Showing 57001 words to 60000 words out of 171903 words

Chapter 20 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

1025

ahankli batare da tacewa umma laure komi ba. Tafi minti goma a tsaye awajen batare da ta yi motsi ba tanajin kamar da ma a halicce ta tazo duniyan nan ba. cire sim dinta tay ta rike a hannunta snn ta jefar da wayar tata a wani rami hawaye masu sanyi suka sauko daga cikin idanunta.

Sosai hanklinta ya tashi da wann labarin dataji na mahaifinta sai kuma taji zafin datakeji aranta ya soma raguwa ta dawo tanamai tunanin yarinyar da ubanta yay mata fyade ya saka mata cutar kanjamau tun tana karama shin ko ya rayuwanta dana iyayenta zai kasance oho.

Jikinta a mugun sanyaye tazo ta samu har layi yazo kanta ta biya aka saka mata mai snn ta kamo hanyar izuwa talba grp of companies.

Wann karon ahankli take tafiya sakamakon dumbin lissafin datake ayyanawa acikin zuciyarta da kwakwarlta.

Shin itama ta karaya da samun rayuwa mai kyau tabi salon umma laurene data zauna acikin inuwar baqinciki da wahala a dalilin munanan qadaddarar mahaifinsu koko tabi shawarar halisa data ce mata koda ka tsince kanka a cikin mutanen da Allah yayosu da mummunn qaddara, tabbas tanada ikon jajircewa dan ganin ya sauyawa kansa rayuwa daga mai muni zuwa mai tsafta sai yaga mummunan qaddarar tasa tayi masa sauki...

Ayanzu haka ita neman rayuwa mai sauki takeyi makanta saidai batajin tana da karfin gwiwar fuskartan irin wancan rayuwar duba da halisa ta taɓa cemata Duk randa ta zaɓi yin rayuwa domin kwato mutuncin kanta to shirya yin rayuwa mai daraja amma mai cikeda rauni da kunci.


Daga ta dayan bangaren kuwa halisar ce a mota suna kan hanyarsu na isa kamfanin Amina talba

Meenal na zaune a office tana waya da wasu business partners dinta duk hanklinta baiya jikinta sosai dan tafi minti talatin tana jiran shigowar halisa amma sai shiru basu shigo ba.

A hanya tasaka uztaz dan dole yakaita wani babban international shoping mall dan ta nemo kwalin tabar marlboro dan yana debe mata kewa dagayin tunani musmmn ma inta zauna shiru.

Dan daga tay shirun abu biyune suke fado mata..
Ko ta hau tunanin rayuwarta na baya ko ta soma nazari akan abunda jasmine ta gaya mata wanda dukkan su basonsu take aranta ba.

Da kyar uztaz ya amince ya je ya siyo mata kwalin tabar dan kwata kwata baisanta da shaye shayen taba ba, duk dama yasan halin datake cikine yake tunzirita tasha ynxu amma bai hanashi sauya yanayin fuskarsa ba.

Bata kulashi ba tana sha tana murmushi dan ji take kamar bazasu taba fahintar cewa dauriya kawai takeyi ayanzu ba.

Wajajen karfe goma da rabi na safe suka isa harabar kamfanin, uztaz yay sauri ya taho ya bude mata kofar mota ta sauko tacemai ya jirata anan snn ita ta nufi ciki itakadai.

Tafiya take tana busa tabarta ahankli, kusan idon kowa nakanta wanda ya dada sakawa taji kanta na juyawa dan sosai jikinta ya bata cewa kowa zancen rugujewar aurenta yakeyi kasa kasa.

Haka Taki sam ta dago kai sama bare ta kalle dumbin mutanen dake kallonta suna masu zancenta a sigar gulma

Kafarta na harhadewa ta ciki amma haka nan ta daure tabita lifter yakaita sama izuwa office din meenal inda ko wani sallama batay ba ta turo kofar ta shigo ciki yanayinta adan dagule.

Cikin sauri meenal ta katse wayar datakeyi ta mike tsaye a mamaknce.
Ahankli tace Halisa ???

Waje halisan ta nema ta zauna tanamai kkrin kunna wani karar sigarin
Dake makale a bakinta

Meenal ta nade hannu tabita da kallon mamaki "what the fuck yau kuma da shan taɓa kika tashi?
I tot you quite smoking.

Hayakin na fita bakinta fuuu cikin nitsuwa ta dube meenal din tace

"Forget it meenal"
Na dawo shan Abuna...

Meenal tay rau da ido tace what? You cant be serious, Keda kike neman saukin jikinki halisa mezaikaiki komawa ga shan taɓa gaskiya i wll not allow you to continue like this .
This is bad for ur health.

Hnnkli kwace kuma ahankli Halisa Tace haba meenal, just for a few more time ai zan dena nace miki ko.

Looking seriouly annoyed meenal ta zago izuwa gabanta ta zauna tare da harde hannayenta akan kirji tanata kallon yarda take busa hayakinta hanklinta akwance gashi ta mugun iya sha wanda hakan yasaka shan taɓar yake mata kyau sosai

Shiru ne ya dan gifta tsakaninsu halisa tanajin kamar tasoma yima meenal wasu yan tambayoyi amma kuma tanajin mugun nauyin hakan aranta shiyasa ma ta dada maida hanklinta akan busa hayakin tabar datakeyi dan ya dauke mata hanklinta daga tunani akan hakan.

Halisa ta dubeta ganin ta hade rai tana hararta tace.."Meenal Mummy fa? Ya jikinta, ko haryau bakuyi waya da ita bane.

Miƙewa meenal din tay sigar kame kame Duk ta rasa me zatacewa halisar atake kawai ta kirkiro karya tace yeah.. I think she is okay
Kinsan tun kafin bikin nan bamuy magana da ita ba, ai da munyi magama zata kiraki ta miki ya jiki da jaje.

Da mamaki Halisa tace
Ohhh its been long...ta kyabe baki "der is no problm dama so nake naji ya nata jikin yake.

Yake meenal din tay cikin kaucar da maganan tace halisa ina fatan kinsha maganinki? so how u feeling today..

Halisa tace "terible"
Inaga zan dena fita dan bazan iya zurar irin maganganun da mutane sukeyi akaina ba..
I dont think my mind is ready for this shhittt!!

Meenal tace To yau da safen ina kikaje dama?

Tace i was with jasmine

Jin sunan jasmine yasaka meenal ta yatsina fuska snn tace"Oh the model..No wnder..kice min dai kinje wajen lalattaciyar kawarki ta dauki taɓa ta jona ki dashi. Mtsww I just dont like dat girl, she is a bad influence amma sam kinki jina halisa..

Halisa ta dada busar hayakin tana cewa
"what ever meenal leave jasmine out of this

Ta kyabe baki to Zanyi magana da sauran babes ai in bazaki jini ba zakiji nasu,mude wallh bazamu bari ki kara komawa wajenta ba if not next time kikaje saidai muga kinfara shan giya.

Ko amsata halisar batay ba wayar meenal ya fara ringing, da sauri ta dauka ganin lambar hajiya zee ne dama kuma ta nemeta kamar me amma bata dagawa.

Tana daukawa tace
"Hajiya ya da haka?
Inata kirarki tun safe amma sai shiru baki dauka ba.

Cikin gigin bacci hade da masifa tace Kai amina talba kefa akwai ki da nacin tsiya yo Inde akan yarinyar can ne toh ai tazo nan da sassafe ta bankadamin rashin kunya snn ta kwashe takardun duka zata kawo miki office dinki.

Meenal tace kikace ta bankada miki rashin kunya???

Hajya tace yess. Ai yar kutumar ubace bata da kunya Wallah zagewa tay ta zageni tass tacemin tsinanniya tsohuwar karuwa. Taci saa ina tare da baqine wallh da saina karya kafafunta amma i trust u to do the needful kici mun ubanta intazo.

Jikin meenal harna rawa tace karki damu hjya ai magana ya kare tunda kince tana zuwa yau kuwa zan mata hukuncin da bata taba gani arayuwarta ba.

Suna tsaka da wayar fadila ta iso harabar asibitin fuskarta a daure sosai dan duk wanda suke mata magana ma bata amsasu ba.

Direct tay sama izuwa offishin meenal dauke da takardun contracts din a hannunta duk anyi signing dinsu.

Meenal na kan bayanin irin hukuncin da zatay mata sai gata nan ta turo kofar..

suna haɗe ido meenal ta wani jaaa tukikin numfashi mai zafi kamar wacce taga mutum me siffar shaidan ya shigo.

Hajya kashe wayarki ga yar iskan nan ta dawo.

Daga tsaye fadila ta zuba mata jajeyen idanunta batace uffan ba bare tayi gaisuwa.

Sosai kan halisa ya daure ta tsaya tana satar kallon su ayayinda suke kallon junansu awani irin yanayi na hatsala da tsana.

Sai can snn fadila ta karaso cikin offis din har gaban table din meenal snn ta aje files din tare da mata wani irin kallo mai wuyar fassara ta juya fuskrta a dore da niyyar zata fice taje ta rubuto resignation letter Meenal din ta wani cakumo ta baya a walakance tabita shakure mata wuyarta da karfi har dakyar take fidda numfashi..

A mugun tsawace tace mata Where did u thin ure going bitch, where have u been With my contrcts?

Da sauri halisa ta miƙe tsaye tayi kansu da zimman zata rabasu.

Fadila ta miƙa hannu tanai mata alaman karta matso kusa bare ta rabasu..

kafin ta hankara fadilar tay juyi ta waina meenal gefe ta hadata da jikin bango jiri ya debeta yuuu kamar zata fadi kasa haka tabita rike bango agigice.

Rai a bace fadila tace i was in hell cos dats where u sent me to be.

Muryan Meenal na wani irin shaking tsabar bacin rai atsawace tace how dare u pushed me. Zuwa tay da sauri tare da daga hannu zata wanka mata mari fadila tay saurim cafke hannunta ta watsar mata dashi acikin wata iriyar raini daya girgiza mata zuciya.

Nan da nan Halisa ta shigo tsakiyarsu da mamaki sosai ayanayinta tana kallonsu dukansu

Tace What are u guys doing Fadila kina da hankli kuwa,..ta juya ta kalli meenal babe wann ba girmanki bane.

Fadila batace komi ba sabida ganin girman halisan datakeyi.

Meenal tace Halisa stay out of this.

Yarinyar nan yar iska ce,.Nan ta soma masife fadilan ta inda take shiga batanan take fita ba.

Tanamai cewa Karuwar banza.. u think bansan agidan saurayinki kike ba..tafara mata gori tana cewa ai ubanki ma agindin matar makwbcin sa aka same gawarsa.

Sosai abun yay ma Halisa ciwo yadda meenal take zagin iyayen fadila amafi munin siga.

fadila na ɓari tana hawaye sosai daga ganinta kasan hakurinta ya riga ya kare.

Duk hnklin halisa saiya tashi tanata kkrin tarufe ma meenal baki amma tsabar masifa tabi ta ture halisar gefe tanata gaggasa ma fadila bakaken maganganu, yar iska kawai mun rufa miki asiri keda matsiyaciyar uwarki marokiya amma wai kinzo nan banda karuwanci babu abunda kika saka agaba? Am going to deal with u and U wil be fired.. ni ban yi gadon abun kunya kamar na ubanki ba, bazaki je garin iskanci kimutu ana cinki ba azo nima ashafama kamfanina gulman mummunan qaddararki irinta ubanki.
In iskanci zakiyi ki aje min aikina ki je bayan gari inda yan uwanki karuwai suke halama kici karo da kannenki awajen.

Abata hankara ba saiji tay an wanketa da maruka daya na bin daya har sau biyu.

Agigice tay kasa zata fadi kasa halisa ta rikota da sauri taki sam ta sake ta dan karda ta kirawa fadilar security.

Saida Meenal tay mintina uku ba'a hayyacinta ba jin saukar marin da tsananin fushi fadila ta watso matashi.

Kuka mai cin rai ya turnuke Fadila tace
Wallahi kinci sa'ar kawarki dake nan wajen daban haka ba da yau sai na nunamiki cewa ni din kwarrriyar yar iska ce.
Amma kisani bashi kikaci,dani kuma kikeja yadda kika walakanta rayuwata kijira kema kiga naki karshen rayuwar duk wanda yaci tuwo dani miya yasha.. Am no longer ur slave, Dake da aikinki u can go to hell and burn to ashes ke baki isa ki rufamin asiri ba Allah ne yake rufamin asirina.

Wani irin kokawa da kukan kura meenal ta somayi a hannun halisa tana firgici alaman tana son ta kufce ta kamo fadilar a hannunta kodama ta rama marinta dan shine yafi mata ciwo aranta, amma haka fir halisa taki ta saketa.

Sai ihu take tana cewa sai ta daureta..sai ta walakanta and she wll make sure babu kamfanin da zai sake daukarta a aiki a kasar nan.

Fadila nacewa inta isa ta Daure ta ita kuma sai ta mata abunda batayi tsammani ba.

Zazzafar cacar bakine ya kaure tsakaninsu.

Halisa ta kalle fadilar cikin mata fada tace
"Its okay, fadila pls get out ure crossing the line.

Fadila na kuka bata kara cewa komi ba ta juya ta fita..wajen desk dinta direct ta wuce ta bude wani locker ta kwashe takardun dake ciki tasss sann ta bude computar ta ta dauko biro da paper tanata rubutu tare kofar wasu numbobi wanda Allah kadai yasan meta ke daukawa aciki.

Daga cikin office din kuwa kusan a fixge meenal ta iya kwace kanta daga hannun halisa. Hawayen tsananin bacin rai da takaici ya gama wanke mata fuska ta dakawa halisar tsawa "halisa akan me zaki rikeni kina kallon yarinya tanamin tsawa tana rainani, halisa why dont u call the police....what the hell cant u fucking react.

Cikin maida mata tsawar
Halisa tace mata
"you want me to fucking React?....meenal ure insane.. ure wrong
..akanme xaki behaving da ita haka Kece kika jawo ta miki tsawa ta kuma rainaki

Muryanta kamr zai daga wajen da buhun masifa Tace "A'a kam halisa baki fahimce fadila bane Haka halinta yake yar iska ce wallhi.

Halisa tace Meenal is enough. Banyi tsammanin wayann maganganun zasuna fitowa abakinki ba..kin shakure mata wuya and ure insulting her parents kuma kina tsammanin tay shiru ta kalleki while ure busy disrespecting her. Cmon dat was so extreme. Aiki take miki ko bauta?

Ranta bace tace bansani ba,..okay fine halisa just get out. Ure annoying me more!!!

Cikin kyabe baki halisar tace kanki akeji, ta jefa karar taɓarta abaki sanda ta buso mata hayaki sn tace 'am out!!.

Ta kama hanya zata wuce meenal din taja mata wani irin tsaki, har takai bakin kofa ta juyo ta kalle meenal din harta dauki waya jikinta na rawa zata kirawa fadila polisawa

Juyowa halisar tay bata hankaraba taji an karbe wayar anyi disconnecting
Tanamai kallon cikin idonta tace meenal please Dont call the police on her..for god sake owned up to ur own mistake meenal wallh kece bakiyi dede ba a matsayinki na babba.

Cikin katseta ahatsale tace wani mistake nayi kina gani yarinya tazo har ofice dina ta mareni snn ta zageni snn kicewai laifi nane? Halisa saiyau na tabbata cewa bakida hankli wallh a matsayinki na babban kawata memakon kitayani cin ubanta saiki rikeni.. tafadi hakan idonta na cikowa da ruwa tsabar bacin rai sai wani huci take saukewa azafafe .

Bama bajinta halisa take ba ahankli tace nide na gaya maki kibarta haka nan,Idan kuma kika yi taurin kai kika walakanta yarinyar nan i swear i will personally testify againts u banason shashanci.

Kamar ta shake halisar take ji taja ta yi shiru tanata kallonta harta fice a office din batace mata komi ba.

Halisa na ficewa ta hango motar fadilar acan lkcin har ta hau kan titi tanata kuka sosai dan batasan ina rayuwarta zai dosa ba, but all she knws is der is no going back, in sha Allah ta rabu da meenal talba kenan na har abada inma akwai wani abunda zai shige tsakaninsu sede na daukar fansa amma ba na mutunci ko yafiya ba.

Halisa dake cikin nata motar, a nitse take ta kallon bayan motar fadilan jikinta na bata cewa da akwai wani abu mummuna daya faru da yarinyar dan bata taɓa ganinta a wann yanayin ba..tabbas duk abunda zai saka tay ma meenal haka to abun mai girma ne, dan haka tay shiru cikin nazari. Sai can ta dube uztaz snn tacemai

"Hey,..Follow that car"

Bai yi wata wata ba ya juyo kan motar a ladabce yana me ce mata
"yes maam..."

Daga Cikin offishin babu abunda meenal takeyi sai jeka ka dawo ranta yay mummann baci tana ziriya tana huci.

For the sake of halisa zata daure yau bazatay komi ba dan tasan halisa sarai ba kyaleta zatay ba,

hakan yasaka bata iya daukar wayarta ta kirar wa fadila hukuma ba..ji take kamar kanta zai tarwatse da bomb tsabar bacin rai dan harga Allah niyyarta shine ta mata gundumammen sharrin da zai saka akaita gidan yari a kulleta na tsawon wasu shekaru.

Ahakan ma bawai zata kyaleta bane,tsaye take cikin huci Tanakan sake saken wasu salon muguntan data mata aranta.

Can ta Wani irin Kyabe baki cikin kunci da tsananin bacin rai ta fito waje, direct gaban desk din fadilar ta nufa danta duba ko zata iya kwashe wasu delicate files na Abubuwan kamfaninta da suke hannunta, tana isa kan desk din iya farar takardan resignation na fadilar kawai ta gani a ajiye. Daukawa tay a fusace snn ta koma cikin ofishinta dashi tana zama ta dauki waya tare da dannawa mahaifiyarta kira.


08060712446
Surayyahms please ayi sharing
[1/24, 9:13 AM] Lady Surayyahms.: _*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
Hp palace


⏯️1️⃣3️⃣


After few minutes da ficewar fadila a harabar talba grp of companies meenal dake cike da fushi tahau dannawa mahaifyarta kira a waya.

Daga cikin wata haddadiyar falo dayasha kayan alatu Hajiya nadiya talban ke zaune akan wani babban royal cushion na falon an tula mata kayan ciye ciye agabanta ta dora kafa daya akan daya tana kan figar gasassen namar kaza dayaji yaji me dan uban qamshin tafarnuwa tanamai taunashi ahankli tana hissing side ways tana kaiwa baki kamar bacin gaske takemai ba.

jikinta sanye yake dawani dan ubansun gown na bugaggen royal blue colour shadda bugun kasar mali, shaddar yana wani irin zuba kyalli an mata cikakken aikin zaren hannu daga saman wuyansa har izuwa kasar rigan kafafunta sanye da golden colour flat shoes na kamfanin huda kattan.

Manyan gwalagwalai da zobunan hannunta na saudi gold daata zubosu tamkar wanda zataje wani babban hidima sai dai yanayinta na hutu da jin nishadi bai nuna alaman zata motsa bama bare taje wani waje, tadai fison taganta tay wanka ta fito kar kar wuce raini tasako abinci masu dadin tsiya agaba tanaci tana jin nishadi aranta.

Sanda ta somajin kmr ta koshi kafin nan ta daga idonta sama ta soma duban me akeyi acikin tv.

Gefe ta juya taga remote baifi ta mika yatsunta tajawo shi amma kasala yasaka ta kasa yin hakan Mai aiki ta kirawo tun daga sama ta sauko batare da ta kalleta ba tace Ke Dauki remote din nan ki miƙamin.

Mai aiki batace komi ba ta dau remote agefenta daf cikin rusunawa ta mika mata tanamai cewa gashi nan."Hajiya".
Tana karba cikin jan tsaki ta sake ajeshi anan agajiye. Mai aikin tay sauri tana shirin komawa sama da wani irin harara ta tsareta ke zo nan uban wayace miki ki tafi?

Kanta akasa tace amin afuwa hajya..tun kan ta kuma kara magana hjy taja tsaki Mtswwww ki dauki remote din nan ki canja min tasha nikam..

Da sauri ta dauka tafara caccanza mata tasha har saida ta kure channel din gabaki daya kafin nan sai can ta fauce remote din a hannunta takai wani tasha inda ake sakin wakokin shaharriyar mawakiyar kasar mali mai suna oumu sangare.

Jin wakar na ratsata ta fara rausaya kai tana Murmushi tabi ta mance da kashin me aiki dake tsaye,sai can dataga ta gaji da tsayuwar snn ta dubeta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login