Showing 93001 words to 96000 words out of 176868 words

Chapter 32 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

Garkuwa duk da nakasata,
Ya Nuruddeen ya haram tawa hannuwana rik'e k'ok'on bara ya damk'a min Al'k'alami da da jarumta.
Ummi ya zanyi da raina? sai yaushe zanyi nasarar tsaida hawayenki?
Sai yaushe zan saku farin ciki,
Ummi bani da baki dana fad'i miki irin k'unar da zuciyata keyi in naga zubar hawayenki bana jin k'unci a kan larurata sai naga hawayenki na zuba. Ummi kalli yadda Hayatuddeen ke kuka tamkar zai shid'e wannan ya nuna min gazawata ce kenan, ni nasan Ya Nuruddeen bai tab'a barina na zubda kwallaba, to ya akayi ni na kasa hanaku zubda naku hawaye ko dai nakasa tace sila? yanzu Ummi kema kuka kikeyi su Rahma Raihana Raliyya kuwa ya zasuyi,
Kalli kunsa Ahmad ma kuka, kalli ishaq bawan Allah da baya ganima kukanku ya sashi kuka, kalli Dr da kanta kun sata zubda hawaye, shin Ummi kin mance imanin bawa baya cika har sai ya yarda da k'addararshi mai kyau ko akasin haka."
tuni wani azabebben kuka ya kwabcewa Ummi wanda yasa ta kife mishi woyar gefenshi tare dasa hannunta tsakiyar kanshi ta shafa sumanshi har zuwa kan goshinsa sai kuma ta juya ta fita da sauri, domin tasan in yaga tana kuka zai birkice,
Abban Farida kuwa, hannu yasa ya kamo Hayatuddeen suka fita.
Yayinda tuni Dr Batulu kuwa tabi bayan Ummi,
shi kuwa Saifuddeen hannu ya mik'o ya kamo na Ishaq kamar yadda suka saba, shi kuwa Ishaq murmushin k'arfin hali yayi still kuma hawaye na kwaranya a idanunshi murya a raunace yace.
"Ya Rabi'u yace in gaidaka da jiki. Kana sak'on gskysuwa daga k'ungiyarmu sunayi maka fatan samun sauk'i."
hannunsu ya k'ara hadewa tare da jijjigawa alamun ya gode.
daga nan sukayi d'an hirarsu sannan Ishaq ya fito.

Nan ya samu Dr Batulu da Abban Farida sunata lallashinsu.
ganin lokacin salla ya kusa yasa suka, sallami Dr Batulu suka tafi ba tare da Dr Adnan ya fitoba.

Shi kuwa Dr Adnan ya dad'e tare da Dr Aliyu yana mishi k'arin bayani,
inda yace mai tunima an fara mishi alluran,
sannan kada su damu zai rink'a taho mishi da abincin daya dace yaci,
a nan asibitin Dr Adnan yayi sallan isha kana daga bisani suka shiga wurin Saifudddeen shida Dr Aliyu d'in.
suna shiga suka samu, nurse biyu maza masu gyara mishi jiki kamar taimaka mishi yayi wonka da al'wala da da juyashi ya fuskanci Al'k'ibllah yayi niya yayi sallanshi a koncen.

Suna shiga su kuma suka fita dan sun gama mishi shirin baccinsa,
Yana ganin Dr Adnan yayi murmushi tare da lumshe ido kana ya bud'esu ya kalli Dr Aliyu dake zaune bisa welchair d'inshi,
a hankali ya mik'o mishi hannu sukayi musabaha,
cikin kula Dr Aliyu yace.
"Ya jikin?." lips enshi ya motsa alamun da sauk'i kana ya jinjina kai,
shi kuwa Dr Aliyu cikin tausayawa yace.
"In sha Allah in an fiddaka zuwa India nanda wani d'an lokacin zaka fara tashi zaune da kanka."
da sauri Dr Adnan yace.
"Allah yasa."
Amin Dr Aliyu yace kana ya duddubashi sannan suka d'an k'ara bashi k'arfin guiwa da sama mishi nutsuwa sannan suka fita,
a bakin harabar wurin Dr Aliyu da Dr Adnan suka had'u da Nurse d'innan Amina,
da sauri ta iso inda suke, cikin shigarsu ta nurses wanda sunyi mata cib a jikinta sai d'an k'aramin hijabi,
hannunta na cikin haljihun gefe da gefen rigardata da iya karta guiwa, rusunawa ta d'anyi tare da cewa.
"Sir barka da dare."
"Barka dai Amina Usman Jada."
murmushi tayi dan yadda ya kira cikekken sunanta, gaida Dr Adnan tayi kana tace.
"Sir bari inje in bashi maganinshi, zan wuce gida."
jim ya d'anyi kana yace.
"To ba matsala amman dan Allah kiyi sammakon zuwa, kinga na damk'a amanar wannan aikin a hannunki, dan naga bafulatanine d'an uwanki."
cikin girmamawa tace,
"In sha Allah ba matsala zan taho da wuri".
daga nan sukayi sallama ita tayi ciki su sukayi woje.

A hankali ta tura k'ofar ta shiga bakinta d'auke da sallama,
kasan cewar idonshi biyu yana rubutawa Ummi text ne yasa yaga shigowarta, baibi ta kantaba yaci gaba da sarrafa woyar tashi,
ita kuwa gefenshi ta tsaya,
tana harhad'a alluran da zatayi mishi,
bayan ta gama ne ta d'an matsoshi, tare da d'an zuba mishi idanu,
kallonshi takeyi tamkar tauraro,
gashin girarshi ta zubawa idanu wanda suke tamkar an zanasu da gazal sunyi lub lub dasu kana hancinshi zuwat har baki lips inshi jazir sai shek'ek'i sukeyi,
ido ta lumshe tare da cewa.
"Matarka taji dad'i koda ranta a bace yake in taga kekyawan fuskarnan taka farin cike zai kauda bak'in cikin."
lip's enshi ya d'an tsotsa ta ciki dan yana kallon motsin bakinta ta cikin fuskar woyarshi. So ya gane duk abinda tace.
ita kuwa yatsunshi ta zurawa ido yadda yake sassarafa wayar tamkar shi ya halicceta,
lips enshi ta kuma kalla kana tace.
"Wannan labban da ganinsu zasuyi taushi, ji yadda suke shek'i."
still bai kulata ba, ganin ta shagala wurin kallonshi,
ido ya lumshe yana tuno Zaleeha a ranshi sai yake jin inama itace kusa dashi,
a hankali taja numfashi kana tasa hannu bisa fuskarshi ta karkad'a mishi yatsunta,
d'ago lumsasshun idanunshi yayi ya d'an kalleta.
ganin ta nuna mishi allurane yasashi,
rumtse ido kana ya d'an mirgina tare da gyara zaman damtsen hannunshi na dama ya bata damar mishi allurar,
a hankali ta zira mishi allurar kana ta fara tura ruwan,
ido ya kuma rumtsewa kana yana sunkuyar da yatsun hannunshi har suna bada sautin k'aras-k'aras.
a hankali ta kalleshi cikin tausayawa tace.
"Sannu."
bai nuna mata ya ganeba dan ya lura bata san yana gane mgnar mutaneba in yana ganin bakinsu,
maganin ta babballa kana ta mik'a mishi.
Hannun dama yasa ya amsa kana ya afasu a baki tare da amsar robar ruwan da ta mik'o mishi,
sannan ya had'iyesu, bayan ta gama mishi komaine ta k'ara mishi gudun AC ganin tunda ta mishi allurar yake d'an had'a zufa,
gaban gadon ta dawo ta gyara mushi mayafin sannan ta kalleshi tare da cewa.
"Zan tafi gida, dare yayi, dan kai gobe da sassafe zan dawo Allah ya baka lfy, da masu kula da kai zasu ku kwana tare."
A ranshi yace.
"Amin ngd." a zahiri kuma bai kuma kulataba,
itako fita tayi,
shi kuwa text yayiwa Rahma da Raliyya da Hayatuddeen kana yayi addu'a ya rufe ido dan allurar ta fara sashi gyangyad'i.


Rahma kam dama da Adnan zai taho cewa yayi ta koma Side d'in Mamanshi dan yana soron kartayi ta kuka,
kuma Alhamdulillahi dake uwar mijintan na sonta suna kuma tausaya mata suna kula da ita shiyasa ta d'an sake bare yanzu da taga text d'in k'anin nata yana ce mata.
"Adda, yanzu Ya Adnan yazo, mukasha hira, yace min wai kince sai dai ku taho tare,
ni kuwa gani garau na samu sauk'i itama Ummi da Hayatudden zasu dawo, an bar gida ba manya ga Ahmad ma yazo nan, duk sun tare a kaina sai kace basu da aikin yi."
murmushi tayi tare da cewa.
"Zan zo kam in su Ummi sun dawo, in banzo na gankaba to wa zai zo ya ganka?."
murmushi yayi kana yace mata.
"Budurwata mana zatazo."
dariya tayi cikin samun nitsuwa tace.
"Iye to me sunanta surkar tawa."
kai ya rausayar tare da cewa.
"Sai na dawo zan gaya miki." daga nanne ya rufe wayar tashi.
Shiko Dr Adnan tare suka tafi da Dr Aliyu a can ya kwana.


Ummi kuwa tunda suka koma ta kasa samun sukuni duk da ta fawwala Allah lamarinta,
Amman ta kasa cin abinci,
Hayatuddeen kuwa ya d'an sake sabida yadda Ya Rabi'u, da Ya ishaq da Ahmad suka rink'a yi mishi nasiha da bashi k'arfin guiwa da nuna mishi yarda da k'addara.

Aunty Mami kuwa tausayin Ummi ya hanata sukuni sabida da ka ganta kasan tana cikin damuwa da fargaba,
shiyasa data gama shirin baccinta ta kuma soya mata gwai da biredi kana ta had'a mata tea ta nufi d'akin da suka sauk'i Ummin inda suke sauk'e Mamansu Ishaq in tazo.
bisa sallaya ta sameta tana rik'e da carbi,
gefenta ta zauna tare da tank'oshe k'afafunta, ganin har yanzu Ummi hawaye take zubdawa cikin sanyi Aunty Mamin tace.
"Kiyi hak'uri Ummi ki dena kuka dan Allah kiyi ta mishi Addu'a, insha Allah zai samu lfy."
cikin sanyin murya tace,
"Mami ya zanyi in banyi kukaba, me zanyi da hawayen nawa, ce minfa sukayi Saifuddeen na bazai sake tsayawa da k'afafunshi ba."
cikin tausasawa tace.
"A a fa Ummi ana kyautata zaton wata rana zai iya mik'ewa."
kai ta jinjina kana tace,
"Kayya ba dai boye min sukeyi ba, hakama sukayi min lokacin Nuruddeen da Abbansu."
Sai kuma ta share hawayenta cikin tarin damuwa taci gaba da cewa.
"Ina rasa nitsuwata da konciyar hankali na in naga Saifuddeen yana cikin wani hali,
ina jin tausayinshi a raina ina rasa samun nitsuwata gaba d'aya a kanshi,
ina tausayawa Saifuddeen in na tuna lfy lau na haifeshi, sai kuma abubuwa suketa biyu bayan rayuwarshi."
cikin tausayawa Aunty Mami tace.
"Ummi. Wayene Nuruddeen d'in da Abbansu?."
a hankali Ummi ta nisa kana cikin sanyi ta fara bata lbrin asalinsu Saifuddeen dama yadda ya samu larurar rashin ji...
Cikin tsananin kuka da tausayawa Aunty Mami tayi saki wani nannauyan ajiyan zuciya.
Numfashi ta fudda a hankali sannan ta jingina da gadon tana mai sheshesk'an kuka har saida Ummi ta dawo tana bata hak'uri,
cikin rauni ta share hawayenta tare da cewa.
"In sha Allah daga yanzu duk sanda nayi salla zansa Saifuddeen cikin addu'o'i na ya bani tausayi tun yana yaro k'arami yayita fuskantar k'alubalen rayuwa."
sai ta kuma gyara zamanta tare da cewa.
"Dan Allah Ummi na rok'eki ki daina yawan kuka,
kiyi ta mishi addu'a in sha Allah Saifuddeen bazai tab'eba."
Sassanyan ajiyan zuciya Ummi ta sauk'e tare da cewa.
"In sha zan daina yawan kukan zanyi ta mishi addu'a."
cikin jin dad'i ta mik'a mata kofin tea d'in,
ba musu ta karb'a tare da cewa.
"Ngd Allah ya miki al'barka."
Amin Amin tace sannan ta mik'e ta fita dan bata wuri.

Washe gari kuwa tuni Doctor Aliyu ya harhad'a dukkan bayanan cutar Saifuddeen ya turawa Dr Acash prasat wanda yake aiki a wani babban asibiti dake New Delhi India,
Ahmad kuwa E passport d'in Saifuddeen da Hayatuddeen da nashi ya tattara ya nufi Airport tun da sanyin safiya ya fara musu cuku-cukun samun visa,
A nan ya samu Adnan ya taho dan tare zasu tafi dole yayi musu jagora a matsayinshi na likita da yaso ace da Dr Aliyu zasuje to shi aiyuka sun mishi yawa,
sai da suka gama duk abinda ya dace na zirganiyar samun tafiyar nasu cikin sauri cikin sa'a kuwa suka samu jirgin da zai tashi jibi nan zuwa India direct New Delhi Indira Gandhi Enternational Airport, saida suka gama komai na tafiyar sannan suka baro airport d'in.

Ummi kuwa da Ishaq da Saifuddeen Ya Rabi'u ne ya kaisu Asibitin.

Suna isa Dr Batulu tayi musu jagora har d'akin da Saifuddeen d'in yake,
sosai Ummi taji dad'in samunshi cikin nitsuwa yana rik'e da wayarshi fuskarshi d'auke da murmushi,
da sauri ta isa bakin gadon kujerar dake kusa dashi taja ta zauna,
ishaq kuwa yana isa bakin gadon ya rik'e k'arfen gadon ya tsaya,
Hayatudddeen kuwa gefen shi ya tsaya kusa da Umminsu,
da sauri ya ajiye wayarshin tare da juyawa inda suke jin Ummi na shafa kanshi,
murmushin ya kumayi tare d'ago hannunshi ya shafa kan Hayatuddeen yayinda Ummi kuwa ke shafa kanshi,
sai ya kuma mik'o hannunshi d'aya ya kamo hannun ishaq.
Ya Rabi'u ne ya d'anyi murmushi tare da cewa.
"Masha Allah. Alhamdulillahi jiki da sauk'i ko?."
kai ya jinjina alamum eh.
Dr Batulu kuwa sai binsu da idanu takeyi cikin shawar shak'uwar dake tsakaninsu.
Cikin kula Ummi tace.
"Sannu ko babana ya jikin?."
wayarshi ya d'auka da sauri ya rubuta mata.
"Alhamdulillahi jiki da sauk'i."
cikin jin dad'i duk sukace.
"Allah ya k'aro mana sauk'i."
Amin Amin ya amsa a saman lab'b'ansa.


Dai-dai lokacin kuma su Ahmad da Adnan suka shigo,
bayan duk sun gaisa sun tabayi ya mai jikine sannan Ahmad ya kalli Ummi cikin nitsuwa yace.
"In sha Allah jibi zamu tafi india,
kuma Alhamdulillahi kafinma muje bayanan zuwanmu ya shiga hannun doctors d'insu."
cikin sauk'e numfashi Ummi tace.
"To Allah ya kaimu lfy ya kuma bada sa'an aiki."
cikin son kontar mata da hankalin Dr Adnan yace.
"Yanzu Ummi keda Ishaq zaku koma gombe gobe."
da sauri Ummi tace.
"In koma Gombe kuma?." Cikin nitsuwa Ya Rabi'u ya gyad'a mata kai tare da cewa.
"Eh Ummi ba matsala ke da Ishaq ku koma gombe,
Ahmad da Hayatuddeen kuwa dasu za'a tafi,
tare da Dr Adnan kuma shima in yaje ba dad'ewa zaiba in yaga anyi aiki dai to zai dawo kiji labarin jikin Saifuddeen d'in kuma,
in ya dawo keda Ishaq da bappa Ali zakuje."
kai ta sunkuyar kana murya a sanyaye tace.
"Yanzu sai in zauna a tafi dashi har wata k'asa ta daban."
Ahmad ne ya d'an kalleta tare cewa.
"Ummi nida Hayatuddeen zamuyi duk abinda zakiyi mishi karki damu zamu kula dashi."
still dai kamar bata gamsuba ido ta zubawa Dr Batulu da ta dafa kafad'unta tare da cewa.
"Ummin Saifuddeen ki kwantar da hankalinki shi jinyan namiji saida namiji d'an uwanshi hakama mace saida macce yar uwarta,
kuma duk sanda kikeson zuwa zakije ki duboshi."
cikin gamsuwa tace.
"To ba komai Allah ya shige mana gaba."
Sai ta kuma juyawa ta kalli Saifuddeen da yake kallonta fuska cike da bege murya can k'asa tace.
"Allah ya baka lfy babana."
Amin Amin suka amsa baki d'aya,
shi kuwa Hayatuddeen wayarshi daketa ringing ya d'aga ganin Salisu ne ya sashi mik'awa Ummi.
"Barka da safiya Ummi."

"Barka dai Salisu ya kasuwa?."

"Lfy lau Alhamdulillahi, ya Saifuddeen da jikin?."

Cikin rawan murya tace.
"To Alhamdulillahi jiki sai dai ace da sauk'i.
Amman yanzuma fa shiri akeyi wai za'a fiddashi k'asar India."
sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa.
"Kuma sunce wai baza'a je daniba."

Cikin k'arfin hali Salisu yace.
"Ba komai Ummi in sha zai samu lfy ki kwantar da hankalin ki,
nima daga nan in na gama abinda nakeyi bazan dawo Nigeria ba zan wuce can india inga jikinshi kafin in dawo,
ki kwantar da hankalinki ai yanzu duniya a had'e wuri d'aya take."
sosai ya bata k'arfin guiwa sannan yace ta bawa Ahmad nan ta bashi suka gaisa.

Daga nan duk suka tafi dan ganin azahar tayi kuma doctor yace su fita su bashi wuri ya huta.


Koda suka koma gidan Ya Rabi'u,
sosai Aunty Mami tayi ta karfafawa Ummi zuciya har dai ta nitsu akan washe gari zasuyi sammako diraban ya Rabi'u zai maidasu Gombe kana ya taho dasu Rahma suma su ganshi kafin ya tafi.

Washe gari bayan an idar da sallan asuba Ayuba ya d'auki Ummi da Ishaq dan zasuyi sammako,
jin zasu biya asibiti ne yasa Hayatuddeen cewa to zai bisu a saukeshi a asibitin.

K'arfe bakwai dai-dai suka isa cikin d'akin da Saifudden yake.
Konce suka sameshi kamar ko yaushe yana tsabtace dan masu gyarashi na fita ne su kuma suka shigo.

Hannu ya mik'o ya kama na Ishaq tare da rubuta mishi text.
"Please Ishaq ga Ummi na dan Allah kake yawan zuwa gida kana kontar mata da hankalin,
kaga tare da Hayatuddeen zamu tafi,
Raihana kuma itama in sunzo kawai ta koma d'akinta kada tace zata koma gombe,
dan Saminu yace min shima ya kusa dawowa,
sannan akwai system na a motar Sule da k'aramar wayata,
duk a bawa su Raliya su kawo min su."
cikin nitsuwa Ishaq yace.
"In sha Allah ba damuwa nima da Ummin zamu zo ai mu dubaka,
ba matsala zasu zo maka dasu."

Ita kuwa Ummi cikin sanyi ta shafa kan Saifuddeen har zuwa goshinsa,
cikin sanyi tace.
"Babana zan tafi yanzu zamu koma gombe sunce ku kuma gobe zaku tafi india,."
sai ta kuma share hawayenta tare da ci gaba da cewa.
"Zan tafi badon na soba sai dai kada suce na raina musu ne,
Allah ya k'addara saduwarmu kan al'kairi Allah ya baka lfy babana Allah yasa da akwai sauran ganawa a tsaka ninmu,
Allah ya baka lfy."
da sauri ya jawo tafin hannunta ya mannashi bisa hab'arshi yana mai zubda wasu zazzafan hawaye wanda ganin hawayen mahaifiyar tashi ne yasa nashi zubowa.
Hayatuddeen kuwa hannu yasa yana share mata hawayenta,
dai-dai lokacin Nurse d'in nan Amina ta shigo,
gefensu can ta tsaya tare da kallon Ummi dake kuka cur-cur da hawaye,
da sauri ta sunkuyar da kanta dan itama idanunta sun cicciko da hawaye cikin danne rawan muryarta ta kalli Ummi tare da cewa.
"Kiyi hak'uri Mama ki daina kuka in sha Allah zai samu lfy."
kai ta gyad'a tare da kamo hannun Saifuddeen d'in tace.
"Allah ya baka lfy."
sai kuma tasa hannunta ta share hawayen fuskarshi dana Hayatuddeen kana ta juya da sauri ta fita.
jin motsin ta fitane yasa Ishaq yabi bayanta, kai tsaye inda Ayuba yayi parking suka nufa,
suna shiga yaja mota suka fita daga asibitin suka nufi kama hanyar gombe.

A cikin room d'in da Saifuddeen ke ciki kuwa Ummi na fita Hayatuddeen ya zauna kan kujerar data tashi,
ya kife kanshi gefen pillow Saifuddeen yana mai shesshek'an kuka a hankali,
shi kuwa Saifuddeen rumtse idanunshi yayi yayinda wasu hawayen ke zubo mishi, a hankali Amina ta matso kusa dasu cikin nitsuwa ta iso gabansu,
ido ta zubawa fuskarshi Hayatuddeen tana kallonshi tamkar Aminu k'aninta mai binta kusan komansu dai-dai da Aminunsu.
a hankali tasa hannu ta tallabo fuskarshi,
ido ya bud'e jin an d'ago kanshi,
kai ta jujjuya mishi alamun ya bar kuka,
sai ta kuma zaro hankicib d'inta dake cikin al'jihunta ta mik'a mishi,
hannu yasa ya k'arba sannan ya shinfid'eshi bisa fuskarshi,
ita kuwa Amina a hankali ta juyo kan Saifuddeen wanda idanshi ke lumshe hawayenshi na zubowa suna gangarowa har cikin kunnenshi kasan cewar konce yake a rigingine.

K'ara matsowa tayi gab dashi,
yayinda shi kuwa yake kallonta ta tsakankanin gashin idanunshi.
hannu tasa dai-dai bisa hab'arshi sai kuma tayi saurin janye hannun tare da zuba mishi idanu,
ganin idanshi a rufene yasa ta sake kai hannunta duka biyu a hab'arshi na gefen dama da hagu,
manyan yatsunta tasa can k'asa idanshi sannan tasa sauran yatsunta hud'un ta tare tsakanin hab'arshi da kunnenshi sai ta jawo manyan yatsun tannan a hankali tana koro hawaye suna gangarowa tsakiyar tafin hannunta.

Shi kuwa Saifuddeen wani irin razanennen bugu heart beat nashi yakeyi so fast,
shiru yayi tamkar baya numfashi,
hakan ya bata damar share mishi hawayen kab ta tarasu cikin tafin hannunta,
sai ta had'e hannunta wuri d'aya ta murza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login