Showing 60001 words to 63000 words out of 176868 words

Chapter 21 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

jumma'a ,
'yan uwa da abokan arzik'i da mak'ota duk sunyiwa Ummi da ahlinta rakiya suna masu kewar rabuwa da juna.

A nan Gombe kuwa sun samu taron iyayen abokan Saifuddeen da Hayatuddeen sai Adda Rahma da mak'otanta da 'yan sirarun k'awayen da ta saba dasu. iyayen Jabeer, Hisham, Ibrahim, Sulaiman, Kakar Zakariyya, da matan Alhaji Kabiru duk sun zo,
anyi walima lfy, Ummi ta shiga ran matan dan tanada sakin fuska da mutunta mutane.

Bayan kwana ashirin da biyu da k'auransu duk bak'i sun tafi sai Ummi da yaranta da sabon gida da sabuwar Rayuwa.

Sauri-sauri Hayatuddeen ya fito daga cikin d'an k'aramin falonshi gaban Ummi ya zauna wacce Raliyya ke yanke mata farce.
fuska ya d'an tsuke tare da cewa.
"Ni wlh a matse nake a gidannan an wani lik'ani a wannan kurkukun side d'in kamar yaro,
kuma ko share min d'akinma Raliya batayi sai a barmin komai a hargitse."
tsaki Raliya taja tare da cewa.
"Ai ni ba baiwarka bace da zaka hargitsa komai kace ni in gyara maka."
harara ya watsa mata tare da cewa.
"To ni macece ni da zanyi shara?."
ita dai Ummi idanu ta zuba musu inda sabo ai ta saba da tsamar Raliya da Hayatuddeen da d'an korensu Faruq,
murmushi tayi jin Raliya na cewa.
"Eh baka iya kimtsa kanka da kayanka ba amman ka iya sabule wondo ka tsallake ka barshi a tsakiyar falo dan gaka isshashe kai kanada Raliya baiwa mai yi maka tattara."
Faruq ne ya mik'e tare da cewa.
"To ai yana jin bacci ne lokacin shiyasa."
tura baki tayi kana ta sharesu,
shi kuwa Hayatuddeen meda hankalin shi yayi kan Ummi cikin lallab'ata yace.
"Ummi kin yiwa Hamma Saifuddeen batun sauyin makarantar da zai mana ne?."
kai ta gyad'a mishi kana tace.
"Eh na gaya mishi yace zai bincika makarantar data dace daku."
ido ya kashewa Faruq sannan ya k'ara motso Ummi cikin sanyin lafazi yace.
"Ba na gaya miki cewar akwai wata sabuwar makaranta MATRIX nan bayanmu kadan a kan hanya gab da kuros mai k'ollo nan hanyar F, C, E , makarantar tanada kyau kice masa ya samu nan kinga kusa da gidane koda k'afama zamuje ko Faruq."
da sauri Faruq yace.
"Eh mana kinga kun huta bamu kud'in machine."
da sauri Raliya ta mik'e kalon tara saura kwata tayi musu tare da cewa.
"Kan bala'i wannan makarantar da sai yaran manya makarantar da sai dai d'an talaka ya gani da ido shine zakuce shi kukeson Hamma Saifuddeen ya saku ko tausayin shima ku bakwaji kaji hegun yara da girman kai da son k'arya da papa, tab lallai aiki ya sameku yaseen Ummi karki yarda zasu talauta miki d'a dan sunga yana musu duk abinda suke so."
da sauri ta kauce ganin Hayatuddeen ya kai mata duka,
d'akinta dake fuskantar d'akin Ummi ta shige da gudu tana musu dariyar mugunta.
shiko Hayatuddeen wayarshi ya zaro ya amsa kiran Imran wanda yazo dan d'aukan Hayatuddeen suje gidansu Zakariyya dan gaida kakarshi ta fad'i ta gurd'e a hannu.
bayan Imran ya shigo sun gaisa da Ummi,
sai suka sallameta suka fito.

A bakin gate suka d'an tsaya wurin Baba buzu,
cikin yanayin sun fara sabawa dashi sukace.
"Baba bari muje gidansu Zakariyya."
murmushi yayi tare da cewa.
"Auho kuce wanda yace zai bani kakarshi in aura in inaso ko?."
Cikin shek'iyamci Imran yace.
"Yauwa to ita zumuje dubowa, me zaka kawo mu kai mata?."
goro ya fiddo cikin aljihun rigarshi irin gara ga nakan nan na buzaye,
ya mik'awa Hayatuddeen su tare da cewa.
"To gashi ku kai mata wannan."
aifa dariya suka sa sannan suka amsa suka tafi.
gidansu Isma'il suka biya sannan suka nufi hanyar da zai sadasu da ceceniya kasan cewar ba nisa sosai tsaka ninsu.

Suna isa,
Zakariyya na jin muryarsu ya fito da sauri yana isa inda suke ya basu hannu suka tafa tare yin murmushi suna cikin haka sukaji wata zazzak'ar murya mai dad'in sauraro tana cewa...!


By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

*PAGE 12*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Cikin d'an d'aga murya take cewa.
"Zakariyya! Zakariyya!! Zakariyya!!! wlh bana son raini kazo ka bani wayata."
cikin d'aga murya Zakariyya yace.
"Ank'i a bada d'in uwar masifa k'arfinki ya kwata miki aikin kawai ke ba dama mutun ya tab'a woyarki sai kiyi ta rashin mutunci."
dariya Imran yayi tare da cewa.
"Yaseen yau sai mun zuk'e cajinki."
dai-dai lokacin ta fito daga ganinta yayar Zakariyya ne dan suna d'an kama kekyawace ajin forko tanada cikar sura,
idanu ta zubawa Hayatuddeen da yake kallonta tare da cewa.
"Wannan itama irin Raliya ce ko sai hegen masifa."
Zakariyya ne yayi dariya tare da cewa.
"Haka suke dan sun samu sun fimu da sharu uku zuwa hud'u kacal sai sukeji kamar sune suka haifemu."
da sauri ta iso ta wabce wayarta dake hannun Imran kana tace.
"Hegu kawai masu jajayen fuskoki."
cikin tsiya Zakariyya yace.
"Shima samune kina bak'in cikin jar fatanmu."
tsaki taja tare da cewa.
"Hauka kawai me abin jin haushi duk kunyi kalar zabiya kuma dai baku fini fari ba."
dariya Imran yayi sannan yace.
"Ke dai dama kina bak'in ciki ace Zakariyya ya fiki kyau."
juyawa tayi tana cewa.
"A ina ka tab'a ganin namiji yafi macce kyau."
cikin sauri Hayatuddeen yasha gabanta tare da cewa.
"Yaseen na miji nafin mace kyau kin ganki duk da kyanki Hamma Saifuddeen d'ina ya fiki kyau, in kin ganshi keda kanki zaki shaida hakan."
bata bi ta kansuba ta shiga cikin parlour inda kakarsu ke kwance tanata raki,
bayanta sukabi da saurinsu suna shiga suka gaida Kaka sannan suka zauna gefen ta. Cikin kula tace.
"Imarana ya gida?."
ba tare da ya juyo ya kalletaba yace.
"Lfy lau Alhamdulillahi Mama tace in gaidaki da jiki."
"Ina amsawa." ta bashi amsa tare da juyawa tana kallon Hayatuddeen da yake nunawa Zakariyya abu a wayarshi tace.
"Kai Hayatu hankalin ka duk yana kan waya, Umminka tana lfy ko."
still idanunshi na kan wayar yace.
"Nace miki ki dena cemin Hayatu, ki cika min sunana Hayatuddeen ko kuma kice min Deen in kuwa Hayatun kike son fad'i to kice Hayat."
dariya budurwannan tayi ganin yadda Tsohuwar taketa buga mishi harara,
Isma'il ma da babu bakin mgna sai murmushi yakeyi
Imran ma dariyar yayi dan da yaji dariyar Budurwar ne yasashi kallon inda take kallo,
d'ago kansu sukayi suma suka kallesu jin dariyar tayi yawa,
Zakariyya ne ya kad'a baki yace.
"Haba dai Inna ai wannan kallo sai ya razanamu, dan Allah ki rage idanunki."
sai ya kuma kalli yayar tashi cikin tsigar tsokana yace.
"Ke ashe ga wacca ta b'ataki da k'uru-k'urun idanu bamu ankara ba."
jin haka ai yasa ta haiyayak'o kanshi wai ya zageta mai k'uru-k'urun idanu,
ita kuwa Inna baki ta tab'e tare da cewa.
"Wannan dokoki na kiran sunanka ai sai 'yan boko ni ba abinda ya shamin kai Hayatu zan kiraka."
dariya yayi sosai jin Imran na ce mata.
"To inna ba sai mu shigar dake makarantarba mu samu ki haddace sunan ba Dukke."
shi kuwa Zakariyya sanin bayanshi Inna takebi yasa ya mik'e yana tarfawa yayar tashi tsiya,
ganin Inna tak'i ta kulashi yasa ta sunkuyo ta zari hand bag nata tare da car key d'inta dake gefen jakar cikin jin haushin tace.
"Yaseen bazan zauna a gidan nan ba,
zan koma gida haka kawai a turoni dan inzo in taimaka miki tunda kin gurd'e kuma kina ganin jikanki ya rainani da yake kin fi sonshi bazaki mishi fad'aba."
cikin sababi irin na tsofaffi masu zafi tace.
"Ki tafi mana kada Allah yasa ki zauna dan ubanki! ai bani na kirakiba ni dama Zahira nace a turo min dan itace mai mutunci,
amman tunda kikace bazaki zaunan ba ni kuwa yanzu zan kira Babanku kina komawa zaki dawo kiyi asaran man motarki kawai."
bata bi ta kan magar tsohuwar ba ta fice abinta,
su kuwa duk bayanta sukabi,
suna fitawa tana figin motarta ta tana shirin barin harabar d'an k'aramin gidan,
Hayatuddeen ne yayi sauri d'aga murya tare da cewa.
"Kadafa ki manta kinada tambarin *L* yaseen ki kula kada kije kiyi ta tambola a titi."
k'ura ta bud'esu dashi kana tayi ficewarta daga gidan.

Su kuwa nan sukayi ta sabgoginsu sai gab da magrib suka fito suka nufi gida duk da akwai 'yar tazara tsakaninsu amman haka suke tattakawa da k'afafunsu har zuwa gida a cewarsu Hayatuddeen yaga garin da kyau,
suna isa gab da gidansu Isma'il ne Imran ya tare machine ya tafi,
shi kuwa Hayatuddeen jan hannun isma'il yayi a kan dole sai suje gidansu a dole ya bishi.

Sannu-sannu su Ummi sun saba da bak'otansu da iyayen abokansu Saifuddeen da Hayatuddeen.

Yau jumma'a shiyasa Saifuddeen bai fita da wuriba,
sai h'ar k'arfe tara ya tashi daga baccin daya koma bayan sallan asuba,
a hankali ya mik'e mik'a yayi tare da yin salati a zuciyarshi,
bathroom ya nufa,
wonka yayi mai rai da lfy kana yayi al'wala sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunshi sai d'an k'aramin dake hannunshi bisa bakin gado ya zauna ya fara tsane ruwan jikinshi,
mik'ewa ya kumayi bisa kujerar dressing mirror ya zauna mai ya fara shafawa sannan ya gyara suman kanshi,
mik'ewa yayi zuwa gaban durowar bud'ewa yayi ya zaro wani tattausan yadi mai taushi yadin bak'i ne mai shek'i yanada zanen gidan dara-dara,
sai kuma ya zaro boxer and vest farare k'al-k'al,
a bakin gado ya ajiyesu,
sannan ya kuma dawowa gefen durowar inda takalmanshi ke jere bisa wani kekyawan abin aje takalma wasu fararen takalma ya zaro,
sai ya kuma bud'e d'aya sashin na durowar inda hulunanshi ke jere,
hula zanna bukar ya zaro fara mai ratsin bak'i-bak'i,
kimtsawa yayi cikin kayan da ya fidda d'in,
bayan ya gama sawane ya dawo gaban mirror yana dai'daita zaman hularshi a kanshi,
murmushi yayi wanda har saida dimples nashi suka lotsa shida kanshi yasan yana kama da Abbansu,
ya kuma san Abbansu kekyawane na nunawa sa'a sosai bak'in kayan ya k'ara fito da farin fatarshi ras,
in ka ganshi tamkar balarabe suman kanshi a konce lib-lib a k'eyanshi da gefen sajenshi,
turare ya d'auka ya feshe jikinshi dashi lungu da sak'o,
ido ya lumshe a hankali tare da shak'an numfashi dan jin sassanyan k'amshin turaren dake ratsa mishi jiki da zuciya.
Towel d'in daya ciren ne ya d'auka ya shiga bathroom ya
shanyashi sannan ya fito,
ya nufi parlour.

Ummi kuwa da yaranta duk suna parlour suna tab'a hira,
Ummi na bisa 3 str Hayatuddeen kuma na konce kusa da ita yayi !!! kan tv,
da sauri Ummi ta d'ago kanta ido ta zubawa steps d'in sauk'owa k'asan dan jin takun d'an nata,
murmushi tayi tare lumshe ido kana tana godewa Allah daya azurtata da wannan kekyawa halitta a matsayin d'anta cikin sanyin sauti tace.
"Masha Allah, babana yayi kyau matuk'a gaya."
murmushi yayi shima dan idanunshi na kanta a hankali yaci gaba da tako steps d'in cikin takunshi mai d'arka hankali har ya sauk'o,
gabab da ita yazo ya zauna cikin kurma-kurma ya gaidata.
"Lfy lau Babana ka tashi lfy ko?."
hannunta ya kamo ya manna a habarshi alamun lfy lau Alhamdulillahi.
cikin girmamawa Raliya ta kalleshi tare da cewa.
"Ina kwana Hamma Saifuddeen."
kai ya jinjina mata ta lamun lfy lau,
sai ya kuma kallin Hayatuddeen dake kallonshi yana mirmushi cikin k'aunar d'an uwan nashi, murya a sake yace.
"Barka da jumma'a Hamma." bai jira amsarshi ba yaci gaba da cewa.
"Kayi kyau sosai Hamma na."
murmushi yayi kana ya shafa fuskar k'anin nashi.
Ummi kuwa mik'ewa tayi ta nufi dinning table tare da yafitoshi tai mishi alamar yazo yayi breakfast."
mik'ewa yayi yabi bayanta,

Zama yayi a kujerar dake dab da ita yana kallon yadda taken had'a mishi tea,
tana gamawa ta mik'a mishi sannan ta zubo mishi soyayyan dankali da kwai sai kuma ta jawo wani filet d'in da alamun wani abun zata kuma zuba mishi,
da sauri ya jujjuya mata kai,
tare da mata alamun sauri yakeyi tea d'in kawai zaisha da d'ankalin,
sanin halinshi da halittarshi ta rashin cin abinci da yawane yasata meda filet d'in sannan ta zauna gefenshi yana d'anci suna kuma d'an tab'a hira sauri-sauri ya gama ya sallameta ya fita ya tafi.

Ita kuwa Ummi ta haura sama kai tsaye bedroom nashi ta nufa ita da kanta ta gyara mishi d'akinshi da bathroom da parlour nashi duka ta sassake mishi labuye sannan ta feffesa turaren d'aki mai suna touch me sannan ta rege mishi gudun AC kana ta fito.

Tana sauk'owa taci karo da Hayatuddeen a tsakiyar parlour yanata kiciniyar kwance bel d'in k'ugunshi,
ido ta zura mishi ba tare da ta k'arisa sauk'owanba hakama Raliya ido ta zura mishi,
shi kuwa baima san sunayi ba yana zare bel d'in yayi k'asa da dogon wondon Blue Jeans dake jikinshi ya rage dagashi sai d'an gajeren wondo dake jikinshi, sawunshi ya zare kana ya tsallake wondon inda ya sab'uleshi ya nufi hanyar d'akinshi tare da cilla bel d'in a tsakiyar parlour,
sai kuma ya fara kiciniyar cire rigarshi tare da cewa.
"Nima bari inje inyi wonka dan yau a masallacin fad'ar jiha zamuyi salla dasu Imran dasu Sulaiman Zakariyya shi yace yama je tun d'azu."
tsayawa yayi tare da juyawa da sauri jin Raliya na mishi mgna cikin tsawa take ce mishi.
"Wai kai kam Hayatuddeen wanne irin yarone mara kan gado,
kalli yadda ka watsa mana parlour dan tsabar sakarci da sakalci inda ka cire wondonka nan kake bar mana shi wato kai gaka auta mai buhun sakalci uwar wa zata tattara maka kwamutsan naka to da ka barshi?."
wani dogon tsaki yaja tare da cewa.
"Uwata mana ce miki akayi bani da gatane banza kawai uwar sa ido."
yana fad'in haka yayi shigewarsa d'an k'aramin side inshi,
ita kuwa Raliya taita zumbura baki dan Ummi ta sata tattaramishi kayanshi daya watsar.


Saifuddeen kuwa yana fita yaci karo da Salisu wanda shine ya d'aukeshi suka nufi hanyarsu da zata sadasu da titin tutun wada,
mik'ewa sukayi direct har kusa da mashigar G.S.U cikin nitsuwa Salisu ke draving suna gab da shiga gate d'in.
Jonapwd k'ungiyar nakasassu ta jihar kenan Salisu ya juyo cikin nitsuwa da kula ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Motocin nan da mukayi mgnarsu last week sun iso jiya,
shiyasa nazo da nufin muje ka gansu ka zab'i kalan da kakeso a ciki,
dan gsky zamanka ba mota baiyiba,
tunda ko bazaka yi tuk'iba zamu iya samar maka amintaccen direba da zai rink'a kaika duk inda kakeso da kai da Ummi kafin Hayatuddeen ya k'ara girma."
murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara zamanshi duk da yaga Salisun yayi parking kai ya jinjina tare da rubuta mishi.
"Bank'i shawararku bafa sai dai kuda kanku kunsan cewa yanzu bani da kud'in a k'asa dan na yashe duk asusuna nayi hidimar k'aurannan to kuma bani son abu da bashi."
a take fuskar Salisu ta sauya yanayi,
cikin sanyin sauti yace.
"Bashi kuma! Saifuddeen yanzu ashe dama kayana ba naka bane,
ashe dan ka d'auki mota d'aya rak cikin jerin motoci kusan takwas wanda kaine silar samar min jarinsu sai ya zama wani abu?."
Kai ya rink'a jujjuyawa cikin nuna alamun ba haka bane,
ganin haka yasa Salisu cewa.
"To kada ka sake kiramin kalmar bashi a tsakaninmu kuma ko bakaje ka zab'i kalar da kake soba ni zan zab'a maka da kaina gobe zan kawo maka ita har gida,
kuma in ba matsala a cikin yaran da suke wonke mana motocin akwai wani yaro Sule yanada nitsuwa ya kuma iya tuk'i na mutunci sai ya dawo nan ya rink'a kaiku duk inda kuke buk'ata zai kuma iya kula da shuke-shuken gidan in yaso duk wata ka rink'a biyanshi abinda nake biyanshi,
to dama kullum ina bashi kud'in abinci,
to kaga kai ba sai kayi ta bashi kud'in abinciba sai Ummi ta rink'a zuba mishi shida baba maigadi ko?." ya k'arishe mgnar cikin yanayin tambaya.
kai ya jinjina mishi tare da rubuta mishi.
"To ba matsala kayi yadda kaga ya dace."
cikin jin dad'in amincewar Saifuddeen d'in yace.
"To ba matsala."

Daga nan suka fito suka shiga cikin harabar wurin,
kai tsaye office d'in Ishaq suka nufa,
jin motsin bud'e k'ofarne yasa Ishaq juyawa da sauri sai ya kuma mik'e da sauri jin muryar Salisu,
numfashi ya shak'a tare da cewa.
"Lalle marhabin da manyan bak'i."
jin Saifuddeen ya rik'e hannunshi ya sashi juyawa gareshi tare da cewa.
"Kai amman naji haushi wlh kaga da kazo awa uku da suka wuce da ka had'u da Zaleeha sabuwar ma'akaciyar gidan radio vision FM gombe wacce take gabatar da shirin *Babu nakasasshe sai rago* yau dani mukayi hira na d'an bata tarihin rayuwata ka ko san dole zaka shiga ciki."
shiru yayi jin Saifuddeen ya rufe mishi baki da hannu tare da zaro wayarshi da hannunshi d'aya kana ya rubuta mishi text.
"Kai dan Allah ka huta mana wai bakinka bai gajiya da surutune? to ni ka bani ruwan sha tukun."
da sauri ya zaro wayarshi jin shigowar sak'o yasan Saifuddeen ne ya mishi mgn,
dariya yayi sanda ya karanta kana yace.
"To sarkin k'warafi ga wuri ku zauna."
sai kuma ya d'anyi taku biyu zuwa uku ya isa gaban firiji ruwan sanyi ya d'auko musu sannan yazo kusa dasu,
Salisu kam har yau bai dena mamakin yadda abota ta kasance tsakanin makaho da kurmaba suna kuma fahimtar juna over,
amsar ruwan sukayi saida suka d'an sha sannan suka ci gaba da hira amman banda Saifuddeen dan TV yake kallon tashar Farin wata wanda duk had'e suke da vision sosai ya zubawa TV idanu yana karanta rubutun daya bayyana a fuskar tv inda aka rubuta Babu nakasasshe sai rago, sosai Saifuddeen ya maida hankalin shi kan tv ganin sun hasko fuskar wata kekyawar budurwa mai cikar haiba,
lips d'inta ya zubawa idanu dan yana son gane abinda zata fad'a da kyau,
wani irin sassanyan ajiyan zuciya yayi jin wani abu na yana zirta cikin zuciyarshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login