Showing 15001 words to 18000 words out of 171903 words

Chapter 6 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

761

wasa ba.

Ahankli Ta bude baki zata kira sunanshi,wasu raunatattun hawayene suka sauko mata zirrrrr gwanin ban tausyi, she just want to tell sumone dat is close to her like a family irin zafin da zuciyarta yake mata ayanzu.

Atunaninta kawu zaiji tausayin yanayin datake ciki ya tausasa mata zuciyarta da kalamansa.

Zaiy magana tay saurin tsareshi da yarensu na idoma tanamai cewa

"Kawu ka rufamin asiri mu tattauna anitse kuma a yare karda yan jarida su debe magananmu su watsashi kafafen sadarwa.

Wani irin kallon raini da kaskanci ya mata tuna yadda ta taso agabansa a kaskance wai hartayi arzikin da yan jarida suke neman jin labarinta?

Wani irin hassada da girman kai ne yaji ya turneke sa,kirjin shi ya dau zafi dau kamar an dora masa itacen wuta akai.

gashi nan dai talauci, da tsinannun bashuka tare da azaban yunwa ya turmusa masa rayuwa amma wai yarinyar daya azabtar ya kaskntar itake take cikin daula ayanzu.

Baqin cikin haka yasashi tuburewa acikin dagon murya ya hangame baki dagangan yaki sam yay yaren dan barakamin girman kai yake dashi ba ya fara mata ihu da masifa yana hargagi kamar wani zai mareta.

Da hausa boro boro wanda bama iyawa sosai yay ba yana huci cikin daka mata tsawa "yace toh ina ruwa na, wann ai ke ta shafa. Yan jaridar suji mana, yo Akan me zaki tara jamaa snn kice musu anfasa aurenki.

Tana hawaye sosai a yanayinta na rauni da yaren ta dakatar dashi,

Tace "kawu meyasa haka ne, i said please please just do as i tell u...wai bakada tausayi ne ka tuna fa a matsayin ƴa nake awajenka wazai rufamin asiri inba kai ba, ynxu danake cikin tashin hankli aure na fa ya fasu ne sabida angon yace bazai aure mace irina ba kuma batare da nasan cikakken dalilin shi ba.

Kuka sosai take ta hau bashi labarin abunda ya faru ayau din, duk atunaninta koma yane aishi jininta ne duk rashin imaninsa zai tausayawa yanayinta na yanxu.

Kallonta ya dingayi da mamaki aransa Dan Tausayinta kam de yataɓa masa zucya sai dai kuma tsananin tsoron matarsa dayakeyi bazai ma kyaleshi ya dawo hayyacinshi ba, iya alfarman da ya mata shine daya sauko da girman kan ya meda mata amsa da yaren.

Duk Ya rasa me zaice dan girman kai bazai iya barin shi ya sauko dan ya l'allameta ba, dubar tsakar idanunta dake fidda ruwa gwanin a tausaya yay yaja tsaki mai kauri kmr abun bai dame shi ba yahau kyabe baki yana tafa hannu.

Bayan dan gyara tsayuwarshi da yay agabanta yaja wata balamar numfashin rashin mutunci cikin turo baki da fushi yace hmm hmmmmmm so dis is what actually happen to you?Tun kan ta amsashi yace "it is Goood for you oooo.."Haaaaaaaa,halisaure truly a curse child. Bansan mesa baki da jinin sa'a ba, ai Koda nake tare dake nima shaidane cewa babu wani sa'a tattare dake..
As simple as Just to keep a real man to urself ki aure me kudi muma mu moreshi amma kin kasa...chaii..nwanu God!! haaa!

I dont blame u oo Lkcin da kike kai mana talle a kasuwa nayi arzikine?u better go for spritual cleansing dan Abin fa ajininki yake sam sam Bakida qashin arziki saina karuwanci!

Ahankli halisa ta dago kai tanata kallonshi wani irin yanayi mai cike da tsananin takaici tsikar jikinta duk ya tattashi tsabar yadda ranta ya gurmutsa ya hautsine da fushi.

A fixge ya Dauke kansa yay gefe dashi wai danma karsu hade ido da juna yay sanyi..

halisa ta cigaba da kallonshi tana huci ahankli

Jikinshi sai rawa yake yana wani kame kame cikin kamkamba.

...yace Kinata kallo na kamar wata mayya ai gaskiya nake fada miki. Im ur uncle ooo Duk duniya wazai gaya miki gaskiya inba ni ba.
Abun baqinciki ne ace mummunan qaddararki ya jawo min asarar arziki, chaiiiii..ya kyabe baki yana jin baqin ciki aransa ya kuma cewa "haaaaa,.halisa mansa ure a deadly disease.. infact ure the corona virus.

"Uselessss..
Like doter like father.
Porvety porvets..

ubanki mansa, haka ya kare rayuwansa duka a shan giya and at the end he died uselessly like a christmas fowl....kema in bakiyi wasa ba haka zaki kare oooo..

Izuwa nan wasu hawaye sabbine suka sauko ma halisa tanajin kamar ta wanka ma kawunta kyakkwan mari akan fuskarsa, kawu bai fasa ba yahau mocking dinta yana cewa" accept it u fail ooo, u don fail, ure a loser..Yanzu haka shikenan Kin rasa wann babban hamshakin me kudin..kin ga abunda nake gaya maki ko,Yanzu wa gari ya waya kinyi kudi har kina kaurace mana mtssss ..

Na Only you be ashawo
Na Only u be gold digger
Natabbata aikin da kikeyi kenan anan lagos da har kika tara wann uban arzikin da kike ji dashi harkika guje mu akai, ynzu ne dayazo na damuwa zaki tutseni kinamin kuka da bayanin ki na banza.. hmmm seee, Dont expect any amount of pity frm me. Nide Kudina danayi asararsa nazo aurenki shi zaki lalumo kibani.. ki aje a mind dinki cewa What ever happen to you is as a result of what u did in ur life. Tsuntsun da ya jawo ruwa aishi ruwa ke doka dama kuma Bawanine yasakai ki zama lallataccyar mace ba. Just bring money and give me make i vamos "nwa stupid girl...ya fadi hakan ko ajikinshi yana gaggayara hular kansa.

Wani irin jimmmm halisa tay ta tsaya cak tanata kallon bakin kawu dake bararraka mata rashin mutunci da tijara babu ko dandanin tausayinta ayanayinsa hawaye masu tsananin zafi kamar ruwan wuta na tsilala a idanunta..

Gaba daya sai taji gangan jikinta ya dadajin zafi gabobinta na mata ciwo ta ciki.

Duk dama da yare yake mata maganan amma bakaramin raunatata kalamansa yay ba musanmn daya ambato mutuwar mahaifinta aciki kuma yake mata fatar mummunan karshe itama.

yadda yake nunawa yanxu kamar baisan meya aikata da rayuwarta ba shiyafi cimata ranta, tamkar itace ta zabarwa kanta mummn qaddara na kasancewa a karkashin zaluncin shi daya dawo mata silar lalacewar rayuwarta gaba daya.

Ko Uban waye ya cusa ta harkan talla da sakata karuwancin dole inba shi ba amma haryau shine yake gaya mata wann baqar maganan hmm Ta tuna irin zagi da dukan mutuwa da suke mata shi da matarsa idan bata kwana da namji an bata kudi ta kawo musu ba.

They did ruined her life, tana da tabbaci aranta cewa da agaban iyayenta ta taso da bazata taɓayin karuwanci ko danta ceto kanta daga mutuwa da yunwa da tagayyara ba.

Lallai saiyau ta dada tabbatar da cewa Kawu baida imani tasan kuma ya samu daman gaya mata haka ne dan kawai yaganta acikin halin rauni da neman agaji

Ranta tafasa yakeyi kmr wuta da aka dorashi a 100°c, babu abunda takeyi aranta sai dan danasanin cewa datayi abarshi ya iso wajenta ynxu, Tasan in har ta amsa shi aynxu itace da babban asara dan kuwa asirinta ne zai tonu abakinshi wanda hala zai jawo mutuncinta ya zube sosai a idanun mutanen datake hulda dasu.

Share hawayenta tay ta juya ahankli batacemai uffan ba ta koma gaban motarta snn ta dubi uztaz dake zaune agaban motar ya rafka tagumi ta kakalo murmushi tace masa hi Uztaz,..ya juyo ya kalleta idanunshi duk yay ja, raunatacen murmushin ta dada masa "tace ka bude scroll din nan ka Bani 200 thousand awajen pls.

Babu bata lokci yace yess boss snn ya bude gaban motar ya fidda sabbin bunch biyu na dubu daddaya ya mika mata hannunta nata rawa amma haka ta amsa.

Takaicin ya turnuke ta sosai tana tahowa a raunace kamar zata yanki jiki ta zube akasa.

wani zuciyar nace mata karda ta bashi kudin tacimai mutunci ta zazzageshi, wani zuciyar kuwa tausasata yakeyi yana mai tunashe ta cewa mutuncinta ya fi mata girman kai da fushin da zatayi ayanzu.

Bangaren zuciyarta mai tausasatan shiya ci nasara tana isowa ta dubi kawu karami a tsakar idonshi sann ta kamo hannunshi ta damke acikin nata,cikin zafin zuciya tace kawu ga kudi amma bana karuwanci irin wanda kake dora ni akai ba ne. wann kudin gumi na ne na halak, aiki da sana'a nakeyi anan lagos tsaftacciya ahaka na samesu in kuma Allah ya yadda karyan Dan adam yaga bayana.

..wani tsillin hawaye ne mai wani irin sanyi ya sauko mata akan fuskrta, muryanta na rawa tace kawu na dauke ka uba amma ka maidani marainiya ka tozarta rayuwana ka cutar dani snn yau danake neman sumting as little as tausayawa awajenka kana budar bakinka kana cemin ni jawo makaina komi? Kana jefamin munanan kalamai. .Toh kasani, inhar banida hakkinka Allah ne kawai zai iya sakamin akan irin abunda kayi min domin kuwa bazan taɓa yafe maka ba har Abada.

Tana fadin hakan ta damka masa kudin a hannunsa hawayenta nata zuba sosai sann ta juyo cikin sauri ta shiga mota tare da su meenal suka karasa cikin gidan hadizar kirif aka rufe babban gate din gidan.

Tsaye cak kawu yay da kudin yana jin wani iri aransa tausayin halisa na neman ya taɓamai zucy sede tun baikaiga tunani ba caraf yaji an wawaushe kudin duka ahannunsa da wani irin karfi da rainin wayo.

Juyowa yay yaga mama G ne atsaye agabansa tana huci tana kkrin cusa kudin a lalitarta,Suna hade ido da wani irin Harara mai zafi na rashin mutunci tabishi kamar wanda idanunta zai zubo kasa tana hura hanci cikin yanayin gatsinawa.

Ya juyo baki bude yace "Haaaaa Gracy what did u think ure doing Meyasa zaki kwace kudin tun ban kirgasu ba.

A hantare Tace kaida Allah matsa can, na kwace.. kudin ka ne ko nawa...abi no be ask u to go and collect am?

Kusan a rude Yace grace are u mad,ki kawo kudin nan fa...

tace naqi na kawo inkana da karfi kazo ka kwace mana banza shashasha bijimin Alade.
Ransa a bace yace
Nine alade ?
Ni kike cewa bijimin Alade.? Grace come here,
Kokuwa suka fara ta tureshi ya fadi kasa ya buge kugunsa yasa ihu wayoooo yahau ihun sunanta Mama G, Grace, Grace, grace, gracyyy grace ooo,see ehn Karki soma tunanin zaki ci kudin nan ke kadai fa i swear to god raba dede zamuyi, a rikice ya dada cewa graceeee. kiris ya rage ta gwabje masa baki dan A masife ta dakamai tsawa tana cewa da Allah tafi can wawa kawai Zaka tashi ka wuce mutafi ne ko na tafi na barka anan.

Masifa takeyi tana juya dirin jikinta da Allah ya zuba mata tana tafiya tana cewa zaka ga raba daidai ai, mtsww...tulin basukan danaci akan muzo nan lagos kana nufin dama nine zan biya maka? Hmm dama na jima banci gasashen naman alade ba,muna isa zanje wajen Ozor mai gashi ya min hadin naman fresh alade da yasoyashi sann abani da sassanyar giyan burkutu kwarya biyar. You Menza, U will neva taste this money ooo..ko nera biyar bazaka lashe ba, Fadin hakan datayi yasa tahau murmushin jin dadi.

Baki bude aka bar kawu dan tun Kafin ya amsata ma har ta kama gabanta tana neman masa nisa a gurguje yabita da gudu yan jarida suna binsa abaya domin neman karin bayani akan rayuwar halisa amma bai iya basu wani hadin kai ba.

Motar kasuwa me kyau sukabi sukace akaisu tasha domin su dau hanyar Benue.


Ata fannin halisa kuwa kusan ajere motocinsu yay parking a cikin kantamemen mansion din hadiza dayay kama da aljannar duniya tsabar haduwarsa dan wani irin neira aka narka awajen tsarashi.

Abunda ya faru da ita hade da maganganun da kawu ya gama gaya mata atake suka taru suka damke mata hanyar fitar numfashi gangan jikintane ya gume da wani irin zazzafar zafin zazzabi mai jigatarwa.

Motocinsu na tsayawa kowacce acikin kawayen ta sauko a gurguje cikin sauri duka suka yo kanta, meenal da vicky ne suka rirriketa uztaz ma ya sauko kasa cikin sassarfa ya iso gareta.

Ahankli halisa ta sauke kafafunta kasa ji tay ta kasa motsi tahau lalume tana rirrike kafadun meenal adan gigice sakamakon bata iya ganin komi agabanta sai duhu duhu ga jiri me tsanani daya mamayeta.

Sama sama takejin muryoyinsu kowa na umartan da akan ta daure tayi motsi domin su kaita ciki.

Zimman yin hakan taji tana kkrin miƙewa tsaye saiiii yuuuu wani irin jiri me bala'in ƙarfi yay wuf ya kwasheta ta zube kasa sumammiya.

Hankli tashe suka ciccibeta suka wuce da ita private hospital dake anguwar Simbiat abiola way na ikeja.

Dawani irin gudu nurses suka gungunro wani gado aka karbeta daga hannunsu duka suka dagata suka daurata akan gadon akai ciki da ita.

shemau ke rungume da hadiza dan kuka kawai takeyi. Victoria kuma jeka ka dawo kawai takeyi hankli tashe tanayi tana adduarsu ta christoci.

Meenal ce tabi har kofar room din ta tsaya duk ta rasa me ke mata dadi.

Jikinsu duk na basu cewa magangnun da kawu ya gayama halisa shiya dada cusa mata baqin ciki snn ya sakata ragwabewa. Dan Rabon halisa data kwanta a asibiti zai iya kaiwa shekaru bakwai da suka wuce dan bata fiye ciwo ba.

Awani babban examination room aka shiga da ita meenal din zata bisu aka hanata shiga snn daya daga cikin nurses din tafito tashiga wani hadadden consultation room saigata tafito tareda wani Dr dabazai wuce 45yrs ba yana sanye da farin glasses a idanunshi wuyanshi sanye da clinical stethoscope.

wajen aljihun Lab coat dinshi ta gaban rigan anrubuta Dr Ahmed Damilare jimada, da sauri sauri sauri gudu gudu ya fito nurse nabinshi abaya daidai zasu shiga dakin kenan uztaz drivern halisa yariko hannunshi gam gamm hakan yasa docton yajuyo tareda tsayawa yana kallonsa snn yakuma kallon hannunshi daya yarike da karfi ba acikin hayyacin shi ba, irin malam lafiya???

kaman wanda yazare ustaz ya damkeshi cikin wata irin raunanniyar murya yace "likita kayi hakuri, wann matar itace gatata kuma yar uwata kwalli daya a duniya dan Allah kataimaka mata kar ka bari wani abu ya sameta..

wani irin calm smile Dr din yayi tareda janye hannunshi daga na uztaz da idanunsa suka ciko da ruwan hawaye sosai snn ya zaunar da shi akan kujeran dake wajen dan izuwa yanzu baida wani karfi jikinshi rawa yakey sosai ..

Doc yace "cmon be hopeful iya abinda nakeso dakai shine ka kwantar da hankalin ka kazauna anan kamata addu'a. I assure u abangarena kuma namaka alkawari zanyi duk abinda zan iya naga na ceto rayuwar........."

bai karasa maganan ba wata nurse tafito a mugun razane ta na cewa "Doctor, doctor Ahmed please come quclky the patient is
Going offf der is no pulse..

Jin haka Jiri ne ya debe Meenal da tunanin cewa itace tai silar mutuwar halisa, hakan ne yahau yawo a brain dinta nan tay kamar zata zube kasa aragwbe vicky ta tarota jikinta tajawota gefe, hadiza da shemau kuwa ba a magana dan har sun kai kasa suna furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun..hadiza dake da rauni sosai bakaramin kuka takeyi awajen ba

da sauri doctor yay ciki yana kallon uztaz daya dora hannu aka cikin rudewa yana kuka kamar dan karamin yaro yace malam kadena kuka kayi mata addua kaji.nan da nan uztaz ya kama rokon Allah akan ya bawa halisarsa sauki.

Da sauri Dr ya shige cikin dakin ya karbi abun gwaji din da wata nurse ke mikamai agurguje yana sakawa a hannu yana kallon patient din sanan yace "ya za'ayi mufara tabata bayan tana kan suffocating, bazaku cire mata wannn gown din ba,pls ku cire matashi and someone should on the Air cone we need vent..

Nurse tace okay sir
Nan da nan suka hau
Yin abunda yace musu

Movable Medical barrier curtain sukaja snn suka sauya mata kaya izuwa na asibiti dark green colour irinna masu operation.

Lkcin halisa bata numfashi ko kadan bare motsi.

Suna gamawa doc ya taho kanta yana kallonta babu karya halisa ta hadu wanke hannu ka taɓa ce, ahankali yakai hannunshi yajuyo da ita tareda karban wani kalan minor shocker da nurse tabashi yakama yay chargin dinsa snn ya danna akan kirjinta.

Saida yay haka kamar sau uku kafin pulse din halisa ya soma dawowa

Wani irin zafin dayaji ajikinta saida yabashi tsoro, babu shiri ya karbi alluran dayasa ahada masa yakama hannunta yanemo jijiyanta yamata allurar awajen dan yay saurin zagayawa jikinta,

ko minti goma ba'a daukaba yay stabilising nata snn ya lankaya mata engine taya numfashi. yasake saka wani sabon alluran ya debo jininta awani a syringe din yabama nurse yace takai lab.

fita yayi bai jimaba suka shigo tareda su meenal kallo daya zaka musu kasan duk sun razana.

Nan yadauki wani paper da biro ya kalli meenal yace "hajiya ya sunanta?

batare da ta kalleshi ba har lokacin idanunta nakan halisa ahnkli cikin sanyin murya tace "sunanta Halisa Roberts mansa .

Yan tambayoyi ya musu gameda abunda ya jefata cikin wann halin suka gayamai sama sama snn sukayi demanding din security dazaina gadin ta sabida yan jarida.

rubuce rubuce yayi sann ya ijiye takardan yadauko wata paper yay rubuce rubuce sanan yamikama uztaz ganin shikadaine namiji awajen Bayan ya sauke ajiyn zuciya yace "yanzu dai afara zuwa asayo wayan nan Alluran anan pharmacyn mu kafin result din test dinta yafito mufara treatment. yanzu kawai stabilising condition dinta nayi ba'a mata komiba tukunna.

sai aje abiya kudin gado dana folder abaka ka kawomin anan da ruwan Alluran dana rubuta.

Ko scnds uztaz bai kqara awajen ba yana amsar paprn agurguje ya fice domin aikata hakan.

Ajiyar zuciya doc ya sauke zai fita shemau ta tsareshi tana cewa Doc baka gayamana conditon nata ba, is she going to be fine.???

Yay shiru yanata kallonta
Sai can yy murmushi snn yace "lets hope for the best hajiya.

Irin kallon da vicky da hadiza suka mai yasaka a baiyi niyyar bude musu bayanin matsalar ba yaga kawai gara ya fada.

Ppr dake hannun shi yake kalla calmy yana cewa uhmmm She is actually in serious Nervous break down due to depression and mental torture. Sann kamata yay ace mun bukace ganin hukuma a wann lamarin sabida inhar bata farfado nan da kwana uku ba zata iya rasa ranta sabida halinda take ciki yaso ya taba mata jijiyoyin zuciyarta bana wasa ba..but ku kwantar da hanklinku zamu iya bakin kkrin mu akanta, Zuwa anjima zanyi wasu kwaje kwaje dan mu tabbatar da cewa jijiyoyin zuciyar nata da suka jigata basu raunatu ko sun tsinke ba.

Har ya kammala bayanin babu wacce tace masa komi sai kallonshi da sukeyi kamar TV kowacce tana ji da abunda yake mata ciwo aranta...

Dama tuntuni seda hadiza ta gaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login