Showing 51001 words to 54000 words out of 176868 words
Chapter 18 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
saba'in kaga ai dama can hamsin d'in sama ribar tasuce a company a d'ari biyu ake basu.
Kaga kuma kai a kasuwane in ka sakeshi da yawa abokan kasuwancinka zasuji haushinka zasuga zaka kashe musu kasuwane hakan kuma zai iya jaza maka matsala shiyasa badon hakaba da d'ari biyu da hamsin d'in zaka saidashi ko ya kuka gani Hajia Ummi."
kai ta jujjuya mishi cikin jin dad'i tace.
"Allah dai yasa Alhaji Ali Allah ya sa munada ranon zuwa makka da madina birnin ma'aiki."
Amin Amin sukace baki d'aya sannan taci gaba da cewa.
"Wannan ai mgnar ta uba da d'anshi ne ni saidai in sanya al'barka ina kuma nema muku tsari a wurin rabbil izzati."
gyara zama Saifuddeen yayi tare da rubuta musu.
"Eh hakanma yayi Bappa Ali amman kada ka damu ni zanbi hamsin d'in a cikin ko wanne leda,
shagunan zanbi in musu talla in zasu sara zan basu a farashin da d'in amman suyi min al'kawarin saidawa shida ashirin sab'anin biyar ashirin d'in da suke saidawa,
kaga zai zama uku goma kenan,
ni zanbi k'aramar ribar,
a dai wannan sarin in yaso a sari na gaba in naga hakan bazai yuwuba sai inbi sahunsu tunda nima dole da tsadan zan sara."
sosai suka gamsu da wannan shawarar suka k'ark'are komai aka gobe in yaje zaiwa su Alhaji Kabirun tallan.
Shi kuwa bappa Ali cikin nitsuwa yace.
"Dole zaka ci gaba da rik'e shagon nan da aka ajiye maggin,
lokaci yayi da zaka samu sauk'in wahala,
zamuje a gyara kayayyakin in an samu wasu sun sara to sai a samu akori kura a cikata da kayayyakin abincin ta kai shagon sai a fara saidawa."
cikin gamsuwa Saifuddeen ya rubuta musu.
"Hakan yayi shike nan kuma nasan Warisu zai kular mana da komai,
zan kuma yiwa ba mishkila talla nasan zai sara kuma zai bari a farashin da zamu bari dan nasan shi adalin d'an kasuwane mai imani".
sosai sukaji dad'in wannan zaman nasu,
yayinda tuni Rahma taketa famam irga kud'in ganin ta kusa gamawa ne yasa duk suka zuba mata ido dan suna jiran suji nawane kud'in.
Minti hud'u tsakani ta d'ago kanta tare sauk'e numfashi cikin sakin fuska da sanyin muryarta tace.
"Kud'in dukansu dubu d'ari uku da tamanin da biyar ne kud'in baki d'ayansu."
sosai yawan kud'in ya basu mamaki sai dai kuma idan suka tuna kusan tsawon shekara d'aya kenan yake tara kud'in da iriyar azaba da hawala da yake sha ruwa da iska zafin rana da wahala sai suga wahalarsa tama zarta kud'in,
amsarsu Bappa Ali yayi tare da mik'awa Ummi yace tasa musu al'barka cikin murmushi tace.
"Allah ya sanya musu al'barka."
Amin Amin sukace baki d'aya kana Bappa Ali ya kalli Saifuddeen cikin kula yace.
"To ga dai kud'i su kuma me zakayi dasu?."
gyara zamanshi yayi tare da tonk'oshe k'afafunshi ido ya d'an lumshe sannan ya rubuta musu.
"Duk shawarar da kuka bada hakan za'ayi."
da sauri bappa Ali yace.
"A a ka gaya min me ka shawarta kaida zuciyarka?."
kanshi ya d'an sunkuyar sannan ya rubuta musu.
"Dama ni tunanin da nayi, machine d'in Salisun nan ta tsufa yanzu wahal dashi kawai takeyi shiyasa ko balance d'in da keret yake had'a 1,500 gashi yanzu ya fara karatu yana buk'atar kud'i to shiyasa nayi tunanin ko zan saida tsohuwar sai in in saya s mishi sabuwa,
zaifi jin dad'in aikinshi zai samu yadda zai kula da ah'linshi da karatunshi muma kuma balance d'in zai taimakawa cefenen gida na yau da kullum."
sai ya kuma yi shiru ya zuba musu idanu
ganin suma shi suka zubawa idanun alamun sun gamsu da bayaninshi suna kuma son jin k'arshen mgnar,
sai ya d'an had'e yatsunshi tare rubuta musu.
"Sauran kud'in kuma inason zanci gaba da karatuna,
zan yi idimar karatun kama da hidimar sharan fage da saurauran hidimomi na sabbin d'alibai da suke harin zuwa jami'a dole in samunda su Jamb waec da Neco to dole akwai kashe kud'i."
Rahma ce ta fara yin Magna cikin jin dad'i tace.
"Alhamdulillahi burin Ya Seyo zai cika,
yayi kyau naji dad'in haka."
Ummi kuwa cikin sanyi tace.
"To ya zakayi da kasuwancin naka kuma?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Raba leda ba wuya cikin awa uku ana hud'u nake gamawa,
sannan akwai uzuri tsakanina da abokan kasuwancin na in banje bama ana rabamin kinga kwanaki da banda lfy ma Jabeer ne ya rarrabawa costumes d'ina,
kinga duk lakacin da bani da darasi inada damar kasuwanci na,
sai dai cinikin pure water dasu omo nane zaiyi k'asa."
cikin bada k'arfin guiwa bappa Ali yace.
"Hakan yayi Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a.
ni kuma in sha Allah daga gobe zan fara d'aukan Warisu zan fara nusar dashi da koya mishi harkan awu da sanar dashi farashin sari da sayan d'ad'd'aya,
dole in koya mishi awun kanshi gudun kar yaje yayi ta tauye mudu."
sosai dai suka zauna suka tattauna yadda komai zai tafi,
shi kuwa Saifuddeen dubu d'ari ukun ya ware kana ya d'auki na saman ya rabawa Ummi da Bappa Ali dubu goma-goma,
ya bawa su Rahma da Aunty Nina dasu Raihana dubu biyar-biyar,
Su Warisu, Saminu, Salisu, Ahmad Mudassir, kuwa duk suma dubu biyar-biyar ya ware musu shi kuma yasa saura a al,jihunshi.
da zummar zai bawa Jabeer da Hisham dubu biyar-biyar sai ishaq inshi dubu biyar shima.
Inda yasan machine bajat zataci kusan dubu d'ari da ashirin,
saura kuma zai ajiyesu dan hidimar karatunshi.
Da haka dai sukayita hira sai har kusan shabiyu na dare sukayi saida safe kana duk suka mik'e kowa yayi makoncinsa zuciyarshi cike da farin ciki.
Washe gari kamar yadda suka tsara hakan Saifuddeen yayi ya tallatawa su Alhaji Kabiru Maggi ba musu kuma suka amince dan ai sune da riba mai yawar,
yayinda Alhaji Sani kuma yaketa taraddadin shigo da yaron cikin harkarsu a cewarshi karfa ya lalata musu kasuwa so amman ya amince da tsarin,
nan take suka buk'aci daya basu account number inshi,
Allah sarki Saifuddeen sai yau ya tuna da wata abba tashi account number shi dan shi tun last year bayan s Ya Rabi'u ya aiko mishi woya da ishaq ya matsa mishi dole sukaje suka bud'e account number d'in da shi a lokacin yanaga account d'in baida wani amfani,
dan babu ko sisi a ciki in bada wanda ya bud'e dasu babu ko asi a ciki dan shi lokacin yafi ganewa asusunshi,
murmushi yayi jin dad'in ya haddace komai na account d'in a kanshi,
nan take ya basu account number,
inda sukayi sallama da cewa sai gobe zasu tura mishi,
inda sun saye kashi biyu cikin kashi uku na kayan.
Daga wurinsu kuwa wurin Bello ya nufa na shagon ba miskila nan yayi sa'a ya samu ogon nasu ya mishi bayanin komai,
cikin farin ya amince nan take suka tsadance suka kuma ajiye farashinsu dai-dai dana juna,
inda ya koka mishi da zai samu yana son ya ara mishi d'aya daga cikin yaran shagonshi dan yaje ya kyautata awun yaran shagonsu tunda su sabbin shigane,
cikin aminci da mutunci da kamala da cikar imani ba kyashi bare hasada ba miskila ya amince inda yace Bello zai koma ya kula da lamarin shagon su Saifuddeen nan ya gayawa Saifuddeen farashin yadda yake sallaman yaran shagonsu a kullum da kuma k'arshen wata,
shima Saifuddeen ya amince duk da yawan kud'in yasan wannan shine adalcin da ubangida zaiwa yaran gidanshi gudun kada su zama masu zagon k'asa.
Daga nan ya shirya yaje makarantarsu yayi cuku-cukun komai daya dace dan ci gaba da fafutukar neman damar shiga jami'ar G.S.U.
Shi kuwa Bappa Ali a ranar ya fara nunawa Warisu harkan kasuwancin inda yaji dad'in haka sosai, dan ko ba komai zai samu damar kula da kanshi da ah'linshi.
Washe gari kuwa saiga Saifuddeen yanata ganin ruwan miliyoyi a account number inshi,
wanda Alhaji Sani Da Alhaji Kabiru da ba miskila suka turo mishi,
a ranar su Alhaji Kabiru suka kwashi kayan maggin da suka sara a wurin Saifuddeen suka kai sito insu.
Bappa Ali kuwa ya nemi akori kura guda biyu yasa aka lodawa ba miskila kayan daya sara a d'aya motar,
d'ayar kuwa yasa aka loda wanda zasu ajiye a shagonsu,
nan aka tafi da Warisu da Bappa Alin bayan yan gama sassauk'e kayan ko wanne an ajiyeshi a muhallinshi,
sai Bello da da Warisu da Bappa Ali suka tare a shagon su Ssifuddeen d'in nan suka k'ara kimtsa komai sannan bappa Ali yayi musu nasiha da suji tsoron Allah su kyautata awun mudunsu, nan kuma sukayiwa shagunan layinsu ihsani da kayan abinci dama duk wanda yazo gilmawa ta gaban shagon nansu,
hakan yasa a take duk layin nasu suka san da shagon dan sanadin bada ala koron.
Wasa-wasa kasuwa dai nata d'an tafiya,
sai dai yawanci masu sarine ke saya,
dan masu sayan d'ad'd'aya basu fara sanin shagonba tukun,
tuni kuma masu dattin zuk'ata sun fara suka suna wani cewa.
"Yoh aiyi dai mu gani, nanda yaushe wai maye yayi amarya tuni zai lamushe abarsa,
sabida wasun gani suke Saifuddeen yazo da wani salo na kashe musu kasuwa da hanasu riba mai yawa,
to dama in ubangiji yayi niyar d'aukaka d'an adam a bakin masu hasada zai d'aukakashi tuni masu hasadan dake k'ananun Magna ne yasa kasuwar gombe ta cika da batunsa inda kamar da wasa suka rad'awa shagon dama layin suna wai ,
*ALHAJI BUTU* wai alhajin araha kenan,
abu kamar wasa sai ga sunan shagon dama layin ya zauna hakan.
Cikin mako uku kasuwanci yaci gaba da gudana,
yayinda Ssifudddeen kuwa har yau bai fasa tallan ledanshi dasu omoba,
ana kuma ta shirye-shirye fara WAEC.
Sun gama zana exam d'in WAEC, hakama NECO tuni kuma ya zana JAMB inshi bayan wasu makonni sakamon jarrabar na Jabm ya fito inda ya samu 220 kuma Alhamdulillahi waec da neco d'inma result yayi kyau matuk'a gaya.
Bayan wata hud'u, tuni Saifuddeen ya samu nasarar zama cikekken d'alibi a Gombe state university.
Warisu da Bello kuwa sosai kasuwa take tafiya dai-dai da yanayin cinikin sabbin shaguna masu araha,
a dai-dai lokacin ne kuma komai na kayan abinci ya dawo gida a hannun manoma,
tuni masu hannu da shuni sun fara rige-rigen saye kayayyakin abincin dan b'oyeshi sai yayi tsada su fiddoshi.
A kuma dai-dai lokacin ne company layin Mtn suka kuma biyansu kud'in hayan filinsu da suka kafa services nan suka had'a kud'in suka rub'anya jarin kayayyakin abinci da bappa Ali zai sararo musu.
Kamar bara haka banama bappa Ali da Saifuddeen sukayi,
bayan sun harhad'a cinikinsu suka ware asalin uwar kud'insu sannan suka ware tarin ribar da suka samu na gefen maggi da kuma sauran kayayyakin abincin da kud'in hayan fiinsu Alhamdulillahi kasuwa kuwa tayi Al'barka dama ance kad'an mai al'barka yafi mai yawan da akasa dan zalumcin,
ware kud'in sukayi na maggin jarin da ribar wanda ya basu million uku ,
sai suka rabasu suka kuma saran maggi million biyu,
sannan suka d'auki million d'aya suka sari 'yan kayayyakin masarufi kamarsu,
spaghetti, macaroni, indomi, sugar, fulawa, da buhunan madarar awu ajiniyo moto, suka had'a da sarin maggin nasu.
Sai kuma suka had'a jari da ribar kayan abincin dana hayan bappa Ali ya fara bin kasuwannin k'auyuka yana sari babu kama hannun yaro,
saida ya cika d'akunan iyayensu mak'il ,
sannan ya fara sara yana sawa Warisu na kaisu kasuwa cikin shagonsu tuni shago ya cika mak'il,
masu sari sukayo musu caa ko yaushe kazo bakin shagon zaka samu dafifin mutane mata da maza manya da yara,
ganin haka yasa Saifuddeen fasa asusunshi na wata hud'un ya fito da kudad'en suka sari buhunan al'kama da acca suka had'a a ciki.
Nan fa kasuwa ta d'auka sosai da batun shagon Butu da yawa suna son sanin asalin mai shagon kuma sun gaza ganewa,
dan wasu kance ai shima wannan shagon butun reshen shagunan Ba miskila ne da yawa kuma suna yarda da haka ganin babban yaron shagon ba miskilan a shagon butun Bello kenan,
wasu kuma na cewa shagon Bappa Ali ne, wasu ko na cewa na Warisu ne,
sam dai mutane basu gane sahihancin zancenba sunata kame-kame dai,
Saifuddeen kuwa time to time yake lek'a shagon.
Salisu kuwa sosai yake jin dad'in sabuwar machine d'in da Saifuddeen ya saya mishi inda yaketa karatun shi a F, C, E Gombe.
Su Ahmad da Mudassir kuwa Karatu yayi nisa hakama Salisu,
tuni Saminu kuwa sune masu gama wannan shekaran.
Yayinda Saifuddeen kuwa sune 'yan level 100.
Bayan shekara d'aya, kasuwa taci gaba da gudana komai yana tafiya dai-dai da tsari na taimakon talakawa da marasa k'arfi.
Kullum jarinsu habaka yakeyi da d'an riban da suke bi da kuma kud'in hayansu,
inda kayan masarufi yake mallakin jarin Saifuddeen ne halak d'inshi ba surkin kud'in gadonsu.
Yau kusan wata d'aya kenan Saifuddeen da Bappa Ali sunata kan harhad'a cinikinsu na tsawon shekarar suna ware ribar su da hauhawar jarinsu.
Koda suka gama had'e komai sai suka fara ware hak'insu Bello da Warisu sunka biyasu biya mai daraja a matsayinsu na masu kula da kasuwancin,
daga nan kuma suka ware adadin zakkar da zasu fidda na shekarar bayan sun gama ware zakkar tasu,
sun bawa wad'anda shariya ta misalta da a basu sai kuma suka fara shirye-shiryen sari tako wanne sashi inda Bappa Ali zai sarar musu kayayyakin abinci a kasuwannin k'auyuka kamar yadda suka saba,
shiko Saifuddeen zai yi musu sarin kayan masarufi wanda wasu direct daga company yake musu sarin shiyasa suke samun damar sakin farashinsu da rahusa,
dole zuwa yanxu sunfi k'arfin shago d'aya hakan yasa suka nemi k'arin hayan wani k'aton shagon dake kusa da nasu, ba b'ata lokaci aka basu da yake na Alhaji Kabiru ne,
cikin kwana uku aka had'a shagunan sannan aka barsu da k'ofofi biyu.
Ya Adnan kuwa tuni ya isar da batun soyayyarshi da Adda Rahma ga manya tuni mgna ta kankama dan iyayensu Adnan sun san nagartar Rahma tunda a gabansu ta girma shiyasa basuyi wata rigimaba,
tuni antsaida ranar aurensu bayan sallan layya da mak'o d'aya.
Saminu kuwa ya gama karatunshi har ya samu damar tafiya bautan k'asa mgnar sosayyarshi da Raihana kuma tanata kankama har iyaye sun shiga,
an bari a kan cewa sai ya gama bautan k'asanshi ya fara aiki sannan ayi musu auren.
Mudassir da Ahmad da Ishaq ma duk sun kusa gamawa.
Hayatuddeen kuwa shima yana shekararshi ta k'arshe a primary school,
Faruq kuwa yana primary 3 Adam na primary 2,
Raliyya kuma tana SS 1.
Abba yaron Bappa Ali shima ya girma har an yayeshi.
Rayuwa dai taci gaba da gudana cikin nasara da ci gaba.
Anyi bikin Ya Adnan da Rahma lfy an watse lfy,
ta tare a gidanshi dake cikin Gombe wanda yake cikin jerin gida jan ma'akatan lfy na Medical Center Gombe,
wannan had'i yayi matuk'ar yiwa Ahmad da Mudassir dad'i dan dama a gidan Ya Adnan d'in suke sukewa kansu girki a cewarsu yanzu sun huta sun samu mai musu girki.
Bayan bikin da mako ukune Ya Adnan yaje har dukku da batun yana son a basu Faruq da Adam a cewarsa zai rik'esu,
to Ummi dai tak'i amincewa ganin ya tasa gabata da magiya ne yasata ce mishi Saifuddeen ne ya hana ba itaba kuma shi yana can gomben,
jin haka yasa Ya Adnan tura mishi text cewar,
yana son ganinshi gobe, yana ganin text d'in ya maida mishi amsa da to Allah ya kaimu.
daga nan Adnan ya sallami Ummi ya tafi gidansu a nan ya wuni sai da yamma ya koma.
Washe gari da safe Salisu da Saifuddeen ko breakfast basu tsaya yiba suka wuce cikin gombe,
kasan cewar basu da lectures da wuri sai zuwa k'arfe biyu so kai tsaye gidan ya Adnan suka nufa,
a harabar gidan Salisu yayi parking,
sannan suka nufi bakin mashigar ainihin cikin gidan,
a bakin k'ofa suka tsaya door bell suka d'an danna,
jim kad'an aka bud'e k'ofar ganin Ahmad ya bud'e musu k'ofar ne yasa su yin murmushi shima murmushin yayi tare da bawa Salisu hannu tafawa sukayi cikin salon gaisuwa ta abokai da suka shak'u da juna,
sai ya kuma juyo ya d'aga hannu alamun zai tafa hannu da Saifuddeen da k'arfi irin yadda yayi da Salisu,
shi kuwa Saifuddeen ganin haka yayi saurin janye hannunshi tare da rab'awa gefenshi ya wuce yayi cikin parlour,
cikin dariyar shek'iyanci Ahmad ya kalli Salisu da shima dariyar yakeyi, sai ya kuma juyo ya kalli Saifuddeen da tuni ya isa tsakar parlour suna ruggume da juna shida Mudassir, dariya ya kumayi tare da cewa.
"Hege mai d'an karen son jiki da tsoron wahala."
cikin dariya Salisu yace.
"Yaseen gskyanshi nima d'in ai bani kuma yarda ka kima min wannan hannun naka, kalli yadda hannuna yayi jazir hege mai suffar samudawa."
duka ya kaiwa Salisu,
da sauri ya kauce tare da cewa.
"Wayyo Ya Adnan kaga Ahmad ko."
da sauri Rahma ta yunk'ura zata tashi ta fita jiyo muryar Salisu tasan sarai da Saifuddeen suka zo.
Shi kuwa Ya Adnan da sauri ya jawota jikinshi tare da cewa.
"Ina zakije?."
fuska ta d'an marairaice tare da cewa.
"Parlour zanje kaji su Saifuddeen sun zo."
ido ya d'an kashe mata tare da cewa.
"Barsu suyi ta sabgoginsu muma muyi namu in mun gama ma fita."
cikin sanyi tace.
"Allah ko nayi missing Saifuddeen tunda akayi bikin nanfa bai zoba."
mik'ewa yayi tare da kamota ya tsayar da ita sannan yace.
"To muje muyi wonka."
a dole ta bishi suka shiga bathroom.
Su Ahmad kuwa a falo hira sukayi tayi na yaushe gamo,
daga nan suka shiga kitchen suda kansu suka fara kiciniyar had'a breakfast nasu.
to Ahmad da Mudassir su sun iya sun saba,
Salisu da Saifuddeen kuwa basu iyaba,
shiyasa suka kame suka zauna gefe,
Ahmad na fire dankali shi kuwa Mudassir yana kiciniyar tafasa musu ruwan tea.
Bayan kamar 35 minutes Rahma da Adnan suka fito a tare a parlour ta tsaya tana kasa kunne dan jiyo ta inda hayaniyarsu take,
jinsu a kitchen ne yasa tayi sauri ta nufi kitchen d'in tana shiga duk suka juyo murmushi tayi musu ganin duk suna murmushi,
sai kuma Saifuddeen yayi saurin tasowa ya iso gabanta murmushi ya kuma yi tare da mata alamun,
"Iye-iye kinyi kyau fa."
kunnenshi ta d'an rik'e tare da d'an matsewa da d'an k'arfi, d'an tsalle yayi tare da yarfa hannu,
Ahmad kuwa sai tsalle yakeyi yana dariya tare da cewa.
"Yauwa Adda Rahma matse da kyau."
Mudassir kuwa fuska ya kwab'e tare da cewa.
"Please Adda Rahma sakar mishi kunne kinsan baya son wahala."
Salisu ne yayi dariya tare da cewa.
"Kaji banza to waye ke son wahala,
kuma a yar wannan matsarne wahalar."
shi kuwa Saifuddeen hannunshi d'aya yasa ya kamo d'aya kunnenshi cikin body language ya mata alamun ya tuba.
ganin haka yasa ta sakar mishi kunne tare da