Showing 117001 words to 120000 words out of 171903 words
atsakninsu face musu da surutayya na mata nayau da kullum.
faffadar murmushin datake sakewa acikin ranta shine ya fito fili dan ganin su datayi ahakan cikin nishadi yasata karajin wani sabuwar farinciki marar misaltuwa acikin ranta.
tun xuwarsu meenal da shema'u gidan halisa take tare dasu..,vicky na karaso kuwa suka cika dedei and since then it has been Banters here and der ana ta tsokanar juna ana kankaro hira na nishadi wanda zaka iya rantsewa sun jimane basuga junansu ba.
Tsayawa cak hadiza tay daga dan nesa tanata kallon irin soyayya da aminantaka tare da nishadin dake wanxuwa atsakaninsu ayayinda suke hira mai ban dariya.
Yadda suke bawa bukatun junansu na rayuwa muhimmanci yasaka duk suka aje abubuwan dake gabansu sukaci kwalliyar kure adaka kowa tay kyau tazo gidan domin amsar kirar hadiza duk dama basusan dalilin wann karamar shanawa da ta haɗa musu ba.
They All look soo beautiful meenal talba acikin peach colour jumpsuit dinta tun zuwanta ta makale kusa da babban aminiyarta halisa mansa data saka wata hadaddiyar black color cascade mini gown na versace dabai kai kan gwiwarta bama tun da suka zauna tambayar halisan kawai takeyi gameda batun lafyarta duk tabi ta damu, wani bin har tausayinta halisan takeji dan yadda take nuna ta damu da ita sosai zaka iya rantsewa cewa babu wata wanda take sonta da amana kamar meenal arayuwa.
shema'u marafa data saka hadadden golden colour valentino garavani dress dinta up and down riga da wando wanda ya fidda hour glass shape din manyan duwaiwakan ta,tun da tazo bata zauna ba dan ayadda takeji da hadadden dirin jikinta wanda tamkar itace kim kardashian wajen shape.
Tsaye tay agabansu tanakan basu labarin dalilin dayasaka bazata taɓa yadda ta haihu da mijinta engr mahmud ayanxu ba.
Acewarta haihuwa da shayarwa suna lalata siffar mace dan haka batason dirin da Allah ya bata take murzawa ya lalace da wuri bare mijnta yazo ya fara reinata dan tun da aka haifeta tazo duniya kallon matar manya kawai take ma kanta.
vicky dake tsaye agefenta sam bata amince da wann ra'ayi nata ba, dan haka suka ta rusa musu atsakanin su.. dake ita haihuwar ne ma yake shiga tsakanin ta da uwar mijinta cewa take itakam koda siffarta zai lalace ta dawo mei shape din Amoeba ne inhar Allah ya kawo mata haihuwa zata amsheshi da hannu bibbiyu sabida ƴaya albarka ne na musammn daga wajen ubangiji.
Kamar yadda Meenal ke bin bayan ra'ayin shema'u akan haihuwa kai da kafa haka halisa ma take bin bayan ra'ayin vicky sosai sabida halisa sosai take son yara duba da taso ne itakadai bata da wani dan uwan jini.
wanda musun nasu ne ya jawo surutayya mai yawa wanda har baka iya jin muryan kowa awajen. saidai hirar tasu ce gwanin ban Dariya,dan a sigar hira ayi nishadi kawai sukeyinshi kowacce Acikinsu na fadin ra'ayinta ne kawai batare da wani manufa ba.
As usual meenal na shiga cikin maganan ne amma sam bata iya fitowa fili ta fadi dalilin bin bayan ra'ayin shemau marafa datake yi saboda aranta ta riga tasan cewa ita da mahaifyarta sunyi agreement akan bazata haihu da mijinta Dr khaleel ba sabida batason taxo ta mutu khaleel din ya gaje arxikinta adalilin abunda zata haifa snn ya auro wata macen su more arzikinta tare.
Ji take da ace ta mutu khaleel ya mallake dukiyarta gara shi din ya fara mutuwa yabarta a duniya inyaso ita ta mallake harda nashi arzikin..
Shema'u kuwa har da yaran ma ta tsana, gani take kamar a child is a burden, haihuwa ai takura kaine kawai,..ko gaisuwa taje daga an mika mata jinjira sai kaji tana cewa "no please babies are messy"hardly kaga shema'u ta dauki dan wani ta rike a hannunta wanda shiyasa sam batasan darajar yaran da ake kawowa dan suke mata aiki ba.
Ana cikin surutun nan halisa ta hango hadiza acan ta makale a hanya da hawayen farinciki taf a idanunta at same time tanata murmushi...
shirya mini girls to girls date iya yasu yasu kusan dadaddiyar Al'adace data zame musu jiki a tafiyar click din nasu sau tarin yawa sukan shirya ire iren karamin meeting haka domin su baja kolin damuwarsu ko su tattauna wani labari na farinciki kona cigaba ko kawai dan hutawa ko a tattauna wani abu mai muhimmanci daya shafe kawancensun musmn ayanzu da suke kallon kansu kamr yan uwan juna.
Miƙewa halisa tay tana murmushi taje ta jawo hannunta ahankli suka karaso cikin filin dayagaji da hadadden gyara, nan da nan hanklin sauran kawayen ya dawo kanta suka mimmike tsaye suna murmushi har saida halisa ta karaso tsakiyarsu tare da ita snn ta saketa
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a tsakiyarsu sann tace you look amazing girls..duka suka amsa da murmushi vicky tanamai cewa we cant wait to hear the good news dan harsashe takey a mind dinta ko ciki hadizan take dashi!!..
Shemau tay kamar bata san komi ba. Murmushi hadizar takeyi snn ta umarce maids suka kawo kala kalan drinks a dump waiter dan kowacce ta dauki kalar abunda take sha. Shemaun ce ta saka hannu ta dauki glass din Mojito mai sanyi ta fara sha,hadizar ta dauki na margrita, piña colada halisa ta rike snnn ta zuba blocks din kankara aciki, snn meenal talba ta dauki chilled manhattan and lastly vicky ta dauki glass of martini duka suka zubawa hadiza idanu suna masu sauraran abunda zai fito daga bakinta ganin she looks really happy nevours and emotional at same time.
Cikin lumshe ido da budewa tace okay guys Abu biyu nake son na sanar da ku..na farko marar dadinji ne, na biyun kuma sabanin haka..
Kallon juna sukayi duka Kirjinsu na dan bugawa banda shemau data dan ja baya tanata shan drink dinta ahankli.
Halisa ce tay gyaran murya kadan snn tace toh da me dadinjin zamu fara ko?...
Vicky tace noo halsy. Negative befor positive dai..whats up hadiza whats bad?..
Meenal da shemau basu ce komi ba. Ahnkli meenal din takai drink dinta baki a kwakwarta tanata nazarin shin wani abun baqin ciki kenan da har hadiza zata kirasu duka ta gaya musu while she is still smiling ita da tasan hadiza da rauni da kuma saurin karaya???
Saidai Ko kammala lissafin nata a mind dinta batayi ba cikin sauke ajiyar zuciya Hadiza ta dubesu su ukun snn tace
Vicky,meenal, halsy mijina ne yay aure jiya kuma.....Tunma bata karasa idda kalaman ba Abazata meenal tay Wani tufffff da qarfi ta fetso da drink din data kurba waje tare da dago kanta sama in shock tanamai kallon bakin hadizar looking confused kamar bataji abinda tace da kyau ba..
Hannun vicky harna rawa ta matso kusa da hadizar a sigar i dont quiet get you well,suna hade ido da halisa kusan atare dukansu uku suka ce ..
"Hadiza kkce mijinki ya miki kishiya?
Shemau dake tsaye bata motsa ba Kamar zatay dariyar tune din da suka furta hakan dashi amma ta fuske jin Hadiza Tace 'yes..wani irin nunfashi meenal taja snn tace tabdi jam...Juyowa hdzar tay ta kalli shemau snn tace shemau is aware of it cos i called her..
..banason na daga muku hankli ne shiyasa..
Cikin katseta da masifa vicky tace"..No hadiza. Wann ba magana bace i mean Matsalarki ai matsalar mu ce akan me zakice haka??? Kishiya gatsau haka sai kace wani almara?
Halisa ta tsaya in silence batace komi ba danji tay kamr kanta na juyawa.
haka kawai ta tsani taji duk wani mummunan labari da zaina daga mata hankli ko ya saka mata damuwa dan muddin tafarajin hakan to atake ciwon depressiin dinta yake dawowa mata kamar sabo a brain dinta sai taji hanklinta yana tashi sai kuma tafarajin kmr batajin dadin komi.
Kacokam meenal ta aje drink dinta akan table jin tarasa taste din bakinta gabaki daya dan arayuwarta gani take kamar cikin kawayenta duka babu wacce bata fi karfin ayi mata kishiya ba bare kuma ita. Yo me namiji zai nema awaje inhar ya aure daya daga cikinsu? Gani tay Suna da kyau, ga diri, kudi, suna da kuma muhibba acikin sauran mata.
cikin sassarfa ta karaso ta dafa kafadun hadiza datakeji kamar ta mata kuka snn tace babe wai wacce shegiyarce ta shigo gidanki kuma yaushe aka shirya wann abun da bamu sani ba, this is an insult to all of us ..to wabillahillazi sai munyi waje road da ita dan gidanki ba gidan zamanta bane .
Hadiza zatay magana cikin katseta shemau tace guys calm down mana aii ni zan muku bayani, but first mu zazzauna tukuna.
A mugun sanyaye su ukun suka zauna dan lkci lkci guda annurin dake yawo akan fuskokinsu ya dauke cak kamar an walkiya an dauke.
Cike da salon lauyanta magana shemau ta kirkiro part din datake son sujin tahau gaya musu shi acikin sauki
Dede wajen da ramatu ta tonawa kanta asiri tare da saki uku da alhaj ya dankara mata a daren farkonta iyashi kawai ta gaggaya musu shi.
Sauran zancen kuma duk bata gaya musu ba dan batason suduka su san cewa itace takai hadiza gidan malami sukayi wani abu Na tsafi sai kawai ta nuna musu cewa asirin ramatun ne kawai ya tonu sabida hadiza bata da haqqinsu wanda Kasancewarta kwararriyar lawyer shiya dada sakawa lkci guda kowa acikinsu ta amince da zancen nata batare da wani tantama ba...
Tunda maganan ya fito fili wani sabuwar surutu ya kaure awajen kowa na fadar ra'ayinta as usual shema'u da meenal sune masu nuna cewa sun mugun tsanar kushiya dan haka su sukafi kowa zage zage da dariyar mugunta.
Hadiza na basu sauran labarin yadda abun ya wakana da aka cicciro kayayykin tsafi ajakar ramatu Abun al ajabi amma dariyar mugunta su biyun sukadingayi suna shewa suna tafawa.
Vicky was busy wajen tausar zciyar hadizan tare da dada bata haquri da kalamai masu sanyi ayayinda zancen ya rikikita ma halisa hankli duk tunaninta shine yadda ramatu ta shirya wnn mugunta kamr bazata mutu ba sai taji ta kara tsorata da lamarin duniyar gabaki daya
"Hmmmm Hadiza tay kkri fa.. Ai randa mahmud ya kuskura yace zaimin kishiya wallh rabuwa dashi zanyi inje cahn in nemi mijina tun ma kafin ta shigo gidan dan banason rainin wayo wann ai raini ne...
Shemau ta fadi hakan cikin nuna isa tana jujjuya kai cikin bunkasa da kadadi .
Cikin kyabe baki Meenal tace Tab di jam..ke shema wani wargin ma waje yake samu. Duk fitinan uwar mijina akan cewa batasona ai kinga bata isa ta kawo masa mace tace ya aura ba bayan ina nan ba bare shi kuma..ai
Inkinga khaleel yay aure to ni Amina ali talba na nabar masa duniyar ne amma muddin ina raye wallh bai isa ya auro wata macen ba.
Vicky dake rike da hadiza tace u guys pls banda cika baki dai kar azo ana amai ana lashewa.
Halisa batace komi ba ta dauki taɓarta ta kunna ta zuka ahankli dan gani take kamar har ta mutu hala bazata san dadin soyayya bama bare tasan me akeji in mijinka zai kara aure.
Cikin share zancen vickyn, Meenal tace guys This actually calls for a celebration...wallh naso ace ina nan akayi draman nan badan komi sai dan inga shegiyar tana hauka..
Shemau tace abeg her chapter is closed...
"good riddance...Vicky ce ta karasa mata da cewa "to bad rubbish!!!
hahahah suka fashe da dariya mai karfi.
Sautin wakar hadiza yar gidan malamai shemau ta saka music player dake wajen suka jawo hadixar tsakiyarsu suka zagayeta suna rawa da jikinsu suna mai mata wakar suna tafi suna balain zugata aciki..
Kai mata!
A rike darajar aure da kyau, A bar hushi da ikon Allah, Dan ikon Allah ya wuce hushi.
Lale Hadiza lale lale
Hadiza yan malamai
Kun ga Hadiza ta burge ni, Ina cikin yawo na, na ga Hadiza ta burge ni
Kun ga Hadiza ta burge ni, Yara suna kiranta amare mata suna kiranta amare, Ni ina cikin yawo Na ga Hadiza ta burge ni
Na aure diya ta amare
Lale Hadiza lale lale,Hadiza yar malamai
Kun ga Hadiza ta burge ni,Ko wa taba Rakumi shi ga hauka, Jaki bai kula da bugu ba, Ko wa taba Rakumi shi ga hauka Jaki bai kula da bugu ba
Lale Hadiza lale lale
Gyara gida Hadiza
Duk naki ne
Gyara wuri Hadiza
Duk naki ne
Gyara mujinki Hadiza
Duk naki ne
Toh ladabi biyayya
Duk naki ne
Ba ni ruwa Hadiza
Sai ta durkusa
Ba ni hura Hadiza
Sai ta durkusa
Ba ni tuwo Hadiza
Sai ta durkusa
Ruwan wanka Hadiza
Sai ta durkusa
Gyara gida Hadiza
Duk naki ne.....
Lokcin da suke rera mata wakar suna zagayeta Zuciyan ta tarr... Wani nishadi ne ya mamaye ta
Ganin yadda kawayen nata sukayi spicing din wakar dan har kasa meenal da vicky suke kaiwa wajen rausayawa
Shemau tana rausaya kanta na kaduwa kamar tsohowar kadangariya
Chan halisa ta dada kunna hayakin tsadadden tabar marlboronta ta hadashi da shisha pot ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki dan ita bata wani fiye son hayaniya sosai ba.
Wajen gabaki daya ya dau zafi da nishadi sautin wakar tana wani irin buguwa a speaker da sunan hadiza evrywher is giving all the vibes na big babes celebrations.
Bayan nan Aka bude shafukan ciye ciye, an sarrafa namar kaza dana tolo tolo ga shawarma da sinasir, sushi, salad da small chops, ana ci ana babbaka dariya akan lamarin hajy ramatu da kusan ince aynxu ta zama tarihi a hannunsu.
Meenal was extremly proud of yadda hadiza ta zama sanadiyar kawo karshen gagarumar matsafiyar can badan komi ba saidan hakan zai karawa wa clique dinsu daraja a idanun manyan mata bana wasa ba.
Duk wata hamshiyar yar iska irinta idan taji labarin cewa clique din sune suka kawo karshen ramatu dolene a basu darajawa ta musammn acikin taro.
To make the date very meaningful yasaka hadiza ta kawo wani karamin words games inda kowa zata bada random advice and motivational quotes.
Bayan sun kammala cin abinci sun koshi Akan wani shirgegen turkish capert awajen haka suka zazzauna vicky ce zata ta rubuta sunan kowa ajikin paper sai ta watsashi akasa wanda ya riga bude nashi zai kira sunan wanda yake ciki sai yazo tskiya ya bashi word of advice ko motivation.
Karon farko ana wurgawa akan uwar gayyar ya fado,hadiza tana bude nata papern taga sunan shema'u ne aciki.
Vicky ta kalli shemau tace ki zo tsakiya ki gayama hadiza one Word of advice or motivation
Babu tantama shemau ta taso ta iso tsakiya tana fuskarta hadiza datake zaune..
Alokacin babu abunda yake yawo a akwarwlta face kishi da kuma kaico.
Dan bansan yadda zan fassara muku radadin yadda takeji aranta kamar qaddararta ne hadiza ta sace mata a duniyan nan ba.
Lumshe ido tay sann ta bude tace "Dear hadiza, i will give a word of advice:
"Hadiza tana murnushi tace am all ears.
Sihirtaccen ajiyar zuciya shemau ta sauke snn tace "Cin amana baya taɓa zuwa daga wajen makiyi sai masoyi. Cos Friendship's demise, is a tale of shifting tides."but alwys rembr dat Betrayal is an inherent part of love!!!.
Tafi wajen ya kaure da shi jin kalaman shemaun ya burgesu.... banda hadizar data tsaya shiru cikin sakin murmushi a mind dinta tanamai kkrin fahimtar sakon da shemaun ta jefa mata acikin maganan nata dan magana ce a dunkule wanda yake nuna alamar cewa da akwai sauran rina akaba.
Murmushin dole kawai takeyi tana cewa thank u amma badan ta fahimce komi ba dan Har shemau ta koma wajen zaman ta zauna hadiza bata dena nazarin kalamanta ba..,tsoro takeji Kode shema'un tasan wani abu akan mijinta ne and she is hiding it from her ko kuma hala kawai shawara take son bata akan ta kula da zuciyarta sosai musmmn wajen trusting mutane.
Ana sake juyawa game din sai takardan ya fado akan vicky wann karon itace zata bawa shema'un option..
Vicky tace oya shema come forwad and choose a Word of advice or Motivation
Shema'u tace anyone.
Snn vickyn ta taso tsakiya ta dubeta tace..
Dear Shemau.. ure a lawyer the hope of the hopeless. Ina son kina tuna cewa" A duk lkcin da kika tsinci kanki cikin yaqi da gaskiya kisani cewa tamkar kina yaqi da rayuwar wani ne. And dat one person you hurt, might put a whole generation in pain...
Gabaki daya kawayen suka dauka da tafi raf raf raf batare da sun lura da wani irin Shiru da shemau tay jin maganan vickyn ya cakke zuciyarta ba.. sede tun kanfin su juyo kanta a cikin sauri ta bi ta hadiye maganan ta bige da murmushi mai fadi snn tace Thank you vicky i wll do my best and deliver justice..
Who is next?
Ana sake rolling sai ya fado kan halisa da meenal..
Atake meenal tafara sauya fuskarta dan taso ace itace zata bawa halisa motivation ko wani shawara domin ta isar da sakonta a
dunkule dan haryau gani take kamar halisa bata warke bane sabida aganinta haryau din halisa tana son zach aboye snn zai iya yuwa inya dawo mata wata rana zata amsheshi su shirya Sede ba haka abun ya fado musu ba.
A nitse Halisa ta je tsakiya da karar taɓarta a hannu hadiza da vicky suna dan dariya a sigar neman tsokana shemau tace sssss halsy kafin ki fara, bari mu baki word of ardvice. Kallon junan su sukayi suna dariya kusan atare suka juyo sukace mata"..smokers are liable to die young...
Meenal tace yes so Quit smoking!!!. Dariya halisa ta fashe da shi ganin yadda suka hade mata baki snn ta offing wanda yake hannunta cikin gyaran murya tace "Dear meenalin mummy,..ure rare, ure a gem..but rembr the things u do in life,can only be forgiven but not forgotten!.
Cikin lumshe ido da budewa meenal tace thank you soo much my love snn tay shiru batace komi ba.
Haka aka sake murzawa ya dawo kan meenal da vicky inda ta gayawa vickyn maganan da itama yay tasiri sosai aranta tafara jin kamar is better tafara nemawa kanta mafita dan tabbas tasan bazata iya cigaba da rayuwar datakeyi aynxu agidan aurenta na har abada batare da samun cikakken gamsuwa awajen mijinta ba.
duk dama bata taba fadawa kowa matsalar dake cimata kwarya a aurenta ba amma jitake kamar tafi kowa shiga matsala da damuwa.
is true, the silent battle might be an endless war dat solves no future problem. Amma ta rasa waye zata gayawa wnn maganan batare da ya bata shawarar rabuwa da mijinta ba.
Gani take kamar inta rabu da femi akan wann maganan tay masa butulci snn taci amanarsa duba da yadda yake nuna mata zallan madaran soyayya