Showing 141001 words to 144000 words out of 171903 words
kamar nayau ba.
bude wani scrolls tayi ta dauki wata sharbaben farar gilashi ta kamfanin rayban ta kimashi akan fuskrta snn tafice da sauri sauri.
Tunda ta fito bata kalle kowa ba bare ta amsa wani gaisuwa, Daga cikin mota shema'u take kallon fitowartan harta karaso wajenta bata iya daukevidanunta akanta ba, Slim fit pper red suit ta saka mai faffadar wando Da wani irin white shoes mai dan karan kyau dede da kalar yar cikin suit dinta daya kenan fari kal shima kuma shara shara....
dan haurawan da fuskartan yay a sakamakon marin da femi yay mata yasaka tay kwalliya mai dan yawa danta rufe wajen dake bata saba ba sao kwalliyar yay mata kyau sai ta fito daban bakamar kullum.
A tsarge ta shiga motar shema'un gani take kamr duk zasu gane halin datake ciki, sede Tana zama acikin motar shemau ta kare mata kallo ganin irin kyan datay yasa tay murmushi snn tace Damnnnn gaskiya yau ina taya prince femi kishi cos what is this vicky?
Rau da ido vicky tay kirjinta na dan bugawa tace 'what?..menayi.
Dariya shemau tay tare da kunne motar tana cewa "girl i aint gonna lie u look super doper wani yaganki ahaka ai zaice ure just 20. U look so gorgeous..hummmmm
Murmushi vicky tay cikin sauke boyayyaen Ajiyar zuciya na relive, snn tace thanks my lady.. kema ai seki yi ahnkli da wann irin wankar dan bazan iyama gayu bayanin cewa ke matar wani bace dan bazasu yadda ba..
Atare sukayi dariya ayayinda shemau ta kama hanya dasu izuwa inda hadizan take tana driving tana jan vicky da hira dan sosai taji dadin cemata da akayi batay kama da matar aure ba dan dama babban burinta kenan yanxu.
Murza stiring motartan take cikin shakar santin hirar tana dariya tana cewa Ai baku ga komi ba vicky, am just getting started.
Vicky tace is a lie ooo, E get why..kode kode engr yafara hango wasu babes dinne
Dariya shemau tay mai karfi snn tace Allah ya sawwake,..yama isa ne ya kalle wata bayan ni? Shin akwai wata warce ta isa ta goga kafada danine ma, hahaha phew..I just want to be a queen that i am..ina son sauran mata akaina su gane cewa aure bashine karshen rayuwar su ba kin gane. I gat to Dress to kill meye amfanin duniyar inbakaji dadinsa ba, Dan haka get ready to see me slayyyy.
Vicky tay dariya tace team slay mamas
Shemau tana shawo kwanan anguwan tun bata amsa vicky ba sai kiiiiiiiiiiiiiiiii sukaji antaka break da karfi saida dukansu suka razana suka firfito da idanunsu waje.
Wani hadadden bakar sport car ne sabuwa ta tsare musu gabansu a acikin yanayin ganganci babu ma ta inda zasu wuce batare da sun koma da baya ba.
Tun daga cikin motar Vicky ta kare ma motar kallo sama da kasa ahankli ta kyabe baki ganin ferrari ce sabuwar fitowa kimanin milliyoyin dala na amurka .
Ran shemau daya riga da ya hatsale a fusace ta buga kan stiring benz dinta yay kara pim pim pim pimmmmm, and who the heck is this bitch.
Vicky tace bana tsamamnin mace ce aciki hala namiji .
Shema'u tace sam namiji bazaiyi tuki haka ba, inba mace bane waye zaina tukin ganganci haka acikin anguwa.
Sunfi minti biyar suna danna ma mei motar horn amma ba'a fito ba sann bai basu hanya ba
Gashi bawajen tsagawa sedei in zasu koma baya su bada hanya which aganinsu hakan bazai taba yuwa ba.
Da alama kowa na ji dakansa.
Shemau already tay zagin duniyan nan ta dauka irin karuwan slay queens din nan ne masu dauko manyan motocin samarikansu yan siyasa suna baqu da shi agari.
Karuwae banza jaka Halama bata iya tuka motar bane ya tsaya mata anan..mtsw
Aikuwa inde bazata mata ba saidai mu kwana anan dan wallh bazan matsa mata ba.
Tana kan masifarta vicky ta saukar da nata girman kan ta sauko kasa ranta a mugun harde tana jan tsaki tanufi gaban motar direct cikin wata mayyar cat walk daya jefa yaron acikin wani irin yanayin da shikansa bai isa yace zai iya fassarashi ba dan tundaga cikin kwaryan kwakwalrsa yakejin sonta na fisgarsa with sparks kamar anjonasa da wutar lantarki.
Jikinshi take ya dau rawa har izuwa tafin kafarsa yakasa yin komi ya tsurawa vickyn ido harta karaso gaban motar snn ta kwankwasa masa glass, kansa ya zamar a kan seat din tareda komawa da baya ahnkli ya jingina amarairace yana sauke ajiyan zuciya batare da yasan yay hakan ba, jin dadaddar muryanta na tsagawa harta zuciyarsa yasashi lumshe ido ahkli jin tana cewa"..Hello..Excuse me
Ure on the way...u got to fuck off.. saida ta fada kamar sau biyar dede inda muryan nata ya qamsheshi kafin nan ya danna wani abu ajikin kofar ahnkli glass din ke sauka dakansa kasa
Lokcin har shemau ta sauko itama ranta abace sosai sun kafe motar da ido suna jiran glass din ya gama sauka suga wata tantiriyace aciki.
Ko rabi da sauka Glass din baikai ba kayden yay tozali da abar kaunarsa kuma muradin ransa wato vicky williams.
Akallon da sukama juna na farko saida wani quick shocking sukaji me mugun karfi, kyawanwan idanunsa ya zuba anata tabi ta lumshe nata idon ta bude atake jinwani abu yana tsarga mata azuciyarta. wani irin maitan kallo yay ma kwayar idanunta dake sarkafe anashi sending her chills all over her body... wani irin zutttt zutt taji na tsarga mata har cikin brain nata atake ta kwace idanunta da karfi anashi cikin sauke ajiyan zuciya mai zafi tare da dauke kanta akansa da sauri.
Itakanta bata san me taji datagansa ba kirjinta kawai ta dafe ta juya tana kallon shemau
Tace "Oh my gudness shema'u its not even a bitch its one mother fucker who can't drive.
Itako shemau mamakine ya rufe mata baki dan dik tunaninta mace ce aciki
Ganin kayden din tay na farko sai kuma tayi sanyi ganinsa saurayi danye sharaf wanda alaman hutu da nera ya gama ratsamai fatar jiki.
Daga gefenta vicky take satar kallonsa cos he is fucking handsome like filthy gorge and cute, skin colour shine iya abunda ya rabashi da kaninta nile wajen tsayi da dirin jikin mai matukar daukar hankli.
Dadaddar sanyi da qamshin turaren da ke fitowa acikin motarsa suke shaka ta waje kamar zai sakasu bacci.
..Gashi nan chokolate skin ne amma irin kyau mai sanyi din nan ne ke tafe da yanayinsa mai sace gabobin jiki da kuma narkarwa, ga wata cool smiles dake zaune daram akan dan karamin bakinsa dats so soft and socculent yashafa gloss akai dake nuna alaman tsaftarsa da nitsuwarsa, daga ganinsa kaga wanda hanklinsa yakenan akwance baida wata damuwa a duniyar nan.
Acikin sanyin jiki da saibi yabude kofar ferrari sport car dinsa ya sauko kasa dukansu suka bishi da kallon tsaf daga sama har kasa dan bai ishe su kallo ba.
Jan riga ya saka da bakin wando wanda basai an gayama maka ba kasan original ne daga can kamfanin parco rabbane koda ya sauka kasa jingina da jikin motarsa kawai yay baice musu komi ba ya tsura musu gajiyayyun idanunsa wanda yay kamar baiya kallonsu sede rabi hanklinsa da brain dinsa nagakan vicky ne data tsareshi da wata iriyar muguwar harara.
Smirks ne ya kufce a fuskar shema'u dan haka kawai taji jinintaya hadu dashi, . a nitse take kallonsa, kafin nan tace excuse me young man, yana murnushi ya kalleta tace i hope u knw ure on our way..?
Tun bata karasa ba vicky dake hararsa tace "Now get in ur car and move back... okay?
Ahankli yace okay.
But i can't move..
Shema'u Tace why?
yace i just cant reverse back.
Vicky tace"Are u insane??
Ure driving a car and u can't reverse?...Where are ur parents kid.
Yace hey am not a kid .
Ranta aharde in a very bossy tone tace
"Then drive.
YiYay kamar baijita ba Saida ya lumshe idonsa ya bude a mugun kasale snn yace i told you.
tsawa ta daka mai
"you told me what kid?
Tun Kafin ya amsata tarufesa da fada.."Baka da Hankine ana maka magana kana kallon mutane cikin ido did i look like ur mate?
Cikin tsareta shema'u tace vicky pls calm down yaro ne fa karkina dakamai tsawa.
Ahatsale vicky tace a'a shema'u zamu tsaya ne yaro yana rena mana hankali waibaisan ya ake reversing mota ba toh Uban wa ya bashi motar ahaka? I can't tolerate this shit. ...jiranmu fa hadiza takeyi and these kids of now adays yan iska ne ba a lallabasu kawai yaja akwalar motarsa anan yabamu hanya jare.
Masifa take amma batasan dadin muryan nata yake ji har cikin kokon ransa ba...
shidai baicewa komi musammn ma daya gane cewa sakalcin dayake baza musu acikin nitsuwa shiyake dada hatsalata, shemau kuwa burgeta yaron yay har cikin kokon ranta dan ita fa duk inda ake harkan kyau, aji da nuna nera a fili tanason hakan aranta.
Abu kamar wasa Hakanan sukayi sukayi dashi yabar kan hanya amma yaki sam yace bai iya reversing ba, sai rigima da shagwaba dayake ma vicky mai ban dariya har da ce mata "mama" "mummy".. har kiris ya rage vickyn ta wankamai mari ta dinga mai masifa kamar wani danta shiko dadin hakan yakeji aransa bana wasa ba.
"I dont blame u i blame ur parents"..go and kill ur self zaka gane, da uwar katon kanka awajen kamar zuma rock.
Intay masifar sai ya sunkuyar dakansa kasa yay karamin dariya inya dago kuma saiya fuske ya marairace mata fuska sai kuma yaita kallonta kamar zai hadiyeta.
Karshe dai shema'u ce ta amshi key din motarsa zata jaaaa tamaida shi baya domin su samu hanyar wucewa tana shiga key din ya ki aiki cos bata iya operating irin wnn cars din ba dake bata san manual din latest edition na ferrari sports cars ba, hakanan ta dinga rokon vicky dake tasan mijinta femi yana iya siyar duk wata sabuwar sport car agidan nasu sede in bai fito ba, hakanan itama taki firrrrrr tace bazata shiga motarsa ba, ahaka saida suka ɓata wani 20 mins awajen dakyar ta amince tana shiga motar shima yabita ya shiga shima ya zauna abunshi ko kallonsa batay ba tajashi baya da mugun gudu acikin yanayin tukin ganganci saida ya raxana ya kureta da ido.
Tana jefashi gefe ta bude motar tafice yanata kallon bracelat dinta daya zame kasa acikin motar nasa baice mata uffan ba. Dadi yakeji aransa kamar shaukin zai kasheshi jin qamshin turarenta da ya cika masa cikin motarsa bana wasa ba, Suna barin wajen ya tsuguna ya dau bracelet din ya saka a aljihunsa yana murmushi ahnkli yaja motarsa ya dau hanyar gidansu hanklin sa akwance
Bakaramin dariyar vicky shemau tay ba ayayinda tke memeta mata irin masifar data zubawa yaron ba.
Tana dariyar sosai har tana shakewa Tace habawa vicky u no get chilll ashe?Ni wallhy bansan kina da wann halin african mummys din ba duk kinbi kin balbale yaro da masifa kamar ke kika haifesa u no even see as the boy fineeee kamar in sace shi
Hade rai vickyn tay tare da jan tsaki tace Abeg abeg forget dat part shema wann ba abun dariya bane the boy is freaking annoying kiga wani rigamar dayakeyi kuma yasan bai iya tuka mota ba zai dauko motar gidansu yahau kan hanya dashi. Inyaje ya kashe mutane fa...ko ya kashe kansa. Shirmen banza kawai i do blame deir parents da suke barinsu suna mana yawo agari da motocin gidansu da sunan nuna musu gata wawan yaro kawai.
Banda dariya babu abunda shemau takeyi
Cikin dariyar tace Dis Adorable angel cannot die ooo he is too cute abeg. Kiga jikinshi so fresh..so young.
Vicky ta ciza yatsarta gwanin ban dariya snn tace naso da wanka masa mari nayi wallah kiji fa harda cemin _"i am sorry mumy"_ ..jesus ..kai kai saiyanzu ma abun yamin zafi..shema shebi u told me i look young and beautiful today amma meyasa dan iskan yaron nan zai karemin kallon snn yace min mumy? Nayi kama da uwarsa ce????
Tuntsirewa da dariya Shema'u tayi tana cewa sugar mummy mana ke kuwa ki gane mana duk ya rude agabanki wallh
har suka isa inda hadiza take bata dena tsokanar vicky akan mummy din da kayden ya kirata dashi ba.
Suna isa wajen hadizan suka sameta harta kammala shiri tana jiransu basu wani bata lkci ba suka rakata airport suna masu mara mata baya harsaida ta bar kasan kafin nan suka rabu kowacce ta wuce inda zataje
**************
Baccin awa biyu masu kyau halisa ta samu agidan jasmine kafin nan ta kira uztaz yazo ya dauketa yakaita gida.
Tun ahanyar har isowarta babu Abunda take tunani face yadda zata soma playing fake friendship da Dr khalid dan harga Allah bata jin shaawar keeping company na wani namiji arayuwarta musammn ma da sunan soyayya ko abokantaka.
Bata wani yanke hukunci ba harsaida tay wanka ta sauya suturarta izuwa kaya marasa nauyi snn ta samu abinci tanaci ahankli har ta amince da maganan aranta.
Tabarta ta kunna tana zuka a brain dinta cewa take She have to do this badan son ranta ba sedan ta rabu dajin fargaban dawowar zach rayuwarta na har abada.
Wani dn karamin mac book dinta ta dauka tana daddanawa can ta bude sabo kuma boyayyen instgram acct dats anynomous ta zuba wasu mayun hotunanta na modeling akai wnda duk wnd ya kalla saiya sake kalla.
Bayan ta kammala nn taje tay searching din acct din Dr khalid din ta dudduba contents dinsa snn tay liking hotonansa dayake posting kamar guda biyar snn ta sauka.
Tana barin wajen ta koma daki sama sama tay kwalliya snn ta nemi wani simple material gown baki ta saka ajikinta tay rolling kanta da veil kalar gown din da wani hadadden flat shoe na kamfanin zara ta dauki side bag dinshi dan karami ta rataya ta fetsa turare masu qamshi.
Kai tsaye ta wuce gaban wata highlander jeep dinta ta kunna bata tsaya ko ina ba sai offishin aminiyarta meenal talba
Ahnkli take takawa tana zukar tabarta batare da ta kalle kowa ba harta shige ciki, agaban new sectarynta ta dakata bayabo ba fallasa tace mata tagayawa meenal din ta iso, mikewa sctaryn tay ta shiga after like 3 min ta fito tace meenal ta bada umarni nan aka kawota ciki.
Juyawa halisa tay tanata kallon sectaryn ganin irin kallon datake mata kamr tasanta.. tana ficewa ta karaso ciki, Suna hade ido Wani irin rungumar halisar meenal tayi kamar na wanda sukayi watanni basuga juna ba.
Tace wayoo Allah halsy bakisan dadin danaji dana ganki yanxu ba dan tsabar damuwa kaina ciwo yakemin, i badly need sumone to talk to.
Please Have a seat.
Halisa batace uffan ba taja kujera ta zauna suka gaisa sama sama.
Meenal na Allah Allah tafara kawo mata korafi akan mijinta cikin katseta halisa tace mata nikam haryanxu baku samu fadila bane?...
Atake meenal ta yatsine fuska Kamar wanda aka ambato mata kashi murya ciki ciki tace waye kuma fadila????
Rau kawai halisa tay da ido bata amsata ba.
Tace ohhh u mean that prostitute of a girl??
Halisa ta hade rai tace ohh please meenal kidena fadin wann kalman mana....Inkin zageta da wann kalman tamkar kin zageni ne..
Ta bata rai tace Halisa kidena hada kanki da wancan kazamar yarinyar fisabilallh wai meye damuwarki da ita.
A nitse Halisa tace Babu..i just want to knw what happen to her..haba meenal. Shekara nawa Yarinyar nan tana miki aiki since when she is 15yrs fa. Bai kamata ace ta bace kuma kun mance da zancenta ba she is qualify to be call a family
Tsaye meenal ta miƙe cikin bacin rai tace
"NOT MY FAMILY halisa
"Not my family, i reject it with every thing within me... gosh...Allah ya kiyaye.. mtchewwwwww.
Mikewa halisan tay cikin sauke muryanta kasa kasa ta dafa kafadunta cikin sanyin jiki.
Snn tace Meenal nifa ba fada nazo muyi dake ba
Nazo ne naji damuwarki yar uwata. And is only fair idan nagaya miki abunda yake raina kinsan bana iya boye miki komi
Turo baki gaba meenal tay ta juyo tana kallon halisar.."Fadilar damuwata ce da zaku tambayeni daga zuwanki haba halisa..i have tons of matsala da aure na baki damu akai ba sai akan wata yar iska jaka da bakisanta bama.
Cikin lumshe ido da budewa halisa tace toh naji,just tell me what happen to her atleast saina dena damunki.
Ajiyan xuciya meenal ta sauke badan taso ba saidan tasan halisa bazata taɓa saurarar damuwanta inbata gaya mata komi akan bacewar fadila ba.
Tace toh shikenan ai sai mu zauna ko.
Suna zama saiga sabuwar sectarinta rukayya ta shigo da wasu files a hannunta tana sum sum alaman itama tsoron meenal din takeji...
tun shigowarta office din meenal din take bin tada wasu irin mugayen kallo harta kammala abunda zatay ta fita a office bata dena binta da tsaki ba
halisa tay kwafa tana mamakin meenal ahankli tace wann din kuma me tamiki haka.
Tace kedai nifa basa burgeni ne..they are all bunch of idiots basa son aiki sai rigima kwakwala ba komi aciki.
Halisa tace hmm
Okay..inajinki ina fadilar take.
Tace halisa nifa bansan inda take ba. Toh uwarta ma ta nemeta ta rasata sainine zan sameta?
Halisa tace you mean she is lost for real...no it can't be...bakida wani clue akan inda zataje ne atleast ai ko mummynki zata iya gane inda zata iya zuwa since itace ta kawo ta lagos din nan in the first place
Cike da shirya karya Meenal tace Halisa yarinyar nan fa first class yar iska ce kece kawai kike kallonta mutuniyar kirki..wallh mun nemeta ask around kitambayi mumyna zakiji..karkiga ma wahalar da mummyna tasha itace kiran gidansu akauye kullum to uwartan ma aicewa tay mudena damuwa zai iya yuwa tawuce gidan wani saurayinta ko tamabar kasan nan da wani yo meyasa zan sama kaina ciwon zuciya akanta. Please and please kibar ni da zancenta hakanan ni iya abunda na sani kenan.
Halisa tace toh shikenan tunda kince haka Amma banso hakan ya kasance da fadila ba. I mean she shud have come to me da na taimaka mata koda da kudi ne amma wann rayuwar ai bazai bille mata ba.
Cikin kyabe baki meenal tace kece ma dakika Damu da ita..
Halisa tace Dolena na damu da ita mana meenal she is a woman like us...nide incase kika sameta kimin magana i want to talk with her ban yarda da cewa babu abunda yake damunta ba.
Meenal tace hmmm kina cikin damuwa kinason ki dauki na wata ki dora makanki ko