Showing 120001 words to 123000 words out of 171903 words

Chapter 41 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

766

sama da uban kowa nashi a duniya snn babu wani abu data nema ta rasa awajensa na more rayuwa.

Sede Taji dadi sosai da meenal ta tuna mata cewa life is too short to be unhappy aynxu mafita kawai yakamata ta fara nema ma rayuwarta mai dorewa.

Halisa kuwa bata wani bata lkcin ta wajen nazari akan shawarar da su shemau suka bata ba dan ji take kamar bazata kara amincewa tay wata soyayya anan kusa ba.

Tasani sarai aranta cewa xata iya dawowa normal tay rayuwatta kamar yadda take adacan amma batun soyayya kam yanxu haka ta cireshi gabaki daya a dictionaryn rayuwarta kenan..


Bayan angama wann games din masu salla sukayi salla snn aka dan sha hira vicky ce tafara tafia tabarsu anan sabida kaninta nile daya bukaci ganawa da ita cikin gaggawa.

Meenal kuwa nason ace sun kebe da halisa dominta kawo mata zancen khaleel saidai hakan baisamu ba dan 7:30 pm na dare nayi Halisa ta kira uztaz awaya akan yaxo ya kaita gida ta huta kadan duba da gobe zata sake komawa asibiti domin ganawa da dr khalid.

after few minute ya iso suka rakata har gaban motarta inda tacewa meenal din zata sameta a office dinta gobe.

Tafyrta ke da wuya meenal din ma ta musu sallama ta wuce gidan ta aka bar shemau ita kadai agidan hadiza dan so take abarsu danta kalalleme adiza taji komi da komi dan karda abarta abaya.


Ata dayan fannin kuwa kimanin mintina arbain da biyar aka dauka ana yi ma mahaifyar hafsa aiki

Koda aka kammala saida aka barta tay hutun awa guda sabida ta dawo hayyacinta dan sosai wahala da talauci ya nakasa mata garkuwan jiki, tsabar yunwa ya shigeta da kyar da wahala ragwamar jikinta yake amsar treatment din.

Ahaka dai aka tattaro ta aka dawo da ita ward banda safa da marwa babu abunda mudi yakeyi yanata zzzare ido kamar wanda yaci kudin aika

duk lissafin shi shine yadda zai isar da sakon shemau dan ya caske dubu gomansa yacikawa rigarsa iska.

Lkcin mahaifyar hafsa tanakan bacci likita ya aiko yanamai bukatar ganin makusantantarta amma hakanan mudi yay kamar baya wajen ya bi ya share ta tabi ta rasa yadda zatayi, shidai Allah Allah yake ya samu shiga dakin domin ya isar da sakonsa ya bar asibitin dan badamuwarsa bane halinda suke ciki bare ciwon dake damunta

karshe Dai alhj aliyu ne yaji tausayinta ya shiga wajen lokutan tare da ita

Suna shiga wajen likita mudi ya garzayo yahau lellekawa ganin bakowa atanan din yasaka yay sanda ya bude kofar dakin ya shiga ahankli

Yana turo kofar ya tsaya cak daga can yanata Kallonta ganin yadda aka sankaya mata igiyar ruwa ga kuma injin taya nunfashi tay wata fayau kamar busasshiyar itace dan ko motsi batay bare kace arayetake.

Ganinta ahaka yasaka yaji wani iri aransa amma bashi ya hanasa karasowa gabanta da daurarren fuska dan ya tasheta suyi magana ba..

A gefen gadon datake kwancen ya tsaya muryansa kasa kasa yace ke uwar hansatu Da Allah ki tashi muyi wata magana ni fa sauri nakeyi ba zamana zo yi wajenki ba mutum yazo tun sahe babu abunda yasaka abakinsa sai ruwa haba da Allah.

Jin bata motsa ba yasaka ya dan taɓata a hannu amma sai shiru.

Nan ma ya kara daga muryans yana me umurtanta akan data farka amma sai shiru.

Abunka da jahili bagidaje
Sai yahau masifa yana cewa dagangan tayi shiru taki ta amsa shi dan ta tsanesa tana gaba dashi.

Nan ya fara zazzago mata bakaken magangnu kamar yadda suka saba yanamai ce mata mayya itace ta cinye musu dan uwansu...

Tun daga cikin kwakwalrta ta fara tsinkayo surutayyar nasa tun tana jinsa sama sama Harta fara jinsa garau amma bata iya motsi bare ta iya bude idanuwanta ta kallesa.

Wamu zaki gwadawa iko da hansatu dan kinga yayan mu baya raye? To wallh baki isa ba...

Yadda kikeji ke tantiriyace to mu munsha gabanki.

karshe ma ya hau tonawa kansu asiri cikin bambami, yanamai ce mata sun tsaneta ne sabida itace ta sauya musu dan uwansu daga jahili ya dawo mutumin kirki har mutane suke sonsa fiye dasu, snn yace mata ai asiri suka rufa mata da suka tashi kasheshi suka barta ita araye akan yarta, da sun so tagayyara rayuwarta da sun hada harda ita sun kashe, snn su bar yar tasu dasukeson sukaita makarntar marainiya mai biye biyen maza ko mabaraciya titina na duniyan nan.

Bakaken maganganun dayake fetsa mata yasaka ta fixge kanta da karfi ta farka da tsananin baqinciki da hawaye masu zafi acikin idanunta...

bata ma iya magana amma bai fasa ba, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har ya kammala isar da sakonsa da shemau ta basa.. kuka kawai takeyi tana nunashi da yatsa da karsashin Allah ya isa a cikin kwayar idanunta datake zubda ruwan hawaye masu rauni aciki...

Nide Kinji na gaya miki
Karda ki sake ki amince ki tura yarinyar nan binni idan bahaka na rantse miki ba bazaki sake ganinta da idonki na har abada ba dan daga mun karbeta ahannunki aure zan mata da almajiri na taje kauyen jikas acan tay aikin niƙa da surfe.

Da karfi yake mata maganan cikin gadara da iko...ɓari jikinta yakeyi kar kar tanata Kkrin fidda magana abakinta kenan sai aka bude kofar dakin nasu abazata.

cikin sauri mudi ya dawo gefenta cikin sauya fuska ganin mutanen da suka shigo ciki. A daburce ya soma sose sosen kunne yanacewa sannu sannu matar yaya karki motsa jikinki, inadai hansatu ne.. ai nace miki zan je na kirawota.

Ciki da kame kame ya daga kai yana satar kallonsu engr mahmhud da mahfyrsa daga can bakin kofa, saican yace ina wuninku hajiya da alhaji? Hihihihii Wani kuke nema ne? banan bane dakin agabane..

Mahaifyar engr mahmud hajy badiatu ta kuresa da idanu batace uffan ba dan kaf zancensa na karshen dayake cewa zai raba hafsa da mahifyta sunji shi akunnensu ita da danta ayayinda suke shigowa ciki.

Bakaramin tausayi matar take dashi ba dan ta saba handling ire iren wann aiyukan na jin kai shiyasa da danta ya kawo mata zancensu hafsa tacemai basuci ta zama ba kawai suzo jigawar tare ta gansu da idanunta musmmn ma dataji yadda suke rayuwa babu me temaka musu ga yunwa ga talauci ga ciwo ga kuma maraici

Engr yace ma mudi sannu malam...kai wayene?

Cikeda kame kame Mudi ya amsa da yawwa sannu ni sunan mudi... yana fadin hakan yanamai kkrin zame jikinshi agaggauce daga dakin dan sosai jikinsa ya bashi cewa sunji irin bakaken magana da tsawar dayake dakamata daga waje.

Dedei zai fice hajiya badiatu tace ikon Allah kai malam kai kuma waye nasu?

Mudi ya juyo yace nine kawun hansatu...yana fadin hakan ya fita da sauri kamar ana hankadashi waje, baki bude hajy badiatu tace ma engr maza kabishi ka kirawo min shi kacemai inada magana dashi tunda shi kawunta ne.

Aladbce engr yace toh mama snn ya fice yabi bayan mudi da sauri ganin bazai cinmasa ba yasaka security suka bishi domun a dawo musu dashi.

Karasowa gefen umman hafsat din hajya badiatu tay da sigar tausayi a fuskarta tana mai cewa sannu baiwar Allah, sannu Allah ya baki lfiya.

Umman hafsa Batace komi ba sai kuka mai sanyi da takeyi tana tuna munanan kalaman mudi wanda ya fi mata ciwo dayace mata sune suka kashe mata mijinta abar kaunarta kuma gatan ta a duk duniya waidan sabida tsanar da suka mata dan ta gyara masa rayuwa da kuma dan yace zai saka yarsa a makarnta tay ilimi.

Inta tuna wani abun da suka mata na tozarci a bayan rasuwarsa sai taji numfashinta ya sarkafe gaba daya bata iya fitar dashi waje, ko ayanzu ji take kamar bazata iya daurewa ta cigaba da rayuwar nan datakey me cike da ababen bqin ciki acikiba. Sedei daga zarar ta tuna da cewa itace gatar hafsa sai taji bata sha'awar mutuwa dan haka take iya bakin kkrinta wajen danne gulluton bakin cikin daya mamaye mata zuciyarta
Ayanxu yake hanata fitar da nunfashi.

Daf kusa da ita hajy badiatu ta zauna harta ta kammala share yan hawayenta kafin nan ta budi baki cikin sanyin murya sosai tace "Ina kwana hajiya?..hjy badiatu tace lafya baiwar Allah ya jikinki..da kyar take kwace maganan daga bakinta daya fayau ya faffashe asanyaye tace lafiya Hajy Allah ya saka da alheri, nagode nagode da kuka taimaka mani naga hansatu,
Nnn...nagode sai kuka ya kufce mata mai karfi mai ban tausayi.

Idanun hajy badiatu atake ya ciko da hawaye mai mugun zafi Ta rikota ajikinta kenan zata soma lallashinta sai ga nan hafsat din ta shigo ciki cikin sauri ta fada ajikinta acikin wani irin raunataccen yanayi.


Lkcin Engr mahmud da abokinsa Alhaj aliyu suna daga waje lokcin harya saka security sun kirawo masa mudi ya dawo yanata kumbura fuska yana kukkuni.


Duk a tunaninsa hansatun ne take so ta kai kararsa wajen yan boko tunda shide baisan mutanen dayake ganinta dasu din ba kuma bai tsaya dan ya tambayeta koda sau daya ba

Alhaj aliyun ne ke mai da ma engrn abubuwan da likitar ya gaya musu cewa chance din survival din matar baida wani yawa amma cikin ikon Allah zata iya samun sauki.

Daga ciki kuwa tunda hafsa ta iske mahaifyarta suke rungume da junansu gwanin ban tausayi suna kuka wanda yay kama dana rabuwa ta har abada.

..tunda taga hafsa babu abinda take saka mata sai albarka, tare da nasiha akan duk rintsi duk wuya ta rike mutunci
Sann tay hakuri da rayuwa koda itadin bata raye.

Hajya badiatu da take gefensu tanajin wasiyyar da uwa take yi ma yarta atake itama tahau tunawa da nata mahaifyar da ta rasu da jimawa da cutar cancern jini, hawaye kawai take saukewa sosai dan bakaramin tausayi suka bata ba.

...kuma gamida birkicewar da hafsan tay yasaka kusan dukansu dake wajen suka gaggauta shishigowa dakin harda mudi..

Samu sukayi hajy badiatu na kkokwar raba hafsa da mahaifyarta sai rokonta take akan karta mutu ta barta...

Da kyar saida umman nata ta lallameta kafin nan tay shiru..

Nan Hajy badiatu ta gabatar dakanta ita da danta engr mahmd tare da alhaj aliyu tanayi tana mata nasiha akan komi zai wuce talauci maraici da ciwo duk jarabawace ta ubangiji bawai nakaso bane.

Acewarta tazo ne domin su teimaka musu sann suna tare dasu har sai ta sami sauki.

Fadin irin Godiyar da tayi musu har babu iyaka dan tunda take arayuwa babu wanda ya taɓa kawo musu dauki bare kuma taimako.

Tunda suka fara maganar take sakwa alhj mahmud da abokinsa albarka da irin halin imani da rike amanar da sukayi. Akabar mudi da kikkifta mata ido acan gefe yanata Allah Allah ta kallesa dan baison yay asarar dubu gomansa.

Koda hajya badiatu ta dawo kansa da tuhuma nunawa yakeyi cewa sune basu nemi taimakonsu ba.

Duk ta gane cewa baida dandanin gaskiya amma Har hakuri ta bashi snn ta nemi alfarman cewa tanason ta amshi hafsa ta tafi da ita birni a karkashin kungiyarta na marayu.

Tunda yaga hajya na neman alfarmansa a mutunce Mudi ya tubure Yayita fadin maganganu masu zafi yana nuna cewa ai zuwansa nan asibitin ma basune suka sanar dashi ba agari yaji dan haka basa darajashi

Borin kunya ya dinga yana cewa an rainasa shiyasa aka kawo bare suna tuhumarsa kamar baishida daraja agaban idanunta har ake neman yanke hukunci cikin iko da gadara da bazasu lamunta ba.

Baqin cikin karerayin dayakey yasaka mahifyr hafsat din taja mai Allah ya isa suka rabu baram baram yacemata zai maka ta a kotu domin ai hafsa din yar yayansu ce banata ita kadai ba dan haka basu amince ta yanke wani hkuci a rayuwar hafsa batare da izininsu ba.

Rashin kunyar da fitsarar dunuyan nan saida ya tamfatsa musu baima ga girman hajiyar ba ya zauna ya gaggasa musu maganganu irinta cikakken jahili dan kauyen kayau duk baqin cikinsa dubu gomansa ne da sukeson sumasa asaranshi a wajen shemau yake damunsa alokcin.

Bayan ficewarsa ta dube hajya badiatu hawaye na zuba a idonta tace mata tunda tana iya taimakawa marayu ta taimaka ma yarta ta kubutar da ita daga hannun yan uwan ubanta. Inde dan itace tabar musu amana hafsa har abada dan bata da kowa da zata mika masa rayuwar hafsa ayanxu inbasu ba.

Hannun matar na rawa ta riko yarta tana cewa hansatu Ko duk duniya zasu tsaneki ki zama me gaskiya, Ko duk duniya zasu gujeki karda ki koma zama a karkashin yan uwan ubanki musmmn ma mudi, wayann mutanen basa kaunar ki basa kaunar rayuwarki. Kisani Allahn daya halicceki bazai barki ahaka ba. In sha Allahu albarka ta na tare dake a duk inda zaki taka a duniyan nan...wani irin jan ajiyan zuciya tay tanamai cewa la ilah illah
SHARE......
[2/5, 7:59 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
*Only chat oo, i no dey Available for calls on this number.*

⏯️2️⃣8️⃣
Wani irin jan ajiyan zuciya mahaifyar hafsat din tay tanamai cewa la ila illallah cikin kakkarfan gurnani ayayinda su hjy badiatu suke kkrin tayata karasa kalman shahadar suna masu tausayawa mata sosai. Rudewa hafsat tay ganin jikin mahaifyartan na rawa kar kar agabanin fitar rai.

wani irin bakuwar sanyi taji na mamayar sassan jikinta hawayenta na diga kasa Ahnkli ayayinda da takejin yadda gabobin jikin mahaifyartata yay sanyi daga bisani ta kwanto ajikinta a ragwabe daga nan sai bata ƙara wani motsi ba..

Ƙureta da idanu hafsa din tay wani abu na gaya mata aranta cewa ta rasa mahaifyarta, kuka mai karfi ne ya shakureta amagworonta sai kuma taji kukan nata ya kasa fitowa fili,sassan jikinta a ragwabe ta rungume mahaifyantan gam gam tana hawaye masu tsuma da rauni dan jitake kamr nauyin duniyar ne gabaki daya ya sauka akan kafadunta ita kadai.

Tantame idanunwanta tay hawayen nata suna sauƙa kamar ruwa amon sautin muryan mahaifyr ta da nasiharta na karshe shiyake mata yawo acikin kwakwalwantan ayanxu.

Kukan bai tashi kufce mata ba harsaida hajya badiatu tyi yunkurin kwacota daga jikin gawar mahaifyartata,a nan ne ragwababben kuka mai mugun saka tausayi ya kufce mata muryanta a dishe tana cewa umma na, ummana, ummana ummana..hjy badiatu na sauke hawaye ta rikito tanamai lallashinta sai kuka takeyi ajikinta bbu kakkautawa kusan kowa awajen hakuri kawai yake bata ayayinda mudi ya bude kofar ya fice cikin sauri batare da sun lura ba,can waje yaje snn ya ciro karamar wayarsa daga aljihu datasha Ɗauri da rubbering ya danna lambar magajiya yanayi yana waige waige.

Da kyar magajiya ta dauki kirar, Ya budi baki zai magana kenan cikin tsaresa da masife tace "toh mudi sarkin son kudi aika jira inga kira daga hajya kafin kafara takuramin da kira akan maganan kudinka haba sai kace akanka akafara talauci???

Muryansa kasa kasa Yace ke magajiya ni ba wann ne yasaka na kiraki ba. A hantare tanajan tsaki Tace toh meye?
Yace magajiya da akwai matsala"..Tace matsala ? Wace irin matsala kuma

Dada komawa gefe yay sann yace wann lamari fa ya zafafa, yuwrsa da kamar wuya halama sai kun shigo ciki.

Tace "assha!!! Tirrr dakai mudi.. ai dama nasan kai fanko ne iya zallan cika baki kawai ka iya bazaka iya tabuka mana komi ba. haba da Allah bafa kisan kai akace kaje kayi ba...magana kawai aka ce ka mata amma ka kasa sabida tsabar tsoro da ragwanci, lallai mudi kai kam kaji kunya wallah kanabada maza haba da Allah....

Yace ke magajiya karki gayan magana ba,da can kinsan da cewa mijin matar nan shine ya kawosu asubutin shine kikace nazo?.. yo gashi yazo da jatumarsa da wani babban mutum sai bubbudemin idanu suke suna min tambayoyi akan hansatu. yanzu haka ma sunce saida na basu hansatun zasu kaita kungiyar marayu

Yana share zufa dake tsatsafowa akansa yakuma cewa "yanxu haka da nake miki magana uwar hansatun ma ta rasu na rasa yadda zanyi na zille gashi nace musu zan kaisu gaban alkali..ni ko zaki gayawa hajyar takine ta temaka ta saka mana baki danni bani da ko kandala da zan ja dasu agaban alkali.

Baki bude Magajiya tace tab di jam yau ana ga wata... yo kai mudi kaji tsoron Allah ka dena zunduma mini karya haba abun naka yay yawa ga wauta ga ragwanci ka karya dame zaa soma maka hisabi a ranar karshe? Mudi Kasan me kake fada kuwa? Yo kaf kauyenku in aka hada bazasu ji kamshin hajiya ba bare kuma mijinta....kai subhanalla amma mudi zanci maka mutunci inka sakemain irin wann karyan rainin hanklin shaye shaye kake yi kome?....

Yace au tsawa kike dakamin to shikenan zakiga shaye shaye kuwa inde bazakuyi wani abu ba nizaan koma ciki muyi cinikin hansatu dasu inyaso suban dubu goman sai na kama gabana dashi.

Har Zai katse wayar cikin sauri da ɓarin baki magajiya tace kai mudi kai mudi tsaya kaji mana?mmmm Kace wai alhaj yana wajen kuma harda kyatumarsa?

Yace to da girmana sai na miki karya?

Da tsananin mamaki ayanayinta ta jinjina kai snn Tace tab ji jam..to wallhi ka nitsu ka gayamin duk yadda akayi saimusan yadda zamu billawa maganan dan mutanen nan nada kudi yanxu sai sukamamu duka su kullemu agidan yari mu bamu samu kudi ba kuma munji wuya..
hajy kuwa cewa zatay bata sanmu ba

Sauke ajiyan zuciya Mudi
Yay sann ya hau gaya mata abunda ya farun tiryan tiryan bai boye mata kome ba.

Mamakine ya hana magajiya magana sai salati da hmm hmm takeyi dan a tunaninta kaf masu kudi irin haka basu kaunar talaka, snn basada lokcin kallon masu aikinsu bare ma harsu bar abubuwanda ke gabansu suzo har wani garin domin taimakawa.

Mudi yana kammala mata bayani ta sauke nannauyar ajiyar zuciya snn tacemasa Duk wann case din me sauki ne amma sai in zaka bani cikakken hadin kai Dan muddin bamu hade kanmu waje guda ba Alhaj zai iya kama mu, idan kuma muka tona magana hajya zata iya kamamu itama kuma kasanta bata da imani wallahi.

Yace toh me zamuyi yanxu.

Shiru tay cikin nazari kafin ta gaggayawa masa iya abunda zai yi da kuma riban da zasu samu aciki.

Shikam bai damu ba dan inde zancen kudi zai fito aciki to komi ma zai yu.

Yana komawa cikin asibiti ya samu har an rufe mahaifyr hafsat din da mayafi. Hajy badiatu na rungume da hafsa da already zazzabi mai zafi ya rufeta ayayinda su engr suke tattaunawa da likitoci akan yadda za'ayi akaita kauyensu a emergncy truck na asibiti inda za'a mata wanka snn a binneta.


Sauya fuska kalar tausayi mudi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login