Showing 162001 words to 165000 words out of 171903 words

Chapter 55 - Cheaters Club Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

798

hausawa. Baku tashi nuna ikonku akan mace sai a fannin kishi ko in zaku cuceta. Inhar kana so na meyasa bazaka bani irin dukkan rayuwar danakeso ba. Hadiza tana can tana zagaya duniya tare da mijinta and u are here shouting at me Kamar kaine ka haifeni to hell with u mahmud. Bazan takura kaina sabida wani banzan aurenka ba

Bata gama rufe bakinta sai tassss taji saukar mari akan fuskarta.

Ransa a matukar bace yace baki da godiyar Allah shema'u..for once kin taɓa gode ma Allah arayuwaki kuwa, akanme zakina comparing dina da mijin kawar hadiza bayan kinsan babu abunda kika nema awajena daban miki ba...

Azafafe ta taso zatay magana cikin katseta yace i have had enough of you shemau ya isheki hakanan Ina ragar mikine sabida ina sonki amma daga zarar raini zai shigo cikin lamarinki i cannot tolerate it anymore. Ki mugun gyara kalamanki..

Yana gama gaya mata hakan yabarta atsaye awajen ya haura sama dakinsa a mugun fusace

Tun daga nan yake jin ihu da zage zagen datakeyi tana cewa wai yaci amanarta.

zuciyarsa kamar zata fashe da baqin ciki haka ya dingaji ya dau lokci sosai kafin da kyar fushin nasa yay subsiding kadan.

Tunda hakan ya faru bai sake saukowa kasa ba. Ita ma bata nemesa ba.

Acikin tsananin Bacin rai ya wuni, he cudnt shake it off dan babu abunda yake raunata namiji kamar ayi masa gori akan wani dan uwansa namijin musmmn ma ace inyana iya bakin kkrinsa,gabaki daya kasa samun nitsuwa aikin presentations dinsa dake gabansa da zai tura gobe yakeyi sede kwata kwata baimasan meyake rubutawa aciki ba.

Itakam shemau batama san yanayi ba baccinta ta warba kamar ba gobe.

Washe gari ran Monday da sassafe shemau ta fito daga wanka kirjinta daure da dan karamin towel daya na hannunta tana daddanawa ajikinta tana shashare fuskarta,

tana kammala hakan ta cilla towel din yy gefe tayi zamnta agaban dressing mirror Tana ta kallon kanta ta na zuba wasu irin kayatattun mayun murmushi,da alaman wani irin ji da kanta yau takeyi wani sabon salon rigima takeyi ita kadanta tana yaba kyaun da Allah ya bata wanda aganinta duk wanda ya sameta ya kure sa'ar samun hadaddiyar mata..

Fair hands dinta ta sakala ta bude dan karamin drawar gaban mirrorn wanda ta rikeshi da fingers dinta sama sama kamar wacce take kyamar handle din, yana buduwa ta hau fiddo wasu mahaukatan kayan gyaran fata dana kwalliya gasunan dai birjik.

Kusan minti ashirin ta dauka a wajen shafa mai kawai,saboda tsilla tsilla take bin jikinta starting frm body moisturizers, face toners,face hand and feet cream,oil and face enhancers.

Tayi masifar kyau kuwa babu laifi,after like 30 min ta mike ta bude wadrob ta dau kayanta data shirya already cewa shi zata saka,black steve meden dinner gown mai uban shape an watsa masa zubin kwalliya da wasu mahaukatan fararen duwatsu ajiki dan kadan ata gaba, kwalban turarenta na samun sa'a da wani alfah ya bata na shafawa jiki ta jawo, tsaki ta saki ganin yadda ya rage dan kadan Aciki,ajiyar zuciya mai qarfi tasauke tana jujjuya kwalban turaren a hannunta,Thinking of yadda zaya kasance mata in har yau manyan bakinsu basu iso abuja ba kamar yadda suka shirya ba,dan kadan ta shafa turaren a gefen wuya da armpit tana kafa kafa dashi dan karya kare mata tana kammala shafawa ta maida shi inda ta ciro takalminta na larboutin dats sooo high tahau kai ta zare wani katoton jaka sannan tayi waje..

Kamar wacce tasan mahmud zai fito nemanta tay sauri sauri ta shiga hadadden jeep dinta tabar gidan fitarta keda wuyakuwa sai gashi nan ya fito nementa har waje. Mai gadi ne ya sanar dashi cewa yanxun nan ta fita.

Da sauri ya koma dakinsa ya dau wayarsa ya soma kiran layinta tuni ta kashe abunta dan tasan zainemeta kuma ba mode din kulashi takeji yau ba.

Daga office dinma bata wani jira ba tabi tawagar tafiya suka wuce airpot suka dauki hanyar Abuja.

Abakin gado mahmud ya zauna sakaka looking so depressed musammn ma daya kira office din nata kace dashi ta wuce Abuja, karshe hakura yay ya fada bathtum yay wanka. Bacin rai yasaka jiya baici abincin rana da na dare ba gayau din ba kwata kwata yaji baya sha'awar cin komi.

Tun da ya fito daga wanka jikinshi yay weak yasoma jin gajiya gajiya alaman baida quzari sam sam. Sai kananan ciwon kan da bai daukesa abakin komi ba..

Gabaki daya sai yanajin kamr komi ma ya fice mai aransa duk dama Bai wani kula hakan ba.

Nan yajeshi gaban madubinsa ya hau shafe jikinsa da mai yagama gyara suman kansa ya tattala ko inansa sosai ya fetsa turare tabi mishi ko ina snn yabude wadrobe ya dauko bakaken suit da farar yar ciki ya suturta kansa dashi yay fess fess.

Jakar laptop dinsa ya dauka ya rataya ya sauko kasa tsabar kansa ta dau zafi ko cofee din yau bai tsaya yasha ba, bai tsaya
Ko ina ba sai office nasu a inda zai presenting din last proposals din nasa.

Wajajen karfe 9 zaiyi presenting amma tun 8 ya iso office din yana zaune shiru babu abunda ke yawo a kwakwalsa face kalaman shemau da dukkan wani baqin halin data ayyana masa a wann satin na raini da rashin nuna godiya .



Ata dayan fannin kuwa yau kusan wani babban ranane awajen dukkan ma'aikatan halisa mansa ayayinda kowa yake da masaniyar cewa yau zata dawo bakin aikinta since after her marriage melt down.

Ma'aikatan mansa companies kusan kowa ya ci wanka ya saka best suit dinsa da dresses dinsu kaf sunyi kyau

ACikin ma'aikatan nata wasu har sun siya mata welcoming flowers na murnan dawowarta, wasu kuma sun siyo babban frame na get well soon dake ba'a bar kowa yaje kusa da ita ayayin da take cikin halin rashin lafyarta ba.

Yawancinsu ma tun ranar aurenta basu sake ganinta ba saiyau da suketa harsashe.

8:oo am dot on monday.

Ahankali uztaz yake murza stiring motar suna driving so calmly acikin Wata munafikar mota kirar Roll royce sweeptail ya shigo harabar babban kamfanin mansa dake ta layin Gidajen gwamnatin dake cikin garin..,"

HRM ne a rubuce in bold and italic writing style agaban deck din gaban motarta black in colour dayasha wanki yana kyalli.

Uztaz dake sanye cikin designer cooperate suit dinsa baki daya yasaba sakawa ya fito ya bude mata kofar motan da sauri kuma yabar wajen tunma kafin ta dago idonta da kyau ta kalle sa..

A lokacin kusan Kowa dake harabar wajen still yayi ana jiran fitowarta Dan kawai asha kallon kwalliyarta data sabayi mai aji da daukar hankli.

Rabonta da zuwa offishintan tun ranar da zach yazo ya dauketa dakansa ya kaita wa yan uwan mahaifyarsa lkcin ana saura sati biyu ayi aurensu daya tarwatse.

Tsabar bugawar da zucyar halisa yake saida tay kusan 5 mints tana dedeta nitsuwarta acikin motar kafin nan ta aje kafafunta ta a kasa,
Akan wata 7 inches na devils wear prada higheel shoes kwas kwas ta sauko ta shiga jera takunta daddaya uztaz na biye da ita da sauran tarkacen ta,her expensive bag her phones,Looking dashing as usual tana jujjuya body structun ta mai mugun dauke hankali ...

Sassanyar kwalliya tay ma fuskarta bamai yawa ba kuma ba kadan sosai ba, her favorite pony tail style da zach yake mutuwar so ajikinta inya gani yau shitayi akanta aka tattara sumankanta duka sama kamar cuku aka dauresu da clip iya jelarsu ne ya zubo mata har kafada ta gaban goshinta kuma aka kawatashi da gel sosai.

Wani irin shining lips dinta yakeyi.
Looking dashing acikin champaign gold skirt da riganta mai tsantsi dark red colour kuma silky smooth wanda ya fidda classy, porchy and boauntiful body structun ta mai dauke hankali.

Tun isowarta Masu aikin wajen suka jeru suka tsaya suna masu miko mata gaisuwa da tarin frames da flowers din da suka kawo mata na nuna jajensu da murnansu na dawowarta. as usual acikin yanayin aji da sanyin nitsuwa ta amsa gaisuwarsun tanamao bin kowannen su da murmushi mai sanyi hadadden Fuskarta ta straight yake kallon gaba cikin kwanciyan hankali manne da hadadden googles champaing white na kamfanin catier daya mugun dacewa da kalar skirt dinta.

a hankali take takun nata har ta shiga cikin office dinta cikin kasaita tana amsa wani wayar daya sake shigowa anan ma har ta kammala bata daga ido ta dubi kowa ba..

Shiganta office din ke da wuya tun bata fara aiwatar da komi ba sai ga kirar Dr khalid.

Ba yabo ba fallasa ta dauka suka fara magana normally in a flirty way kamr yadda suka saba kwana biyun..

Da fara'a sosai a muryansa Yace mata yaji dadi data daure ta fito dan matakin su na farko kenan dazasu cimma a wann satin..

Sai wani yabata takeyi tanajinshi sai de tay murmushi amma batace mai komi, he went futher to promise to come and pick her up after work، suna cikin wayar ne saiga Wata dattijar mace ta shigo da rawar jiki.

Lkcin Halisa tanata murmushi cikin son ta katse wayar tace pls I will call u back khalid..

Dagangan tadan danna speaker yadda matar zataji muryansa ayayinda yake ce mata okay darling i will see you later..take care.

Wani kayataccen murmushi tay snn
Tace thanks. Bye dear.

Tana katse wayar ta dan dauke kanta looking un aware da shigowar mrs ogumka da ta kafe cikin mamaki tana kallonta, Da gefen idonta take kallon yadda matar tabi ta kureta da wani irin kallo mai cike da baqar rudewa da ya kasa boyuwa. Wanda ko da ba'a agaya maka ba zaka iya sanin cewa sam sam batay tsammanin cewa har zata zo taga halisa ahaka looking good and sounding happy awaya da wani namiji ba.

And then who is that khalid datake magana dashi....hmmmm wonders shall never end, yaran xamani kenan. Yaushe yaushe step son dinta zach ya rabu da halisa wai shine har tay wani sabon saurayi?

Jan kujera tay ta zauna agaban halisar a dofane, har halisa ta dago kai suka hade ido bata dena raye rayen maganganu acikin ranta ba. Ba karya Ganin halinsan ahaka ya mugun girgizata dan atake yanayin faraar dake kan fuskata ya dauke mai gabaki daya.

Halisa tace good morning mrs ogumka

Ciki ciki ta amsa da cewa good morning. so ure back? Toh ya jiki

Batare da amsawa ba halisa tagyada kai tana kallonta direct acikin idanuwanta tare da sassanyar murmushi dake tafe akan fuskarta dake mugun kara mata kwarjini.

Kwarjinin da halisan tay mata gabaki daya yasata kasa zama waje daya sai daddaure fuska take tana yatsinawa kamar maijin kashi.

Itade kawai bataso dataga halisa ahaka bane taso ace tay baki ta rame ta fita hayyacinta badan komi ba saidan ta samu na cewa akanta sosai.

Cikin katse mata tunanin halisa tace naji labarin cewa kina nemana???

Tace ohh yes dama akan masu saka hannun jari ne nace indan bazaki samu dawowa bakin aikinki ba wani acikinmu saiya zauna akan kujerarki ya yanke crucial decisions but then i heard that u didnt grant the meeting.

Kai tsaye Halisa tace yes..dats bcos i will be handling it myself like i alwys do.

Cikin shanye maganan mrs ogumka tace "Soo how are u feeling now Halisa..munji abunda ya faru dake da step son dina zacharia,its sad da kika rasashi dan zach mafarki kowani ƴa mace ce, its so unfortunate for u. are you really okay..u seems to heal so fast huhn, kinsan alot of girls kamarki sukan rudi kansu da cewa sun warware daga hrt break while atacikin ransu ba haka bane its all pretence da taurin kai
....am not saying u're pretending....just asking for the sake of this companie's reputation.

Murmushi mai sanyi halisar ta katsetsa dashi tanamai cewa so what are u tryng to achieve with this conversation tho..

Zatai magana cikin katseta halisa tace mrs ogumka,i truly aprceciate ur concern for this company. altho the company is mine not anyones. So Basically, is my job To protect its reputation and u dont have to remind me of my job..

Ranta sosai ya baci da wann amsar da halisa ta bata sai batace komi ba acikin ranta taja tsaki tanamai cewa ai basai kin min gorin cewa kanfaninki bane shashasha. A fili kuma ta hadiye maganan tace its okay am sorry abt that.
Sanyi jikinta ya dada yi dataga ko kallonta halisa bata karayi ba bare ta kulata.

Sounding Uncomfortably tace So,Sai yaushe kenan zaki kira mana meeting sabida akwai abubuwan da yakamata ahadu atattuna akai.

Ba yabo ba fallasa halisa tace Karki damu da wann idan lokci yay maria will call ur attention.

Cikin kyabe baki Tace okay..i gues am going to be on my way since evrything is okay dama nazo ne nadan dubaki

Halisa tace yeah it is thanks.

Bata sake cewa komi ba ta kama hanya ta fita zucyarta baimata dadi ba.

Tunani take taya kenan zata cimma burinta akan halisa aranar meeting intazo da yan jarida musmmn ma dataga kamar babu wani alaman damuwa atattre da halisar ko kadan..a tunaninta ko dan halisan ta samu wani saurayine ta warke to wanene wann saurayin cos she wll like to knw him taga shikuma waye akasar nan??

Haushin hakan yasaka bata iya zama a office din ba ta wuce wajeb sauran magulmatan kawayenta dan ta basu kanun labarai.

Normally halisa ta tsunduma acikin aikinta time to time haka uztaz yana shigowa yana dubata, ganin All her wokers are so happy to have her back ya dada sakawa hanklinta ya kwanta sosai.


9:am dot aka kira engr mahmud cikin hall dake dauke da manyar jugdes da turawar da aka gayyato zasuga final proposal dinsa.

Tasowa yay jikinshi babu wani karfi yana tafiya yanajin kamar kansa na sarawa, bai wani kula hakan ba har saida ya shiga hall din. Tun dayaga idanun mutane yuuu akansa Sai kuma ya somajin jiri jiri cikin dauriya ya fara setting din proposal dinsa a power point inda zai nuna musu komi daya tsara akan wata katuwar majigi datake jikin bango

Tun yana hadawa yaji jikinsa na mutuwa gabobin jikinsa na tauna taciki. Ya kammala kenan zai mike yafara maganan hasken da screen din majigin yay ya hitting kansa kafin kace wani abu sai luiii yaji jiri ya sharbesa sai ga kansa nan akasa take take ya tafi unconsious adan dole aka dakatar da abun aka rushing dinsa neaby hospital nan da nan aka bashi gado tareda sakamai ruwa.

Lkcin su Shemau har an isa Abuja ana holewa cikin taro. Already ta riga ta kashe wayarta dan bata son mahmud ya dameta da kira dan haka ba lallai bane a sameta.

Karshe dai mahaifyarsa hajya badiatu aka kira aka sanar da ita halin dayake ciki anan lagos sabida jininsa ya dan hau sosai sann yunwar dayake yawan ji shiya dada jefashi acikin wann hali. Kusan awa uku engr yay yana amsar ruwa bai farfado ba, kafin nan har Hajya ta aiko wani dan uwanta asibitin yana tsaye akansa.

Koda ya farka yaga kansa agadon asibiti tun ba'agaya masa meke damunsa ba yasan dacewa damuwa tare da baqin cikin da shemau take kkrin cusa masa aransa yana daya daga cikin abunda ya kwantar dashi.

Bai jima ba akwance ba yaji labarin cewa har anyi replacing dinsa da wani abokinsa akan aikin dayasha wahala yana neman. Abun bai masa dadi ba ammma haka ya hakura ya zauna kawai a asibitin yana dan jinyar jikinsa ahankli.

Mahaifyarsa da mahaifinsa da abokansa kaf kowa na kiransa awaya ana masa jaje amma har waje ya rufa matarsa shema'u bata nemesa ba.

Dake ta samu abunda take so a abujan ganin idanun manyan maza na yawo akanta tuni saita fada cikin wata harkan nadaban.

Da yamma bayan halisa ta tashi a aiki Dr khalid din ne yazo ya dauketa yakaita gida sukadanyi hira.

Sosai taji dadin game din da suke bugawar ganin burinta ya fara cikawa akan zach Dan kuwa tun shigarta motar dr khalid taga boys din zach na bibiyarsu abaya.


******
Abubuwa sun taru sun ma zcyar victoria yawa ta farka da damuwa kala kala aranta femi bai sauko daga fushin dayakeyi ba gashi haryanxu bataga wani sako daga wajen hadiza ba kuma investors dinta sun tsaya mata a wuyarta akan maganan kamfaninta.

Cikin wann yanayin damuwar yau tazo makaranta amma bata iyayin ma students dinta komi ba ta karbi permission ta wuce kamfaninta domin duba meke faruwa.


Yau ne ranar da kayden ya fara zuwa schl din sede bai kula kowa ba
Har aka gama lectures ya koma gida.

Agajiye vicky ta dawo gidanta tay wanka kenan tadan huta ko abinci bataci ba wayarta ya fara kara..daukawa tay jin muryan hadiza ne yasata sakewa suka sha hira.

Nan ma hadiza ta kara jadadda mata cewa sabuwar kamfanine amma mai kamfanin billionare ne, bata sama mata numbar el mario din ba amma ta samar mata da genuine email dinsa Nan hadiza ta bata shawara akan tana tura masa sakonni direct ta email din tanamai tallata masa nata kamfanin hala zata ci saa ta samu shiga.


Ayayin da hanklinta baiga kansu anan ne kayden ya samu lkcin zagayawa cikin makaranta, Its seems like jira kawai yake ya dawo kafin ya fara exploring skills dinshi, shiru shirun dayake kwana biy yana playing hard guy ba shi ya hanasa sa ido akan kowani sashin activities din schl din ba,aransa har yasan iya ina ya dace ya tsaya iya ina kuma ya kamata yama kanshi madakata.

Snooker, foot ball duk ya san dole ayi da shi,he had basket ball skils amma bejin anan schl din zai shiga salon masu yi.

But parties in the bar and babarque nan kam be ma hakura ba sanda yaje yayi exploring ya sha iya abunda zai sha ya huta, gashi a time din waje yadan yi shiru dan rabin dalibai ana wajen gasar competition din da victoria take hada ma daliban nata so har yazo ya fita a schl din bama wanda ya san ma da shi.


Fannin halisa tunda taga plan dinta akan zach na tafiya bisa tsari sai tafara kawo salo salo datasan bazai iya jurewa ba.

Tun monday data lura suna bibiyarsu ta kara kaimi wajen jawo Dr khalid ajiki, kwana biyun nan haka zata kirashi tace masa yazo yakaita office ko inta tashi yazo yakaita gida.

Wani lkcin danta tabbatar da zach na bibiyarta bata bari su wuce gidan direct sai sunje wani restaurant sun dan ja lkci awajen cin abinci.

Ayayinda Dr khaled ya gama sakankancewa cewa ya gama cin nasara akan halisa ita kuma gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login