Showing 150001 words to 153000 words out of 171903 words

Chapter 51 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

774

ta manta amma kuma bazata taɓa iya nunawa halisa haka ba gudun karta masifeta.

Itade rainon carpet da carpet aka mata shiyasa tun tasowarta batasan me wahala ba, ta taso ne cikin kazantacciyar gata wanda ko hanyar kitchen din gidansu ma bata sani ba.

Daga karatu sai kallo sai tay kwalliya da sauran ababen nishadi amma duk wani abu daya shafi rayuwar ya mace inba na gayu bane bata taba saka kanta ta iyashi ba.

Zuwan halisa gidansu yasaka wasu abubuwan daga halayyarta na raina mutane suka dan sauya amma dake halisa na neman kudin kanta bata dogara dasu ba yasaka abun nasu baiyi nisa ba

Meenal always feels like Allah bai halicceta dan ta zauna akarkashin kowa ba...

dik yan uwan ubanta ta koresune da baqin hali da sharri kuma mahaifyrta itace babban me daure mata gindi.

Shiyasa take living life inta in the spirit of feminism. That is, a Women is equal to man in all. Abunda namiji zaai yi itama zatayi, she dosnt even blive in respect or secrifices. Itade Kawai asota snn abauta ma heart desires dinta

Money, beauty and knowledge are the true powers, and she have all of that at her beck and cour.

Maza masu ruwan kudi sun bibiyeta adacan amma duk taki zama dasu, dan Bawani abune yasaka ta aure khaleel ba saidan mummunan son shi datakeyi acikin ranta kuma tasan yanada hankli da tausayi sosai infact shikadaine acikin manemantan data amince cewa zai iya zama da ita awann yanayin nata na mesonkai da kuma makirci.

Koda zatayi aure ma halisa ce tafi kowa shan wuya wajen kimtsata..

Girki, iya zama da mutane da salo salo na zaman auren duk ta kaita inda ake koya amma haryau bata san cewa meenal bata iya aikata komi ba sedei ta fannin sex din intanason tay masa walaknci takan tuno da ababen da aka koya mata wajen motsa sha'awar ɗa namiji danta wahalar dashi.

Anata karatun ra'aayin gani take kamar the more namiji yake samun jikinka the more darajarka yake raguwa a idonshi. Saidai ko kadan batay la'akari da cewa a babin aure good and respective sex life kamar gishiri ne mai kara dandano acikin shaanin zamantakewar aure wanda inhar babu shi fatak rayuwar auren zai kasance babu taste babu gardi kamr yadda zaka ci abinci marar maggi da gishiri.

Duk wayann shafukan bata sakewa ta gayama kowa dan tasan raayinta yasha bambam dana halisa..gara gara shemau wani bin yanayin tunanin su akan rayuwarsu yakanzo musu daya.

Ita Gani take kamr halisa da vicky da hadiza duk wawayene masu karancin wayewa yan son soyayya shiyasa mazajensu suke abunda sukaga dama akansu.

Bayan sun kammala cin abinci da kamar awa guda uztaz ya taho ya dauki halisa suka koma gidanta dake victoria island.

Hakanan meenal ta tsallake kwanukan da sukaci abincin anan falo ta koma dakinta ta kunne computerta ta cigaba da ayyukan dake gabanta as usual khaaleel ya kirata yafi sau akirga amma dake bataga daman katse aikinta ba se bata dauka ba, bayan ta kammala aikin nata anan tay bacci bata nemesa.


Ata fannin halisan kuwa da kyar ta samu baccin sabida abubuwan da meenal din ta cusa mata a brain dinta ya nugun daga mata hankli
Har wani hawayen tausayin meenal din takeyi sosai

Iya saukin datake samu wani bin shine inta tuna cewa yawancin accusation din meenal akan mijintaa din harsashe ne babu wanda ta kawo mata sheda ko guda daya amma duk da haka ji take aranta kamar dagske ne khaleel din ne mai laifi..


******
Washe gari Early morning wajajen karfe biyar dede
Halisa ta farka tarasa abunyi saita bude mac book dinta data bude boyayyen instagram acct aikuwa nan taga Dms daga wajen Dr khalid har guda biyu ya mata Hi yana tambayarta ko ta san Halisa sabida tarun hotuna masu kyau dayaga ta zuzzubasu a shafiin nata.

Tana amsashi baifi da minti biyar ba sai gashi nan yay replying inta.

chating suka fara yi dashi in a flirtious way

Tanata wasa da hanklinsa karshe dei ta gaya masa cewa ai ita din sectariyar halisan ce.

Take ta bashi wasu information yana dubawa kuwa yaga hakane...

Nan da nan ya sake jikinshi yanata famar tambayarta akan halisa

Kai tsaye ya gaya mata cewa yana son halisar ne sabida she is beautiful and a very rich woman mafarkin kowani dan adam. Haka Ya share fage ya zuzzugata da dadin baki atunaninsa sectaryace baisan da ita kanta yake chat din ba.

Yay yay ya kirata waya amma taki, ganin hakan yasaka yace mata ta masa hanya wajen halisan konawa ne zai biyata..wasa da hanklinsa ta dingayi daga baya ta masa alkwarin zata amso masa lambar halisa she assure him in suka soma chatting he will find it easier ya isar da sakonshi.

Suna gama chat din ta kashe tab din cikin mamakinsa sosai.

Duk dama dacan tay tsammanin hakan daga gareshi sabida rudewar dayake inya ganta amma daya tabbatar mata da zargina sai abun ya daure mata kai sosai..

Ta jima akan gado kafin nan tahau watsap, ganin grop dinsu na kawaye biyar tayi cike da sakonni alaman kusan kowa yana online tarasa meke faruwa taga ana ta zubo sakonni babu iyaka.

Tana hawa tabibbi chat din tun daga sama anan ne take sanin abunda ya faru da hadiza harma bata kasar.

Tanayin kasa kasa sai kuma taga hotuna dayawa da hadzan ta turo musu dashi.

Kaf dinsu sai murna suke ma hadiza dan kuwa labarin ashe ba haka bane. Tafiyarta na jiyan ashe babban suprise ne mijinta ya shirya mata a miami acan united state.

Taje da zimman mijinta baida lafiya amma sai taga ashe ya hada mata gagarumin lovers eve ne
Ya narka kudi yasaka asalin indian professionals decorators suka decorating wajen aka mata cakes ga flowers, snn ya siya mata huge huge gift boxes me dauke da 20 pieces of valueble jeweries na gold da rubies da emiralds da na diamond guda daya. Sai 10 pieces na other baby girl stuffs kamar su designer perfumes, italian rosale shoes, pret a poter, paris gowns. Flowers and teddys. Her favorites chocolates and drink da wanda aka saka sabbin kudade aciki.

Wajen da aka shirya domin suprise din agefen babban tekune and is all decorated in red and white balloons. Hatta kayan data saka ranar is all part of the suprises rana ne da hadiza bazata taɓa mancewa arayuwarta ba dan batayi tsammanin cewa mijinta zai nuna mata cewa ya gane value inta arayuwarsa har haka ba. He also gave her a beutiful azurfa ring and a sport car na kamfanin mustang snn yace mata wann suprise din nuna godiyarsa ne daya kasance ta zama mace mai amana da nuna masa so na gaskiya badon abun duniyar dayake dashi ba, yace mata samun mace me amana irinta yay karanci
And he promise to value her for the rest of his life.

It was rhe most romantic day of her entire life hadiza tay murnan tay kuka tay godiya ma Allah har babu iyaka.

Ma kawayenta kawai ta iya nuna musu dukkan abunda ya wakana dansu tayata murna.

Dukkansu hudu babu wanda bai mata hawayen murna ba

Shema'u tafi kowa kuka acikinsu dake nata harda na makirci aciki,duk sai da tafi meenal zakewa tanata yabon hadiza tana cewa haqurine yakaita wann matsayin while a zuciyarta it become more reason enuf to hate her own marriege da mahmud.


Sunfi awa guda a grop din anayi ma hadiza son barka. Mijinta yace zata zauna tare da shi for a while tay hutu dan haka bazata dawo nigeria akan lokci ba.

Angama hira lafiya kalau
Masu bata shawara sun kara mata, masu yabonta duk sunyi angama kowa ya fara shirin abunda ke gabansa amma banda shema'u marafa.

She wasted almost 30 min tana sake kallon hotonan da hadiza ta turo musu agrp one after the other tana musu kallon kurel wanda kafin tagama kallonsu gabaki daya nunfashinta ya sauya salo.

Zaune take agaban mirronta taci kwalliya tanata kallon kanta A raunane ta rike saman kirjinta da hannunta tana wani furzan da huci mai zafi waje.

A mind inta she was Like
Whaat the hell is she doing here with mahmud.
Gacan Hadiza da bata fita da komi ba ta samu arzikin nan har kaman na banza. Itakenan ta rako mata duniya????duk wann kyanta da kwalisan tan nan saidai ya kare abanza kenan???

Wani irin Lumshe idanunta tay cikin karsashi jin zuciyarta ya raunana ya dawo baqi kirin. Cikin wann yanayin taji an dafa kafadunta qamshin turarensa kawai taji ta kwace kafadarta da sauri snn ta mike tsaye da wayarta a hannu tana masa wani irin matsiyacin kallo.

Mahmud tagani acikin blue pyjamas dinsa ta versace yanata murmushi. Ko kallonsa bata tsayayi ba ta bi ta mugun hade rai ta maida hanklinta kan wayarta.

Tsabar hanklinta baikansa A iska taji muryansa ayayin dayake ce mata good morning my love.

Bata amsashi ba ta nuna masa wayar dede wajen da hadiza ta sako musu hutunan expensive jewries nata ya karba yanata kallo, tsaki take ja up and down tanamai ce masa "see what ur mates are busy doing to thier wives and kana nan kana damuna da good morning my love toh bazan amsa ba..
TO BE CONTINUED....
*PART 2 DIN SHINE GUNDURIN ROMANSIYYA DA NISHADI TARE DA DRAMAR DAKE CIKIN LABARIN.. ME SON YA SHIGA CIKIN WANN TAFIYA YA MUN MAGANA DOMIN YIN REGISTER PAID GRP*
08060712446
[2/16, 11:19 PM] Lady Surayyahms.: 34#CHEATERS CLUB.....
_SURAYYAHMS_

mahmud na riƙeda wayar yay shiru baicema shemau komiba sai kallon hotonan kawai shima yakeyi da wani tunani nadaban acikin zuciyarsa. Bayan ya gama kalla, Murmushi mai dan sanyi yay dan yasan hadiza maitama sosai sabida sunyi karatune a makaranta guda.

Harara shemau takekan banka masa up nd down kamar wacce idanuwan ta zasu zubo kasa ganin yana murmusawa ta hargitsa taja wata mumnunan tsaki,..

Tace "Ka kalla da kyau dai".."Kaga yadda mazan asali masu kaya akasa suke tarairayar matansu ba irin su oo masu cewa good morning my love ba, mtchewww Good mrning my ass..who gud morning elp?

Calmly Yayi Murmushi ya dagokai yanamai kallon face dinta baice komi ba ganin yadda tay masa maganan da muryan hatsala ayanayinta, kallo daya ita kam ta masa ta dauke kanta akansa mai gaba daya.

Ganin ya aje mata wayarta akan table baice uffan ba yasaka ta mugun fusata dashi...

Zata bar wajen kenan sassanyar muryansa mai ratsa kwakwala ya dakatar da ita. Cak ta tsaya batare da juyo ba tanajinshi, Cikin sauke karamin smirks kamar abun datacemai din bai darashi ba yace I am truly happy for mrs kyari,
Hadixa maitama ai mutuniyar kirkice kuma tadamu da lamarin mijinta so whats the big deal der dan ya kyautata mata shima??? Well, i think She derseves it.

Atake shemau ta juyo ta kalleshi wanda daga yanayin fuskarta kawai zakasan cewa furucin nasa yay mata ciwo bana kadan ba..

Ji tayi kamar da biyu ya fadi wann maganan haushi take yabi ya rufe mata idanuwanta, kirjinta ya dau wani zafi, jikinta na ɓari hartana missing kalma tace Ohh ooooo hadiza ce mutuniyar kirki nikuma mutuniyar banza kenan ko mahmud??? No just ka fito fili ka fadi abunda ke ranka..

Yace a'a sede ayadda ke kika fassara maganata..

A masife ta hargitso ta fara balbaleshi, respect ur self man.. bana so.. banason haka. mahmd ya daga nuna maka abun arxiki zaka fara gasa min baqar magana kana comparing dina da hadiza bayan ba samar min irin wann rayuwar kayi ba?hmmm Kodan Ni banyi dersving haka bane daga wajenka?..itama ai mijinta ne ya mata abun arzikin nan kaime kake jira da bakamin ba, toh gaskiya banaso, dan rayuwar hadiza daban nawa daban..u cant campare us while u do nothing for me..this is mental Abuse...Akan me??? Meka tabamin?

Duk sanda tace masa meya taɓa mata bakaramin raunatashi kalman takei ba, duk da haka ya daure cikin nitsuwa Yace calm down shema Nifa ba baqon zafi bane, amma Tunda yanxu kinsan rayuwar taku daban daban ce so magana ta kare kawai abar wann maganan

Tsaki mai sauti taja masa batace komi ba,
dan Bakaramin haushi yaka bata in tana masa ihu shikuma yana amsata da nitsuwa ba...

ta tsani wann nitsuwar tashi na fitar hankli harji take kamr zatayi hauka dan gani take kamar har yanxu baisan zafin da takeji aranta inta gansa agabanta ba.

"To saikayi tay cos im not in the mood to waste my time with u.

Zata wuce ya dan sha gabanta suka hade ido muryansa a sanyaye yace pls shema what is wrong with u wai meyafaru kwana biyun nan gaba daya kin canjamin,nayi lefine?? waiyaushe rabon ki da bani hakki na?..haba baby girl menayi ne..sai ya dan saussata murya kasa kasa yana binta da sassanyar kallo

mugun hade rai tay cikin yanayin giggiwa snn tace "ni dan Allah karka dame ni cos i dont know... mtcheww...tafada a takaice fuskan ta ba alaman rahma acikinsa..

"ni kawai kabani hanya na wuce ba dama mutum yadan sha iska it always about sex and you wont get it from me today gaskiya don ni nagaji aiki ma zanyi kafin na fita...


Galala ya sake baki yana kallon fuskarta snn yace
Banfahinceki ba Are u tryn to starve me or what?...Satin nn gabaki daya ure busy with friends and office stuff na barki, and whenever its my time dolene kina bani hakkina....

Maganan nasa na tunzira ta dan haushi take ji lokacin sosai sai Ta dada jan tsaki batace komai ba .

Nan ta matso daf jikinsa looking so pissed off zata bangajeshi ta wuce ta fita yayi saurin jawota ta fada jikin sa baiwata wata ba numfashi mai zafi ya sauke mata a karar wuya saida taji tsigar jikin ta ya tashi sosai.

cikin muryan lallashi mai kashe jiki ya rungumeta sosai snn yace shemau please am begging u kar kimin haka yau din kiyi hakuri ki saurare ni ur man is soo horny kiyii agaji mana. Jin shi kawai take don Itakam abun sam ya fice mata arai bai damun ta ynxu cos hankalin ta yafi tafiya kan plans dinta na neman wani mijin mai shegen kudi irinna hadiza meitama..but she knows yadda ya manne mata yanzu bazai kyale ta ba sai ta bashi hakkinsa..

wani mugun murmushi mai dauke da alaman" zaka kuwa yi da nasani" tay sannta juyo tareda manna masa Wani hot vampire kiss a gefen wuyarsa kamar wanda zata zuge masa kurwan sa daga jikinshi mai gabadaya.

Shocking din dayaji ya saka ya sake nishi mai uban karfi yana jin yadda abun yatabo brain dinsa ya dada jawo ta yana sumulmukata so hard itama tana mayar masa ya shiga binta da lock lip kisses a zauce kamar wanda zai maidata cikinsa.

Ahaka har suka fada kan gado bayan yan shafe shafe da taɓe taɓe har yayi nasaran zame mata mata kayanta ya barta naked a jikin sa yana shafa ta cikeda kwarewa
Jin kamar salon nasaa yana neman ya taɓa kwakwarlta anan ne shemau ta soma tada mugun tan ta, juya shi tayi ta baya ta shiga bashi wani irin rough romance tana chakumo sa passionatlely kuma da karfi tana yakushinsa kamar ta samu bayan kadangare, hannun ta daya na cuddling dinsa ta baya tana caccaka masa jiki da nails dinta iya son ranta bata damu da ko zataji masa ciwo bama, Tun yana iya daurewa har yaji jikin sa ya soma jin kansa kamar a filin dambe duk sassan jikinsa ya dau zafi ga uban radadin kwarzani da yakushin datake aika masa a zafafe.

Amma da shike a matse yake haka ya bari tagama kwarzana masa jiki kaf sannan ta biya masa bukatun sa sama sama dan yanayin one round tacemai ita tagaji daga nan ta juya mai baya ta fara baccin karya

Cike da rashin samun gamsuwa ya kwanta agefenta idanuwanshi a lumshe..ya rasa yadda za'ayi yay pleasing din shema'u. Ta yaya zai nemo wasu kudaden da zai soma mata ire iren wann surprises din datake so din kodama hanklinta zai kwanta. Yay lissafin duniyar nan amma baiga wata mafita me sauki ba dan rabin ribar aikinsa akan shema'u kawai yake karewa duk dama bata taba nuna godiyarta ba saidai ma tanemi kari. inyace zai mata irin wann abun da akama hadiza toh kudinsa kaf zai zuba aciki harma sai ya kara da cin bashi ko siyar da wasu muhimman assets dinsa. Mijin hadiza babban dan siyasa ne akasar gabaki daya kuma ya jima ana gogawa dashi babu yadda zaice zai hada karfin arzikinsa danashi Wanda yasan yin hakan ma ganganci ne babba.

Gashi zuciyarsa baison ya hakura dan sosai yake kaunar matarsa baison ace yau wani abun duniya shine ya rabasu.

Da Wann tunanin aransa bacci yay awon gaba dashi.

tsam shemau tay tanajin sauyin numfashinsa ta tashi tabarsa akan gadon taje bathrum tay wanka ta kintsa kanta akaro na biyu.

Kafin ace 8:15am har ta riga ta gama shirin ta, yau kam Riga da wando tasa falazo baki wuluk da rigarsa red colour ta ciki tabita dora wata bouchra jarrar blazer akai shima baki snn ta sauke expensive straight brazillian cap hair dinta side by side wanda ya dada bata wani kalar kyau na ban mamaki.

wani irin kwalliya tay mai sanyi wa fuskarta ta fito zakkk slay queen dinta wanda ko kudi akabaka baza kace tana da auren wani akanta ba.

Allah Allah take ta isa office sabida yau din suna da get together na hidiman Swearing in na new chief judges na kasa
Da za'a gudanar dashi acan agarin Abuja a karshen sati.

Already Ta riga tay working kanta cikin wayanda za'a je taron dasu sabida babu tantama ko shakku manyan jigajigan kasa zasu halacci taron is an event dat she cant afford to misss ko dan sabida cikar burinta na samun sabon masoyi.

Satin nan gabaki daya hidimar zatay attending a ranar da za'a nadasun ne zasu jesu har supreme court na Abuja.

Kkri take taga anbata programes coodinating member inda kowa sai yasan da ita awajen

Tana ficewa agidan direct wajen aikinta ta nufa. Tafara shirin yadda komi zai kasance mata acikin sauki, duk sunayin bakin da zasu zo tay karamin backgrund check akansu tana me neman wanda zaifi dacewa da ita sosai.

Koda mahmud ya farka it was already around 10am in the morning gani yayi shemau bata ma nan a dakin sai ya mike ya shiga bathrum kawai don ya kimtsa knsa ya samu ya fito yanemi abunda zai saka abaki.

Yauma da shirinsa na zuwa aikinsa shima ya fito, tsabar yunwar dayakeji har wani jiri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login