Showing 93001 words to 96000 words out of 171903 words

Chapter 32 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

785

Wanda sanitary pad ne aciki da pants,har cikin ranta taji tsananin kunyar hakan but she know have to do quick tun kafin ya dawo.
Share to ur groups.
SURAYYAHMS 08060712446

[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_

⏯️2️⃣2️⃣

Da kyar hafsat ta mike snn ta tattara bedsheet dinta lalatar a hannu ta shiga bathrum dinsa dasu,babu bata lokci ta hau wanke jikinta tabi tasaka sabon pant da pad din daya kawo mata lkcin tsananin fargaba duk ya cika mata kirji tanayi hannunta na ɓari dan gani take kamar shemau zata iya shigowa yanzu ta kamata.

Abatasan ya zatayi ba ta zabge jikakken kayan dake jikinta agaggauce ganin ya gama lalacewa da jini ta hadashi tare da zanin gadon sai ta jawo towel din dake wajen ta daura shi bisa kirjinta.

Kayan data lalata ta tattaro a hannunta tana rungume dasu tafito cikin dar dar da jin tsoro ganin He is still not around bai dawo ba hakan ya bata daman falfalawa da uban gudu ta shige dakinta dasu tay sauri tabi takulle kofar dakin tareda jingunuwa da bayan kofa tanamai sauke nannauyar ajiyan zuciya.

Har Saida ta dan samu nitsuwa snn ta karaso ta gaban jakar kayanta ahankli ta tsuguna ta bude zip din tafara ciro wasu kayayyaki ayan kayan sawarta da kwata kwata baifi kala biyar ba

Wani doguwar rigar kwanjo abaya baki ta jawo ta zurashi ajikinta snn ta aje kayan wankin datazo dasu din agefe sabida zazzabin dake cin jikinta yasa ta kwanta bisa kan gadonta dan kuwa sosai cikinta shima ya balle da azababben ciwon har ji take kamar itama mutuwa zanyi.

After 1hr ta farka jin kanta na mata nauyi duk saita kasa iya budesu gaba daya idanuntan sunyi sanyi sunyi wani luiii jikinta gabaki daya yayi lagwas kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi saboda azabar yunwar daya gama nakasa ta.

Tana daga kwance ahakan Batasan anshigo dakin bama bare ta gane ko waye ne ,ji tayi an dan taba goshinta alaman ana feeling tempureture inta wni nishi ta sake sai taji kmr mutum ya zauna agefe da ita. Dada kame idanunwata tay sabida tsananin kunyarsa data somaji aranta, all She can feel is his scent and warmth dan haka taki sam ta bude ido ta kalle shi da kyau.

Waya ya kammala yi da likitan da zata zo ta dan dubata,kafin nan ya juyo, Kallonta yake yi while his face isnt showing any emotion Har likitar tazo ta dan duddubata,iya Allurai kawai akamata snn docton ta rubuta mata magani ta fita.

Nan da nanbbacci me nauyi yay awon gaba da hafsat all she know is hartay nisa cikin bacci yana zaune awajen yana dubata batasan kuma yaushe ya fita ba.


Daga ta fannin Gidan hadiza kuwa yadda kasan anyi mata mutuwa haka ta kasance da bacij rai dan ko Abinci yau bata iya sawa abakinta ba harsaida shemau tazo kafin nan tadan sake jikinta tay wanka harta danci abinci wani karfin gwiwar ya jiyarceta.

Yau daurin auren mijinta da ramatu ex minister dan haka gaba daya bata cikin mood ,shemau ce ta dinga bata baki tana danneta wanda iya kalamanta na sanyayawa shiyasaka tadanji sanyi harta warware suka tsunduma cikin shirin Abinda zasu yi.


***************

A fannin doctor khalid yau ma still aikin daya wuni yi kenan wato jiran saƙon go ahead daga wajen Dr asim akan case din halisa wanda har yanzu bai sameshi a waya ba. Da kyar da wuya yaji labarin cewa Abuja doctor ya tafi.
yasha matukar mamakin jin hakan saidai aransa atake ya qudirta cewa hala maqiyinsa khaleel ne yakeson ya kwace masa slot din jinyar halisa mansa a wann karon ma, gashi ya riga da ya dora buri mai yawa akanta izuwa yanzu.

Tun bai tabbatar da zancen ba zuciyarsa ta dau zafi da khaleel ya hau jin mugun haushin sa yanaji kamar ya kashesa.


Tsaki ya wuni yi yau a offishinsa, minti kadan zai dau waya ya kira abokansa da suke da alaqa da board sai kaji yana buga kirji yana cewa Khaleel yana kishi da shi.

Last call din kenan daya shigo wayarsa ya dauka ransa bace yace Hello Doctor wasiu... Dagata dayan bangaren wanda aka kira da wasiun yace

"khalidi why are u calling me like dis naga 10 miss calls dinka wani abu ya faru ne ata wajenku?

Fuskarsa a daure Yace "eh mana.. wani abu mummuna ya na shirin faruwa dani, i just call to let you knw that Dat dr khaleel is a very wicked man,i swear to god he is evyng me kuma zan dauki mummunan mataki akansa inbe dena shiga harkata ba.

Da mamaki a muryan Dr wasiu yace meyafaru haka what did khaleel do to you now khalidi?hmmmm Acikin watan nan sau nawa kake kawo maganansa arent u tired?

Cikin katseshi da ihu yace " i am not, i cannot be tired this is getting out of hand.. da mamaki sosai dr wasiu yay shiru yanakan jinshi "..can you imagine an bani aikin therapy akan wata babe yaron nan yaje Abuja yanaso yahana Dr asim yay min aproaving just bcos he knws i am better than him in this hospital?a zafafe yace See Wallh yaron nan bai isa yaga bayana ba fa. U ppl shud help me take his matter to the medical board of directors azo ayi mana sharia ya gayamin mena tsare masa da baison ganin cigabana.

yaron nan yasakoni agaba da hassada ni bansan meye tsakanina dashi bafa ...

Doguwar ajiyar zuciya DR wasiu yaja dan yasan ba haka dr khaleell yake ba sam... snn yace is okay naji but u knw what?..


Yana huci Yace what??

A nitse Dr wasiu yace zan kiraka anjima let me first talk to DR ASIM and confirm first.

Yace okay wasiu but you must do sumtin oo cos i knw khaleel is behind His silent, nasan shine yace masa karyay min aproaving aikin yarinyar nan..i just knew it.

Agajiye Dr wasiu yacemai calm down khalidi..will call u later..

yana fadin hakan ya katse wayarsa baima jira amsarsa ba,nan shima ya jefa nashi wayar a silent yana mai sakin masa tsaki dan already ya riga yasan shirya maganan kawai yay amma ba gaskiya ba, ire iren gaba da baqin ciki irin hakan is now very comon yanzu a tsakanin ma'aikatan gwamnati.

izuwa yanzu kusan kowa yasani cewa shine yake nuna tsananin hassada da kishinshi akan khaleel boro boro amma sam yaki amincewa da haka.


A fannin vicky kuwa yau tun da isa schl babu abunda yake fado mata aranta face yadda business dinta ya soma tafiyar hawainiya nazarin new stratergy takeyi wanda zai farfado da ita, sede a duk sadda ta fara lissafin hakan sai nazarin zaman aurenta hade da strange email din nan ya dawo mata cikin ranta.

Game da boyayyar email din Suspect dinta na farko students dinta ne sedai a iya zamanta a makarntar haryau dai babu wanda ya taɓa samun private email dinta bare ta tabbatar dan is highly encrypted and confidential irin wanda ba a samunsu a sauki sai insune suka bayar da hannunsu.

Wani zuciyar raya mata yake ko wani babban mutum ne yay mistaken personality yake mata magana batare da yasani ba, ko kuma hala mijinta ne dakansa ya batta da kamanni yake son ya gwadata.

Ta balain jimawa da wann nazarin aranta bata wani samu saida ba saida kirar kaninta nile ya shigo.

Jin wayarta na ringing ya sata sauke Nannauyar ajiyar zuciya sann ta dauka muryanta adan sanyaye tace "Helo nile, whats up, how far?? Hows work today, did u need anything frm me?

Sautin Muryansa mai bala'in dadi da sanyi ta shako yana murmushi dan aduk sadda zai magana sai ya nitsar da kanshi sosai snn yake fitar da kalaman acikin sanyin kasaita da nitsuwa.

Yana murmushi me sanyi yace "hey Sis..im gud sorry i call u at work.

Gyara zamanta tayi tanamai cewa no no ba komi fadi meke tafe dakai..did u need anything?....

Ahankli Yace no......
shiru yy sai can yace
Sis its about ur husband.

Tun bai karasa maganan ba cikin tsaresa tace ohhhh yesss i totally forgot dama femi yace min na hadaku.

...cikin datsar numfashinta yace sister vicky hold on Ina fatan bake kikacemai yana kulawa dani ba...

Zata budi baki cikin haderai yace sister vicky i told u am fine Meyasa zakina daga hanklinki akaina,.inyace baison na zauna masa agida ba wani abu bane u dont have to force him to take care of me in return banason abunda zaije ya dawo mana abun raini.

Idanunta dake lumshe ta bude snn tace.."Nile is not what you think okay..i swear to you ra'ayinsa ne. Altho yace min is a way of making me happy please nile ka yadda dani nifa ban gindaya masa komi akanka ba.

Ajiyar zuciya ya sauke yace shikenan to naji amma...cikin katseshi da magiya tace please nile..kayi hakuri ka kyaleshi ya maka abunda yake da niyya din sabida already yafara tunanin ko zakace ya tsaneka and he doesnt want that to affect our relshp..Kayi hakuri nasan kafi karfin ana kulawa dakai amma tunda hakan zai kawo mana zaman lafiya just let him do this.


Tun da tafara maganan nile baice komi ba ya lumshe idanunsa yana lissafin abubuwa dayawa aransa. Gani yake kamar har yanzu basu fahimce waye shi ba, dan Shi namiji ne dayake bala'in son yaga yana zaman kansa tare da dogaro da kansa wanda hakanne yasaka shi acikin jerin mazajen da sam basuda kwadayin abun duniya arayuwarsu. Duk wani Abu dayakeso na rayuwa yafiso ya sameshi ne da guminsa bada gumin wani ɗa namijin ba besides a iya zamansa dayayi a kasashen waje he belive dat kowani dan adam yana da ra'ayin kansa.

Duk abunda Prince femi falana yay masa agidan sa ranar shi baima dauki abunda zafi har haka ba ..

Daurewa kawai yay yabar maganan aransa badan komiba sai dan sabida samun cikakken kwanciyar hanklin yar uwarsa victoria dan bakaramin kaunarta yakeyi aransa ba.

Ahankli ya bude lumsashun idanunsa jin tanakan lallamarsa, murmushi yay snn yace mata karta damu Bakomi
Ya amince.

Sosai taji sanyi aranta daya fahimce ta, dan Hira kadan sukayi nan yake sanar da ita cewa mijintan har ya aiko masa estate developers da yamma zasu zaga dashi gari su nunamai gidan da zai kama masa yana zama aciki instead of zaman da zainayi a hotel.

Murna vicky ta dingayi tana ta suggesting masa ire iren gidajen zamanin da suka dace dashi irin wanda akwai enough bedroom spaces,fully loaded kitchen and gym da swimming pools da bar dan tasan mijinta yana da kudi sosai zai iya kama masa kowani irin luxurious estate to his taste.

Shidai kawai binta yake yana azzama hirar dan ta saki ranta taji dadi amma har ransa bason hakan yakeyi ba, muryanta cike yake da xumudi da murna shikuwa a kwakwalsa yagama tsara yadda zai dauko wani abokinsa da sukazo nigeria da shi dan su zauna a gidan tare.

Ahaka har suka kare hirarsu awayan bai yadda ya gayamata abunda yake shiryawa aransa ba sede sosai ya sakata ta kwantar da hanklinta akan maganan kafin nan kowannen su ya cigaba da abunda ke gabansa

*******
Daf ana kkrin kiran sallah azahar hafsat ta farka babu wani karfi ajikinta sabida azaban yunwar data kwana ta wuni dashi.

Jin bazata iya daurewa ba yasata sauko kasa rike da kanta dake mata wani irin nauyi da ciwo.

acikin yanayin jiri ta daddafe ta kai kanta cikin kitchen dan sauran Breakfst din data dafa ma mijin shemau da baici ba shi ta dauka ta nemi waje ta tsuguna tahaucinshi da sanyinshi ham ham tanata Allah Allah ta kammala ci ta cigaba da ayyukanta tun kan shemau ta dawo ta rutsata.

Hannu a baka hannu akwarya take tura abincin abakinta kamar wata yar gudun hijira, kafin kace wani abu har zufar hucewar zazzabi tareda gushewar yunwa ya fetso mata a saman goshinta nan da nan tafarajin kanta dama dama.


Cikin dauriya tare da azama ta soma gabatar da ayyukanta data bari, jin gidan ya dau shiru yasata bari aranta cewa hala Ficewa sallah ko kuma wajen aikinsa yaje.

Tunda ta kama bakin aikin babu abunda yake dawo mata aranta sai tausayinta da kuma temaka mata dayau yayi wanda yakamata ace da shema'u ce a matsayinta na mace kuma lawya me kare hakkin dan adam zata kyautata mata haka amma ina sai aka samu akasin hakan agareta.

Tunda take bata taɓayin tsammanin cewa akwai masu kudi irinsa masu tausayi da kula talaka irinta ba, barema a matsayinta na yar kauye wacce batayi karatu ba har ace namiji hadadden kamrsa ya bata lkcinsa wajen teimaka mata, Itade sosai wann abun ya bata mamaki aranta bana wasa ba..

a wani bangare na zuciyarta kuwa tsoro mai balain yawa ne ya cikkeshi dan tasan idan har shemau taji wann labarin to hala kasheta kawai zatayi ba zallan korarta a aiki ba.

Dukufa tayi akan aikinta cikin azama da dauriya, dan Iya Tunanin daya debe mata kewa kenan kafin kace wani abu harta dafa musu spaggeti jollof na dede iya bakinsa dan already suna da soyayyen kaza ga kuma kifin sardines dan haka dasu kawai tayi amfani bata wani yi mintu goma ba abincin ya nuna ta saukar.

Fiye da rabin Abincin ta juye masa a warmer da ake serving dinshi takai kan dinning table ta jera shi a nitse.

bayannan kitchen din ta dawo ta dauki wanda ya rage a tukunyar ta kankare kanzon ta cinye shi a nitse duk da baida yawa amma sai taji cikinta ya cika babu laifi.

Kallon agogon dake kitchen din tay ganin karfe biyune harda rabi na rana,tunanin me zata dafawa shemaun ta hauyi dan tasan izuwa karfe shida na yamma ko takwas na dare zata iya dawowa gida, itade a iya Kallon datakeyi ma tsarin rayuwar shemau sai taga kamar kwata kwata bata dace da mijin da Allah ya bata ba.

hakan take ayyanawa aranta ayayinda take kkrin kimtsa wajen datay aiki sabida taje ta huta kafin yamma yay ta sake fitowa. Ta kammala wanke tukunyar ta kifa kenan Kakkarfan sautin Gyaran muryansa ya dakatar da ita abazata ta waigo ganinsa a tsaye yasata kusan daburcewa tana me shirin rusunawa cike da ladabi da biyayya tanacewa "san..sannu da dawowa Alhaji.

Tun kan ya amsata ta tsaya a daskare chak kamar wacce akayi freezing tana kallonshi dan ko iya dauke idan ta akan sa batayi ba.

haduwar sa da hasken fatar sa is flawless nd faultless..

Duk a tunaninta yay nisa bayanzu zai dawo gidan ba sai taganshi gatsau acikin wata sabuwar shiga datamai kyau bana wasa na, Sanye yake cikin kassaitacciyar collection din fitted jumfa na voile material kalar cool custard yellow da hadaddiyar hular zanna bukar me laushi a kife akansa duk Alamu sun nuna cewa Suman kanshi is silky black and shiny plain,askinsa low cut ne amma is very carved and stylish dan haka har hasken fatar kan na nunawa sosai..

Hannun sa daya dafa kofar kitchen din ta sake bi da kallo inda ta cikaro da wata xpensive clive cristian watch dake makale a tsintsiyar hannunsa tana wal wal sann kafafun sa sunsha takalman alfarma.

Tunani tafarayi aranta ko shirin tafiya wani kasar yayi.

Kasa nitsuwa tayi dan gaba daya ya tsura mata idanunsa cikin rudewar kallon tsaf dayay mata for the first time arayuwarsa.

Kanta ta sauke kasa tayi shiru ganin har yanxu bai amsata ba kuma bai dena kallonta ba alkcin ko kwakkarn motsi ba ta iyayi bare tari.

Hafsat karamar yarinyace sosai amma ALLAH ya albarkaceta da jikin manya tana da cikakken hips tare da madaidaitan nonowarta da yanzu ne suka soma fitowa sosai, ita ba fara bace sann bakinta bai shiga wacce za'a ce dashi Baki wuluk ba,

Daidaituwar shape din Karan hancinta ya samo kyakywan asali ne tun daga Shatin kerarren Sajenta wanda yabi cikakken giranta masu dauke da dogayen eye lashes.

Alkcin kusan Duk abunda yakeji aransa na rudewa haka nan ya kaucar fuska ba yabo ba fallasa yace mata "ya jikinki?

Ahankli ta dada sunkuyar da kanta for the moment tana sauraran bugun zuciyarta duk abubuwan da suka faru dazun ne suka shiga dawo mata daya bayan daya atake taji kunya ya rufeta.

kakkauran sautin muryan shin ne ya daki tsakar kwalkwarta har yasa ta saki siririn numfashi, ji take tamkar kirjin ta zai fado kasa tsaban tsanan ta bugunsa..not withstanding sai ta daure ta amsa cikin sanyin murya mai tafe da tsoro tsoro aciki tace..jiki na da sauki, Sannu da dawowa.. duk de ta rasa me zatace, sai can yaga ta sulale kasa ahankli bisa kaan tiles cikin sanyin jiki muryanta na rawa rawa tace Alhaji dan Allah kayi hakuri bisa abunda ya faru dani dazu, nasan ban aikata maka daidai ba, ka gafarceni kamini rai karka koreni a aiki na maka alkwari bazan sake ciwo agidan nan ba.

Acikin wata rudaddaiyar kuka ta karashe magiyar duk atunaninta hala zai mata masifa tunda bata tabbatar da cewa acikin masu kudi akwai masu saukin kai da imani kamarsa ba.


Kallonta ya dingayi yanata mamakin furucinta aransa harta kammala rokonta da magiyar datake masa tay shiru baice mata komi ba.

Sai can snn ya hade rai ya soma mata tambayoyi duk dama tanajin mummunar shakkarsa amma bata sake ta gayamai cewa shemau ce ta hanata zuwa duba jikin mahaifyarta ba amma duk wani halin ciwo datake ciki tay masa bayani dalla dalla.


Binne kanta kasa kawai tay tanata kuka marar sauti jin yadda yake mata fada acikin sanyin murya mai tattare da nasiha aciki. Yaune karo na farko dataji wani mutum mai kudi kamarsa yana mata magana acikin sassaukar harshe batare da hantara da cin mutunci ba.

"Ce mata yake ba a wasa da umarnin iyaye, bare ma uwa da Allah ya daukakata sama da kowa. Snn yaja kunnenta yace mata karta sake boye musu irin wann damuwar idan yana damunta dan itadin kamr Amana ce agaresu shida matarsa tunda duk wa'adin zamanta dasu anan gidan sei Allah ya tambayesu akanta ranar gobe.

Jikinta sosai yay sanyi tanata kuka tana bashi hakuri.

Kamar a wasa taji yace mata inane garin naku..tun bata kammala shako ma'anar tambayar ba, yasake cewa maza ki tashi yanxu ki dauko kayanki driver yana jira awaje ni zanbi na ajiyeki acan saiki dubata.


Jikin hafsa harna bari ta dago ta kallesa da wani irin yanayin tsantsar mamaki da ya mamaye fuskarta dan jin kanta tasomayi kamar a mafarki.

Godiya tafara masa tana sauke hawaye kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login