Showing 51001 words to 54000 words out of 171903 words

Chapter 18 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

768

days har tana ganin kamar ba ita bace yanzu.

Feeling soo weak ta lumshe ido kadan ta bude ta kuma sauke ajiyar zuciya sau uku ajere,maganganun doc Ahmed jimada ne ya soma dawowa mata a brain dinta. Ayayin da yake mata bayani akan cutar damuwa wato depression.

Sunkuyar da kanta kasa tay dan Izuwa yanzu ko itanan ta gamsu da cewa tana dauke da wann cutar duba da halin data shiga yanzu..which she thinks is normal, but is not..mutum ya tuno da abu na baqin ciki ko rayuwarsa na baya snn ya fara kuka akansu yanajin yagaji da rayuwarsa is just a huge sign of a chronic mental depression.

Doc Ahmed yace mata
If sumone is depressed kullum tunawa yake da mummunan yanayi daya taba shiga ciki ko yake ciki ayanzu wanda yake ganin kamar bazai taɓa wucewa ba,ko yake auna yawan illarsa ga rayuwarsa yanamai alakantashi da nisan har Abada.

Misali kamar yadda itama yanzu takejin baqin cikin cewa past life dinta kamar wani mummuna taɓo ne ga rayuwarta wanda bazai taba wucewa ko ya goge ba.

Hakama inta tuno da yadda ta so awahale babu soyayyar iyaye batayi rayuwar yaranta kamar sauran yara ba saidai survival of the fittest game akan street.

And When ever she think about this zuciyarta yakan mata mugun nauyi da zafi sosai.

Duk alamomin depression da doc ya zayyana mata saida ta alakantasu da yanayinta datake ciki yanzu kuma alamu sun nuna shine kawai yake damunta ayanzu.

Ajiyar zuciya ta sauke cikin katse nazarin hakan datakey aranta, da can har zata shiga bathtube sai ta fasa kawai ta bude gidan shower ta shiga ruwan sanyi ta sakar ma ilahirin jikinta badon komi ba saidan sanyin ruwan dake sauka mata ya tayata sauke ajiyan zuciya akai akai kodama zata dawo cikin senses dinta sosai.

She felt really good bayan tayi hakan ta fito tanajin kanta da zuciyarta very light babu wani nauyi sosai.

gaban madubi ta wuce direct ta hau shafa mai ahankli kamar bazata gama ba, ji tay aranta kwata kwata batajin sha'awar kwalliya dan haka ta shafa mai abakinta ta bar gaban mirror din.

shirya kanta tay cikin wata oversized shirt na dolce and gabbana fari sosai irin neat white din nan, girman rigar yakai mata har kan cinyrta ta sako wani pink bomb shot ataciki ta nemi roam about sleepers na fenty mai kyau shima white ta zura akafafunta

Babu marabar Suman kanta dana buzayen asali dan shi yolo yolone baida cika sosai, tsayinshi ya wuce kafadunta kadan kuma is very dark and curly duk ta gaban goshinta sumane sun kwanta liff, har iyanxu sauran kyallin gyaran da aka mata tun na aure na nan a jikinshi dan haka har wani tsantsi yake yi yana shining sosai, da kyar ta parkeshi in a messy bun ta daure da rubber ring baki dan shine kadai zai iya tarkata matashi.

Batare da ta kawo Tunanin me zataci wa cikinta ba ta soma tunanin hanyar da zata bi dakanta danta samu saukin depression din dake damunta yake kuma sakata kuka da baqin ciki.

Drawer drawa ta soma budewa tana tarkato dukkan wasu gifts da present, flowers, da duk wani kaya dake tattare da memories din saurayinta zach tana yowa waje ta back yard dinta dasu tana jibgasu akasa.

Ita kadanta take aikinta dan tun jiya cikin dare ta bawa uztaz hutun dole duk da ransa baiso hakan ba amma haka ta nace mai tacemai yaje gida wajen matarsa ya huta intanada bukatar sa zata kirashi awaya.

Duk ma'aikatan ta na gidan ta basu hutun bacci cos she wanted to be alone kwata kwata bata son hayaniya, dan ganin yadda suke nuna damuwa da itan ma kara mata wani damuwar yakeyi aranta sai tanajin kamar duk wanda ya rabeta sai ta jefashi cikin baqinciki da damuwa.

Cikin kankanin lokaci ta tarkata komi da komi daya dangance zach hotunansa da kaya da kyautuka.

Valuable items kamar su tsadaddun agogo turarruka da manyan gwalgwalai duk tay parkaging dinsu a box ta rubuta sako ajiki ta aje a dakin uztaz, akan inya dawo yaje ya siyar dasu akasuwa ko nawa ya samu ya raba musu kudin shida su malam liman ko suyi sadaka dashi dan tasan suna da son yin sadaka wa mutane marasa karfii acewar su addininsu ne ya tanadar.

She is alwys proud of masu mata aiki agidanta shiyasa take dada ganin su da daraja dan kuwa har murmushi takanyi inta tuno da cewa Allah ya riga ya zaɓa mata nitsatsun mutane masu Addinini ya kewayeta dasu a matsayin ma'aikata.

Malam liman duk ya fi uztaz ilimin Addini dan haka yake koyar dashi qur'ani da wasu littafai kowani lokaci inbasu da aikin yi zaka ga sunata bitar karatu.

Mai kula da security system dinta kuma christian ne amma shima akwaishi da rike nashi addinin snn mahaifyarsa itace rayuwarsa sam babu ruwansa da neme nemen mata.

Its been years suna zamansu a haka agidan wani bin haka kawai zata fito ta zauna tanajin daddadar sautin kirar sallah da malam liman yakeyi a kofar gidanta dan sosai hakan yake sanyaya mata zuciya.

She Admire them in All aspect, koda ma ace akwai saɓanin dayake kiftawa a tsakanin su nayau da kullum duk dai baifi a kirga ba.


Gidan yadau shiru dake safiyace sosai.

Halisa bata dawo back yard inta inda ta tarkata kayan ba harsaida ta hadawa kanta coffe sann ta taho da gallon din kerosine da Lighter ta dawo ta tsaya agaban kayan zuciyarta na bugawa, bata kulashi ba saida ta gama tuttula keron akan kayan tanajin kamar zach din gabaki daya zata kona ba kayan ba.

Nannauyar ajiyar zuciyane ya kufce mata snn ta kunna lighter ta jefashi acikin kayan ya kama fuuuuuuuuuu ya fara ci sosai.

Haka kawai taji wani abu mai nauyi na zamewa mata daga kan kirji kamar ana narkashi.

Hawaye masu sanyi ne suka shiga sauko mata nan ta dauki cup din coffee dinta tana sha ahankli tanata kallon wutar dakeci bal bal ji take aranta kamar zach din ne aciki yake konewa.

Waje ta nema jikinta a sanyaye ta zauna akasa tare da matse kanta a tsakanin cinyoyinta cikin wani yanayi na rauni, Addua takeyi da dukkan zuciyarta tana rokon Allah ya cire mata digon soyayyarsa aranta dan burbudinsa dama mata zucyarta yake har yanzu.

Tana cikin wann yanayin
Taji saukar wani hannu mai bala'in sanyi ya dafata ta baya, a firgit ta dago Da tsananin mamaki suka hade ido da babban kawarta na modelling wato _jasmine tacha_ Da wani irin rauni jasmine ta jawo ta akasa suka rungume juna sosai dukansu sunamasu fashewa da kuka.

She was out of the country, modelling for french designers in germany saiga mummunan labarin abunda ya faru da halisa ya isketa.

Hakan ya girgiza jasmine tacha bana wasa ba sabida bayan kawayenta biyar din nan banajin akwai wanda take kaunar halisa da gaskiya da kuma amana kamar jasmine dan sun bala'in tsayawa juna ayayin da suka fara career dinsu ta modeling Atare, dan a modeling schl din suka soma cin karo da juna.

Duk dama iyayen jasmine billionaires ne amma sosai take daukar halisa mansa kamar yar uwan jini..

They have alot of memories together
Suna fahimtar emotions din junansu sosai.

Rungume da juna suka sha kukansu har saida ya ishesu snn suka sassauto.

Jasmine tafara share ma halisa hawayenta da suke sauka kan fuskarta muryanta a dishe take cewa "queen, my halsy.. are u okay?taja kumanta tace Awnn queens dont cry...cmn wipe ur tears.

Halisa tafara murmushi kadan kadan. Jasmine
Ta kalle wutar dake cin tay murmushi tace good that u burn that bastard...

Kallon juna sukayi halisa tana murmushin jin dadi ganinta,cikin sanyin mura tace tacha, you came for me? Dada goge mata hawaye jasmine tay tace "i have to"..Halsy tace thank u jasmine, ya kike..ya aikin yake tafiya

Jasmine bata amsa ba ta jawota gefe tana cewa forget about all that halsy...ni ba tambayarki abunda gayen nan ya miki zanyi ba..just let me deal with him please, i am sure i can make him pay..wallh lokci guda zan ci ubansa.

Halisa ta riko hannunta da sauri sanin how dangerous jasmine can be for men, hankli tashe tace noooo..Dan Allah jasmine kar kice zaki masa wani abu..na rokeki kiyi hakuri.

Jasmine ta mike tsaye a masife tana cewa cmn halisa, dats crab... akan me baza aci ubansa ba, dont tell me you still love him after all the embrassment and pain he caused you? Shi asuwa tsinken goge tsuliya? Mtswwww.

Halisa tace no jasmine, ni walhhi bana son ma nasakejin sunansa akaina, Banason na sake bawa lamarinsa wani attention dina..i just want to forget him Like totally..totally. but
inkuka ce zaku daukar min fansa he will surely knw and he wll keep coming after me to destroy my peace.

Karki manta izuwa yanzu wata tsinannayar dabba mahaukaciya ta je ta juye masa sirrikan dake boye arayuwata..duk wani digon kazantar dake cikin rayuwata saida yasani.

Shiru jasmine tay in shock najin haka sai batace komi sabida sosai ta soma fahimtar inda halisa ta dosa..

Ajiyar zuciya tay ahankli ta dube halisan tanata karantar yanayinta
,ta lura kamar Aranta so takema ta mance da shi a sigar da zai zamo kamar basu taɓa sanin junansu ba.

Can ta riko hannayenta cikin nata tace "What ever happen..knw that im alwys with u halisa.

cikin sauke nakasashen murmushi halisar ta gyada mata kai ahankli tana sauke ajiyar zuciya mai sanyi

Jasmine tace why are u alone.. ina uztaz?

Tace.. ya gajine jasmine nacemai yaje gida kawai ya huta..he was with me the whole time kuma fa yanada mata agida.

Jasmine Tace its okay Yanzu ki tashi muje gidana cos u cant be alone,zama ke kadai shine sai saki tunani
..see..i wont let u suck urself up in depression ki tashi kawai muje gidana

Halisa tanaki tanaso haka jasmine ta jata suka shiga motarta suka wuce gidanta dake cikin anguwar lekki ta layin da manyan mansion din nigerian celebrities dake lagos yake.

Its a cool sleeky duplex mai kyaun gaske, kana ganinsa kasan is just one of her past time houses bawai tana rayuwa aciki bane dan tanada gidaje akasashe daban daban
Masu kyan gaske.

Suna shiga cikin gidan halisa ta nemi waje akan
Kujera ta zauna, tacha ta dau wayarta tay odering musu breakfast a online
Chicken wings,burgers da salads da mashed potatoes da drinks dan ta riga tasan halissa robert mansa batashan giya da duk wani abu mai bugarwa arayuwarta dan komin baqin cikin dake damunta bata amfani dashi.

In 35 minutes Abincin safen su zai iya isowa

Halisa tanata danne dannen remote tama rasa wani channel zata kamamusu tsabar bata saba zama haka idle tana kallon tv ba.

Jasmine kam tuntuda giyarta na herrnesy xo mai uban tsada tay a wine glass, ta kurba ta kora baqin cikin zach daya cika mata kirji, snn ta fidda tabar marlboro ta kunna tsinke biyu ta miƙawa halisa guda.

Da Kamar bazata amsa ba sai can ta karba ta saka abakinta tafara zuka tana fetsar da hayakinshi ahankli.

Rabonta da tasha taɓar shima bakaramin jimawa yay ba, but akan data sha giyar ta gwammaci ta sha tabar kawai.

Kan kace wani abu wajen ya kaure da hayaki, jasmine ta taho ta zauna agefenta suka fara hira kada kadan suna busa hayaki atare.

Tambayoyi take ma halisa akan wanda take zargi game da asirinta datace an tonashi awajen zach.

Halisa was still insisting cewa hala matar kawunta ne ko kawuntan ma dakansa.

Duk wani bayanin da halisa take mata jinshi kawai takeyi da kunnen basira da kuma nisan tunani..

Batace komi ba har aka kawo musu Abincin suka zauna suna ci,sosai ta cusawa halisa ra'ayin cin abincin sosai hardai tay nasaran sakata taci sosai ta koshi zufa duk ya fetso mata akanta.

Bayan sun gama ne jasmine ta kunna musu cool music na shyne ward ta jawota tsakiya suna slow dance a tare, lokacin sosai halisa ta saki ranta tanata dariya mai tsafta bamai tattare da burbushin damuwa ko tunani ba saidai Kallon da Jasmine din take mata shine sam ta kasa ganewa sai chan ta kwace hannunta daga nata taje ta kashe music din ta jawo jasmine dake adan buge dan tasha giyar sosai, tace Hey hey jasmine,..a cikin layi jasmine tace what? Ido ta zuba mata tace why are u looking at me dat way?..meye...

Jasmine tay dariya sai can ta sauke ajiyar zuciya tace halisa kina son na fadi miki gaskiya?

Gaban Halisa yay mummunan faduwa
Tace inaso mana why not .please tell me..

Gyara zama Jasmine tay kafin nan ta dada daukar giyarta ta kurba tace are u sure...cos folks say that when they dont mean it.

Halisa tay murmushi mai cike da fargaba batace komiba danta lura kamar da akwai wani abu acikin zuciyar tacha saidai batasan meye ba wanda shine yake sakamata jin faduwar gaba sosai

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu,banda karar Ac babu abunda ake ji.

Agefe kuma Banda kurban giya babu abunda Jasmine takeyi After around like 10 minutes ta sauke ajiyar zuciya ta juyo tana kallon kwayar idanun halisa dake cike da fargaba.

Cike da seriousness ayanayin muryanta tafarayi ma halisa tambayoyi gameda kawayenta daya bayan daya kamar wata kwarariyar CID yar bincike.

Kan halisa sosai ya kulle tarasa ina jasmine ta dosa da wayannan tambayoyin nata amma nitsuwa yasata kwantar da hanklinta sosai tana amsata dan tanason taji ina zasuje da karshen zancen.

Bayan jasmine tagama tambayarta tabita sauke ajiyar xuciya dan zarginta bai kai kan kowa ba sai kan SHEMA'U DA MEENAL..

Dalilinta na farko shine kowa yasan shemau irin munafukan lawyoyin nan ne dat are so ambitous kuma jasmine tasan shema'u da son rayuwar karya ga baqin ciki tun a camp na nysc da sukayi team daya A kaduna.

Acewarta hala baqinciki yasaka shemau already ta binciko dark secrets na past din halisa dan ta rabata da samun arzikin zach dan kowa yasan kalar hankli da kudin da gayen yake dashi.

Ata bangaren Meenal kuwa cewa tay meenal tafi kowa yin shisshigi wa zach dan ko baison hira haka take janshi da surutai, jasmine tace it is obvious dat agarin hirar makircinta ne ta zazzage masa labarinki dan ta baqantaki tunda itakam kowa yasan tasan komi akanki halisa.

Nacewa da jasmine tayi dacewa tafi zargin meenal din ma shiyafi saka ran halisa ya dan baci ta miƙe tsaye tana cewa "ohhh god...ya isa haka jasmine just shut up..nifa nasan kawai dan jininku bai hadu da meenal bane yasaka kikeson lallai ki laka mata wann maganan.

Jasmine taki sam, ta cigaba da fidda mata dalilai manya manya da yasa zarginta yafi karfi akan meenal amma sam halisa taki amincewa.

A musu musu fada fada suka aje maganan.

Jasmine cikin nanata mata tace nide na gaya maki wallahi..kifara bincikar munafukarki acikin kawayenki..if not dat sly shema'u, then its Definately that "BITCH AMINA ALI TALBA".
Dan banyarda da wayann mutane biyun nan ba.

tsaki halisa taja tana jin saukar maganan wani rambatsau acikin kunnenta da zcyarta. Aranta cewa take It cant be true cos Her best friends will never ever betray her like dat, barin ma meenal..kai No way..

Jasmine bata karace mata komi ba har suka rufe chapter maganan
Sede sosai ta bar halisa cikin rikicewar tunani.

After a while tajawota sukeje swimming pool suka danyi games masu saka nishadi tanata bata labarin abunda ke faruwa a fashion and modeling industries yanzu.

Hakan ya saka halisa samun nishadi wasu labaran abun dariya wasu na abun mamaki

Ba karya she had a good time with jasmine, kafin chan sai ga uztaz ya zo.

Jasmine acikin kudi ta taso kasancewar babanta billonaire amma sam bata da girman kai

Tana ganin uztaz tafara masa murmushi..tace halsy To fa your guiding angel harya biyoki..

Dariya halisa tay.

Uztaz Ya gaishe u a ladabce yanamai sanar da ita cewa shemau da meenal duk sunzo nemanta agida yau da safe har sau uku basu same ta ba shine yace bari yazo ya duba musu ita.

Jin hakan yasaka suka kalle juna ita da tacha dariyane ya kufcewa halisar me dan uban karfi jin yadda jasmine take cewa ohhh ohh my suspects gang..kode mayu ne suna jina inata miki huduba akansu..to wallh nikam nafi karfinsu

Halisa na dariyarta tace Uztaz jirani acan ina
zuwa.

Yay murmushi yace yess maam snn ya fita.

Ajiyar zuciya haliisa tayi
Tace ma jasmine See girl i gat to go karsu fara tunanin wani abunebya sameni sufara daga hanklinsu.

tana fadin haka ta fito a ruwan ta jawo towel ta rufe jikinta dashi bayan tay drying kanta ta bushe tass snn ta mikawa tacha hannu itama ta fito suka koma can sama cikin luxurious closet dinta tana daga tsaye halisa ta zabi Wani doguwar riga mai kyau aciki, bakine highneck mai three qtr lenght amma very simple babu design ko kadan jikinshi.

Sosai ya amsheta ya mata kyau jasmine tay mata kwalliyar dole tana ta mata dariyar ganin har ta dan zube.

Bayan sun gama komi
Har bakin motar da uztaz yazo dashi jasmine ta rakota suna hira mai ban dariya suna dariyar hauka mai cike da nishadi aciki..

Murmushin uztaz har kasa boyuwa yake ganin
Yadda miss jasmine tacha tay kkri a bugu daya ta fuxgo halisa acikin yanayin damuwar datake ciki.

Dede zasu rabu suka dan Rungume junansu sosai, akunne cikin sanyin murya halisa tace mata thank u soo much jasmine i love u soo much, ure more than a friend.. kwalla ya cika idanun jasmine ayayin da kwace jikinta anata ahnkli tanata kallon idanunta tace
"i love u halsy..the queen of all the Alpha ladies in the world, halisa ta fashe da dariya..itama dariyar tay snn tace and please dnt forget what i told u okay?..Alwys rember that the cruelest betrayal will neva come from ur enemy but a freind..

Halisa batace komi ba ta gyada kanta ahankli tace thank u..i will take care!!

Daganan sukayi sallama uztaz ya bude mata gidan baya ta zauna acikin hadadden Rolce royce nata Yabi ya kunna mata Ac tare da kunna mata sautin music me dadi "unstoppable by ava max,Tunda ta suka fara tafiya ta jinginar da kanta akan chair babu abunda take juyawa aranta face maganganun jasmine akan shemau da meenal

wani zuciyar na zugata tay wa meenal din wasu yan tambayoyi amma wani zuciyar kuma yana ce mata is better tay shiru sabida zargi zai iya kawo rashin yadda da rikici atsakaninsu.

Har sunyi nisa ta bude lumsashun idonta ta dubi uztaz tace." Kiramin meenal awayrka naji inda take saika kaini wajenta.

Uztaz yace okay,baiyi wata wata ba ya kirata haka wayar yaci ringing ganin nmbrsa ne yasa meenal taki dauƙa, haka yay ringin kmar me da kyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login