Showing 66001 words to 69000 words out of 176868 words

Chapter 23 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

sabida tsananin tsoro da firgici.

Shi kuwa yana isa gaban motarta cikin rumtse ido ya wore tafin hannnshi kana ya mari glass d'in gaban motarta a take ya tarwatse yayi cikin motar,
jin sautin tarwatsewan glass d'in yasa gaba d'aya mutane sukayi cirko-cirko domin duk cikin fad'in gombe ansan waye Dalla domin yayi k'aurin suna,
akan izaya da d'agawa da zalumcin Mace koda aurenta ko ba aure in dai ya ganta kuma ta mishi tofa zaisa yaranshi su d'auko mishi ita ya biya buk'atarshi da ita so yana cin karensa babu babbaka tunda yana ganin yanada manya gashi cikekken ɗan kalare mai girman daba.
Bata dawo daga firgincin daya sataba taji ya bud'e marfin motar tata kana yasa hannunshi ya damk'i hannunta da azaban k'arfi wonda saida ta saki k'ara,
fincikota yayi woje ya tsaidata gabanshi sannan ya ware tafin hanunshi ya yarfa mata wani gigitaccen mari mai azabar tsiya wanda saida taga taurari na gilmawa kana taji kunnenta yayi dummmm.
A take sai ga jini ta hancinta,
shi kuwa Dalla ba tare da yace mata komaiba ya juya ya shiga motarshi, dan ya sawa ranshi wannan jan kunne kawai ya mata yanke hukunci kuma na nan tafe a kanta haka yasa ya juya
don fitilar bada hannu ta basu damar wucewa.

Shi kuwa Saifuddee ganin abinda Dalla yayi mata tun fasa mata glass da yayi ya nufo kansu da gudu so kasancewar akwai 'yar tazara tsakaninsu gashi sai ya ratsa gaban babura da keke napeps da motocin da suka cika titin yasa kafinma ya isa tuni Dalla ya shiga motarshi,
kana babura da napep da motoci duk sun fara shirin wucewa wonda dole suke ratsawa ta gefen motarta. Itako tunda ya mareta zafin marin da gigita yasa ta fad'in gaban motar tata ta kifu samanshi.
Cikin gudu da sassarfa ya isa gareta, yana zuwa yasa hannunshi duka biyu ya kamo kafad'unta, kana ya d'agota ya tsaidata suna fuskantar juna yadda in tayi mgna zai iya ganewa,
idonshi ya rumtse da k'arfi ganin jini na bin hancinta kana tuni fuskarta tayi jazir hatta shatin yatsunshi sun taso a fuskarta,
ga wasu zafafan hawaye dake kwaranya a idanunta sabida rad'ad'in marin da k'unar zuciya kan cimata zarafi da tozartata da akayi a tsakiyar gari.
shi kuwa Saifuddeen tuni fuskarshi ta sauya launi daga fara ta koma jazir kana idanunshi tamkar su amayar da wuta tuni jijiyoyin kanshi suka taso,
yayinda jijiyar kan goshinsa tayi ziwat har kan tsinin karan hancinsa a fili zaka gane zallan b'acin rai, gaba d'aya jikinshi tsuma yakeyi,
ido ya zubawa fuskarta kana itama ido ta zuba mishi cikin rauni da muryar kuka tace.
"Wlh ban saniba bada gaggan na buga mishi motarshi ba hankalina ya tafi wurin kallon wani ne."
lips enshi na k'asa ya taune da k'arfi tamkar zai hudashi,
kana ya kama hannunta tare da yi mata nuni data shiga motarta,
cikin rawan jiki ta nufi gefen direban,
hannunta ya kamo da sauri, juyowa tayi tana kallonshi itama kai ya jujjuya mata alamar a a kana ya nuna mata gefen mai zaman banza,
ba musu ta zagaya ta shiga ta zauna.
Shi kuwa gefen driving sit ya shiga ya zauna,
sit bell yaja ya sank'ala jikinshi,
kana ya juyo ya kalleta tare da yi mata alamu da idonshi tasa nata sit bell d'in.
ba musu ta saka,
sai ta kuma d'ago kanta da sauri jin ya dannawa motar Key kana ya figi motar a guje,
ido ta zazzaro ganin yadda yake tsula gudu tamkar zai tashi sama,
gudu yakeyi da tsanani amman cikin bin k'a'ida da dokar tuk'i cikin abinda bai gaza 5 minutes ba ya cimma motocin su Dalla, yayinda su kuwa tuni sun mik'a hanyar data ratsa bakin kasuwa zata kuma wuce zata bi ta kaisu fantami daga nan su ratsa bayan gidan goje,
binsu yakeyi kib da kib haka yasa suka gane binsu akeyi,
tuni kuma an fara kiraye-kirayen sallan mangrib,
murmushin mugunta Dalla yayi kana ya juya akalar motarshi ya shiga cikin sitadiyon ,
shima binsu yayi a baya kusan a tare sukayi parking.
cikin azama da zafin nama ya bud'e ya fito kana ya zagoyo inda take ya bud'e mata tare da kamo hannunta ya juyo ya nufi inda motar Dalla take,
shima Dalla wurinsu ya nufa,
a tsakiyar sitadiyon d'in sukayi kicibus,
cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa Saifuddeen yayiwa Dalla alama da hannu akan ya bata hak'uri.
cikin izaya da tak'ama Dalla ya gyara tsayuwanshi tare da cewa.
"Baka da bakine ko iskanci ne zaka zo kana min mgnar kurame?."
cikin tsuke fuska Saifuddeen ya kuma yimishi alamu daya bata hak'uri, ganin haka Dalla ya kuma motsotsu kana yace.
"OK kyautarta ka kawo min kenan?, baka san waye Dalla bako? shiyasa ka biyoni da mace kana nufin in bata hak'uri ne ko?."
cikin sauri da jin dad'in Dalla ya fahimci abinda yake nufi ya tsare fuska kana ya gyad'a mishi kai alamar eh ka bata hak'uri.
wani fatsik'in murmushi Dalla yayi tare da lashe manyan lip's enshi yace.
"Hmmm aini Dalla bana bada hak'uri sai dai in bata ciki tunda ka biyoni da ita, gata kuma zata iya kashe kishin dake addabata wunin yau gaba d'aya ban hutaba kaga yanzu na samu wurin hutawa gashi tanada lafiyayyun kayan marmari a jikinta, yanzu zan mata inkiyata Dalla-dalla da budurcinta zan rab'i jikinta."
Ya k'arishe mgnar tare da kai hannunshi kan k'irjinta.
Wani irin wawan ihu da kururuwa Dalla ya kurma jin wani irin damk'a da Saifuddeen yayiwa hannunshi ba tare da ya samu ya isar da hannun nashi kan k'irjintan ba,
ihu Dalla ya kuma kurmawa jin Saifuddeen ya kuma murd'a mishi hannunshi har saida ya bada sautin b'as alamun ya k'arya mishi hannun, ihun daya sane yasa tarin zugan matasan dake cikin sauran motoci hud'un nan duk suka fito,
wando gaba d'ayansu 'yan kalarene domin duk kansu da makamai a hannunsu wasu da sanduna wasu da kataki wasuma da wuk'ak'e.
A guje suka nufin inda suke, shi kuwa Saifuddeen ko kad'an bai karaya da ganinsu ba,
asalima zagewa yayi ya fara dukan Dalla tamkar Allah ne ya aikoshi,
kunsan fad'an kurma babu sauk'i shiyasa basa tsokana basa tada husuma sabida sun san zuk'atansu basa iya jurar suga ana raini ko zalumci bare fajirci.
sam Dalla ya gaza bawa kanshi kariya,
shiko Saifuddeen dukan ƙaton gargadi yakewa Dalla tare da dandatseshi ta yadda bazai sake sha'awar wata d'iya maceba a duniyar nan har gaban abadan, ita kuwa Zaleeha ganin yadda suka nufo kansu haik'an k'adaran ne yasata sakin ihu tare da bubuga tsalle tanayi tana yarfa hannu tana cewa.
"Zomu gudu zasuyi maka illa zasu kasheka fa,
kazoo mugudu karsu isomu zasu illata ka."
ganin sam bai sararawa Dallanba yasa tayi sauri ta shiga tsakanin su kana ta rik'o hannayenshi tare da kallon fuskarshi tace.
"Mu gudu zafa su kashemu."
ido ya d'ago ya kalleta yadda jikinta ke rawa tamkar mazari tsoro da firgici k'arara a idanunta da ka ganta kasan cikekkiyar matsoraciya mai lasisi ce, haka yasa ya kamo hannunta kana ya juya da ita inda motarta take,
su kuwa zugan 'yan kalaren nan kansu suka nufo a guje ganin hakane yasa,
yajata da k'arfi sannan ya bud'emata motartata wurin zaman direba ya ajiyeta kana ya meda marfin ya rufe sannan ya sunkuyo kanta tare da kad'a mata yatsunshi biyu kana yayi mata alama dataja motar ta gudu, gane abinda yake nufine yasa ta jujjuya kai tare da zubda hawaye cikin haki tace.
"Mutafi zasu kasheka fa 'yan kalarene fa yaranshi ne."
ganin zata b'ata lokaci har suzo su sameta suyi mata illane yasashi buga marfin motar da k'arfi tare dayi mata gurnani irin nasu na kurame wanda in bawai ka saniba sai kayi zaton tsawa ya buga mata hakance ta kasance ga Zaleeha dan jin sautinshi tayi a sama haka yasa ta figi motarta a guje, tana jan motar suna isowa inda yake, yayinda shi kuwa yake kallonta so yake yaga fitanta a wurin, su kuwa suna isa inda yake ba tare da ya juyoba don shi dai kurmane bazaiji sautin takun k'afafunsu ba,
suna isa d'aya daga cikinsu ya narka mishi k'aton katakon dake hannunshi a tsakiyar gadon bayanshi kafin, yayi wani yunk'urinma
d'aya daga cikinsune ya dab'a mishi wuk'a a tsakiyar bayanshi kana ya zaro wuk'ar wanda tuni sun farka mishi rigarshi
wani irin razanennen ihu Zaleeha tasaka tare da zubawa bayanshi ido sabida tana ganinshi ras dan hasken motoci dake haska wurin da hasken fitulun dake zagaye da farfajiyar wurin
cikin tsananin tsoro da firgici taja motarta ta bar sitadiyon d'in,
tana fita kai tsaye gombe division ta nufa.

Shi kuwa Saifuddin tuni sun mishi illa sun daddatsa mishi kataki a tsakiyan bayanshi.
yayinda duk da haka bai bar kare kanshiba sai dai ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi gashi sun zomishi ta bayanshi kuma sunzo tare da makamai yayinda shi kuwa babu ko allura a jikinshi,
haka yasa sukayi mishi illah mafi muni a jikin d'an adam, haka suka rink'a hankad'ashi kan k'arafun wurin suna buga bayanshi a kai
saida sukaga yabar motsi kana suka dauki uban gidansu da Saifuddeen ya daddaga mishi jelershi sukaja motocinsu suka tafi,
yayinda tuni mazauna wurin kuwa sun watse don kowa yasan rashin mutuncin Dalla.

Shiru cikin sitadiyon d'in ba ko tsuntsu sai Saifuddin dake yashe tamkar mamaci,.

Ita kuwa Zaleeha bayan ta sanarwa hukuma, ganin ita macece kuma sananniya kana yar babban Malamin da akeji dashi a fad'in jihar dama k'asar bak'i d'aya yasa aka had'ata da police officer d'aya ya rakata gidansu dake New G.R.A...



A haka police officers na station d'in gombe division suka iso,
yayinda aka had'a da sosojin Anty kalare,
kana
suna isowa ganin halin da yake ciki ne yasa suka d'aukeshi,
kai tsaye general hospital Gombe suka nufa dashi, kai tsaye aka wuce dashi o,p,d. suna isa ma aikatan wannan sashin suka turo irin yan wannan gadaje na d'aukar marasa lfy,
tare dasa hannun hukuma aka karb'eshi bayan an duddubashi ganin aikin babbane ya kuma ji rauni sosai ne sai aka basu takarda wacce zata sadasu da babban likitan dake Medical Center.

Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon Saifuddin
ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o,
text ne aka turo kamar haka.
```"Babana Saifuddin Kana ina? ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."```
shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa.
"Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan."
sai kuma ga wani sak'on da yaga suna no daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa.
```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."```
haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi,
dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe,
kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa
d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace.
"Saifuddeen!."
sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu,
mazuk'in numfashin suka manna mishi,
kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi.
Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba.

Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta,
amman abin yaci tura,
sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu,
shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su.
Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa,
canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu,
bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa.
Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi,
sai ya kuma mik'ewa da sauri kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen.
cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa.
"Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy."
sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi,
dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu,
da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro,
cikin kad'uwa yace.
"Doctor Adnan meke faruwa?."
kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace.
"Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne."
cikin firgici Arabi yace.
"Innalillahi Saifuddeen! to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana."
cikin kad'uwa police d'in yace.
"Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi."
cikin rauni Arabi yace.
"officer kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?."
cikin kauda kai officer d'in yace.
"Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane,
domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya,
itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto,
to ganin a firgice take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu."
cikin rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa.
"Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?."
ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa.
"Please officer ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in."
da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost
babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi,
a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace.
"Sannunku lfy kuwa?."
cikin saisaita fuska mai jan motar yace.
"Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate."
cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo,
bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito,
hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace.
"Kayi mana sallama da Hayatuddeen."
to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa.
"Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?."
ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi,
"Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi."
cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa.
"Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?."
cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala, jiki a mace yace.
"Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi."
cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau.
A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen ,
cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace.
"Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi, komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho."
cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa.
"Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma."
ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne."
dariya Raliya tayi tare da cewa..
"Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi."
dariya sukayi baki d'aya dan shima yasan halinshi kenan.
Raihana kuwa cikin dariya tace.
"Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka."
Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo,
cikin raha tace.
"Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya."
dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras.

Shi kuwa buzun nan
wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17 years da yan watanni ba, Hayatuddeen,
Raliyya matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login