta, so sauran kawayen na kasa,sai ni na kaita cikin bayan gida zatay wanka and she was telling me how she feels abt him now,mum naji tausayinta sosai, it breaks her soo much walllh. Zucyrta ya raunatu Fiyeda yadda muke zato, Kamar nayi mata kuka datake cemin bazata kara memeta kuskeren sake amsar soyayyar wani namiji arayuwarta ba...yanzu babban damuwata shine yadda zan janyeta kwata kwata daga tunaninsa sabida banason tay doguwar bincike akan wanda ya gayawa zach labarin past dinta she wll definatly be mad at me if she knws my secret.
Hajiya tace Kedai kibar wann maganan Amina banace miki ina dawo zanzo lagos din ba?
Just give me some time to think about it..ai Allah ya riga ya rufa miki asiri ma da bai furta mata ba kijira ni nazo muyi maganan ido da ido kinji?
Tace toh mummy
Yanzu dai na iso gida we wll talk inkin dawo,wow this is 11:0 pm na dare ya banga motar miji na a parking lot ba.. tafada taba lekawa sosai.
Muryan Hajiyar ne ya katse ta tace hala bai dawo bane daga wajen aiki,just take care sai ki gaida shi mijin naki inya dawo.
Tace to shkn zaiji mumy bye. Snn ta katse wayar da sauri tare da sauke ajiyar zuciya aranta tana ta tunanin dalilin rashin dawowar khaleel gida.
Lkoci guda taji zuciyarta ya dau wuta da tsananin zafin kishi da tunanin ko hala khaleel ya yanke hukuncin soma yawon neman mata ne agari.
Da can harta dau mummunan zafi
Wani zuciyar yace mata Ba halinsa bane, sanin cewa shikam ma dawuya ne mace take burgeshi.
Nan Tay kwafa tanamai sassautowa da zuciyarta
Sai kawai Tabari akan cewa hala surgery ne ko wani meeting ya rikesa.
Zama tay tajira har Driver ya sauko kasa snn yazo ya bude mata kofar motar kafin nan ta sauko
Ahankli take takawa akan heels dinta tana bin kanta da lallami kamarma bazata taɓa taƙa kasar ba,gabanta kawai ta nufa batare da ta kalle uban kowa ba har takai cikin babban falon nasu wanda Kusan yadda ta fice ta bari haka tazo ta sameshi, tsaki taja dan tasan da khaleel ya bari ta debo masu aiki da bahaka zata zo ta tarar da gidan babu wani shara ba qamshi ba.
Bin ko ina tay da mugayen harara Aranta tana cewa Shi da ya damu dana zame masa matar gida sai yazo yana share gidan dakansa Nonsense ..Tana fadin hakan ta bubbugga kafafunta akasa cikin bambami ta haura sama bangarenta a fusace tana sauri sauri kamar wacce zata tashi sama.
Har yau mamaki take da khaleel yay ruwa yay tsaki wajen hanata kawo me aiki gidan,Altho iya abunda kawai yaci nasarar hanata yi kenan arayuwa but after then bai isa yahanata aikata komi ba dan iya Abunda takeso aranta shine kawai take aikatawa
As usual tana bude dakin baccinta nan ma wani takaici ne ya toshe mata makwagoro taja ta tsaya cak jin kamar tay kuka dan kusan ko ina a dakin nata babu masaka tsinke,kayane akasa chan da nan babu gyara babu kimtsi hatta kan madubinta towel ne arataye yana reto dan anan inda ta cire anan take barinshi bata dagawa.
Yasar da jakarta akasa tay yaje ya samu na tun last week data bari akasa bata tattarasu ba, bakin ta ta turo gaba tahau cire kayan jikinta aranta tana cewa toh shi khaleel din meyasa bazai tattara mata kayanta ko ya dan kimtsa mata dakin ba.
Tasan inbadan shi bama hala da yanzu dakin bazai ganu ba, mostly shike zuwa ya tattara kayan inya dawo da wuri daga aikinsa, saidai wann satin gabaki daya ta lura kamar bai samu ya shigo ya tattara mata kayan ba kamar ma fushi yake da ita.
A mugun gajiye Ta kammala cire kayanta ta wuce bathroom, ganin duk towels dinta sun yi datti yasaka ta dawo dakin ta daga wanda ta yasar atakan mirror dake shi baiyi datti sosai ba ta karkadeshi.
Daurawa tay ta koma bathrum ta haɗa warm bath snn tafada ciki tanamai wani irin sauke balamin ajiyan zuciya.
After like 40 mint ta fito jikinta na qamshin shower gels datay amfani dasu, suman kanta dake nan kamar na fulani ta warware ta hau busar dashi sa hair dryier, kafin nan ta koma gaban mirror ta zauna tafara abunda tafi so da iyawa arayuwanta wato kwalliya.
Lungu da sako na jikinta babu inda baiji tattali ba, kafin kace wani abu qamshin guilty absolute na paco rabbane ya gauraye jikinta harma da ilahirin dakin. Suman kanta dayaji man gashi mai qamshi ta tufkeshi da ribbon ta maida shi baya.
Miƙewa tay ta isa gaban wardobe ta bude wani gefe tanami kure kayayyakin wajen da idanunta cikin rasa na zaba tsabar yawan su. Wani Lumshe ido tay Ta janyo wanda hannun ta ya sauka akai kawai ta ciroshi akan shine zata saka ayau.
Yau Bata wani damu ba, She dont really mind in khaleel zaizo mata su kwana tare sabida gajiyar datake ji na ratsa gabobin jikinta tasan cikakken namiji kamar khaleel ne kawai zai iya warware mata shi acikin sauki.
Wani irin kwalliya mai shegen karfi ta zana wa fuskarta yadda kasan ba dare bane akanta, batare da ta damu da yanayin nittyn da hannunta ya canko ba tahau zurawa.
Irin dark shade of Pink din nan, amma plain net ne kamar rariyar tata iyakar bakin lace din da akayi kwalliya dashi ne kawai mutuncinsa amma bayan nan babu wani marabarsa da tsirara.
Ko ajikinta ta zurashi, ya mata mugun kyau sabida hadadden dirin jikinta hadi da kwalliyar data zubawa kyakywar fuskarta na tashin hankli.
Kallon kanta ta dingayi a madubi tana murmushi kafin nan ta dau turare ta kara fetsawa ajikinta wani karamin veil ta dauka ta rufa akanta snn ta kamo hanyar waje cikin sauri.
Tana isowa cikin falo ta kalle agogo ganin karfe 11:56 na neman gocewa
She just want to make sure ko khaleel ya dawo gidan amma bataga alaman hakan ba har saida ta leka can waje cin karo da motarsa awajen parking yasa ta wani sauke ajiyar zuciya da sauri ta dawo ciki
Muhawwara ta dinga zabgawa da xuciyarta wani bangaren nace mata taje ta sameshi wani nace mata ba ajinta bane ta koma gefenta kawai ta jirashi ai mayen love ne zaima biyota kodan biyan bukatunsa.
Daga karshe dai Bangarensan ta nufa tana kawo daf falonsa na can sama ta soma jin muryan Kaninsa Aliyu maska, tsaki tay ta harde hannu taja ta tsaya tanamai yatsina fuskarta dan ta tsani yan uwan khaleel aranta bana wasa ba.
Tafi minti biyar a tsaye cikin son taji me ake ciki dagata ciki dan tasan duk danginsa sunajin haushinta bakuma kaunarta sukeyi ba.
Kome aliyun yazo musu agida oho..wani shuumin murmushi ne ya kufce mata jin wani devilish idea ya fado mata lokci guda ta warware veil din data rufe jikinta dashi ta yasar ta tsaya tsar daga ita sai wann tsinannen nity din tana wani juyi tana checking kanta kanta babu dankwali.
Sadaf sadaf ta taho basuji karar shogawarta dake kafafunta babu takalmi, batare da tay sallama kawai sukagan ta kwasam ta fado acikin falon, kusan atare suka juyo suka zuba mata ido a wann yanayib datake take Aliyu maska yay saurin dauke idanunshi ya maidashi can kasa yanajin kamar kasa ta bude mishi ya nitse ciki tsabar kunyarta dayaji
Ko ajikinta ta hau murmushin mugunta ta kalle khaleel dat is in shock da karfi tace good evening baby ure back..
.,duk da karfin xcitemts din datasa baisaka shi ya amsata ba just normal ya kau dakansa tare da jan tsaki a fili.
Aliyu dake jin kamar zai nitsine yace ina wuni anty Amina, a kisinance tace ohh Aliyu dama kaine anan. Soo how u?Yasu mumy da daddy.
Kasar wuyarsa Yace fine snn ya miƙe tsaye cikin sauri ya fice waje ya basu waje agugurguje tabishi da wani irin kallo aranta tana karta dariyar mugunta.
saukar diran miskilallen sautin muryansa yasaka yace kinyi batar hanya ne ko? Girl, You need to get out!!
Tay kamar bataji meyace ba A kisinance ta wani fado jikinshi tana wani irin squezashi tana murkususu,hannunta ta dora akansa tana shafawa, uhm baby nooo, im just so glad to see u,..wallh yau na gaji...tayi sauri ta kwaco hannunsa daya dunkule da karfi ta dora akan fuskrta cikin sauri ya kwace hannun sa yamike tsaye fuskarsa a daure yace mata i wll see u down stairs,bai jira ba ya tureta ajikinshi ya sauka kasa cikin bacin rai. Ta daga ido da mamki tana bin bayansa da kallo kafin nan ta tuntsire da wani irin dariya.
Tsabar takaici idonshi a rufe ya sauko, gaba daya sai yaji yanayin shigartan ya kuntata masa aransa sai yanzu ya fahimce abunda yasa Aliyu tafiya ya barshi anan kenan kallonta yay ganin ba marabarta da tsirara,wat d hell zata fito harnan da irin wnn nity? ransa yaji ya sosu sosai..
Yana saukowa kasa ko kammala sallama da dan uwansa Aliyu basuyi ba sai gatanan ta sauko itama. A daddafe aliyu ya wuce quest room ya barsu wani harara ma ta banka masa ta rakashi saman dashi.
Tace"khaleel am asking u kamin shiru, i said why are back late? Ko aiki ne ya tsareka..ta daure ta furta kmar an roketa
...kallo bata ishe sa ba ya kada kansa batare da ya amsata ba ya juya ya koma room dinsa cikin tsananin fushi.
Tana kallon inda yabin ta dafe kirjinta Dake mata wani maqudan zafi tanaji tamkar an cakka mata kibiyar mashi daya shareta..sanda ta duba sama ta tabbata aliyu baiga hakan ba snn taji sanyi.
Sai kuma ta rasa ta inda zata saka kwayar idanunta da suka rine bayan yay banza da gaisuwarta yana nufin haka zata daure takalla annoyin fuskar dan uwansa agida gobe ne ?
Girgiza kanta tay cikin turirin nunfashi mai karsashi tace toh wallh bazai yu ba..fuuu ta wuce room dinsa dan ta masifeshi snn taji dalilin dayasaka yazo da aliyu gidan har zai kwana batare da izininta ba.
Acikin kunnenshi ta bude kofar dakin duk da tunani mai nauyi da zuciyarshi takeyi bai hanasa shaqo yanayin shigowartan ba,
waje ta nema ta tsaya durus tana kallonsa dan bazata iya cewa dason ranta ta biyo bayansa awannan lokacin datakeji kamar ba a cikin hayyacinta take ba.
Rashin iya bude idanunsa dayayi yasa wajen ya dauka da wani irin shiru sam Shigowartan bai katse masa tunanin datazo ta iske shi yanayi ba,tun daga ranar auren sa har izuwa yau inyatuna,wasu sukance sukanji kansu kamar a saman gajimare tsabar kwanciyar hankli da farincikin ranar auren su amma shi haryau baisoma jin wannan farin cikin ba,aure dai yasan yana cikinshi da wacce yake ganin kamar yana so amma bazai iya cewa zuciyarsa a nitse take da aurensan ba, shiyasa ma sam ya kasa gane ma kansa bare ma ajega ya fahimce bala'in dayake ciki da matarsa meenal.
alot of times in his heart yakanji matukar dana sanin auren ta,saidaii tabbas akwai wani bangare a zuciyarsan datake hanasa tantance komi saiyaji kamar eh dagasken sonta yake yi kuma bazai taba iya rabuwa da ita ba,shidai yasan acikin Rudani yake rayuwarsa na aure yau Ko meenal ta fahimce shi ko bata fahimshi ba oho, shikadai yasan abunda yake damun sa aransa yanzu.
Meenal dake tsaye kansa bakinta gumm bata iya ko jan numfashi kwararra ba tsabar ji dakai da isa,
kokowa yake da fushinsa dan kar zuciyarsa tayi bindiga ta fashe ya yarwatse bare ajega ya sauke mata tulin ruwan balain dayayi dako tsawon kwanaki domin ta na musamman.
Gani yake kamar Tura yakai bango,in akwai makurar karshe to tabbas haqurinsa akan meenal yakai yau,
Ji yake kamar lkci yay da zata fito fili ta gaya masa shin shi mene ne awajen ta dan bai gane metake nufi da shi agidan ba.
Karkkarfan ajiyar zuciyar daya kufce masa badon yasoba ya tursasa shi adan dole ya bude limsashu kuma gajiyayyun idanunshi wanda suka so suyi luhu luhu tsabar nauyin magananun zuci da zuciyarsan ta dade tanayi ita kadai.
Meeenal Tana daf da bude bakinta ya miqe tsaye cikin sauri mai nanike da jarumtar kasaitarsa dake saurin sakata jin yankewar gaba, a nitse ya karaso har gabanta yana kallon figaggiyar nityn data sakan up and down fuskan sa adan daure, cikin wata girmanmen muryansa data fito da yar tashen masifa har yana lullumshe ido yace
"What the fuck is this ure wearing meenal, zatay magana cikin katseta da tsawa mai razanarwa yace I have had enough of your nonsense!tunda ke baki da hankali daga yau kar in kara ganin ki awani waje agidan nan da wannan shigar banxan.. are u insane.
kaiwa nan ya dakata da maganan yay shiru yana huci, can sannan yaja numfashi game da sassauto da muryan sa kasa kasa yanai mata kallo mai dauke da tsantsar comand da nuna ya isa.
Ji take kamar ta yanke jiki ta fadi kasa dan Ta mugun tsanar namiji yay mata tsawa aydda take ganin darajarsu dayane bai fita da komi na duniya ba dan haka bai isa ya mata ihu akai ba.
A mugun raunane ta sadda kanta can kasa tana kkrin danne zucyarta.
Da gefen idonshi ya kara jefo mata wani kallon aransa yana ta mamakin Yanayin ta yace"ohh ok i think is time for u to go park ur things ..zamu koma can gidana kawai..
Adan hargitse ta dago kai ta kallesa Tace what?
bai kulata ba yana kkrin juyawa yace "u heard me"..
Inadai dan nan gidanki ne nan yasaka kike min abunda kikaga dama to nima ai ina dagida..
Yunkurin juya mata baya yake bayan ya kammala furta hakn sai caraf ya tsinceta agabansa a mugun masife har jikinta na rawa, kwayar idanunta ya kalla yaga wai har sun rine sunyi wani rau