Showing 30001 words to 33000 words out of 176868 words

Chapter 11 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

da fulawa da sugar.
cikin kula ya auna mishi kana ya bashi kud'inshi shi kuma ya bashi ledodin daya zuba shinkafar a ciki.
Karb'a yayi sannan ya wuce ya sayo mai dasu yis, dan yana son a rink'a had'awa da masa a sadakan da ake kaiwa masallacin.
Sai kuma ya sai kayan marmarin daya saba saya, sannan yaje layin masu nama,
zabbi ya saya guda uku aka yanka aka fige aka gyarasu.
sannan ya fito bakin inda Salisu zai sameshi nan ya irga sauran kud'in inda ya samu ya shigesu sosai yau dubu uku zaisa a asusunshi,
yana zama ba jimawa Salisu yazo sauk'e wota mata kuma lokacin biyar saura aifa yace kawai su tafi gida,
to dama shima Salisu ya gaji kawai sai suka kama hanyar dukku.

Suna isa gida Hayatuddeen da Faruq suka tarbeshi,
da murnarsu bayan ya ajiye ledidin yayiwa Ummi alamun tayi musu ferfesun zabbin da asuba suci ko da biredi da tea
ai kam Raihana murna ta rink'a wai zata huta yin miyan asuba.
Shi kuwa gefen Rahma ya zauna sai ya kuma manna kanshi a kafad'arta cikin nuna tsantsar alamun gajiya domin Saifuddeen yana da tsoron wahala to kuma Allah ya jarab ceshi da ita,
cikin tausayawa ta shafa fuskarshi dan gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi,
cikin tausayawa tace.
"D'an uwana sannu yau azumin da wuya anyi rana."
ido ya lumshe yana mai jin azabebben k'ishi,
a hankali ta kalli Ummi da tuni idonta sun cicciko da hawaye,
sai ta kuma kalli Raihana cikin sanyin murya tace.
"Raihana kai mishi ruwan wonka."
da sauri ta mik'e duk da tana jin wahalan azumi amman tasan dole ya fita shan zafin rana,
a randar tab'onsu ta d'iba saida ta cika mishi botiki sannan ta kai mishi bayan gida wanda yana wonke stab dan shi kad'ai ke amfani da bayan gidan tunda Nuruddeen da Abba suka rasu Hayatuddeen har yanzu bayan gidansu Ummi yake zuwa.
Tana kai ruwan taje ta d'auko mishi kondon sosonshi ta kai mishi sannan tace.
"Hamma na kai ruwan."
kai kawai ya iya gyad'a mata kana ya k'ara lafewa jikin Adda Rahmanshi,
jin hannun Ummi a kan gishinsa ne ya sashi d'ago kai ya zuba mata idanu,
ganin alamun zatayi kuka sai ya yunk'ura ya mik'e jiki na rawa,
cikin sanyi tace.
"Babana baka da lfy ko."
kai ya jujjuya mata a hankali kana yasa hannunshi kan cikinshi da yake a d'akale bafa irin d'akalellen cikin maceba a a irin nasu na maza,
sai ya kuma nuna mata mak'oshin sa alum k'ishi yakeji,
cikin kula tace.
"Je kayi wonka zakaji sanyi Babana."
Kai ya gyad'a mata sannan ya juya a hankali ya shiga kayan da zai sa ya d'auka sannan ya shiga bandakin,
yana shiga ya zare kayan jikinshi duka sannan yaje ya zauna bisa dutsen wonkan da yaketa shek'i da yake a inuwa yake baiyi zafiba,
surarshi ya k'arewa kallo idon ya zuba kan mararshi a ranshi yace.
"Hmmm yau kam kaji haza bayan baccinma har b'uya kayi ka koma cikin cikina ko?."
sai kuma ya fara watsa ruwan.

To Alhamdulillahi da yayi wonkan ya ji dama-dama gashi yana fitowa ana kiran salla,
al'wala yayi wanda tuni Ummi na gabanshi rik'e da dabino da surki mai d'umi,
dabinon ya amsa addu'a yayi kafin yaci guda uku,
da sauri ya jujjuya kanshi alamun shi bazai sha surkinba.
infa da sabo Ummi ta saba don haka yake ba komai yake ciba kuma zai tace maka yana jin yunwa kana kawo mishi abinci in ya tsakuri kad'an sai ya cire hannu wai ya k'oshi.
da sauri Hayatuddeen ya mik'o mishi pilet d'in su kankana to nan ya amshi fork a hannun Raihana sannan ya fara sokawa jikin kankanan da Rahma ta zuba mishi madara da sugar kad'an sabida ta sanshi da son zak'i,
ido kawai Ummi ta lumshe tana kallonshi sai yana tuno mata k'uruciyar Abbanshi,
bai shanye rabinshi bama yayi wani sassanyan gyatsa tare da mik'ewa wai ya k'oshi kenan,

jin ana tada kabbarane yasa Ummi bata hanashi fitaba,
shi kuwa kama hannun Hayatuddeen yayi suka fita zuwa masallacin.

Suma su Ummi sukayi haramar yin sallan.

Bayan an idar da salla, suna fitowa, Mudassir, Warisu, Salisu.
Suka nufi cikin gidansu Saifuddeen kai tsaye a babbar taburmar da Ummi ta saba shimfid'a musu suka zauna.
Rahma mace ta mik'e a hankali ta fara jero musu abin motsa baki, kankana da ayaba da dabinon suka fara ci, sunaci suna hira Rahma kuwa ita da kanta ta matso gefensu zama tayi tare da yi musu harara sannan ta jawo kulan dake gabanta cikin fidda numfashi tace.
"Daga yau bazan sake biye mukuba,
kun sani yi muku yambos wallahi ba k'aramar wuya na shaba kirba doyan nan wuya gareshi, gashi Raihana k'in tayani tayi wai ai nike biye muku."
Saminu da yanzu ya shigo tare da Saifuddeen ne ya harari Raihana tare da cewa.
"Yan ubanci zatayi mana shareta Adda Rahma ran salla ke kad'ai zamu bawa barka da salla."
tab'e baki Raihana tayi tare da cewa.
"Kada ku bani mana ni dama ban rok'aba."
Muddassir ne yayi d'an gyaran murya kana ya kalleta cikin tsuke fuska da bada umarni yace.
"Ni bazanma ci wannan yambos d'inba, yanzu ki d'an soya min dankali."
tura baki tayi tare da mik'ewa tana cewa.
"Ni wlh na gaji kuma yunwa nakeji."
Ummi ce ta d'anyi dariya kana tace.
"Zo Raihana taho nan ga dankalin dama na soyawa Bappa Alinku na kuma d'iba musu zoki basu nasan Mudassir so yake ya wahal min dake."
da sauri Saminu yace.
"To ni kuma indomi nakeso mai ruwa-ruwa yaji yaji da al'basa."
dariya sukayi baki d'aya dan sun san bazata iya musa mishiba,
sai kuma suka zuba musu ido jin tana ce mishi.
"Yanzu ne kakeso ko sai kun taso daga tabsir ne zan maka?."
ido ya lumshe kana ya zuba mata ido cikin sanyi yace.
"Ki huta sai mun dawo zamuyi aikin tare."
Ummi kam kauda ido tayi Warisu kuwa da Salisu tuni suketa hirarsu,
Mudassir kuma tuni ya zuba musu yambos d'in har ya fara ci Adda Rahma kuma tea tai ta had'a musu, nan suka fara ci sunaci suna hira.
Shi kuwa Saifuddeen gefen Ummin shi ya rab'a a hankali ya konta tare da d'ora kanshi a cinyarta, gyara zamanta tayi dan yaji dad'in konciyar,
kanshi ta d'an shafa cikin ido ta zuba mishi ganin sosai fa ya rame hancin shi zuwet har bisa baki idanunshi sun k'ara fitowa,
farinshi ya k'ara baiyana cikin kula ta kalleshi ganin ita yake kallo tace.
"Tashi mana Babana kaje kaci abinci da yan uwanka ai zakafi jin dad'in cin."
sanin in bai ciba hankalin ta bazai konta bane ya sashi yunk'urawa ya tashi zaune sannan ya amshi cup d'in da Adda Rahma ta cika da zazzafan tea mai k'auri sai k'amshi yake, gyara zamanshi yayi kana ya mik'awa Warisu hannunshi alamun ya bashi abinda suke ci d'in,
ganin Warisu zai kwatso mishi da yawane ya sashi nuna mishi yatsa d'aya alamun guda d'aya zai bashi,
kauda kai wWrisu yayi kana ya mik'o mishi guda biyu,
fuska ya d'an had'e dan shi cikinshi ya cika da ruwan da yaketa sha, ya kuma san Ummi zata sashi dole ya cinye biyun da ya sako mishi,
haka kuwa akayi dole ta sashi yaci sannan ta samishi soyayyan dankalin turawa, nanma yanaci yana d'an korawa da tea d'in a haka dai yaci kad'an.

Jin an fara kiran sallan isha yasa suka mik'e duka dan yin al'wala, dai-dai lokacin kuma Ahmad ya shigo shida Raliyya,
da sauri Rahma tace.
"Ke Raliyya meya kawoki a daren nan?."
kai ta d'an rausayar tare da gaida su Saifuddeen sannan ta zauna gaban Ummi cikin sanyi tace.
"Kai Adda Rahma ai nida Ya Ahmad ne muka zo nayi kewanku ne especially Hamma Saifuddeen, shiyasa nace yau mu taho tare kuma tare zamu koma."
Cikin fad'a Saifuddeen ya mata alamun da kada ta sake biyoshi gwara tazo da rana.
kai ta gyad'a mishi kana itama ta d'auki buta dan yin al'wala.

Su kuwa suna gamawa suka nufi masallaci koda akayi insha akayi asham, suna fitowa suka shiga cikin gida ruwa suka sha sannan suka nufi hanyar fita dan tafiya wurin tabsir kamar kullum,
har sunje bakin k'ofar fita Ummi tace.
"Ahmad ka dawo da wurifa ku tafi kasan Raliyya yanzu zatayi bacci anan."
juyawa yayi ya d'an kalli Raliyya cikin lumshe ido yace.
"Shike nan in tayi bacci sai in goyata mu tafi gida abinmu."
Warisu ne ya d'an bugeshi tare dayin k'asa da murya yace.
"Kai a gaban Ummin kake mata wannan kallon kamar wani tsohon maye."
ita kuwa Ummi cewa tai.
"Asheko yau sai dai ku kwana anan."
dariya sukayi kana suka fita,
Raihana kuwa da sauri ta isa gaban Saminu da shi yanzu yake shan ruwan,
cikin kauda kai ta mik'o mishi dabinon data ciko hannunta dashi guga bakwai ya tsinta kana yace.
"Ya isa sai mun dawo."
"To". tace dashi a sanyaye.

Daga nan suka fita suka tafi masallacin fad'an Dukku.

Ita kuwa Ummi ita da kanta ta shiga kitchen dan k'arisa aikin ferfesun zabbin data fara dan tasan yau Rahma ta gaji sosai,
Raliyya kuwa k'ofan bappa Ali ta nufa wurin Aunty Nina,
Raihana kuwa Attaruhu da al'basa ta d'auko tazo ta zauna gefen Rahma da keyiwa su Hayatuddeen homework shida Faruq, d'an k'aramin bilandan dake hannunta ta had'a kana ta yayyanka su ta jajjagasu sannan ta juye a roba mai marfi,
Hayatuddeen kuma saura su kankana da ayaban da akaci ya d'an rage guntayen yake ci shifa a dole baya son cin abu mai nauyi a rayuwarshi.

Ummi kuwa a kitchen tuni gidan ya cika da k'amshi dan zabbin sunji kayan had'i bayan ta gama zuba komai ne sai ta rufeshi bisa rushin yaci gaba da bararraka,
tea ta kuma tafasawa ta d'ura a filas sannan ta fito gudan dubu ta bawa Hayatuddeen ya sayo musu sabon biredi, guda biyu,
da sauri ya mik'e ya amshi kud'in yana zuwa ya kwaso biredi har guda hud'u.

Yana shigowa ganinshi da ledodi har biyu yasa Rahma cewa.
"Kai amman dai kai kam Hayatuddeen kaga ta kanka shin ba biyu aka aikeka ba?."
da sauri Ummi tace.
"Barshi ai bazai b'aciba nida nakeda samari yanzuma sun kusa dawowa."
Raihana ce ta d'an harareshi kana tace.
"Ai shiyasa yake komai na sakalci sabida yasan ba abinda za'ayi mishi ana tab'ashi kad'an Ummi da Hamma Saifuddeen zasuyi ta fad'a."
sai ta kuma kalli Rahma daketa dariya tace.
"Baga irinta nanba ai harda ke ake sakaltashi."
dariya sukayi baki d'aya ganin yana yiwa Raihana gwalo, Raliyya kuma da yanzu ta shigo dungure k'enyashi tayi nan suka fara 'yar tsamarsu ta sak'o da sak'o.

Daga bisani suka zauna suna hira cikin nitsuwa Raliyya ta gyara zamanta sannan ta fuskanci Ummi a hankali tace.
"Ummi Ya Ahmad yamin d'inki kala biyu ya kuma sayamin takalmi da mayafi ya kuma yiwa Faruq da Adam ma,
sai ya kuma yiwa Hayatuddeen dashi da Hamma Saifuddeen iri d'aya."
cikin mamaki Ummi tace.
"To shi Ahmad duk samunshi a kanku zai k'are ne, yayi ta zaman d'inki yana shan wuya ya kuma k'arar da samunshi a kanku ai wannan d'awainiya tayi yawa."
cikin sanyi tace.
"Wlh yana wahala kam Ummi kwana fa yakeyi yana d'inki, to amman kuma yana samun kud'i kinsan ya iya d'inki wasu ma daga bajoga da Ngalda duk shi suke kawowa d'inki gashi nan dukku duk ba wani tela daya fishi iya d'inki kinga fa duk zuriyar gidan sarki shi suke bawa d'inki tunda Ya Saminu ya hadasu dashi."
sai ta kuma kalli Raihana tare da cewa.
"Ai naga kema Ya Saminu ya bada aiyi miki dunkuna har kala uku, d'aya atampa ce d'aya kuma lace d'aya kuma shadda ce kedashi iri d'aya."
shiru tayi kamar bataji ba dan kunya takeji bata son a gane Ya Saminun sonta yakeyi tunda yace mata sai ya gama karatunshi, dan yanzu yana level 2 a G.S.U kunsan duk abokan Saifuddeen sun wuceshi da shekaru biyu sanadin nakasar daya samu ta sashi tsagaitawa da karatunshi sai daga baya da Nurudden ya kawo shawarar ya fara zuwa gombe dashi yana kaishi makarantar kuramen.
so shi Saminu shiyasa bai fiye zaman Dukku ba Salisu kuma kusan shine ya rik'e kakarshi inna shatu,
Mudassir kuwa yanzu iyayensu hankalinsu na kan karatun Ya Adnan da yake karatun likita yakeyi shiyasa basu bi ta kan mudassir ba tukun tunda sunaga shi Adnan ya kusa gamawa ason ransu sai sun gama da Adnan sannan su dawo kan Mudassir.
Warisu kuma yak'i ya nemi sana'a sai dogon buri to shima mudassir ai da yanada sana'a da duk sun d'auki nauyin karatunsu tunda su ba nauyin ciyar da wasu a kansu, to Saminu kuma da yake d'an gatane dan sarki kuma shalelenshi shiyasa tuni yayi nisa a karatunshi shiyasa ma yakeda damar yiwa Raihana hidima

Ganin Raihana tayi kamar bata jisu bane yasa suka kauda zancen.

Suna cikin haka suka jiyo hayaniyarsu Ahmad alamun sun dawo daga wurin tabsir d'in.

Bayan sun shigo duk suka zauna bisa taburma
sunata hirarsu ta abokai matasa,
ganin Ahmad ya sake ko a jikinshi kamar ba har Shabewa zasu komaba ne yasa Ummi ce mishi.
"Kaida zaku tafi kuma shine harda konciya kallifa har tara da kwata tayi."
sai ta kuma juyo ta kalli Raliyya dake konce kanta bisa sallayar da aka ninnenke.
"Ke maza tashi ku tafi."
cikin alamun bacci tace to,
Saifuddeen kuwa gyara zama yayi tare fuskantarsu cikin body language yace dasu.
"Ba inda fa zaku tafi a daren nan ku bari gobe kwa tafi da safe."
ido Ahmad ya zaro tare da cewa.
"To uban wa zaimin d'inkunan da na yanka na ajiye da kake cemin mu kwana."
hararan shi Saifuddeen yayi tare da rubuta mishi.
"Uban uwarka ne zai maka d'inkin."
dariya Ahmad yayi sosai yayinda Ummi taketa hararansu tare da ce musu.
"Kada ku sake samin kawuna a shirmenku kuyi da iyayenku banda salihan iyayenmu kam da suka bar duniya da dadewa."
cikin dariya Ahmad yace.
"Yoh dama wa zaice iyayenshi ba salihaiba mu nan gani muke duk duniya ba salihai kamarku."
shi dai Saifuddeen murmushi yayi had'i da shafa k'eyanshi da Ummi ta d'an dungura.
kana sai ya kuma tsuke fuska sannan ya musu alamun, dolefa su Ahmad su kwana da shi kad'ai yazo kamar kullum da zasu rakashi so tunda ya taho da Raliyya kuma dole su kwana,
ita kam Raliyya tuni ta b'ink'ire,
shi kuwa Ahmad tsaki yaja tare da cewa.
"Yaseen d'inku nanka sai bayan salla zan maka su, tunda dama gashi har yanzu baka kawosuba kuma kasan tun kafin azumi nake rufe karb'an d'inki amman da yake kai d'an gadarane da can da saya maka akeyi ma kullum wai sai ishirin da d'aya ga watan kake mik'o min dinkin ka kakuma samin naci dole in d'inka maka."
Tab'e baki yayi tare da d'aga mishi girarshi duka biyu alamun dolenka ai,
Warisu da su Salisu kuwa kanshi sukayi da cewa kadafa yayi musu al'k'awarin teloli.
mik'ewa yayi ya nufi d'akin Saifuddeen tare da ce musu.
"Kunga kada ku d'aura min jakar tsaba kaji su bini su tsatstsageni ni tuni na gama dinkunan maza yanzu na mata nakeyi, sai irin nasu Saifuddeen da basu badaba.
Saminu kuwa shi tuni yana bakin k'ofar kitchen ta woje yayinda Raihana keta ciki inda take dafa musu indomin,
sunata yar hirarsu,
nan ta dafa musu ta gama komai a wani babban tire ta juye musu kana ta jera musu fork sannan ta fito yana binta a baya suka isa a tsakiyar su ta ajiye musu tiren zazzafan indomin da yaketa k'amshin sai dafaffan kwai da tasa guda shida kowa daddaya kenan,
tana ajiyewa Ahmad daya canza kaya yasa jallabiyar Saifuddeen ya fito nan suka yiwa tiren zobe sunaci suna hira,
shi kuwa Saifuddeen kwan kawai ya fasa yake d'anci kana ya kalli Ummi data yunk'ura ta mik'e cikin body language yace mata ta zubo musu ferfesun in gama kai ta gyad'a tare da mishi alamun dama abinda ya tada ita kenan,
kai tsaye kitchen ta nufa kasan cewar zabbin guga ukune shiyasa ta zuba musu d'aya da rabi sannan ta d'auko biredi biyu kana tazo ta ajiye a gabansu aifa tuni Mudassir yayi gyaran murya tare da cewa.
"To yaseen ni dai na k'oshi da indomi ferfesun zansha."
dariya Ahmad yayi tare da cewa.
"Ni kuma dama mura nakeyi."
nanfa suka ture tiren indomin wanda dama kad'an ya rage,
nan suka fara cin tab'arb'ashin naman zabin da biredi,
duk sun nitsu sunaci shi kuwa Saifuddeen kad'an yaci sannan ya juyo ga Adda Rahma da Raihana Raliyya da suke ci a tare ido ya d'an lumshe ya musu alamun.....!








BY
*GARKUWAR FULANI*


*NAKASA BA KASAWA BACE*


*PAGE 7*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


_Pleees in kin san baki turo kuΙ—inki ba,kada ki wahal da kanki ki wahaΖ™ dani, ga nan hanyoyin da zakibi ki biya dan Allah masu cewa ina zan biya to gata inda zaku biya, katin mtn na 300 ta wannan number 0909783276 ko kuma ka/ki turo ta ac na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar kin biya ta wannan number 09097853276 to kina yin haka ko baki cemin komaiba zan saki a groups Ι—in da zanke post. Kada kuce zakuyi min transfer Ι—in katin etisalat bana so! In kuwa kikayi to yaseen sadaka kika bani, gareku masoyana mutanen Niger ga number da zakuyiwa mgna +22788137740 500CF zaku tura_


Zai sha tea. Da sauri Raliyya ta mik'e ta shiga kitchen tea d'in ta had'a mishi kana ta dawo ta bashi sanan ta zauna sukaci gaba da hirarsu suna kuma cin ferfesun,
shi kuwa gyara zama yayi ya d'an matsa ya basu daman su sake dan kamar sun matsu zaman taburmar ta d'an musu kad'an.
Bayan sun gama cine, Hayatuddeen ya mik'o

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login