Showing 27001 words to 30000 words out of 176868 words

Chapter 10 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

sarki kuma wani rumfane da mata ke taruwa a ciki.

Suna shiga duk sukayi gefen da aka ajiye mazaunin malam,
wuri d'aya suka zauna yayinda tuni,
Saifuddeen kuma ya zagaya bayan Bappa Ali da alarammanshi Abdurahman gyara tsayuwarshi yayi gefen d'an agajin dake bayansu Bappa Alin.
shi kuwa Bappa Ali da alarammanshi gyara abin sautin mgnar dake gabansu sukayi tare da d'an sunkuyawa kan Qur'anen dake bud'e a gansu inda bana zasuyi tabsir d'in ```suratul Maedah.```
shi kuwa Saifuddeen ta cikin glass d'in table d'in gabansu yake ganin fuskar Bappa Ali ras har yadda zai gane motsin bakinshi da abinda yake fad'in.
dan haka ya maida hankalinshi bisa bakin bappan nashi.

Bayan anyi addu'a an bud'e taro kana ya kuma jero addu'o'i. gyara zamanshi yayi kana cikin sakekken sauti yace.
"Alhamdulillahi Allah ya kawomu watan Ramadan tun kafin mu shiga cikin tafsirin namu zan d'anyi tsokaci ga yan kasuwanmu."
sai ya kuma d'ago kanshi ya d'an kalli taron jama'ar dake cike da masallacin ido ya d'an zuba musu tare da ci gaba da cewa.
"Shi watan Ramadan wotan rahama ne da jink'ai da kuma tausayin juna. Amman abin takaici abin haushi tun gabanin zuwan watan zakaga wasu musulman suna k'arawa kayayyakin sana'arsu kud'i domin suyi tsada, maimakon su rage musu k'ud'in domin tausayawa juna da tallafawa tallakawa."
sai ya kuma tsagaita. shi kuwa Saifuddeen tuni yake fassara abinda yake fad'in da body language yadda masu matsalar ji zasu iya gane komai a sau k'ak'e.
cikin nitsuwa Bappa Ali yaci gaba da sharan fage akan bayanin Ramadan inda yake cewa.
"Yana daga cikin fa'idojin azumi,
Azumi na sanya bawa godewa ni'imomin Allah mad'aukaki.
Azumi na taimaka wa bawa gurin barin abinda Allah ya haramta.
A cikin azumi akwai tsanani ga shaid'an da raunatashi.
Sannan Azumi na karya k'arfin sha'awa mu samman ga matasanmu.
Azumi na gadar da samin rahamar Allah da jin k'ansa.
Azumi na koyarwa bawa tsoron Allah, da tausayin na k'asa dashi.
Azumi na tafe da wasu falaloli na musamman,
da yawa sai a azumi suke samun dama da k'arfin guiwar shiga itikafi.
Itikafi shine keb'ewa ko zama cikin masallaci domin ibada.
Mafi falalan itikafi lokacin goman k'arshe, yin itikafi sunnace mai k'arfi
yin itikafi a masallacin jumma'a idan kwanakin da za'ayi sun had'a da jumma.
Idan zaka shiga itikafi zaka shiga kafin fad'uwar rana a daren da kake son fara itikafin.
Mustahabbi ne ga maiyin itikafi ya keb'ance da ibadu yawan salloli, zhikiri, addu'a, karatun Qur'an, tuba, istik'afari, salatin annabi, da dai sauransu domin nemar kusanci da yardar Allah.
Mai itikafi idan ya gama kwanakin da yayi niya zai fitane bayan fad'uwan rana.
Baya halatta ga mai yin itikafi ya fita zuwa duba mara lfy da kusantar iyali.
Amman mai itikafi zai iya fita domin abinda ya zama dole kamar buk'atu irin na d'an adam,
kamarsu zagayawa bayan gida da neman abinda zaici.
Idan rashin lfy ko jinin haila suka zowa mai itikafi,
zasu fita idan ya samu sauk'i ko ta samu tsarki sai a dawo."
gaba d'aya wurin anyi tsit ana sauraron bayanin malam Alin.
daga nan ya d'anyi k'arin bayani game da azumin kanshi inda yake cewa.
"Abubuwan k'i ga mai azumi,
Kaiwa matuk'a gurin kurkuran baki da shak'a ruwa.
Sumbatar iyali da makamancin haka ga wanda baya iya mallakar kanshi.
D'andanon abinci badon buk'ata ba.
B'ata lokaci kawai wasannin banza da surutai marasa amfani.
Zarcewa da azumi kwana biyu zuwa sama."
A k'arshe yace a tak'aice abinda ya kamata ga mai azumi ya kiyaye harshensa daga dukkan maganganun banza zagi annamimanci giba isgilanci da sauransu kodako a social media ne.
Daga nan suka shiga cikin tafsir d'in nasu gadan-gadan,
mutane sun nitsu wurin jin fad'in allahu subahanahu wata ala.

K'arfe tara dai-dai aka tashi, Saifuddeen ne ya karb'i d'an jakar Quran d'in bappan nashi kana suka wuce gida da abo kanshi,
suna shiga su suka wuce d'akinshi shi kuwa ya bi bayan bappa Ali da jakarshi saida suka shiga ya bashi sannan ya juyo ya nufi side insu,
murmushi yayi ganin suna fito daga d'akinshi suna zuwa tsakar gida Ummi kuwa taburma ta shimfid'a musu kana ta zuba musu zazzafan colof d'inan a tire tare da basu forks Mudassir ne ya amshi cokulan ya raba musu kana suka fara ci,
Raliyya kuwa babban kofi ta d'auka ta d'ebo musu ruwan randar d'akinshi ta kawo musu,
shi kam bai kula abincinba suma basubi ta kanshiba dan sun sanshi sam baida cin abinci,
Warisu ma kad'an yaci ya ajiye spoon d'in sabida baison yayi teb'a
suna gamawa suka sha ruwa kana suka fita suka raka Ahmad har shabewa sannan suka dawo,
tuni sha d'aya tayi shiyasa kowa ya nufi gida.

Yauma da dare kamar jiya haka Ummi ta tashi yaranta,
sai k'arfe uku Rahma ta tuk'a musu tuwon shinkafa dama kuma Raihana tayi musu miyar zogale tun da dare.
to yau Saifuddeen ya d'anci mai d'an yawa kana yasha tea,
suna gama sahur din ya shiga wonka kafin ya fito anyi assalatu,
so alwala yayi tasa Hayatudden a a gaba suka tafi,
su Ummi kuma sukayi nasu a gida.
Ana idar da salla ya fara azkar nashi sai da ya gama sannan ya shiga suka gaisa da Ummi kana ya bata 5k d'innan yace ta sama musu asusu na daban ta rink'a sasu,
ita kam Ummi tayi mmkin yawan kudin to ganin yana sauri Salisu na jiranshi yasa ta barshi ya tafi sai ya dawo suyi mgna.

Suna isa Salisu ya sauk'eshi a bakin masallacin bakin kasuwan,
shi kuma ya wuce kabo-kabonshi.
shi kuwa Saifuddeen cikin masallacin ya shiga kamar jiya yayi baccin awa d'aya da rabi kana yana farkawa yayi Al'wala yayi walaha raka'a biyu sannan yayi addu'o'inshi kafin ya fito ya nufi cikin kad'uwa.

Yana shiga kai tsaye dilansu na leda ya shiga inda ya samu mutun biyu a gabanshi dole yabi layi,
bayan an basu shima aka bashi na 60k Lamar na jiya kenan k'arfe 10:00 Am dai-dai suka bashi nashin,
with full confidence ya fara bin layi-layi shago-shago lungu da sak'o yana raba musu suna bashi kud'in na jiya, 1:35 pm ya gama rabawa da yake kusan fiye da rabin kasuwar duk a wurin baba bello suke sayan ledan to shiyasa yake dad'ewa yana yawata kasuwan da k'afa tunda shi bashi da keke kamar baba bello,
yana gamawa yazo ya had'a lissafin kud'in ya samu dubu settin da bakwai da dari biyu, cikin aminci ya basu 60k d'insu sannan ya adana ribarshi a jikinshi godiya yayi musu bayan an rubuta ya dawo da kud'in na jiya,
tafiya yake yana nazari shifa gani yakeyi kamar kyauta suke bashi kud'in duk da ko azabar nauyin kwalin da yake azawa a k'afad'anshi na dama aikine mai matuk'ar wuya ga yawo cikin rana har ji yake k'afafunshi suna yum-yum dan azaban rana da nauyin kayan da yake azawa a kafad'anshi.

Ganin azahar ta kawo kai yasa ya zauna ya d'an huta dan yana jin kafad'arshi na mishi ciwo ga zafin ranan da yabi sai yake jin wani irin azabebben k'ishi ,
ganin an kira salla yasa ya mik'e yaje yayi al'wala kana ya shiga sahu,
bayan an idar ne ya mik'e a gajiye yana tafiya a hankali yaje ya karb'i omo dasu sabulu,
sai kuma ya zage da talla dan yanada burin ya maida Raihana da Raliyya makaranta in kes dai ace sun gama koda d'an Secondary school,
yana kuma fatan ya ink'anta karatun Hayatuddeen da Faruq da Adam kuma yana fatan Allah ya hanasu sake tsammatan abinda zasuci daga wurin wani.

Da wannan tunanin ya zage yaketa yawa tawa cikin ikon Allah ranar ribar 1,200 ya samu.
Ganin ya fara ganin jirine ya sashi neman inuwa ya zauna saida ya huta sannan ya maida sauran omon.

ganin hud'u da rabi tayi sai yaje shagon ba mishkila gero ya auna mudu shida sai wake mudu shida sai sugar mudu d'aya da rabi,
daga nan yaje ya sayi mai k'aramin galam sai ya saya musu lemu da ayaba da kankana,

A tak'aice dai ya kashe dubu uku d'ari biyun nan sai dubu biyar ya bari su kuma na sawa a asusune.

Biyar na cika Salisu yazo nan suka kama hanyar Dukku, cikin sa'a suka isa da sauran rana.
Yauma kamar jiya tare da abokanshi sukayi bud'a baki.
ana idar da sallan asham suka tafi tabsir.
koda suka dawo suka ci abinci sannan suka raka Ahmad.

Yana dawowa ya sumu Ummi a tsakar gida,
bisa taburma Rahma na gefenta tana bacci yayinda take ruggume da Adam.
gefenta ya zauna ita kuwa Ummi tea ta had'a mishi sannan ta bashi,
yana sha ne taje ta d'auko asusun duka biyu yana ganinta da asusun ya d'an kaikaice tare da cusa hannunshi a aljihun wondon Jeans d'in jikinshi zaro kud'in yayi tare da mik'a mata,
cikin kula ta amsa kana ta irgasu ganin dubu biyar ne sai ta fuskanci da kyau cikin maganar kurame tace mishi.
"Kud'in waye ne."
kurb'an tea d'in ya d'anyi bayan ya had'iye ne sai ya nuna mata kanta.
fidda numfashi tayi tare da gyara zama dan tasan in abu nashine in ta tambayeshi na waye ne sai yace mata natane haka yasa ta gane kud'in nashine cikin tsoro da tuhuna da gudun masifun zamani wanda dole in kaga d'anka da kud'i ka bincikeshi ina ya samesu a hankali tace mishi.
"Ina ka samesu? Me kayi aka baka su? Ya jiya ka samu da yawa yauma kuma gasu da yawa gashi harda su gero naga ka seyo Babana ina tsoro duk da tabbas nasan halinka amman kud'in sunyi yawa."
Allah sarki Saifuddeen ganin firgici a fuskarta ya sashi ajiye kofin tea d'in kana ya juyo suka fuskanci juna da kyau,
a hankali yasa hannu ya kamo nata hannun cikin sama mata nitsuwa ya mata bayanin komai yadda ya samu kud'in duk da body language yakeyi so Ummi tana bala'i gane body language shiyasa wasu lokutan takanyi mgna dashi cikin mutane ba mai ganewa sai Rahma,
sai kuma yanzu sun lura Hayatuddeen ma yana ganewa kad'an-kad'an ajiyan zuciya ta sauk'e lokacin daya gama yi mata bayi,
sai tayi murmushi tare da hamdala kana ta godewa Allah,
sai kuma ya fara rubutu a gefensu kamar haka.
"Yauwa my Ummi ko kefa kada kiji tsoro Saif d'inki da halal zai cigar daku ya shayar daku ya tufatar daku da guminshi."
kanshi ta shafa tare da samishi al'barka shi kuwa rubutun ya kumayi.
"Amin Amin ya rabbil izzati.
Yauwa Ummi batun gero da wake da sugar kuma,
a jik'a geron sai a markad'a ayi kamu a rink'a dama kunu kullum da yamma sannan d'auki wake mudu d'aya kullum a surfa ayi k'osai da yamma sai asa a manyan kwanuka a rink'a kaiwa bakin masallaci sadaka,
gobe zan sayi dabino a rink'a had'awa da dabinon."
Allah sarki Ummi ji tayi tamkar ta ruggumeshi sai kuma taji wasu zafafan hawayen farin ciki,
cikin raman murya tace.
"Ya Allah ya yimaka al'barka babana Allah ya k'ara maka imani da tausayi ya Allah ya bud'a maka k'ofofin samu mai al'barka in sha Allahu nida kaina zan rink'a wannan aikin har zuwa k'arshen Ramadan su Rahma da Raihana kuma suyi na gida."
Wani irin farin ciki yaji yana ratsashi sabida ganin yasa mahaifiyarshi farin ciki.
ita kuma cikin bada shawara ko ince neman izininshi a matsayinshi namiji kuma babba tace.
"Goggonku Dada ta aiko Ahmad d'azu yake cemin wai dan Allah a bata Raliyya mana taje suyi azumi acan zata d'an taimaka mata da aiki."
cikin sanin makamar girma ya rubuta mata.
"Ummi in dai kin yarda ba matsala dan na yarda da tarbiyar Goggo Dada, amman ki gayawa Bappa Ali in ya amince ai sai taje."
kai ta jinjina kana tace.
"Shi na fara gayawa kasan ai bazai hanaba yace taje ba matsala."
gyara zamanshi yayi ya kalli Rahma data zuba musu ido,
sai kuma tayi maza ta rufe ido wai ita bacci takeyi.
Jin sautin murmushin sane ya sata tashi zaune kana tace.
"Yoh tun d'azu na farka sai naga kamar hirran sirri uwa da d'an lelenta sukeyi shine nayi likimo ai, kai kuma da yake ka shahara da body language ko kallonka akeyi jikinka ke gaya maka kawai sai naga ka zuba min wannan fararen idanun naka."
dariya suka d'anyi baki d'aya kana ta zauna sukaci gaba da hira,
inda itace ta amshi kud'in ta cusasu a asusun babban goggonin milo.

Daga nan sukaci gaba da hirarsu tasu ta rayuwarsu sai shad'aya suka shiga.

Shi kam Saifuddeen saida yayi wonka sannan ya yayi al'wala kana yazo ya shafa mai tare da fesa turare wanda wannan al'adar rayuwarsa ce domin Saifuddeen mutunne mai tsananin tsabta sam baya son k'azanta ko kad'a shiyasa yakeda kenkeyani over.

Washe gari kamar kullum yayi suka tafi gombe da kafin bakwai na safema sun isa,
baccinshi ya d'anyi na awa d'aya da rabi kana daya tashi yayi walahan shi kamar yadda ya saba,
sannan ya shiga cikin kasuwa ya fara rarraba ledodinshi ana bashi kud'in na jiya yana bada wani, cikin awa hud'u da kad'an ya gama rabawa ya had'a kud'insu 60k sannan ya ware ribanshi dubu bakwai da d'ari biyu,
yaso yayi ragin d'ari bibbiyun saman to kuma sai ya shawarci Jabeer sai yake ce mishi kada ya rage dan kar ya zama yayi azarb'ab'i a kasuwar ledan tunda du du du a wata d'aya ne zaiyi sana'ar kar yayiwa baba Bella shisshigi to da wannan
shawarar ya hak'ura.

Daga shagonsu Jabeer wucewa yayi yaje ya amso omo aifa nan ya samu sa'an shiga layin masu wonki da guga sukayi ta kwasan sabulun kamaru da omon ranar ribar 2k ya samu a omon ma,
da zai koma ya saya musu naman miya da kuma fruits.


********

Rayuwa ta ja yau da gobe asarar mai rai,
kwanaki sun tafi tuni azumi ya shigi jikin al'ummar annabi
anyi dibi-dibin goma na marmari gashi har an shiga goma na wuya inji hausawa da fad'i.
Cikin izinin Allah an gama na wuyan ma yau, gobe dai na d'okin sallah za'a fara.
Iyaye da yan uwa da masu wadata dama talaka kowa na hidimar d'inkunan sallah.

Saifuddeen ya k'ara sabawa da mutane sosai ko ta ina an sanshi a kasuwar sabida dalilai uku sana'arsa ta yawoce dole yana ratsa ko wanne lungu,
sannan shi kurmane da hakane duk wanda ya had'u dashi baya manceshi kana shi mai gsky da amanane da yawan ibada to sai Allah ya sanya soyayyarsa a zuk'atan bani adam.
Uwa uba Allah ya yalwata mishi surarshi da kyau mai d'aukar hankali yana da muhibba, kima, daraja, kamala, haiba, da cikar zati,
so wadannan abubuwan sukasa ya sanu tako ina.
Alhamdulillahi kasuwarshi kuwa sai son barka dashi dama Ummi da Rahma sai godewa Allah suke suna k'arawa sabida sune kad'ai suka san kullum sai yasa dubu buyer a asusunshi, sauran na saman kuma da balance d'in machine dasu sukeyi buk'atun yau da kullum,
ribar omo kuma yaci gaba da zurawa a asusun ribar pure water.

Abota tsakanin shi da Jabeer da Hisham da Kabir kuwa sai gaba-gaba sun shak'u sosai yanzu ya saba da wani yaron shagon Alhaji ishaq Ibrahim shima yaron yana sonshi, sosai hakama wani shagon ba miskila Bello sun saba over amman shi ya girmi Saifuddeen sosai so da yake Saifuddeen ya gaya mishi sunan Abbanshi gareshi shiyasa yana kiran Saifuddeen da Bingel am d'ana kenan.

Rayuwa ta mik'a d'aura kwalin ledodi a kafad'a da Saifuddeen yake yawan yi sai ya d'an canza mishi salon tafiya
sai ya d'an karkace ka d'an mu samman ta samanshi karkacewar da bafa zaka ganeba sai in ka zuba mishi ido sosai baranma in ka sanshi kafin ya fara tallan ledan ne zaka gane hakan sosai,
wannan 'yar karkacewar sai ta zama wani abu da yake jan hankalin mutane a gareshi domin daga saman wuyanshi zakaga time to time yana tonk'oshe wuyarshi irin yadda manyan sara kuna keyi sabida nauyin rawani da k'asaita,
da yawa kuma cewa sukeyi kyanshi ne yasa yake hakan wai a zatonsu rigimace da izza,
sabida in dai ka kalli yadda yake tafiya to sai kayi zaton d'an sarkine ko matashin d'awisu domin dama a nitse yake sai tafiyarshi da tsarinshi suka koma tamkar na jarumI R.K na seris film d'in Madubalah wanda aka tab'a nunawa a Bollywood
in ka ganshi sai kayi zaton tsantsar izzace da gadara da tak'ama kasan cewarsa karma ba ko yaushe yake mgna ba sai wasu suke zaton miskilanci ne.

Yakan je gidansu Is'haq time to time musamman in yaji zafi ya matsa mishi sai ya ajiye omonshi yaje yayi wonka ya canza kayan inda zaisa na is'haq sabida bashi da shamaki a gidansu is'haq so yawan tsabtarshi yasa kawai wasu ke masa kallon tabbas rigimace tunda gashi a wuni d'aya a kasuwa sai a ganshi da kaya kala biyu,
in yaje gidansu is'haq yakan amshi wayar step mother in is'haq din su gaisa ta hanyar rubutawa juna text.

Kullum duk bayan kwana uku zai sayi wakenshi mudu shida geroma haka sannan sugar mudu d'aya da rabi sai mai k'aramin galam da dabino mudu d'aya.
Umminshi ta dama koko ta toya kosan a kai masallacin k'ofar gidansu.

Yau jumma'a kana ana tsula zafin rana kowa ido yayi zuru-zuru sabida k'ishi da yunwa mazauna inuwama suna shan zafin azumin bare masu k'ananan sana'o'i irin Saifuddeen mai sai da leda da yan dako da yan garuwa da masu gonjo da kafintocin sama da kuma 'yan acab'a da direbobi.
Gashi yau shine azumi na 20,
Sosai Saifuddeen ke azabar jin k'ishi hakane yasa k'arfe hud'u dai-dai ya maida omo inda yauma ya samu riba sosai,
dama ya gama had'a ribar leda wanda yanzu masu sayan sun d'an k'ara sabida karatowan salla yasa cini kaiya k'aruwa.
Shagon ba miskila yaje yana isa Bello ya kalleshi cikin kula yace.
"Bingel yau ba omon ne?."
cikin gajiya ya lumshe ido tare da sharte zufar da yakeji da hankicib d'inshi cikin gajiya ya lumshe ido tare da mishi alamun akwai ya gajine yasa ya maida.
cikin kalato yawu Bello yace.
"Gsky kam bingel am azumin yau yanada dad'i."
murmushi sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya nunawa Bella d'anyar shinkafa da fulawa da sugar da geron
sai yaga kuma kamar bai fahimtaba hanne yasa shi zaro biro ya rubuta mishi cewa yana son d'anyar shinkafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login