Showing 15001 words to 18000 words out of 176868 words
Chapter 6 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
amsar 1k yasanya al'barka.
Shiko yaje ya bawa Ummi dubu uku sannan ya d'auki dubu d'aya.
Ummi kam sai sanya mishi al'barka takeyi.
Washe gari kamar kullum suka shirya suka tafi cikin. Gombe a inda ya saba sauk'eshi yau ma nan ya sauk'eshin, bayan Salisun ya tafi shi kuma Saifuddeen sai ya d'anyi tattaki zuwa bakin mashigar kasuwar, addu'a yayi kamar kullum kana ya shiga da k'afar dama,
yauma bakin shagunan yayi tabi har kusa k'arfe shad'aya lokacin rana ta tsala zafi ya fara,
sai ya nufi layin masu robobi,
yana zuwa shagon wani bayerbe sai ya tsaya,
bokatin kand'e tsirara ya saya wanda wasu ke cemai ganta sarai,
bayan sun gama ciniki cikin mgnar kurame ya bashi dubu d'ayannan,
kana bayerben ya bashi canjinshi,
daga nan ya nufi wani layin tafiya kad'an yayi sai gashi a wani babban shago da yake cike da d'ima-d'ima firiji masu tsawo da masu fad'i.
Yana zuwa d'aya daga cikin yaran shagon yace mishi. "Kana son ruwane?."
da sauri ya gyad'a mishi alamar eh.
shi kuwa yaro bud'e wani k'aton firiji yayi kana ya juyo ya kalleshi, sannan yace.
"Leda nawa kake so?."
hannunshi ya d'ago kana ya had'a yatsunshi biyu yayi mishi alama da leda biyu yakeso.
cikin mmki yaro ya kalleshi kana ya kawo mishi leda biyun sannan yace mushi.
"Kai kurmane?."
murmushi Saifuddeen yayi kana ya gyad'a mishi kai tare da mik'a mishi d'ari biyun,
amsa yayi tare da bashi canjinshi kana yace.
"Kuma naga kamar kana gane abinda nake fad'i ko?."
still kai ya gyad'a tare dasa lododin ruwan cikin bokatin daya saya d'in,
a take botikin yayi sanyi sabida ruwan yanada tsananin sanyi wasu har sun fara yin k'ank'ara,
shi kuwa yaron shagon ashirin ya kuma zarowa a al'jihunshi kana ya mik'a mishi tare da cewa.
"Gashi nayi maka ragin naira 10 cikin ko wanne leda akan yadda muke sararwa Allah ya baka sa'a inka k'arema kazo zan ajiye maka mai sanyi."
cikin murmushi Saifuddeen ya jujjuya mishi kai alamun baya son ragin, kana ya juya ya nuna mishi sauran yaran ya mishi alamun da sai dai in suma duk za'ayi musu ragin,
cikin sauk'e numfashi yaro yace.
"To sadaka na baka."
fuska ya had'e kana ya tsuguna gefe tare da rubuta mishi.
"Bara nazo makane da zakace sadaka ka bani? in sadaka kakeson badawa kaje gidan marayu da gajiyayyu, ni karka kashe min zuciya,
ka dai ajemin mai sanyi in wannan ya k'are zan kuma zuwa."
hannu yaron ya bashi sukayi musabaha lokacin daya karanta rubutun kana yace.
"To kayi hak'uri abokina sai ka dawo d'in."
kai ya jinjina kana ya juya hannunshi rik'e da botikin.
ya fara bin layi-layi yana yawo,
amman babu wanda yace mishi kawo,
har ruwan ya fara rage sanyi.
cikin gajiya ya dawo bakin shagon masu kayan kitchen inda ya huta jiyan nan, inda ya zauna jiyan yauma nan ya zauna ya tasa batikin a gabanshi.
yaron jiyan ne ya kula dashi cikin fara'a yace.
"Balarabe yauma ka zone?."
cikin gajiya ya lumshe mishi idanu alamar eh,
shi kuwa yaron shagon cikin karantar yanayinshi yace.
"To yau ma hutawa kazo yine ko zaka sayi abune?."
da ido ya nuna mishi botikin pure water enshin,
cikin sauri ya zaro ido tare da cewa.
"Wai kai dama tallan ruwa kakeyi ne?".
Kai ya gyad'a mishi tare gyara zamanshi,
cikin sanyi yace.
"To wai kai kurmane naga jiyama har ka tafi body language kakeyi min."
still sai ya d'aga mishi gira duka biyu alamun eh shi kurmane.
da sauri yaron ya kalli alajin shagon cikin tausayawa yace.
"Abba kalli wai wannan Balaraben kurmane kuma wai ruwa yake saidawa."
sai ya kuma kalli Saifuddeen tare da yin rau-rau kamar idanunshi zasu zubda hawaye,
ganin haka da sauri Saifuddeen ya jujjuya mishi kai sannan yasa hannunshi bisa idanunshi alamun kar yayi kuka.
still shima wanda ya kira da Abba sai ya zuba musu ido tare da cewa.
"To Hisham kafi ubangijin daya halicceshi a haka sonshi ne?
kada kayi kuka kasa mishi rauni,
ai ita Nakasa ba kasawa bace,
bare wannan mai nagartane Kaga dai jiya kun dad'e tare amman duk bamu gane kurma bane kuma kaga yana gane duk abinda muke cewa.
So shi bai sa nakasar jikinsa ta zamar mishi na zuciya ba."
Jin haka sai Hisham ya sharshe hawayenshi kana yayi murmushi tare da bawa Saifuddeen hannu yace.
"Daga yau kai aboki nane."
shima Saifuddeen murmushi yayi,
shi kuwa Alhaji Ibrahim al'barka ya samusu.
Sai ya kuma kalli costumers insu da suke cike da shagon inda d'aya daga cikinsu ta kalli botikin ruwa tare da cewa.
"Yauwa mai ruwa bani biyu, wlh tun d'azu nakeji k'ishin kamar zai karni."
gane abinda tace yasa Saifuddeen d'auko guda biyu ya mik'a mata,
amsa tayi tare da bashi ashirin d'in,
shi kuwa Alhaji Ibrahim cikin iya kula da bak'inshi yace.
"A a Hajia bar kud'in."
sai ya kuma kalli Saifudddeen tare da cewa.
"Basu ruwan kowa ya d'auki yadda zai isheshi."
ai nan matan nan kowa ta d'auka wasu bibbiyu wasu d'addaya wasuma cikin hand bags nasu suke ajiye ruwan,
tuni sun d'auke yafi rabi.
lissafi akayi don lokacin ne forko-forkon da pure water ya tashi daga d'aya biyar ya koma d'aya goma,
to nanfa had'a lissafi inda kud'inshi ya kama d'ari da hamtsin.
aifa sai yaji k'arfin guiwa ya mik'e yabi layin masu saida gonjo wanda kusan a rana suke,
cikin k'udurar ubangiji ya saida ruwan tsab,
ba tare da yin k'asa a guiwaba yaje ya kuma saro leda biyu,
nan sai ya fito bakin kasuwa nanfa 'yan acab'a suka rink'a saya wani a take yake shanye leda biyu wani har leda uku ya saya bar masu sayan d'ad'd'aya,
kana masu taxi ma wasu sai su sayi lada hud'u su aje cikin yar durowar motar nasu.
Cikin awa d'aya wannan leda biyun suka k'are,
ai da sauri ya kuma komawa ganin azahar tayi sai ya amso leda d'aya,
kafin kace kobo ya k'are dan masuyin Al'walene sukayi ta kiranshi suna saya,
ganin saura d'aya sai yayi Al'wala dashi ganin a layin shagonsu Jabeer yake sai yaje ya ajiye botikin a barandar shagunsun gefen gadajen jarirai,
sahun salla ya shiga,
bayan an idarne ya yi addu'o'inshi sannan yaje d'aukan botikin nashi, Jabeer na ganinshi yace.
"Aboki balarabe dama har yanzu kana k'asar tamu ne?."
hararan wasa Saifuddeen ya cilla mishi dan ya gaya mishi shi bafullatanine ba balarabeba, so da yake Jabeer yanada far-far da jama da wasa da dariya sai yace shi dai yasan sai in satoshi akayi daga saudia.
botikin ya d'auka kana ya d'an harari Jabeer tare da tsuke fuska irin na abokai sannan ya bashi hannu.
da sauri Jabeer ya kamo hannunshi tare da cewa.
"Yoh ai dole ma in baka hannu ko zan samu ka rab'a min farinka da laushin hannunka."
dariya yaran shagon sukayi baki d'aya,
kana sai ogansun yace.
"Gashi dai duk muna inuwa fanka na kad'awa muci abinda mukeso, shi kuma gararamba kawai yake a kasuwa amman in ka ganshi sai kace daga fadar masarautar saudia ya fito."
cikin had'e fuska Saifuddeen ya zaro biron dake aljihun rigar Jabeer kana ya fara rubutu a tafin hannunshi yana gamawa ya nunawa ogan nasu tafin hannun nashi,
kusan a tare suka lek'o da idanunsu bisa tafin hannunshi cikin mmki suke karanta rubutun da yayi da fillanci.
"Oga ba gararamba nakeyiba fa inada sa'a ta nima ba yawon banza nake a kasuwarba pure water nike saidawa."
cikin mmki suka kalli juna tare da had'a baki wurin cewa.
"Ikon Allah kunga wlh da gaskene fa bafillacene."
shi kuwa ogan nasu murmushi yayi tare da cewa.
"Eh gskyarka ba gararamba kakeyiba ai shi mai sana'a ba matsiyaci ba,
yanzu je ka kawo mana ruwan dan yanzu zamuci abinci."
aifa da jin haka ya juya ya fita su kuwa sai Al'ajabi sukeyi,
yanzu dai sun tabbatar shi kurmane kuma bafillatanine kana yana gane abinda ake fad'i in yana ganin bakin mutun.
Leda biyu ya kuma sarowa cikin sa'a kafinma ya isa wurinsu rabin ledane ya rage,
nan suka d'auka to ganin bai ishesu bane sai ya kuma komawa ya dauko leda biyu.
kai tsaye wurinsu ya nufa
nan suka k'ara guda uku.
sun bashi kud'inshi ya juya zai tafi kenan sai yaga wannan dottijon mai keke wanda suka tab'a had'u a shagonsu Hisham kusan tsawon sati d'aya daya gabata kenan,
still yauma kamar ranar dottijon ya kalleshi tare da mik'o mishi banduran leda guda hud'u irin kitika-kitikan ledojin da in an sayi koda katifan jarirai zai iya shiga ciki kai hatta gadon jariran zai iya shiga cikin ledan,
kana in zaka sai setin kayan sanyi dana abin goyo dasu rigunan yara dasu setin mayukansu da takalma duk leda d'aya zata iya d'aukansu dan irin manyan ledodi bak'ak'ennan ne,
sai kuma masu binsu sai masu zane bak'i da yellow nan,
cikin alamun gajiya dottijon yace.
"Yauwa yarona dan Allah mik'a musu."
da sauri ya ajiye botikin nashi kana ya amshi ledodin ya juya ya mik'awa Jabeer dake kusa dashi,
sai kuma ya kalli ogan nasu ganin yanayiwa dottijon mgna.
"Yauwa Baba bello ya a bamu ledodin na dubu hud'u dan na dubu ukun basa isanmu sabida yanzu iyayen yara sun fara sayayyan kayan sallan yaransu ga masu haihuwa nan nata zuwa ga yan mata da samari masu sayan kayan aure."
murmushi dottijon yayi kana yace.
"Masha Allah ai haka mukeso domin cini kinku shine namu,
domin sai kunyi ciniki da muyi tunda mu duk kasuwa abin mune k'arshen saya dole sai an gama sayyaya ake tuna sayan leda."
Jabber ne ya murmusa tare da cewa.
"Gashi kuma kasuwar taku da yawan al'barka take duk mai saida abu dole sai ya sai naku."
murmushi sukayi baki d'aya kana Alhaji Adamu ya mik'owa Saifuddeen 4k d'in sannan shi kuma ya mik'awa dottijon amsa yayi tare da sasu a aljihu sannan ya kalli Saifuddeen da kyau kana yace.
"Ngd matuk'a yarona Allah ya maka al'barka."
Amin Amin duk suka amsa harda Saifuddeen daya amsa a zuciya,
Jabeer kuwa cikin tsokana yace.
"Kai Baba bello wannan fa balarabene."
ba tare da mmkiba Dottijon yace.
"Yoh ai ba musu in akace hakanma."
Tahir ne dake gefe ya d'an bugi k'eyan Jabeer kana ya kalli Dottijon yace.
"K'aryafa yakeyi maka baba bello shi ba fulatanine kawai dai kurmane."
da sauri Baba bello ya kuma kallonsa cikin tausayawa yace.
"Allah sarki bawan Allah dama ance ko wani d'an adam tara yake bai cika gomba, wato kai kuma nan tawayar ka take."
sai ya kuma kalli Saifuddeen da kyau sai ya sauk'o bisa keken nashi.
hannunshi yasa ya jawo wuyan Saifuddeen yadda zai iya ganin tsakiyar kanshi ido ya zura mishi tsawon 38 minutes shi kuwa Saifuddeen shiru kawai yayi ya bashi kai d'in,
bayan ya gama dubawa yace.
"Masha Allah lallai kam wannan kan naka zai d'auki nauyin abu da yawa,
domin magergerar gashi tushe ukune a kanka wanda ba kowa Allah ke yiwa wannan halittarba."
shiru sukayi yayinda shi kuwa Dottijon ya kalli Alhaji Adamu tare da hawa kekenshi kana yace.
"Akwai al'khairi cikin yin mak'otaka dashi."
daga nan yaja kekenshi ya tafi,
shi kuwa Saifuddeen d'aukan botikinshi yayi tare da bin bayanshi,
yana ganinshi ya nufi shagon masu d'inka hijabannan da alamun suma a wurinshi suke sayan leda. Har zaibi bayanshi sai kuma yaga ana kiranshi a shagon alhaji ishaq haka yasa ya nufi can.
Pure water suka sassaya bayan sun bashi kud'in ya juyo kenan sai yaga Dottijon nan tuni ya bar wurin,
to sai kawai yaci ga da zageye da ruwan,
amman sai cinikin yayi d'ib tun bayan azahar ya d'aukosu amman har la'asar basu k'areba,
to saida aka kira sallan la'asarne sai kuma akayi ta saya ana al'wala nan ya samu wannan leda biyun suka k'are.
To koda aka idar da salla ya gaji sai ya koma layin shagon ba mishkila ya zauna ya zuba musu idanu yana ganin yadda aketa seye da sayarwa yana kallon yadda suke ink'anta awunsu.
Ya d'an jima a wurin sai biyar dai-dai ya mik'e a ranshi yake cewa.
"Uhmm Saif tashi kaje ko leda d'aya ka samu ka saida kafin magrib ai yafi zaman mutuwar jiki da zuciyan."
daga nan yaje ya k'aro leda d'aya,
to kuma lokacin rana tayi sanyi ba ciniki sosai,
ya jima yana yawo kafin ya samu aka sayi gwara shida na arba'in kenan daga nan yaita zagayawa,
tuni ya gaji dan yau kusan wuni yayi bisa sawunshi,
saida magrib ta gabatone akayi ta saya nan ya saida kab sai gwara d'aya da ya bari na al'walanshi. Bayan yayi alwalan ne ya bawa Jabeer botikin ya ajiye mishi a shagonsu,
sannan ya fito bakin gate d'in fita kasuwar yana lissafin bag nawa ya saida a cikin ranshi yace.
"Alhamdulillahi leda goma cib na saida, ya rabbil izzati kayiwa wannan kasuwa tawa al'barka ya Allah ka jib'anci lamurana ka fad'ad'amin hanyar samu in samu damar tallafawa k'annena marayuwa da mahaifiyata da yayata da marayun yaranta,
bayan anyi sallan magrib d'inne ya dawo inda Salisu zaizo ya sameshi yana ko zuwa Salisu na isa,
yauma kamar jiya shi dai fura da nono yasha shi kuwa Salisu ya sai nama yaci.
daga nan sukayi sallan isha kafin suka kama hanyar Dukku.
Bayan sun isa wonka yayi ya canza kaya kana yazo yaci abinci,
sannan ya fita woje sugar ya seyo da madara da Lipton sai biredi d'aya.
kafin ya dawo duk sunyi bacci sai Ummi da Rahma.
Rahma ya mik'awa ledan kana ya zauna gefen Ummi data zuba mishi ido,
cikin kula tace.
"To kuma d'an dubu d'aya daka amsa d'inne zaka kasheshi a kanmu? buk'atunka zakayi dashi ba namuba ai dubu ukun nan zasuyi min sati ina cefene kullum d'aribiyar zata isheni cefenen dere da rana, tunda munada gari da shinkafa harda sauran taliya da mai da manja."
mik'e sawunshi yayi kana ya fara rubutu a k'asa yana bata lbrin ai ya fara sana'ar saida ruwa kuma Alhamdulillahi sana'ar tana gudu dan ya samu ribar 700 a wunin yau kawai.
Cikin tausayawa Ummi tace.
"To Babana ka dai nuna kai sana'ar tayi maka, amman ni tausayinka nikeji kaje kayita wuni a rana kana yawo da robar ruwa, amman Allah ya baka sa'a yanzu asusu zan saya zaka rink'a tara kudin in ka samu jari dai ka fara wata sana'ar kabar wannan."
cikin girmamawa da shak'uwa da tsantsar biyayya ya gyad'a mata kai tare da fara rubutu a k'asa yace.
"To Ummi na yadda kikeso haka za'ayi."
sai ya kuma kalli Hayatuddeen dake konce yayi pillow da cinyar Ummi ture kanshi yayi kad'an kana ya zame ya konta tare dasa kanshi gefen na Hayatuddeen da nufin wai zasuyi hira.
Amman ina tsananin gajiyar yawon daya wuni yanayi ne yasa tuni yayi bacci.
ganin baccin zai nisane yasa Rahma sa hannu ta d'an mari kumatunshi a hankali ya bud'e ido,
sai ya kuma kalli Ummi dake shafa suman kanshi da alamun bacci a idanunta.
cikin sanyi ya mik'e kana ya musu saida safe sannan ya kamo hannun Hayatuddeen da nufin suje d'akinshi su fara kwana tare amman sai k'ara mak'ale Ummi yakeyi hakan yasa ya barshi, yaje ya shiga kana suma suka shiga.
Still yauma kamar jiya cikin ikon Allah ya saida leda goma kamar jiya.
Koda ya koma ya samu tuni Ummi ta sai asusu ta zura mishi d'aribar din jiya dan ya sai musu kayan tea na d'ari da biredin d'ari kana ya bata sauran d'aribar d'in duk cikin ribarshi 700 d'in jiyan,
kana jarinshi kuma na nan. To Alhamdulillahi yauma haka ya samu kamar na jiya,
toh sai ya bawa Ummi duka kud'in tasa 500 a asusu 200 kuma ta d'auka ta ajiye dan 'yan buk'atunsu irinsu omo ko kud'in break d'insu Hayatuddeen da Faruq
haka dai lokaci yaita shud'ewa.
Duk randa Salisu ya basu kud'in balance kuma zai bawa bappa Ali 1k kana ya damk'awa Ummi 4k d'in.
Alhamdulillahi rayuwafa ta fara juyawa kasuwa na tafiya tuni Saifuddeen ya saba da mutane da dama,
wani lokacin har leda 14 yake saidawa inda yake samun riba kusan 900,
sosai yayi abokai sa'anninshi manyan mutane kuma na son mgnanshi sabida yanada dad'in zama ga tsabta da girmama na gaba dashi.
Abu gaba-gaba yanzu harda robobin Faro, yake sara dasu Fanta, Coca-Cola, molt etc. Wanda yawanci matasa shi kan seya.
Yanzu ya saba da wahalar da yawon da ranar saidai ya d'anyi duhu farinshi ya disashe sabida rana da yake shiga.
Yana yawan had'uwa da Dottijon nan baba bello, mafi akasari shike mik'awa mutane leda su bashi kud'i ya bawa baba bello,
Alhamdulillahi yanzu littafi da biro yake yawo dasu a aljihu duk mgnar da kai mishi zai baka amsa,
wasu da dama dan suga rubutunshi suke son Magna dashi sabida Allah ya mishi baiwar iya rubutu in yayi tamkar na'urace tayi.
da yawa da Balarabe suke kiranshi wasu kuma suce Saifuddeen balarabe.
Azumi nata gaba towa dan yanzu baifi 8 days ya rage Ramadan ba,
Yayinda dukkan Al'ummar musulmai keta shirye-shiryen azumi.
kuma zuwa yanzu kusan tsawon kwana 46 da kafa asusun Saifuddeen.
To ga azumi yana zuwa gaba d'aya ya rasa sana'ar da zai kama dan yasan cikin azumi cinikin ruwa bazaiyi guduba tunda duk musulmai baki a rufe yake.
Yana dai ta nazarin abin yi amman har zuwa azumi saura kwana uku bai tsaida sana'ar da zaiba da fari yayi niyar ko zai koma saida dabino dasu kwakwane sai ya kuma ga sana'ar yawoce kuma ga azumi so yasan zai wahala,
a haka dai yau kam yayi niyar yin shawara da abokinshi Jabeer ko Hisham, duk da yaso ace da is'haq zai shawarar to is'haq kuma yanzu ya fi kwana 36 da tafiya Abuja wurin yayanshi Rabi'u kuma acan zaiyi azumi dan shida Ummarsu ne suka tafi,
dan bayan ya fara zuwa kasuwar da sati d'aya ne yaje gidansu Is'haq sai ya samu ranar sukayi sammakon tafiya Abuja.
Yau tunda yaje yaketa sintirin saida ruwanshi dasu Fantan har sai bayan la'asar ya je shagonsu Hisham da niyan zai tattauna dashi sai ya samu tuni ya tafi gida ya kai cefenen dare.
haka yasa ya wuce shagonsu Jabeer yana zuwa suka zauna dan lokacin mata sun d'an tsagaita,
rubutu yayi na neman shawarar sana'ar da zai fara saida ya gama rubutawa kana ya mik'awa Jabeer takardar dai-dai lokacin daya karb'a dai-dai lokacin kuma baba Bello ya iso wannan dottijon.
karantawa Jabber yayi kana ya kalli Saifuddeen da yake mik'o mishi banduran ledodin daya amsa a hannun Dottijon cikin yanayinshi na wasa da dariya yace.
"Yoh balarabe ga sana'ar da zakayi a hannunka ai kawai ka fara saida leda, gashi dama Baba bello bai saida