Showing 135001 words to 138000 words out of 171903 words
faruwar abun nan taketa wasu shirye shirye, already ta hada wani boyayyen comittee na wasu tambatsasun mata da suke neman labaranki kullum,am sure tanason in anzo meeting din ne za su cimma burin su akanki shiyasa ta matsamin lallai sai an hada baki ance miki kizo.., but amma ya akayi kika ganota haka?
Karamin Dariya halsy tay snn tace ai abakine kawai ake cewa "Women support women" amma a zahiri women are the biggest enermies of each other..ina lura da moves din kowacce mace acikinsu sabida kamfani na ne..nina san wahalar danasha kafin na daga shi..so, i knw the real ones wanda harkan arzikine kawai ya kawosu wajena snn nasan wanda cutane ya kawosu,wasu kuma kudina ne kawai sukazo kwasa.
Yace toh ya kenan zamuyi dan inhar wann meeting din ya tabbata yau Allah kadai yasan me zata gayawa mutane akanki. Ni Bana tsoronta but Am scared of irin mutanen datake tare dasu dan yan siyasa ne masu karfi.
Hmmmm kawai halisa tace snn ta juyo ta kallesa tana murmushi me sanyi....a shashance tace "Mance da su kawai uztaz.. ina wayarka yake???
Cirowa yay daga aljihunsa lokci guda ya mika mata ta amsa
Wani layi tay dialing akai yana ringing biyu aka dauka, "Good morning sir this is mansa cosmetics and materials. how can i help u today.???
Halisa tace .."maria Abolarin?
Tsaye sectaryn ta mike jin muryan halisan ne dakanta bakinta har na bari tace yes maam.. gud morning maam..
Kai tsaye halisa tace... "maria i want you to Cancel all my meetings today. new time will be updated to u soon and no one shud question that.
Acikin girmamawa tace yes maam. Righ away!!
Halisa tana katse wayar maria ta koma kan computarta dake gabanta batare da wani bata lokaci ba ta turawa kowa sako mai tattare da odern da halisa ta bayar.
She is the owner and the ceo of her company dan haka dolene kowa yayi mata biyayya.
Mikawa uztaz wayarsa halisar tay snn tace ka kawomin breakfast din nan kawai zan fara shiri ahankli.
A ladabce Yace okay maam Yana fita bai wani jima ba sai gashi nan ya dawo da tray din abinci
Soyayyen irish ne da sauce din kwai da tea da bread da akayi toasting dinsa into golden brown colour. Yana aje mata abincin ya fice waje yana ta amsa waya daga officials na office dinsu kusan dukkan suna masu tambaya ko halisa zata dawo bakin aikinta ne yau ganin sakon daga meeting din daga wajenta ya fito directly.
Tunda halisa ta zauna agaban abincin tunanin Abunda zatay da rayuwarta kawai takeyi musammn ma da makiyanta dake zagaye da ita suka dada bayyana mata asarari.
Dan Yana daya daga cikin manyan temakon da zach yay mata arayuwa daya koya mata gane kan halayayyar mutane cikin sauki. Shine ya nuna mata yadda ake binciken sirri akan ire iren mutanen wajen aiki da kake zarginsu da zagon kasa and thats how tasan suwayene masu cin kafarta acikin share holders dinta.
Sama sama taci irish da sauce din sabida man gyada yaana yawan kashe mata jiki.
Toasted bread din ta dauka ta cinye ta sha da tea din duka snn ta mike tsaye ta koma bathrum ta kara wanke fuskarta da sabulu da cleanser ta fito tay parting dinsa dry
Ta shafa cream da lock in oil snn tabishi da Spf ta shafa concealers da foudations tay wani irin karamin kwalliya wanda ya wani irin sauya mata kamanni daga na wanda take cikin damuwa.
Wani irin bone straight wig cap mai dan karan tsada ta ciroshi a park dinsa black colour ta kima akanta ta wani irin gyarashi da coiling gels ya zauna mata cif cif ya mata kyau kamar nata ne.
Closet dinta data jima bata bude shi ba ta nufa ta dauko wata arniyar cool grey colour palazo da white coller shirt na steve meden me gutun hannu ta saka su ajikinta sann ta bi kan rigar dede kan hadadden kugunta ta dora masa bakin belt na gucci wani irin kyau na daban tayi.
Bakin takalmi me tsini da karamin jakarsa na kamfanin gucci ta dauko snn ta feshe jikinta da turaren yara da lattafa masu azaban sanyi ta dauki littafin Dr asim din ta saka ajakarta sann ta fito ta samu uztaz yanakan amsa waya haryanzu bai gama ba.
Suna hade ido yace maam we are late doctor nan ne yaketa kira tun dazu..
Agaggauce Tace am here lets go mana.
Jakarta ya amsa ya mata jagora har sukakai waje.
Daga ganinsu kasan uztaz yana balain ji da halisa a duniyarsa dan kallon yar uwansa na jini yake mata ba ogarsa ba
Hadadden jeep wrangler dinta baki daya dace da hadadden shigar datay ya dauko tare da bude mata kofar ta shiga ciki..
Tana zama tace masa
Nayi ma meenal alkwarin zanje na sameta idan mun fito daga asibitin wajenta zata kaini.
Bai mata musu ba
Yace okay maam
Horn yay malam liman yazo da gudu ya bude musu motar yanamai daga mata hannu daga windon ta leko snn ta masa murmushi me sanyi.
Yana rufe gate din tun basu kara da gaba ba wata farar lexus ta sha gabansu adede hanyar mafitar anguwarsu tun daga cikin motar uztaz ya gane cewa doc khalid ne dan Shide harga Allah bawani burgesa likitan yakeyi ba dan aransa yaga alaman kamar shidinma shishigewa halisan kawai yakeso yay.
Juyowa yay ya kalleta snn yace maam I think is the Doctor.
Tace okay. Kaje kaji me yake tafe dashi bazan iya sauka kasa dominshi ba
Dr khalid ya sauko da rawan jikinshi saiga uztaz nan ya sauko shima atake ya sauya fuska suka gaisa sama sama.
Yace I came to check on ur boss you knw she is now my responsibility too.
Uztaz yace ahanyar zuwa asibitin muke yanxu sai kaje ka jirata acan.
yake dr khalid yay masa gashi babu halin ya rainashi ganinsa fes fes acikin tsadadden suit kamar wani presidentual escort, mimmika wuyarsa yake da wayo wai koda halisan zata dan hangosa ta fito amma uztaz yay masa babakere ya hanasa sakat.
Ganin bazai samu shiga ba yace its okay..cant i speak with her?
Uztaz baice mai uffan ba ya zura hannunsa a aljihu
Wayarsa ya ciro agabansa ya kira layin halisar bugu daya ta dauka tace what wai meya kawosa?
Ahankli yace He said he want to talk! Tace badamuwa its okay ina zuwa. Tana fadin hakan ya katse wayar baice masa komi ba harsaida halisan ta gama jan minti biyar dinta snn sauko ta iso.
Tun da ta bude motar ya dan hango ta yaji gabaki daya ya rude..
Tsabar maitar mata jikinsa har rawa yakeyi ta ciki duk ya kasa tsayuwa akan kafafunsa idanunsa kamar zasu fadi kasa wajen kallon halittar halisa musmmn ma yau dayaga ta danyi kwalliyar daya fito sosai..
yay nan yay nan dakansa sekace kadangare, sai hangame baki yake yana sauke wasu kananan giggleskamar wanda ake sosamai ramin tsuliya.
Tana karasowa uztaz yaja baya ahankli tana dan murmushinta mai aji gamida tafiyarwa tace
Hi doctor ???
Kusan a rude Yace khalid..my name is Dr khalid..
Da murmushi ayanayinta tace yes i remember you... ina fatan babu wata matsala
Cikin dedeta nitsuwarsa yace no bawani matsala
Naga bakizo ba and i was passing by nace bari na dubaki..
Tace dats totful of u amma next time idan zakazo gidana u can call my personal assistant for permission is dat okay?
Yace sure. So shall we???nace In ba damuwa i will love to drive with u tunda yau munyi latti se mufara tattaunawar mu tun ahanya ko.
Da kamar bazata amince ba daga bisani tace okay yeah Why not..Ji yay kamar zai tashi can sama dan murna duk bakinsa yakasa rufuwa.
Da ido tay ma uztaz alaman ya bisu abaya
Doc khalidi nata saurin yaje ya bude mata gaban motarsa uztaz yay sauri ya rigashi kafin tazo har ya bude mata motar.
Kasa kasa yay ma uztaz din wani irin kallo uztaz ya bishi da harara a bayyane har sede ya make sure halisa ta zauna snn ya rufe mata motar ya zago yace masa" sir,...doc khalid ya juyo wani irin stern look yagani afuskarsa yace masa "Be careful while u Drive..
Adan tsorace dr khalid Yace okay.
Uztaz bai kulashi ba ya koma mota abunsa ya fara binsu abaya.
Suna fara tafiya kamr wanda yake jira akan uztaz din ya soma janta cikin hira yace that guy is tooo hot oo baya wasa da alaman yanada zafi...So is he ur bodygurd.?
Atakaice Tace masa no.
Ya kuma mata wani tambayar yaga kamar bata da lkcin jan hira dashi dan dolensa ya dawo da maganan bisa abunda ya shafe lafyarta.
Nan ya fara tambayarta akan book din..Tafara gaya masa cewa ta fara karantawa. Hira kawai yake mata kala kala kamar irin sun jima da sanin juna din nan.
Yace Kinsan nima naso na rubuta book irin wann amma Doc asim bashine ya koyardani ba soo only his student are allowed to featured in his editions.
Tace really?..
Yace yess oo ai dana rubuta wani kalma aciki da bazaki jima ba zaki warke sosai.
Tace hmm but dis is one also is good...i like it.
yace yeah yeah kananan likitoci akwai rawan kai so its obvious u will like it.
Cike da jan aji Tace wow kananan likitoci ne ma, so Who wrote chapter seven then, ai na dauka ma kaine?
Da mamaki aransa Yace har kin kai chapter seven? ..
Tace no na tsallake nayi naje wajen..cos the begining is soo boring
yace okay its one unprofessional therapist haka a hospital namu inata kkrin ma kar asakashi a case naki.
Yana fadin hakan kawai se mind dinta ya tuno mata da ranar data jiyo sa yana magana akan Dr khaleel kawai saita share zancen bata kara tambayarsa akai ba dan batason ma taji ance shine bare ta tsane book din shiyasa har suka iso cikin asibitin bata kara tambayarsa komi akan book dinba
Suna sauka a harabar tafara dube dube dan Mamaki tasha da bataga uztaz abayan su ba, har saida dr khalid ya sauko ya sameta snn saigashin nan ya shigo.
As usual yana bayansu har suka kai office din after like 40 min suka kammala tattaunawa da Dr khalid akan sauran abubuwan daya rage basu kammala jiya ba.
Yaukam Tasha tambayoyi game da rayuwarta amma hakan nan dai ta daure ta boye abubuwa dayawa acikinta dan amincewa da dan Adam akan sirrin rayuwarta yana neman yay mata wuya ynxu.
Shawo kanta da Dr khalid yake tunanin zai masa sauki sai gashi yana neman yay masa wuya sosai dan sai ya kwaso wani tambayar dayasan zai mata ciwo ya raunata ta sai ta shanye aranta snn ta juya zancen ta bidashi wani ma'ana na daban.
Gashi next session dinsu sai next week kuma practical sesseion ne baison suyishi a asibitin shiyasa yau din ya gwada zuwa gidanta direct koda zai samu sakin fuska daga gareta, yin excise din yadda yake so a asibitin bazai masa dadi ba dan yasan alkciin khaleel yana nan zai iya tsoma masa baki gashi ya tsanesa sosai.
Yauma har waje ya rakata dan yanata cusa mata kai yanason su dawo abokan dole sede har sukayi sallama yau din bai wani gane hanklinta ba dake yanayin uztaz kawai take dubawa.
He look very alert and suspicious akan asibitin
Har Allah Allah take su shiga mota ta dan tambayesa ko lafiya
Tana shiga kuwa taga ya dau hanyar anguwar lekki
Da ita gashi gudu sukeyi
Ba kakkautawa gani tay suna ta tafiya ciki cikin anguwar harma bata gane ina suka dosa ba.
Abun ya dameta aranta tun tana shiru taji bazata iya ba Tace uztaz kamanta abunda nace maka ne ..i said zaka kaini wajen meenal wani hanyane kuma wann
Yace i know maam i just want to confirm sumting..
Nervously tace Something like what?
Bai amsata ba ya waina kan motar yasha wata kwana da ita tun kan tay magana sai ganan wasu motoci dasuka sha bakakeken tintted har biyu abaynsu daf daf sun wuce su fewwwww sun wuce caannn gaba harsaida taji ta mugun tsorata da su .
Kashe motar yay snn yace mata maam someone is following us tun daga asibitin nan amma nasan inda suke buya anan anguwarne
'A mamakance Tace really? So How did u know about it.
Bai jira ba ya ciro wayarsa ya mika mata pictures din daya dauka na garajin bata gane komi saida tay zoming hoton sosai ajikin badge din rigarsu taga logon kamfanin zach wani irin sarawa kanta yayi.
Tace "Ka tabbata sune suke bibiyata?..yace eh na tabbata jiya har nan na biyosu yauma kinga sune suke binmu ahanyar asibiti shiyasa na tsaya ina marking dinsu.
Dafe kanta tay jin yana sarawa mata da karfi snn tace "I know them.
Yace who are they
Adan rude cikin yanayin rashin jin dadin jikinta tacemai mubar nan wajen kawai uztaz just take me to the jasmine.
Batare da bata lokaci ba ya juyakan motar basu tsaya ko ina ba sai gidan kawarta jasmine.
Sauka tay a rude tun bai zo ya bude mata ta kama hanya zata nufi ciki
Yace shud i wait for u
Tace nooo kaje ka dada bincikamin masu wann motar and make sure they belong to this logo
Idan ka gama ka kirani awaya.
Yace yes maam . but are u okay?
Ahankli tacemai i will be.
Da sauri ta shige cikin gidan ta same jasmine na zaune akan kujera ta kunna slow music tana video call da saurayinta tana kuma shan shisha.
Yanayin da halisar ta shigo yasaka ta kashe wayar ta miƙe tsaye
Tace"Babe..whats wrong ya naganki ahaka
Hawayenta datake dannewa suka sauko kasa yarrrrrrrrrr. Cos she is emotionally weak.
A rude jasmine tace meyafaru halisa???
Karamin Kukan gajiya da ryuwar nan ne ya kufce mata tace jasmine..the devil is really working againts me.. im never going to have any peace of mind
Jasmine Tace how?
What happen..meye
Ahankli ta goge hawayen snn tace Ive met my doctor.. yafara min treatment har yau din nan nafara jin sauki sauki nafara kkrin yin tunani akan rayuwata.
Then kawai saiga wasu motoci suna bina and gues wat???
A tsorace Jasmine tace "what?
Bakinta harna rawa tace its zach..
Take jasmine ta hade rai tare da zare karar tabar dake bakinta tace what?
Halisa tace wallhy shine jasmine..zach is after me. See, I knw all his secret logos shiya nunamin. his boys are following me..im just scared.. what if he came to destroy my life what if he want to come back to me for a secnd chance jasmine am soo scared zuciyata baida wani karfi kuma banason na sake komawa cikin halin da nashiga ciki akansa da ko warkewa banyi ba.
Da sauri Jasmine ta rikota suka zauna ta debo ruwa mai sanyi a cup ta bata tasha ahankli tana rarrashinta hartay shiru...
Sai can snn Tace halisa
Kinsan inde zach ne ya dawo bazai bi wani kwana kwana ba direct zaizo ya gaya maki feeling dinsa ko?..
Ahankli Ta gyada kai tace eh na san da haka
Tace toh Sede in an gaya masa wani abu akanki
Or..maybe yana son ya tabbatar da cewa baki tare da wani or he saw u with sumone else and he thinks u have replace him dis quickly.
Halisa tace and so what? Ba rabuwa dani yayi ba
Nide tsoro nakeji kinsan yanzu fa yasan komi akan past dina i dont want my present life to get ruined by my past
Ayanayin lallami jasmine ta riko hannunta tace haba halisa babu abunda zai iyamiki daibJust calm down kiyi tunani a inane suke bibiyarkin?
Tace uztaz yace min tuna asibiti ne.
Dan shiru jasmine tay snn Tace okay here is what we will do dan musan asalin gaskiyar shi.. Is dat ur doctor friendly with u?
Tace yeah..
Jasmine tace perfect
Toh ai dashine zamuyi amfani wajen warware wann lamarin. Dan Inde akan soyayya zach ya dawo he will follow u more often idan kika soma kulla kawance da Dr dinki...amma idan dan wani abu ne we wll act ahead of him..ina uztax yanakan bibiyarsu? Did u tell ur friend hadiza...zata iya sawa a temaka mana da wasu bayanai.
Shiru halisa tay acikin tunani bata amsata ba tukuna......
SHARE TO UR GROPS
[2/11, 9:58 PM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB*_
_BY SURAYYAHMS_
30.
Duk yawan Daƙikanin lokutan da halisa ta dauka acikin shiru bashi yahana jasmine tsura mata idanuwanta ba.
Ajiyar zuciyane ya kufce mata tace "Hey Halsy i am asking u a question kin min shiru, nace kin gayawa hadiza maitama kuwa?...Juyowa halisan tay ta kalleta Ahnkli snn ta sauke ajiyan xuciya fuskarta kamar na wacce bata cikin hanklinta tace.."No...bangayawa kowa ba. jasmine batace komi ba ta kura mata ido tanata kallon mood dinta daya sauya gabaki daya yadawo na damuwa.
nauyin idanun jasmine dake yawo akanta shiyasata lumshe idonta ahnkli snn ta juyo ta fuskanceta tace...
"Jasmine look,..nifa bana son nagayama kowa maganan nan ne, atleast kedin ma kawai ya isa..ni de kawai banason tashin hankaline. Atake jasmine tace but why not?Akan meye sauran bazasu san me kike ciki ba cos dis is pretty serious ba abun wasa bane..zach yana miki kwantan bauna ne halisa, kafin kizo ki hankara zai kamaki a inda bakiyi tsammani ba so, we all have to think fast..
Idanunta ta lumshe muryanta na rawa rawa nervously tace ..."Im thinking jasmine...i am seriously thinking..kawai de...kasa cigaba da maganan tay dan dede nan taji wani baqon rauni ya rufeta atake kalma ya dauke akan harshenta cak tanajin kamr ta fashe ma jasmine din da kuka.
wani irin yanayi mai gajiyarwa taji yana kkrin shigarta, idanunta a lumshe sosai cikin yanayi mai kashe jiki ta cusa hannayenta can cikin suman kanta tana calming kanta ahnkli kasar makoshinta tace "ohh jesus christ, i am sooo done..wayyo Allahna na shiga uku na!
Da sauri Jasmine ta riko hannunta sigar lallami tace baki shiga uku ba halisa,i am with u..kawai ki kira hadiza yanxu kuyi magana dan ita kadaice take da cikakken hanyar da zata binciko mana moves din boys din zach acikin kankanin lokci. Kekanki kinsan mijinta yana da iko da security system na garin nan, it wont take them a minute to figure those guys out.
Agajiye halisa ta bude lumsashun idanun nata da suka jike da ruwa aciki ta kalle jasmine da sacewar jiki tace
" ..Jasmine i knw..
Amma wann fa ba mafita bane ki yarda dani.. Dan dukan kawayena bazasu tsaya su fahimce komi ba dan suna balain jin haushin zach, sun asalin tsanarsa wallh idan na gayawa hadiza ka ita daima she will make sure tamasa wani abu mummuna, snn koda hadizar batay ba shemau da meenal fa? They dont have chill..sunajin cewa zach ya dawo kaina wallh komi zai