Showing 141001 words to 144000 words out of 176868 words

Chapter 48 - Nakasa Ba Kasawa Bace Book 1 Complete Hausa Novel

da ishaq.

Kai tsaye parlour'n Saifuddeen suka nufa.
zaune suka sameshi bisa wellchair ɗinshi, mai kalan golding ash.
Wani irin murmushi Ahmad yayi tare da cewa.
"Fatabarakallahu fi hasanil Kaliƙin, tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da yayi wannam kyakyawar halitta."
Ishaq ne ya amshi zancen da cewa.
"Masha Allah!."
Murmushi Saifuddeen yayi wanda yake sanye da wata ɗanyen yadin getzner mai azabar kyau kalar dark green mai turuwa, irin dark mai shinng ɗinnan, yayinda aka zubawa kayan wani fitinennen ɗinkin half jumper and pencil trouser, daga wuyan rigar kuwa aka watsa mishi wani tattausan zaren surfani.
yayinda ya murza wata kyakyawar hular damanga mai ratsin dark green akansa,
daga ƙafansa kuwa wasu irin fitinannun toms mai kalan shaddarsa yasa, ƙiran company'n Gucci, me matuƙar tsada,
still kuma zazzafan agogon company'n Gucci ne ke ɗaure atsintsiyar hannunsa wanda kuɗinsa kaɗai ya haurawa 80k,
sai wayarshi ƙiran iphone 11 pro max daya zura cikin al'jihun gaban rigarshi, wanda abayyane ta saman al'jihun rigartasa, kake iya hango kyawawan camera's ɗinta guda uku dake jere reras, biyu asama ɗaya aƙasa.
Yanayin shigar tasa ta matuƙar ƙara fito da farar fatarshi kai ka rantse da Allah cewa balarabe ne.
Sajen nan nashi yayi wani lub-lub yayiwa fuskarsa ƙawanya sai sheƙi da ƙamshi yake,
red colour lips ɗinshi sai shinning skeyi tamkar an shafa mishi mai a kansu.

Shida kanshi ya sarrafa whellchair ɗinshi suka fito zuwa parlour.
Ummi suka samu ita da Hayatuddeen azaune.
gabanta suka tsaya
cikin shirinsu na fita, murmushi tayi tare da godewa Allah daya bata wannan kyakkyawan ɗan, cikin gane batun da ya mata tace.
"Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, Allah ya baku nasara da sa'a kan abinda zakuje nema.
Allah ya sadaku da al'khairin dake cikin tafiyar ya rabaku da sharrin dake tare da tafiyar."

Da "Amin." Suka amsa baki ɗaya.

Shi kam Saifuddeen wani sanyi da farinciki ne suka rufeshi sabida addu'o'inta gareshi.
Shiko Hayatuddeen sai hotuna yaketa musu.

Daga nan suka fita,
har bakin gate Hayatuddeen ya rakasu, saida yaga sun fita sannan shima ya ɗauki machine ɗinsa ƙirar UD, ya nufi gidan Inna dan zaije wurin Zakariyya.


Su Saifuddeen kuwa suna isa G.R.A.
Ahmad ya rinƙa bin ƙwatancen da Baffa Ali yayi musu,
suna isa bakin gate ɗin suka danna horn, sunyi biyu ana uku aka wangale musu makekem gate ɗin.
Cikin nitsuwa Ahmad ya dai-daita parking ɗin motar,
a hankali ya buɗe marfin motar ya fito cikin shigarsa ta al'farma,
both ɗin motar ya buɗe tare da fiddo whellchair ɗin Saifuddeen,
ta inda yake yazo, buɗe mishi murfin motar yayi kana ya gyara mishi keken.
Yayinda tuni Ishaq kam ya fito.

Yana gama gyara zamanshi kan whellchair ɗin sai ga Ahmad ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da Unaisa
ganinsu yasa cikin sauri ya nufi inda suke,
ganin haka Ahmad Abban farida ma ya saki fuska kana ya nufi inda suke hannu suka bawa juna,
Abban Farida ne ya fara magana, inda yace.
"Assalamu alaikum."
"Ameen wa alaikassalam, barkanku da zuwa."
"Yauwa barka dai."
Murmushi yayi tare cewa.
"Ahmad yayan Zaleeha."
cikin sakin fuska Abban Farida yace..
"Ni kuma Ahmad yayan Saifuddeeen."
Murmushi sukayi baki d'aya,
sannan suka taho inda su Ishaq ke tsaye,
cikin tsananin son Saifuddeen ya sunkuyo ya bashi hannu sukayi musabaha,
sannan suka gaisa da ishaq wanda shi sam bai gane cewa Ishaq makaho bane.
Jagora yayi musu zuwa BQ inda dama yasa Lubna ta gyarashi fes tunda safe.

Bayan sun zauna ne yace.
"Bari naje na turo muku ita ko."
cikin fara'a Abban Farida yace.
"Ayi haka babban yaya."
"Ai anyima." ya bashi amsa yana ɗan murmushi, kana yafice daga cikin babban falon BQ ɗin.

Shiru sukayi kowa da abinda ke ransa,
shi kuwa Saifuddeeen azkar yakeyi azuciyarsa cikin nutsuwa.

Zahira yasa ta kai musu abin sha, kana ya nufi side ɗin Mama.
A Parlour Mama ya samesu suna hira sama-sama dan kowacce da abinda takeyi.
cikin tsare girar sama data ƙasa yace.
"Ke Zaleeha tashi kije BQ kinyi baƙi."
wani irin tsuke fuska tayi tare da yamutsa fuskar kana tace.
"Baƙi kuma ya Ahmad."
Ya Habune da yanzu ya fito ɗakin Mamansu yace.
"Ke shi sa'anki ne yana miki Magana kina zaune,
Zaleeha kifa kiyayeni nagafa baki da kunya ji kike kamar kin kamomu ko?."
Da sauri ta jujjuya mishi kai tare da miƙewa jiki na tsuma domin ita dai Allah ya sani tana tsoron ya Habu da Ya Aminu mugayene na bugawa a mujalla yazu zasuce zasu kai mutun mari.
"Maza ɗauko mayafinki ki ɓace mana daga nan."
Da sauri ta nufi ɗakinta,
shi kuwa ya fice daga falon.
A zatonta yana nan shiyasa tayi maza ta fito tana mai yin rolling kanta da ɗan kwalin lafiyayyar Arabian gawn ɗin dake jikinta,
ganin baya nanne ta zumbura baki tare da cewa.
"Bilkisu muje ki rakani."
Kai bilkisu ta jujjuya tare da cewa.
"Tab ina cikin kallon wannan film ɗin ai babu inda zani,
Rashida ta rakaki mana tunda ta gama zanen da takewa Aunty Lubna."
Ahmad ɗinne ya kalli Rashida cikin bada umarni yace.
"Rashida rakata ko."
"To" tace tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta.
Suna gab da fita aka tafi talla,
ganin haka Bilkeesu ta miƙe tare da cewa.
"MBC Bollywood iyayen talla sun tafi,
muje inga sahibin namu kafin in dawo sun gama tallarsu na tsiya."
dariyan mugunta Rashida tayi, kana suka nufi BQ.

Shi kuwa Ya Ahmad parlour'n Baba Malam ya nufa.
Yana shiga ya samesu da Mamy da Mama da kuma Baba Malam ɗin.
Gefen da littatafan addini wanda suke jere ya nufa yana mai cewa.
"Baba Malam su Saifuddeen sun zofa."
kai ya gyaɗa alamun to kana yace.
"Ka tura mishi Zaleehan"
"ai tama tafi."
ya bashi amsa yana me zama kusa dashi,
kai ya ɗan kwantar cikin sanyin sauti yace.
"Naji tausayin Saifuddeen baba ya bani tausayi, mutun kyakkyawa matashi Allah ya jarabceshi da nakasa mai zafi,
wlh Baba sai ka ganshi yama fi kyau a zahiri akan a hoto,
in dai Zaleeha ta yarda dashi to haƙiƙa tayi dace da miji managarci,
domin sam nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, in ka ganshi kamar ba kurmaba, haka inba dan wellchair ɗin da yake zaune a kaiba bazaka taɓa cewa gurgu bane."
Cikin mamaki Mama ta ƙara haɗe fuska tare da cewa.
"Wai maganar me kukeyi hakane ban gane inda kuka dosaba,
Gurgu kurma wurin waye yazo!?."
Cikin isa da tsare fuska Baba Malam ya mata bayanin komai akan Saifuddeen ya ƙara da cewa.
"Kuma ni yamin na yaba dashi muddin bata fidda waniba to niko zan aurawa Saifuddeen ita!."

Kaƙa ƙara ƙaƙa wayyo Mama ina wuta ta faɗa ciki, don baƙin ciki da takaici,
cikin tsananin hatsala da takaici tace.
"Kurma! gurgu!? Yar tawa zaku haɗa baki kuce gurgu zaku aura mata?
ai Wallahi bazata taɓa saɓuwa ba."
Mamy ne tayi saurin cewa.
"Kiyi mata fata da addu'an abinda yafi al'khairi zaifi akan mugun furuci baki san inda rabonta yakeba."
Wani irin mugun kallo ta watsawa Mamy tare da cewa.
"Mugun furuci? Akwai wani mugun furucine daya wuce abinda kuka haɗa baki kuna cewa,
dan tsabar son k..".
Shiru tayi da bakinta sabida yadda taga Baba malam na watsa mata kallon ki shiga hankalinki kana ya nuna mata ƙofar fita.
Kamar kububuwa haka ta fice cikin zafin zuciya da takaici,
tana isa parlour'nta ta rinƙa kai mari ta kai gwarzo cikin tarin takaici tace.
"Shike nan ga irin ta nan, ni dama sam-sam ban taɓa yin farin ciki da wannan aiki na Zaleeha ba,
ta ƙare lokutanta cikin waɗannan kurame da makafi da guragu,
abinda nike tsoron shike bina,
in banda tsinennen gurgu mai shegen tsaurin ido inashi ina ɗiyata da ƴaƴan ministers ma basu isheta kalloba,
wayyo Allah ni Halima Allah ka dubeni da idon rahama wannan kurma kuma gurgu ya Allah tsole idonsa ya zama makaho inga ta inda zai sake kallarmin ƴa bare yace yana sonta."
zama tayi bisa sofa cikin zafin zuciya da tarin masifa, sai ta kuma miƙewa tamkar an tsikareta, cikin ɗaga sauti tace.
"Ina ai wlh muddin ina raye bazata taɓa saɓuwaba, ɗiyata ta zama matar gurgu kurma nakasasshe.
lallai shima Ahmad, wato ɗan ubanci zai nunawa Zaleeha dan ya gadi munafurcin uwarshi, a rinƙa musu kallon salihai kuma mugaye ne." haka dai tayi ta safa da marwa tana surfa bala'i.

A parlour kuwa tana fita sukaci gaba da abinda ya damesu,
inda Ahmad ya matso mahaifin nashi yana karantar dashi.


A can BQ kuwa suna shiga Zaleeha tayi mamakin ganin Ishaq so sai ta saki ranta a zatonta kawai ziyara ya kawo mata ba wanda Baba malam yace zai zo ɗin bane.

Cikin ɗan sakin fuska tace.
"Malam Ishaq kaine yau a gidanmu kai lale marhaba."
cikin jin daɗin yanayin muryarta yace.
"Yauwa ƙanwata yau kam dai gani na kawo miki ziyara."

"Ai kuwa ka kyauta naji daɗi sannunku da zuwa."
ta ƙarisa maganan tana mai kallon Ahmad.
"Yauwa Amaryarmu." Ahmad ya faɗa cikin sakin fuska,
da sauri ta ɗan waro idanunta wanda kuma sai lokacin ta kalli Saifuddeen dake gefen Ahmad,
kamar abin tsafi idanunsu suka sarƙafe cikin na juna.
wani irin azabebben faɗuwa taji gabanta yayi, wanda a take ta janye idanunta dan sam bata iya juran kallon cikin ƙwayan idanun wanna ɗan ruwan injita da faɗi.
Wani dogon tsaki taja tare da cilla mishi wani zazzafan harara, kana ta janye idanunta da sauri.
wanda ganin haka yasa fara'ar Ahmad daƙushewa.
Rashida ce ta kalli Ahmad cikin kamala tace.
"Ina wuni."
jiki a sanyaye yace.
"Lafiya lau ya gida."

"Alhamdulillahi"
Bilkisu tace dashi,
ita kuwa Zaleeha juyawa tayi ta fuskanci Ishaq rai a ɗan ɓace tace.
"Ya Ishaq ya mutane na?."
gyara zamanshi yayi tare da shafa cinyoyinshi irin yadda al'adar makafi take yace.
"Duk suna lfy sunce in gaidaki."
Cikin ɗan sakin fuska ta kuma cewa.
"Ina ko amsawa."
sai kuma ta ɗan daure ta ɗan kalli Ahmad a fizge tare da cewa.
"Ina wuni."
A gajarce yace. "Lafiya!."

Juyawa sukayi kan Bilkeesu jin tana cewa.

"To waye ne angon namu a cikinku?."
Dan so take taje taci gaba da kallonta.
Ahmad ne ya kalleta cikin cikar haiba ya nuna Saifuddeen da yake hukunta Zaleeha da ƙwayar idanunshi kana yace.
"Gashi nan wannan shine angon naku mai jiran gado in Allah ya yarda."
Kusan a tare su duka uku suka zuba mishi ido.
ita Zaleeha wani irin mutuwar zaune furucin Ahmad ya jaza mata,
hatta bakinta data buɗe dan cewa hahhhh Allah bai bata iko da damar rufeshi ba.

Bilkeesu da Rashida kuwa wani irin kallo sukewa Saifuddeen tare da cewa.
"Masha Allah. Kai angon nan da amaryarnan sune sirrin kyau."
sai kuma Rashida ta kalleshi cikin mutuntaka taka tace.
"Ina wuni ango mai jiran gado."
shiru bai amsaba sai ta kuma yin murmushi tare da cewa.
"Rowar murya ne angon zai mana?."
Ahmad ne ya d'an tab'ashi wanda sai yanzu suka lura cewa kan whellchair yake zaune.
kusan a tare suka kalleshi suka kalli Zaleeha sai kuma suka kalli juna cikin tarin mmki.
Bilkeesu ce tayi ƙarfin halin cewa.
"Ina wuni angon Zaleeha."
Kai ya jinjina mata alamar lfy,
tare da yi mata mgna cikin body language.
"Ya kuke."
tofa abin ya fara zarta zatonsu cikin son gano gaskiyar abin Bilkeesu tace.
"Wai meyasa baya Magana ne? Kodai zuwanmu tarene ya ɓata mishi rai?."
Ishaq ne ya ɗanyi Murmushi tare da cewa.
"No, ai kurmane bayaji kuma baya Magana."
Ya ƙarishe maganar cikin rashin damuwa dan shi a wurinshi sam nakasa ba kasawa bace.
Da ƙarfi suka haɗa baki wurin cewa.
"Toh kurma kuma gurgu a kan whelchair!."
sai kuma Bilkeesu ta tuntsure da wata iriyar dariya mai cike da jin daɗi kana ta bugi ƙafar Zaleeha tare da cewa.
"To Hajiar babu nakasashe sai rago. Lallai yau shirinki ya miki rana kin samo zankaɗeɗen saurayi kurma kuma gurgu."
ina ita ma Rashida tuni dariyarta da take dannewa ya subce mata.
Ahmad kuwa wani irin haɗe fuska yayi tamkar zaiyi ruwan jini.
Ishaq kuwa cikin kaushin murya yace.
"Ke Zaleeha waɗan nan ƙawayen naki wasu irin muta nene da basu san daraja da ƙimar ɗan adam ba?
me a jikinmu da zasuyi ta mana dariya."
cikin dariya Bilkisu tace.
"Kai tafi daga nan makahon banza makahon wofi.
In banda iskanci ina wannan gurgun ina zankaɗeɗiyar baby kamar Zaleeha."
Cikin zafin rai da tsawa Ishaq yace.
"Ke Zaleeha ki dakatar da wannan mahaukaciyar ƙawar taki da wanna hauk..".
Shiru yayi ba tare daya ƙarasa zancen nasa ba jin wani irin kuka mai cin rai da Zaleeha ta saki da ɗan ƙarfi cikin ɗaga murya tace.
"Ya isa! Ya isa!! Ya isa!!! Haka malam Ishaq ka farka daga wanna wawan baccin da kakeyi har ya kaika dayin mummunan mafarki.
Ƙawata ba mahaukaciya bace,
sai dai ko wannan dutsen da ka zo dashi shine mahaukaci."
Cikin tsananin fushi Ahmad ya yunƙura,
sai ya kuma koma ya zauna jin wani irin zazzafan riƙo da Saifuddeen ya yi mishi wanda ya zubawa su Zaleeha da ƙawayenta ido yana gane duk abinda suke faɗin.
Cikin zafin rai Ahmad yace. "Waye kike cewa dutsen?."
A zafafe ta kalleshi tace.
"Shi wannan halittan ruwan da kuka zomin dashi.
Me marabarshi da dutse, kurma kuma gurgu, kalleshi kamar al'jani dan kyau.
Ginennen taɓo kawai."
Sai ta kuma juyo ta kalli ishaq cikin kuka ta haɗe hannayenta duka biyu wuri ɗaya alamun neman al'farma tamkar yana ganinta tace.

"Dan Allah Malam Ishaq kada ka sake min wanna haukan, kadai san ina ganin ƙimarka da darajar ka, so please bana sonshi na tsaneshi!."
Sai kuma ta juyo ta kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Wallahi kurwata kurr ko kaine sarkin mayu to ni nan Zaleeha nafi ƙarfinka, nan gani nan bari, ƙwalelen kare da hantar kura, mcheeww banza kawai!! "
Hannu tasa ta jawo hannayensu Bilkisu daketa dariyar ƙeta tayi, fuuuuu suka fice daga cikin falon...

Ina Ahmad fa bazai iya magana ba, dan tsananin ɓacin rai da jin tsanar Zaleeha a ranshi.
Miƙewa yayi a fusace ya koma bayan Saifuddeen tare da tura whelchair ɗin cikin ƙunan rai yacewa ishaq.
"Mu tafi ishaq."
shima ishaq rai a ɓace ya miƙe yabi bayansu.

Mota suka shiga, kana Ahmad ya figi motar ya bar harabar gidan.

Suna isa gida ko Dai-dai ta parking baiyi ba ya fito tare da kawowa Saifuddeen whelchair ɗinshi ya zauna kana suka nufi cikin gida.
Kai tsaye parlour Ummi suka shiga,
suna isa tsakiyar parlour'n Ahmad yayi wani irin z...!



By
*GARKUWAR FULANI*
8/19/20, 2:32 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *NAKASA BA KASAWA BACE*

                          *Page 28*

   *NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Zamewa Ahmad  yayi ya zauna bisa kujerar dake bayanshi tare da sanya hannayensa duka biyu ya dafe kansa, dake bala'in sarawa, wani irin kukane ya ƙwace masa ransa cike yake da ƙuna haɗi da takaicin abun da Zaleeha tayi musu, yanda yakejin ƙuna acikin ransa harya zarce misali, wani  irin tafarfasa zuciyarsa keyi masa, harzuwa yanzu kalaman da su Zaleeha suka faɗa ga ɗan uwa kuma abokinsa basu daina yawo acikin kunnuwansa ba,  Ishaq ma zama yayi tare dayin shiru, tunda yake bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan ranan ba, sam shi bai ɗauki nakasarsu amatsayin kasawa ba, baitaɓa tunanin zasu fuskanci irin wannan tozarcin da cin fuska dalilin nakasarsu ba,  shin menene aibunsu? Menene aibun nakasarsu? Ashe Allah Bashine ke aiwatar da komai bisa abun daya so ba? haƙiƙa bawai don Allah Bayasonsu bane ya jarrabesu da nakasa, ƙaddara ce wacce yayi imani tanakan kowani bawa, babu wanda yafi ƙarfin nakasa kuma babu wanda ya isa ja da ikon Allah.
Shin ashe dama da gaskene Nakasassu na fuskantar iriren waɗan ƙalubalen yayin nemanaure da lafiyayyu, anya kuwa anayiwa nakassasu adalci? ace wai dole sai dai nakasasshe ya auri nakasasshiya ƴa uwarshi".
  Shi makoho ne bazai iyayin kukan cikin idanu ba, hakan yasa yakeyin na zuci wanda yafi na fili ciwo.
A hankali Ahmad ya ɗago jajayen idanunsa, cikin wani irin tururi da zuciyarsa keyi masa, ya dubi Saifuddeen,  hawayene suka sake gangarowa daga cikin idanunsa sakamakon wani irin tsananin tausayin Saifuddeen ɗin daya kamasa. Cikin muryarsa dake rawa  yace.
  "Sam ba matar aure bace Saifuddeen, wannan bata dace dakai ba, kabarta Saifuddeen, dan Allah ka ƙyaleta kasayawa zuri'armu mutumci, sannan ka sayawa ƴaƴanka tarbiya, Kabarta Saifuddeen ba irinta ya dace ka aura ba, sam batasan menene Ƙaddara ba, batasan me ake nufi da ƙudurar Allah Ba!". 

Idanu Saifuddeen ya lumshe tare da cije laɓɓansa, shikaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, shikaɗai yasan yanda ƙirjinsa ke duka,   ahankali ya ware idanunsa wanda suka ɗan sanja launi, hannayensa yasanya ya dafe dai-dai inda zuciyarsa take,  cikin nuna alama yace.
"Ina sonta Ahmad, Ina matuƙar sonta, sonta tamkar numfashi yake agareni, bazan iya rabuwa da ita ba, kasan so Ahmad!".
Hannayensa ya haɗe waje guda alaman ban haƙuri agaresu.

Tasowa Ahmad yayi tare da ƙarasowa har gaban keken Saifuddeen, cikin yanayi me ɗauke da tsananin tausayawa Ahmad ya rungume Saifuddeen, tare da sakin sabon kuka, tunda yake bai taɓajin zafi da ciwon Nakasar da ta samu Saifuddeen ɗinba sai yau.
Ummi datun shigowarsu ke tsaye abakin kitchine tana jinsu batare dasun kula ba, wani irin karyewa zuciyarta tayi, yayinda tsananin rauni ya bayyana akan fuskarta, idanunta ne suka cika tab da ƙwalla, cikin sanyin jiki ta tako ta ƙaraso cikin falon,   jin motsinta yasanya Ahmad sakin Saifuddeen ya juyo tare da kallonta, ganin yanda hawaye ke gudana akan idanun Ahmad ɗin yasanya hawayen dake cikin idanunta samun daman gangarowa, murya araunane tace.
"Kada ka ɓoyemin komai Ahmad, taƙisa ko? taƙisa saboda Nakasar dake tattare dashi ko?".
Wani murmushi mai ciwo Ummi tayi tare da duban Ahmad cikin rawar murya tace.
"Sanar dani gaskiya Ahmad kada ka ɓoyemin!".
Kuka Ahmad ya fashe dashi tare da zama akan kujera, ayanda yakejin zafi da tsanar Zaleeha acikin zuciyarsa bayajin zai iya rufe cin mutumcin da tayi musu, cikin muryar kuka yasanar da Ummi duk abun daya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login