Showing 171001 words to 171903 words out of 171903 words

Chapter 58 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

784

izinin kowa ba.

Wann zancen gida data sako aciki ya harzukashi sosai dan ya tsani ikon datake nuna masa akan gidan boro boro, har sama ya biyota suna masu haurawa juna yace mata tunda haka tace ta zabe ko shi ko halisa.

Ihun da suke ma junansu yasaka halisan bude idanunta tanajin abubuwan da suke fada.

Gani yake kamr meenal ta rainasa ita kuma banda gorin gida babu abunda take masa har cewa take dama can neman hanyar rabuwa da ita yakeyi bawai dan ta kawo halisa gidan ba.
Tace masa halisa tamkar yar uwar jininta ne, muddin bazai hakura ta zauna dasu ba saidan su subar mishi gidan mai gabaki daya.

Da kyar halisa ta sauko akan gadon da niyyar fitowa ta samesu sai caraf taji an doka musu sallama.

Mahaifyar meenal din ne tataho ta nitsar dasu As usual ana maida maganan tabi bayan yarta khaleel yaji haushi ya fice yabasu waje.

Yana barin wajen Meenal tay wuff ta rungume mum dinta tanamai sauke ajiyar zuciya mumy thank god kinzo...kinga abunda yakemin ko??

Hajiya nadiya ta daure fuska tana kallonta wani iri...snn tace ke amina dakata min..wai me nake ji ne kamar kina cewa halisa zata xauna agidan nan tare dake akanme?
Karkiga na goyi bayanki agaban mijinki ki dauka ko na aminta da wann wawan decison din dakika yanke ne, dats bcos ure my doter. Wann maganan sam bai gamsheni ba akanme zaki dauko katuwar budrwa kice ta zauna miki agidan aurenki?

Tsaye halisa tay abakin kofa tanajinsu bata iya fitowa wajen ba sabida furucin dataji hjy nadiya tayi akanta.

Cike da sautin shagwaba
Meenal tace mum please dan Allah karki bi na khaleel ..shifa kawai dan ya tsane halisa shiyasa yake fadin hakan.

Acikin hatsala hajy nadiya tace to ke meye naki na cewa saita zauna miki agidan toh

Saukar da murya kasa kasa meenal tay snn tace mum na riga da na gaya maki abunda ya faru tun bayau ba, i cant abandoned halisa ke kanki kinsani nine nan nakai magananta wajen zach na lalata mata aure..each time i see her broken i feel sorry for her mummy bakiga abunda ya mata jiya bane wallh zach baida imani azzalumi ne baida tausayi, and its all my fault da ban gaya masa komi akanta ba da bazai mata haka ba nide Inason halisa tazauna min ne na danna kula da ita kodama quilt din dake damuna zai dan ragu jiyafa ko bacci banyi ba ohh my poor halisa. Nide Allah ya saka har mu mutu bazata taɓa sanin cewa nice silar dukkan wani baqin ciki datake ciki ayanzu ba.

Cikin katseta hjy nadia tace Amina kenan toh shedan ma tsoronki yakeji..dacan kinsan da tausayin kika bar kishi da baqar hassada yasaki kika mata hakan..nifa bana son makircin kin nan..idan zakiyi ma mutum muguntu do it with ur full chest da Allah

Meenal tace mummy ba mugunta bane..i love halisa amma kema fa kinsan da ace na barta ta aure zach da ynxu tafini daraja da arziki a duniyn nan..gashi yana bala'in sonta kamar zai haukata kansa..kowama yasan attention dinta kawai yake nema da abunda yay mata jiyan nan...All this love is too much for her mana mumy. What about me???How did u think im going to feel idanna zauna kallon wata kaskantaccan yarinyar dana dauko daga slum cikin baqar talauci tazo tafini komi da komi, ilimi, mutane, farinjini sai kuma na kyaleta ta auri mijin dayafi nawa kudi?? dats not fair nowww..bazai taba yuwaba gaskya shiyasa kawai na rabata dashi na har abada na gwammaci mu zauna ahaka ayadda muke.
Halisa cannot be any step further ahead of me.

Da wani irin karsashi da zafin zcya meenal din take maganan, cikin sauri hajya nadiya ta rufe mata baki tana cewa ke Amina ya isa haka ..ure shouting untop of urs voice idan tajiyo mu fa..

Saida hjya nadiya ta fadi hakan snn meenal ta dawo hayyacin ta ..bakin ta na rawa rawa tace Bacci fa takeyi mummy she have been sleeping since yestade nite

Cikin sauke ajiyar zuciya hajya nadiya tace toh toh toshikenan...but lets go and check on her to be sure..saimuje ta dakinki mu karasa maganan

Kirjin Meenal na bugawa tace toh...muje

Daga bakin kofar taciki Kasa motsi halisa tayi jin zuciyarta da kwakwlarta sun dena aiki gabaki daya dan tun data fara jiyo kalaman da meenal take furtawa akanta jikinta ya dau wani irin mummunan zafi ita kanta bata san ya akayi tay wuf takoma kan gadon tabi ta kwanta tay kamar tana bacci ba.

Ahnkli suka bude kofar suka lekota...ganinta ahaka yasaka meenal tay murmushi ta juyo tana kallon mum dinta tace mummy i told u she is sleeping..lets go to my side..

suna barin wajen halisa ta wani irin bude lumsashun idanunta a fixge ruwan hawaye na bulbula acikinsu kamar an kunna kogi, sai hamm hmmm hamm takeyi dan dakyar take amfani da bakinta tana kwaco numfashinta daya toshe mata makogoro dakyar tana fizgarsa waje da azaban karfi tanajin kamr mutuwa kawai zatayi atake, birkicewa kanta yay ta fara sosa kanta a haukace cikin rasa mema zatayi jikinta na wani irin kyarman da bai tabayi ba, ba acikin hayyacinta ba ta miƙe daga kan gadon a birkice hartana fadowa kasa tabi ta mike cikin layi layi..not minding what she is wearing danko takalmi batasaka akafarta ba ta fice agidan acikin gaggawa...
ALHAMDULLAH anan muka kawo karshen part 1 maison ya biyo mu cikin tafiyar sai ya biyomu a littafin CHEATERS CLUB BOOK 2..!!!! CHAT 08060712446....
OR
TO SUBCRIBE
Cheaters club book 2 subcribtion
500, via 0152983148 Moh'd surayya sule .GTB bank

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login