Showing 105001 words to 108000 words out of 171903 words

Chapter 36 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

786

tunda yatashi yakejin sabon desire ajikinshi Daga Nan ban kara hutawa ba sai yanxu daya dan koma bacci

Shemau dake jinta ata daya bangaren dakyar tayi Murmushi snn tace toh I'm glad hakan ya faru dama ai Kece bakiji hadiza, ai yanzu babu macen datake zama da damin wulkancin namiji
Bakisan yadda nakejin haushin abun bane, shi wai daga Kin Dan masa laifi kadan saiya hau shareki yana gaya miki Duk abunda yaga dama.
..Wallahy ya bala'in samun kanki ne amma inda ace irina ne da bai isa ba.

Dan dafe kai hadiza tayi a gajiye da boasting din da shemaun takeyi snn tace kawata just forget it, anji an kuma sheda ke din ta dabance snn baki daukar walakncin namiji., as for me Bana ma son Ina tunawa da komi yanxu, Am just happy dat hanyar da kika dorani akai ya dawo dashi cikin hayyacinsa...he is now acting lovey dubey with me. Yace ma zai canja min duka cars dina, yau da asuba yay oderin min sabbin jeweries from wittel batch, he is also planning to take me on vacation..

Mentally Shemau ta zaro idanuwanta waje aranta tace whaaat?.

Wani cak kakeji dariyar fustarta ya dauke kamar nepa ne suka sauke, wani sudden shock taji ajikinta jin maganan da hadizan take furtawa dan haka kawai zancen ya mugun cakkarta a zciya ya kuma shakure mata wuya yanamai cusawa zuciyarta baqinciki a lkci guda.

Jin ta bata shiru yasa hadiza cewa "hello are you der? Shema....
shemau..kai innalillahi netwk.. tana shirin daga wayar a kunnenta dan taga ko ya yanke ne caraf sautin tarin shemaun ya gauraye mata dodon kunnenta da kara.

Ahahhhu ahhhu tafara kakalo Tarin karya, can tay kamar bataji me hadizar tace ba. Ahankli Tafara cewa hello hello dije? Hadiza Kina jina kuwa, tana cikin tarin tace ohh my god netwk ni wallh bana jinki kawai mubar wayar zan nemeki anjima Or inzaki iya kisameni a office yau wallh ni banajinki. Tana kammala fadin Hakan ta katse wayar agaggauce batare da ta jira jin me hadizar zatace mata ba,

Jikinta harna rawa ta tashi fuuu ta nufi gaban room dispenser ta tsiyayo ruwa mai sanyi snn ta sha.

Yadda takafe kai akan ruwan tanashansa kwat kwat kmr zataje yaki zaka rantse da Allah cewa gobara take kashewa acikin zuciyarta ba kishir ruwa ba

Wani irin lumshe idanunta tay tanajin baqin ciki dan take zuciyarta yay baqi qirin tanajin kamar An cuceta da aka aikota duniya da irin wann qaddarar bayan ga can mijin daya dace da ita hadiza ta sameshi a banza.

Tunda taji hadiza tace za'a sauya mata duka cars dinta ga manyan gwalagwalai datace wai har an siya mata dis mrn ga kuma vacations a new zealand kawai sai taji kmr ta gigigce ne ta kasa cijewa sai huci takeyi kamar wata zakanya

Sosai ta shaqa wann lamari dan bakaramin girgiza mata xuciyarta hakan yayi atake ba

Dagata fannin hadizan kuwa murda kofar bayin tayi ahankli snn ta dawo cikin dakin....zama tayi a bakin gadon daf dashi can ta Juyo suka hada idanunsu waje guda, numfashin shi ne ya dauke na seconds biyu yayi Wani lwgas kamar wanda baida sauran karfi ajikinshi yanata kallon fuskarta he tot ko zai sameta kwance kan bed ne dan yasan ta jigatu a hannun sa jiya babu laifi amma he was suprised dayaganta ahaka kamar ma ba itaba.

Wani kallon so ta jefa mishi tana sakar mishi murmushinta mai jan hankali ta aje wayar dasauri, ya jawota ya kara rungumeta a jikinshi yana lumshe idanunsa jin kamshin turaren victor rolf na flower bomb me mugun dadi dake fita daga jikinta,Hakan yasa shi kara rikicewa yakara matseta sosai jikinshi yana Wani irin fidda numfashi..

bakinta takai dede setin kunnenshi in a whisper tace good morning my love, Idanunsa ya lumshe snn ya kamo hannunta cikin nashi yana murzawa jin yadda tsikar jikinshi suka tattashi gabadaya sai yaji wani yarrrrr nabinshi akoina har tsakar kansa.

Idonshin a lumshen yace morning my honey,..kai hadiza duniyace ke wallhi im so blessed, yanzu ki kalleki faaa tunma ban warware ba u alreadt look awesome kinason
na haukace miki ko? Kar nakara yin na jiya fa saboda kina rikitani da salonkin Nan I honestly wish we cud stay like this all day.

Batasan sanda murmushi mai sanyi ya kufce mata ba, a salon mai tafe da jan aji irinna manyan mata tay rau rau da idanunta tai dariya tana cigaba da kallonshi can tasa yatsunta akan fusjarsa tana shafa masa layin kan sajenshi da yake matukar bata sha'awa,...

cike da sigar shgwaba tace nayi missing dinka da yawa nee..if u want we can have 24/7 dama ai ina binka basassuka tafada tana jan hancin sa lightly yay murmushi sosai. Kara Wara idanun shi akanta yy wanda har sun sauya kala babu komai cikinsu face wata sabuwar matsananciyar shaawarta dayakeji aransa,yana bin fuskarta da kallo especially Her lips da ta shafawa red colour shiny lipstick hannu biyu yasa ya kamo fuskarta,a hankli ya shafe hannunsa akan lips din nata sann yafara tsotsar bakin nata a dimauce,wani lumshe idonta tayi tanajin mugun dadin yadda yake tsotsar lips dintan ya meda hannunshi kan kirjinta a hankli yashiga mammatsa su yana shafawa at the same time yana rungume da Ita Wani uban zafi takeji saboda sunyi tsami daga rikon jiya daya mata amma duk da haka bata hanashi ba jin yana yin kasa da hannu going to her throbe yasa tai sauri Ta hauro ta samanshi baiyi wata wata ba idonsa a lumshe ya shiga bata wuta.


**********
Acikin kwana biyu kacal Korafe korafen Dr khaleed yabi ya karade kunnuwan manyan asibitin duk dama an binciki maganar nasa an samu tabbacin cewa duk hadawa aransa yakeyi ma'ana ba abu bane wanda ya faru agaske.

Musamm cewa dayake wai Dr khaleel ne yasaka aka ki bashi go ahead akan case din halisa mansa.

Koda wasu board members suka bibiye kan maganan atake suka samu cewa ba haka bane gudun kar a lalatawa khaleel career dinsa da kananan maganganu yasaka Dr asim yay aproaving masa case din yau da safe amma bawai dan ransa ya so ba.

Sassafe da Dr khalid yaga saƙon email din aproval a computersa, tun a lkcin yake cikin dumbin farinciki dan ji yay kamar an bashi ranshi ne a hannunsa akace jeka kayi duk yadda kaga dama dashi

Yau sassafe ya taho asibitin tare da umrtan sectarynsa akan cewa karta bar kowani irin baqo ya shigo masa izuwa yanxu cos he wll need his time wajen tsara therapy sections da zasu nayi tare da halisa.

Sedei so yake ya kawo wayanda zasu janyo masa samun yarda da kusanci tare da ita..

Dan har yanzu yanakan bakansa na burin amfani da salonsa na yaudara domin cimma babban burinsa na yaudararta da zancen aure domin yasan inta mutu shine zai gaje dumbin dukiyarta datake dashi.

Tunda ya zauna agaban computersa bai ko shaki numfashi ba bare ma ya motsa daga wajen..
All the list of activites da zasuyi ya lissafo su daya bayan daya...

Domin ya samu cikar burinsa na samun kusanci da ita sosai Zai fara ne da CPT wato cognitive processsing therapy,..inda zai yi assesing dinta domin ya gane ta inda depression din yafi kaimi. Sai PTSD,
Zai kuma tattauna da ita akan yadda take reacting ma trauma din,da yanayin feelings dinta ko tunaninta ko wani abnormal behaviour datake exbiting. Kusan abubuwa masu muhimmanci har guda goma ya lissafo su daki daki daya na bin daya.

Snn yay fixing date da time na first meeting dinsu a doka shine ya turawa receptionist a computer dan ta aika ma halisar sako aamma zumudi ya kasa barinsa yay hakan, direct ya dauki lambarta dayake jikin file din akasar sunanta, saida yay gyaran murya sosai sann yay dialling inda abugu daya akacemai the number he dialed does not exist.

Cike da jin haushin hakan ya sake gwadawa kusan sau biyar ana gayamai abu daya, dayan numbar dake jikin file din inda babu suna ya dauka yana bugawa kuwa wayar yafara ringing.

Lokcin Kirjinsa har bugawa da sauri sauri yake yana Allah Allah a dauka yaji muryan halisa

Kusan sau biyu ya kira sann aka dauka wani irin karya muryansa yay salon rigima sann yace "Hello lady...i am speaking with miss halisa mansa.

Bai shirya ba yaji dirar wata husky voice a kunnensa, muryan uztaz ne..cikin harshen turanci yacemai "yes..im her personal assistance may i take ur message doctor.

Cire wayar yay a kunnensa sann yaja tsaki ahankli ya dada dawowa dashi cikin muryansa ma asali yace "yeah..i am doctor khalid from NISA premier hospital i want to speak to my client directly

Uztaz yace well she is unavailable at the moment.

A gatsale cikin katseshi yace oga When will she be available, ni da ita nakeson nayi magana badakai ba abeg!!

Respecfully uztaz ytace mai babu wata matsala..inhar yana son yay magana da ita din then he shud call her next week dan oder data bayar kenan kuma shi bazai karya dokar aikinsa ba..

Da sauri dr khalid yace nooo ahhh bawai nace ka karya dokar aikinka bane, my own case is urgent..I insist inason nayi magana da ita banason nabada sakon ma kowane sai ita.

Uztaz baija dashi ba yace masa its okay u can talk to her by urself next week sir..

Ganin bazai samu hadin kan uztaz ba yasa ya katse wayar rai abace gashi sam sam baison ya turawa receptionist sakon yafison lallai ace shine ya isar da kansa.

Tsabar naci bai daddara ba ya rubuta tex mai zafi mai dauke da time da date da numbers da wasu maganganu ciki harda private phone numbarsa da sunansa akan wai halisan ta kirashi kafin ta zo ganinsa a asibitin gobe.

Ta wayar uztaz ya turo as usual ya bude ya dan dudduba dake ance daga asibiti ne, baiyi wata wata ba ya shige cikin gidan lokcin halisa tana can cikin wani dakin motsa jiki...kokari take ta dawo dakanta in shape and strong sabida ta koma bakin aikinta koda maa zai taimaka wajen warkewa daga cutar datake fama dashi na chronic depression akan lokaci.

Tun daga bakin kofa uztaz yay kncking batare da ta kallesa ba ta bashi izinin ya shigo.

Sport Skin tight ne mai kyau na kamfanin Puma ajikinta baki da crop top dinsa iya cibewarta tay parking suman kanta into a messy burn tana da zaune akan floor tana Streching kafafuwanta sosai.

Babu yabo babu fallasa suka gaisa, snn ya kawo mata sakon tagani da idanunta.

Meeting din nasu na farko Gobe da safe ne wajajen karfe goma.

Sanda ta tabbata ba sunan Dr khaleel hashim wato mijin meenal tagani ba snn hanklinta ya kwnta dan aganinta shidinma wani ciwon kaine agareta sam sam bata bukatar ganinsa a inda take neman sauki.

Batace ma uztaz komi ba tadan ja karamin tsaki taci gaba da abunda takeyi cos what kind of a professional doctor will ask her to call him kafin tazo asibitin sai kace wata yar karamar yarinya mtswchh.

Uztaz yay murmushi da sanyin murya yace boss is time for ur breakfast kin jima anan wajen tun asubah fa...

Akasale ta dago ta dubesa tace kaje toh inazuwa.

Yace okay..har ya juya zai tafi ya dawo yana ssnyar murmushi cikin girmamawa yace maam toh me zaki ce game da sakon likitar...

Jinjina kai tay kadan snn tace "uhm ba matsala we wll go on time amma Zaka kasance tare da ni, kuma karka sake wnn doctor din ya samu lambata kasan banason ana damuna da kira ko.

Aladabce Yace hakane..
Ur breakfast will be ready
In 15 mins.

Batacemai komi ba ta gyada masa kanta yana fita bada jimawa ba itama ta bar wajen ta wuce dakinta domin ta watsa ruwa kafun tazo taci abinci dan tanason yau din tadan fita taje Talba grp of companies kodama zataji labarin yarinyar nan farida awajen kawarta meenal talba duba da yau kusan sati kenan ana nemanta ba sameta ba.


*********..
Da wani irin haushi tare da tamke fuska shemau ta yi alwala tazo ta fara sallahn da tun data farashi harta kammala shi bazata iya tuna ko sunan surar data karanta aciki ba.. tunda ta tsaya akan sallaya zancen daular hadiza kawai takeyi acikin ranta..tana ta imagining dama ace itace yau zata same dukkan wayann abubuwan duniya da hadiza ta lissafo gabaki daya ta share shatar mijinta aranta.

Koya dawo gidan jiya ko bai dawo ba duk wann ba damuwarta bane yanxu.

Kusan ranta a mugun hargitse ta sauko kasa daga ita sai nitynta da niyyar saukewa hafsat guguwar fushi tare da hassadar dake kona mata zuciyarta akai..

Kafafunta ta saka ta tokare kofar dakin saida engr dake dakinsa yana shafa mai ya firgita ya miƙe tsaye.

Daga bakin kofa ta tsaya da wani irin murya marar dadinji tun bata hangota ba tahau dirin masifa tanamai cewa keeeeee
Hafsa...dan ubanki yauma ni kike jira inxo na tasheki kafin kiyi mana aiki???..jin ba amsata ba yasaka ta shigo dakin fuuuu kamar iska da niyyar jan wayar wuta dan ta zazzana mata jiki tana wara idanunta akan gadon taga wayam.

Sai snn ta lura da kamar ma ba akwanta akan gadon ba, cikin azama taje ta bude bathrum nan ma shiru, tabi ta bude wardrb bataga yar jakarta ba..

Wata doguwar hatsalallen tsaki ne ya kufce mata aranta tana cewa hmmmm kaji min shegiyar yarinya itama yanzu wai guduwa tayi kenan? ...kyabe bakinta tay tare tahowa tabakin kofar abayyane take cewa"...ahap, duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, ko angaya mata gidana gidan cin banza ne...taje ta duk inda zataje dubu irinta zasu zo...kuma bashi ne zai hana ruwa gudu ba...
Wann hafsat din ma ai rakaice, Allah ya raka taki gona...tana kammala furta hakan sukayi gamowar kicibis da mijinta abakin kofa.

Wani irin kallon dayay mata mai wuyar fassara shiyasata takoma da baya ahankli...
SHARE PLEASE
[1/31, 8:42 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_

⏯️2️⃣5️⃣

sanyin kallo mai saurin cusa faduwar gaba da engr ya bita dashi yasa shema'un taja baya Ahankli sai kuma atake ta dedeta nitsuwar ta daga idonta sama kar takalleshi da tamkakken fuskarta da babu wani alamar gaskiiya akai

cike da ynyin jefamai tambayar rainin hankli muryanta ciki ciki tace hmm engr kaikuma meya kawoka nan tabi ta karashe maganan da makalallen humm ayanayinta da alamar tambaya abakinta tayi kamar batasan ma yaji zaga zagen datakeyi ba

Hannunsa ya naɗe bisa kirjinsa snn ya kureta da idanunsa masu cike da kwarijini baice mata uffan ba ayayinda dukkansu suke tsaye daga kofar dakin hafsa dayake nan a wangale..

Idanun daya xuba matan shi yasata kasa gane manufarsa sai Duk ta rasa yadda zatayi ta kallesa, already zuciyarta a hargitse yake da fushi dan hatta Daddar qamshin turarensa dake busota ma haushinsa takeji bare ajega kan me turaren..

Hade da makirtaccen kishin rayuwar hadiza data shaƙa a daki ynxu sai Gabaki daya dataga nata mijin a tsaye aranta sai taji haushi, ji take tamkar ma shine yajawo mata duk wata rashin sa'ar aure dataci karo dashi arayuwarta datake zaune dashi.

Aranta ji take kamar da
acan baya bata biyewa dadin soyayyarsa ta auresaba da hala ire iren su mijin hadizan itama zata aura masu mulkin kasa da kuma narkakkun kudi wanda zasuna zuba mata uwar milliyoyin kudi da nuna mata gata.

Ayayin da egnr yay shiru yana tunowa da zantukan hafsat data gayamai jiya tare da irin maganganun dayaji shema'un tanayi yanxu atake sai lamarin nata yahau bashi mamaki acikin ransa dan bai taɓa cin karo da wann hali nata ba,..

Nauyin idanunshi ne yasata saurin kau dakanta gefe cikin yanayin sanyin izgili da renin wayo ita hanklinta ma gabaki daya ba ajikinta yake ba ita haushin rayuwarta ma takeji daya kasance mata ahaka.

Muryansa a nitse yace shema'u Banfahimce abunda kika furtamin ba. I heard ur voice shouting. Ko nayi lefine danazo nan dubawa.

Adan fizge ta juyo cikin son ta huce haushi tare da maida lefukanta akansa, ta ɓata ranta tana huci snn tace

A'a mahmud dakata min..karma ka soma bani wani excuse kawai kacemin abunda kakeyi kenan idan bana nan just Explain urself to me akan me zakazo har kofar dakin mai aiki dakanka
..aini matar gida ce, dan nazo nan ina ihu dolene in tadata tazo tay aikinta tunda ba baccine ya kawota ba kai kuma fa?

Cikin katseta yace" ohhh ai Bantaba sanin da ihu da zagi ake tada mutum a bacci ba...so, is dat how u treat dat poor girl???

Wani rau rau da idanunta tay jin ya basar da sharrin datake son lakamasa ya kamo wata zance, a fuske tace kamar ya..nide ban zage kowa ba..zai yi magana cikin katsesa tace..
mahmud nidan Allah abar wann maganan ya wuce dama nalura tuntuni yarinyar nan bason aikin nan takeyi ba besides ma guduwa fa tayi dan babu kayanta acikin dakin.

Koda ta fadi hakan sai taga ko wani alama na mamaki bai nuna ayanayinsa ba, tare da kyabe baki waidan ma karta gano inda yadosa bare ta sauya masa kan maganan, acikin nitsuwa yace mata toh Meyasa ta gudu, Did u knw anything abt it. Ko ana mata wani abune da bata so agidan nan.
.
Tace me kuwa za'a mata banda yan aiyukan gidan nan danake sata tayi? Kaji ka da wani magana fa ni inama nake da lkcinta, Kawai de tsinanannen son kudine irinnasu na talakawa ai ba saima an tambaya ba dama can dan sace sace da take min da dauke dauke nan ne na hanata Shine kwanan nan tazo min da wani sabuwar salon makirci wai nabata kudi takaiwa mamanta nikuma nace mata bazan basu ko asi ba sai ta yimin aiki and am sure dats why she ran away. yo hakuri dama nakeyi da ita banda haka wazai juri zama da barauniya.

Cikin katseta engr yace shemau kiji tsoron Allah and watch what u say dont lie to me..ce miki tay zasuje suci kudinki ko zancen rashin lafyar mahaifyarta ta furta miki?

Da sauri ta kallesa da mamaki a fuskarta jin ya furta hakan cikin basarwa tace Wani rashin lafiya? toh nide batacemin uwarta bata da lfya ba..

karasowa daf da ita yay hannunsa duka na cikin aljihun wandonsa tare da daure fuska ya tsaya yana kallonta fuskarsa babu alaman wasa ackii.

Yace "kiyi Adalci wa rayuwarki shema'u
Kisani akwai ranar kin dillanci. Nasha mamaki danaji cewa yarinyar ta rokeki hutu akan batun lafiyar mahaifyarta amma kin hanata zuwa da zancen banzanki na zargin dakike mata na sata shin meta taba sace miki..and why

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login