Showing 126001 words to 129000 words out of 176868 words
Chapter 43 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel
ai nace maka munyi faɗa ko".
tana gama faɗan haka ta kashe wayarta, dariya sosai Hayatuddeen yayi, Ummi dake tsaye abayansa ne ta ƙaraso cikin falon, dubansa tayi tare da cewa.
"Kai kuma kaida waye kake waya haka?"
Murmushi yayi tare da cewa "Amina ce fa Ummi wannan nurse ɗin da ta kula da Hamma Saifuddeen lokacin da muke Abuja, to shinefa yanzu da ta ƙira nake shaida mata dawowar mu shine wai ita tayi fushi da har jiya muka sauƙa a Abuja ban gaya mata ba taje ta duba jikinshi".
Murmushi tayi cikin tsananin jin dad'i tana matuk'ar son duk wani maison Saifuddeen d'inta,
murmushin kawai Ummi ta kumayi tare da zama akan kujera kana ta maida hankalinta ga TV inda sunna tv ke haska wa'azin Malam Isah Ali Pantami.
Yau tunda tazo wajen aikin nasu fuskanta aɗaure yake tamau, sam takasa sakin fuska ga kowa wanda hakan ya matuƙar bawa abokan aikinta mamaki, don kuwa sunsan bahaka take ba ita takowace sannan itaɗin me yawan fara'a ce saɓanin yau da suka ga ta tsuke fuska, fitowarta daga ɗakin gabatar da shirye-shirye kenan inda ta gabatar da shirinta na mushaƙata, kaitsaye ɗakin hutawansu ta nufa inda anan tabar jakarta harma da wayarta.
Koda ta shiga cikin ɗakin kan wata kujera ta zauna tare da ɗaukan jakarta, zip ɗin ta zuge kana ta ciro wayarta, 4 missed call ta iske acikin wayar wanda kuma duk daga Abdussalam ne, tsuka tayi tare da kunna data'n wayarta ta shiga Instagram, Raveel ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, can ƙasan maƙoshi ta amsa masa sallaman batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba,
asanyaye ya tako ya ƙaraso zuwa inda take, kan wata baƙar kujera dake facing wanda take ya zauna murya asanyaye yaƙira sunanta "Zaleeha!"
Bata amsashi ba haka kuma bata ɗago kai ta kalleshi ba, ganin haka yasanyashi sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗan langwaɓar gefe guda cike da tsananin shauƙin mayen soyayyarta yace.
"Dan Allah M B S Dukku ki saurareni mana, ashe shikenan don zuciyata ta kamu da soyayyarki tayi laifi? Dan Allah Zaleeha kiyi haƙuri ki fahimci irin sonda nake miki, wallahi inasonki ina miki son da nikaina bansan adadinsa ba, rasaki dai-dai yake da daiɗaicewar tunanina Inasonki Zaleeha, dan Allah ki Amshi soyayyata!!"
Tsananin rauni da damuwar dayake cikine ya bayyana ƙarara akan muryarsa.
Idanunta ta lumshe tare da cizon laɓɓanta wanda suka sha pink lipstick, jin kalaman nasa take tamkar sauƙan ruwan zafi afatar jikinta, waye zai fahimceta? wanene zai gane me takeji azuciyarta? tabbas da ace mazan dake kawo kansu gareta da sunan soyayya sun san metakeji acikin ranta tabbas da zuwa yanzu sun ƙyaleta hakanan ta huta, tana matuƙar ganin ƙiman Raveel saboda koba komai abokin aikinta kuma suna shiri sosai dan yanada abin dariya tamkar abokin wasanta haka suke kodan kasan cewarshi babarbare ne, amma ayanzu furta mata kalman so da yayi yasanya taji gaba ɗaya batako son ganinsa, burinta ayanzu shine kowa yafahimci halin da take ciki na tsananin soyayyar dake cinta azuciya.
Ganin yanda ta rumtse idanunta ne yasanya Raveel ƙiran sunanta murya atausashe yace.
"Balaifina bane Zaleeha don Allah Karki tsaneni, laifin zuciya da ruhina ne da suka matuƙar kamuwa da soyayyarki, najima ina dakon soyayyarki araina Zaleeha, please and please ki amshi soyayyata ki amshi soyayyata kozan samu sauƙin abun danakeji azuciyata!!".
tuni idanun Raveel suncika tab da ƙwalla, ji yake kamar yajawota jikinsa yayi hugging ɗinta sannan yasata ta amsa masa soyayyarsa.
Idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe tare da watsa masa su, saida yaji wani yaarr acikin jikinsa, cikin dakiya tare da ƙunan zuciya ta dube shi murya asarƙafe tace.
"Please Raveel i say leave me alone!, dan Allah kabarni na huta, kana ta faɗin kana sona! kana sona! na tausaya maka, kai kasan ni me nakeji acikin tawa zuciyar kuwa! to ji nake tamkar zan mutu in bar duniya in ban sameshi ba? har yanzu ina mutuntaka amatsayinka na abokin aikina,saboda haka kana da sauran daman da zaka janye batun soyayya agareni, bana sonka Raveel bana kuma tunanin zan soka ko anan gaba!!".
miƙewa tsaye tayi tare da ɗaukan jakarta ta nufi hanyar fita daga ɗakin, Sunanta Raveel yashiga ƙira amma sam bata tsayaba balle ta waiwayo ta kalleshi haka ta fice daga cikin ɗakin.
Idanu Raveel ya rumtse take saiga hawaye sun biyo kan ƙuncinsa, ya zaiyi da matsanancin son Zaleeha da yakeyi? Tayaya zai soma rarrashin zuciyarsa akan ta haƙura da Zaleeha? Kansa ya kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabansa yana mejin wutar soyayyarta na ƙara kunnuwa acikin zuciyarsa.
Itakuwa Zaleeha kai tsaye motarta ta nufa tana shiga tayi mata key tare dayin reverse, maigadi ne ya wangale mata gate ɗin fita daga cikin gidan redi'on nasu na vission FM. gudu takeyi sosai akan titi gaba ɗaya komai ya cakuɗe mata waje ɗaya, ko ina tasanya kanta batajin daɗi, gida babu daɗi haka wajen aiki ma babu daɗi ko ina ta kutsa zancen aure akeyi mata kamar ita d'aya ce budurwa a duniya, hannunta tasanya ta bugi steering motar tata da ƙarfi tare da ɗan sake sautin kukanta, kuka takeyi ƙasa-ƙasa hadda sheshsheƙa, kai tsaye unguwar sarki tanufa hanyar da zai sadata da shagon A.A ALIYU PHARMACY a dai-dai wajen a dai-dai lokacin kamar wannan ranan anan ta tsaida motarta tare da zubawa ƙofar shagon A.A ALIYU PHARMACY ɗin ido, dai-dai inda tafara ganinsa ta sauƙe idanunta, sannu ahankali tasoma ganin tamkar alokacinne abubuwan da suka wakana tsakaninsu ke faruwa, lumshe idanunta tayi tare da sakin sautin kukanta ya fito fili, cikin magagin soyayyarsa da ta rufe mata ido tace.
"Inakake? Inakatafi kabar zuciyata cikin tsananin kewa da begenka? Kaine mafarkina haka kuma Kaine Zahirina, Koba danni ba kodan zuciyar da ka dasawa soyayyarka acikinta dan Allah kabayyana agareni na ganka, kowa yanamin kallon zautacciya wacce take son gaibu, wasu suna faɗin cewa kai ba mutum bane, kafito ka nuna musu cewa kai mutum ne kamar kowa, kazo gareni Ina Tsananin buƙatarka ayanzu fiye da wancan ranan, Dan Allah kazo gareni!!!".
Kuka take sosai tare da kifa kanta ajikin steering motar, wani irin zogi zuciyarta keyi mata yayinda idanunta ke ƙoƙarin rufewa, kuka tayi sosai harsaida wani irin azababben ciwon kai ya rufeta kafun ta zaro wani baby pink colour handkerchief daga cikin jakanta tashiga share fuskarta wacce tayi dama dama da hawaye, sake duban ƙofar shagon tayi, sai kuma ga wasu hawayen na sake sauƙowa daga cikin idanunta, dai-dai lokacinne wani matashin saurayi ya shiga kukkulle ƙofofin shagunan yana samusu kwaɗo kasancewar anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba saboda haka zasuje sallah, ganin cewa sun rufe shagonnasu ne sannan da ɗai ɗai da ɗaiɗai jama'an dake wajen ke tafiya izuwa masallaci hakan yasa cikin rashin kuzari ta tada motar tata, ayanzukam ahankali take tafiya da motar kasancewar gaba ɗaya jikinta yayi weak ga wani irin zazzaɓi da ciwon kai da suka kawo mata cabka lokaci guda.
Agaban tankamemen gate ɗin gidansu dake cikin New G.R.A ta tsaya da motartata tare da danna wani ɗan siririn horn, Malam Kalla me gadi ne ya wangale mata gate ɗin, yayinda ta tura hancin motar tata cikin gidan, ko parking mai kyau yau batayi ba haka ta fito daga cikin motar, kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, don acanne kaɗai take da yaƙinin samun nutsuwa, cikin muryarta da ta dashe ta yi sallama, Unaisa da Unaid yaran Yaya Ahmad ne keta wasa acikin tsakiyar falon, suna ganinta suka taho da gudu cikin ƙaunarta su duka sukace.
"Oyoyo Aunty Zaleeha!"
cikin yanayin sanyi daya rusketa haɗi da rashin kuzari tashafa kayinsu kana ta zuge zip ɗin jakarta, kasancewarta uwar mak'ulashe da shan zaƙi hakan yasa sam bata rabo da abubuwan zaƙi dangin su chocolate's da sweet's, chocolate ta basu sannan ta nufi ɗakin Mamy nan tabarsu sunata murna.
Sallama ɗauke abakinta tashiga ɗakin Mamy'n,
Mamy dake zaune abakin gado tana ninke kaya ta amsa mata cike da kulawa tana me dubanta.
"Sannu da hutawa Mamy!" tafaɗa tana me ajiye jakan hannunta kana ta sanya hannu ta zare mayafin dake jikinta.
"Yauwa Zaleeha sannu da dawowa ya aikin?".
cewar Mamy tana mebinta da kallo.
"Lafiya". tafaɗa ataƙaice kana ta faɗa kan gadon Mamyn blanket taja ta rufe jikinta dashi.
Cikin damuwa haɗi da kulawa Mamy tace .
"Yadai Zaleeha bakida lafiya ne?"
cikin muryarta dake neman sarƙewa tace.
"Mamy kaina ke ciwo, sannan zazzaɓi na damuna!"
"Subahannallah! kinsha magani kuwa?".
Mamy tafaɗa aɗan rikice tana mai taɓa jikin Zaleeha'n, aikuwa nan taji jikin yaɗau zafi zau.
Kai Zaleeha ta girgiza alaman batasha ba, tashi Mamy tayi tare da cewa.
"Bari naje na kawo miki abinci da magani kisha inyaso idan yayanku Ahmad yashigo sai ya kaiki asibiti"
Mamy na fita Aunty Lubna matar Ya Ahmad tafito daga cikin toilet ɗin dake ɗakin Mamyn, jikinta duk ruwa da'alama alwala tayi, ganin Zaleeha akwance lulluɓe da bargo yasanyata cewa.
"Lafiya kike kuwa Zaleeha duk wannan uban zafin shine ke hadda lulluɓuwa".
Zaleeha da zazzaɓi yasake cin ƙarfinta ta ɗago idanunta ta kalli Aunty Lubna'n sai kuma ga hawaye shaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta.
Ganin hawaye na fita daga idon Zaleeha yasanya jikin Aunty Lubna yin sanyi, zama tayi akusa da Zaleehan tare da sanya hannu ta dafa kanta cikin kulawa tace.
"Kuka kuma Zaleeha? share hawayenki kinji komai yayi tsanani yana tare da sauƙi ki sawa ranki jarumtar yadda zaki fuskanci k'addararki!"
Kai Zaleeha ta girgiza mata tare da kife kanta akan cinyan Aunty Lubna'n cikin dasashshiyar muryarta tace "Menene laifina Aunty Lubna? meyasa kowa agidannan bazai yarda cewa inada wanda nakeso ba, sannan kuma ba aljani bane kamar yanda suke tunani, mutum ne shifa kamar kowa, Inasonsa! Aunty Lubna Inasonsa!, bansan meyasa kowa yaƙi fahimtan hakan ba hatta Ya Ahmad ɗina ma fa shima kallon bansan me nakeyi ba yakeyi mini gani yake wai ba mutum nake soba aljan ne!".
shiru tayi da maganan tare da ƙara sautin kukanta.
Cikin lallashi haɗi da tsananin tausayinta Aunty Lubna ta sanya hannunta ahankali take shafa bayan Zaleehan, cikin son kwantarwa da Zaleeha hankali tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha ki kuma kwantar da hankalinki, nafahimci yanda kikeji kuma insha Allah zaki gansa harma kuyi aure dashi kidaina kukannan kinji shalelen Ya Ahmad ɗinta!".
Wani irin sanyi kalaman Aunty Lubna suka sauƙarwa Zaleeha acikin zuciyarta, take taji son matar Yayan nata ya ƙara shiga ranta, nan tasoma ƙoƙarin share hawayenta harma da sakin murmushi, Mamy ce ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da plate ɗin abinci da kuma magani, kasancewar taji sanyi acikin ranta bisa kalaman da Auntyn nata tayi mata hakan yasanya ta ci abincin saidai ba sosai ba magani tasha inda tayi alwala tayi sallah bata bar kan sallayan ba saida tayi sallan isha, anan ɗakin Mamy ta kwanta, mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa, ana idar da sallan Isha kuwa saiga Abdussalam yayiwa gidan dirar mikiya, koda Mama taji zuwan Abdussalam nan tashiga zazzaga masifa wai Zaleeha batajin magana tayi baƙo me mahimmanci kuma taje ɗakin uwarta tabiyu tayi zamanta, koda akaje ɓangaren Mamy ƙiran Zaleeha nan aka iske tana bacci, inda Mamy ta shaida cewa bata da lafiya ne, haka Abdussalam ya koma gida batare daya samu ganin Zaleeha ba, Mama kuwa ba irin faɗa da maganganun da bata faɗa ba ita kaɗai taketa ɓaɓatun ta harda cewa wai Mamy ce ke zuga Zaleeha akan kada taso Abdussalam, haka tayita aikin baƙin ranta ita kaɗai awannan daren dai Zaliha aɗakin Mamy ta kwana.
***
Alhamdulillahi yau kwanan su Saifuddeen uku da dawowa Nigeria, inda acikin kwanaki Ukunnan sauƙi kullum ƙara samuwa yake ga Saifuddeen yana mai ci gaba da shan sabbin magungunan da aka loda mishi.
sannan kuma acikin kwanakin kullum gidan nasu cikin karɓan baƙuncin mutanen dake zuwa gaisuwa yake,ciki kuwa hadda matar Alhji Sani, da kuma Matar Alhaji Kabiri da Mommyn Hisham.da kuma matar Alhaji Adamu Hajia Kingi damn k'anwarta Aunty Kubra yar kasuwa ce mai zuwa Dubai sari kayan k'awa na mata, time to time da ita Ahmad ke zuwa sari, suma sunzo sun duba jikin Saifuddeen inda Ummi taji daɗi sosai.
Ranan yau takasance laraba kuma yaune ranan da Ishaq ya sanar da Saifuddeen cewa Zaleeha zatazo gidan nasu na nakasassu don gudanar da shirinta mai suna BABU NAKASASHE SAI RAGO, hakan yasa tun safe yau Saifuddeen yatashi yanajin kansa cikin wani irin shauƙi yayinda yakejin zuciyarsa wasai.
Ɓangaren Zaliha kuwa kwana biyu kenan yau bataje aiki ba sakamakon ɗan jinyan da tayi, amma yanzu Alhamdulillah jikin nata yayi sauƙi sosai, yayinda kullum Aunty Lubna ke ƙara kwantar mata da hankali, hakanan yau tatashi tana mejin faɗuwar gaba yayinda takejin zuciyarta na tsinkewa akai akai haka dai ta kawar da duk wani abu da takeji ta shiga shirya kanta don zuwa gabatar da shirinta.
Fitowarsa daga wanka kenan lafiyayyar skin ɗinsa sai fidda daddaɗan ƙamshin tsadadden sabulun wankansa, zaune yake agaban mirror yana shafawa jikinsa mai, yana kammalawa ya shiga gyara ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ta sauya gaba ɗaya kamanninsa na da, taƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini. Wata dakakkiyar shadda me kyau da tsadan gaske wacce take da kalan skay blue ya sanya, sosai shaddar ta amshi jikinsa inda tayi bala'in da cewa da white skin ɗinsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar wacce jikinta ke ɗauke da ratsin sky blue yasanya, yayinda aƙafansa kuwa yasanya lafiyayyun takalma sau ciki ƙiran kamfanin bally suma kalar sky blue garesu hakan yasanya haɗuwar tasa ta ƙara bayyana, bakaɗan ba Saifuddeen yayi kyau yayinda kyakkyawan sajensa keta ƙyalli, tsadadden turarensa me daɗin ƙamshi ya fesa ajikinsa take ɗakin ya gauraye da ƙamshinsa, agogonsa ƙiran kamfanin rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa na dama, wayarsa ƙirar iphone ya tura acikin aljihunsa tare da sarrafa kekensa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Daddaɗan ƙamshin turarensa shiya ja hankalin su Ummi da Hayatuddeen da kuma Raihana dake falon suka dawo da kallonsu garesa, "Wow Hamma Saifuddeen ka ganka kuwa? Wallahi Hamma na baka taɓa yin kyau irin na yau ba!!".
Hayatuddeen yafaɗa cikin santin kyawun da yaga hamman nasa yayi.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen tare da duban Ummi cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan wai maganan da Hayatuddeen yafaɗa gaskiya ne?
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"A kullum a koda yaushe kai kekyawa ne koda bakayi wonkaba bare kolliya.
to ya kake zato idan kayi kwalliya to sai kayi kyau tamkar balarabe.
kaga kenan sharrin Hayatuddeen ne kawai dama tuncan kai kyakkyawane!"
Dariya gaba ɗayansu suka sanya banda Saifuddeen wanda shidai saidai yayi murmushi.
Cikin yabawa da kyawun da yayi Raihana tace.
"Hammana wallahi kayi kyau sosai".
murmushi yayi mata tare da yi mata alama kan cewa ya gode, Hayatuddeen kuwa cikin azarɓaɓi ya ciro wayarsa hoto yashiga ɗaukan Hammannasa yana me cewa ya samu na sawa a status da kuma Instagram.
jin haka Raihana ta amshi wayar tare da yi musu hoto shida Ummi da Raliya data shigo yanzu. Sunyi kyau matuk'a duk suna murmushi Ummi ta d'an roggofo kanshi.
Cikin body language ɗinsa yayiwa Ummi bayanin inda zaije, fatan Alkhairi Ummi tayi masa tare da cewa.
"Adawo lafiya".
Har bakin mota Hayatuddeen ya raka hamman nasa yayinda da kansa ya sauƙa akan kujeransa ya shiga cikin tsaleliyar motarsa ƙiran mercedes benz, agidan baya ya zauna sannan Hayatuddeen ya sa mishi weelchair d'insa a but yayinda Sule driver ke tuƙasa...
Tana gama shafa mai ta ɗauki tsadaddiyar hodan ta ta goga akan fuskarta, tana gama shafa hodan ta ɗauki black eye pencil ɗinta ta goga acikin manya manyan idanunta dake matuƙar gigita masu kallonsu, pink lipstick ta goga akan ƴan ƙananun laɓɓanta, yayinda tayi amfani da Mascara wajen miƙar da tulin eye lashes ɗinta, ita ba mace bace wanda take da yawan cika meckup akan fuskarta hakan yasa bata ƙara komai akan fuskarta ba bayan wannan ɗan kwallian da tayi.
Wani haɗaɗɗen lace wanda yaji dinkin riga da sket maroon colour wanda keda ratsin golding ash ta sanya, sosai kayan suka amshi jikinta inda sket ɗin ya bayyana haɗaɗɗiyar surar jikinta da kuma cikakkun hips ɗinta, parking dogon gashinta tayi atsakiyan kanta tare da zama akan stull ɗin mirror tashiga tsantsarawa kanta ɗaurin ɗan kwali, wani irin haɗaɗɗen ɗauri tayiwa kanta wanda yaƙara bayyana kyawun shigar nata, wata ƴar siririyar sarƙa golding ash ta sanya awuyanta tare da liƙa ɗan kunnensa me kamar manne akunnenta, wani takalmi me tsananin tsini da kyau wanda keda kalan lace ɗinta ta sanya aƙafafunta tare da ɗaukan wani vail shima maroon colour ta yafa ajikinta, baƙaramin kyau Zaleeha tayi ba ita kanta yau kyawunta ya ɗauki hankalinta, turarenta dake rikita maza ta fesa tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta me kalan kayanta ta riƙe ahannunta, wayarta tariƙe aɗayan hannun nata tare da car key ɗinta kana ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa take taku ƙwas-ƙwas hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance, cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo".
Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace.
"Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?".
Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce